Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 45-46

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*45&46*

 

………tab’ashin da hamma yusuf yayi yana fad’in yaya dai? yasaka shi dawowa tunaninsa”shi kansa daddy dake zaune kallon su kawai yakeyi… shariff kaga dai daddyn Amaan yace”gaskiya wucewa zasuyi yau da k’arfe 12:pm zasu d’auki hanya zuwa magrib sun sauka”naso subari sai goben Amma sun k’iya”cewar Ammi”narai narai da Ido Amaan tayi tana shagwab’e fuska tace”dan Allah daddy Abari se goben mana”ah ah salma gara dai mu wuce gida”karka damu shariff kamana uzuri”babu Abinda zamuce maka sai Allah yasaka maka da Alkhairi “cewar daddy yana murmushi”shidai shariff yayi shiru yakasa mgn”gefen zuciyarsa na tambayarsa daga yau kaida Amaan saidai Ayi ziyartar juna??kije ki had’a kayanki salma kinga har 10 am ta kusa”cewar mommy tana kallonta”Adaidai nan kuma madeenah da sadeeq suka shigo cikin parlourn”wanda kowa yayi mamakin ganinsu A tare”illah shariff ne kawai beyi mamaki ba sbd yasan halin sadeeq idan yana muradin abu baya b’oyewa”daddy zanje nadawo kafin ku gama shirin tafiyar”cewar shariff yana nufar k’ofa yafita be jira Amsar suba”saidai yana fita Amaan taji kamar ta bishi”gabanta na wani irin fad’uwa ta juya ta nufi d’akin baccin Ammi”tana shiga tasami wayarta na ringing”da mamaki ta nufi wayar sbd tasan babu wanda zai kirata sai family nata tunda ba kowa yasan ta canza new sim card ba…..dam ! k’irjinta yabuga sakamakon ganin sunan *hamma nah* datayi saman screen d’in wayar”bata b’ata lokaciba ta d’auka da sallama”Amaan kina jina?”yafad’a cikin b’oye damuwarsa”kukan shagwab’a tasaka masa…kinga ya Isa haka yi shiru ki fad’amun menene?”basu daddy bane sukace yau zamu tafi”yanzun kina Ina?”Ina d’akin Ammi mana”okay jeki bud’e window yanzun zan iso muyi mgn “to hamma”ta fad’a tana yanke wayar”ta nufi wajen window ta janye labulayen dake a jiki “d’an lek’owa tayi ta hangosa yana nufo wajen…komai na hamma shariff me Ajine da nutsuwa”dubi ko tafiyarsa Abin kalloce “matsalarsa guda MISKILANCI NE kawai “saidai banga damuwar zai rabu dani a fuskarsaba??duk take maganar itada zuciyarta”Adaidai lokacin da shariff ya iso gaban window d’in yazuro kansa yana tsurama mata kyawawan idanuwansa masu haske… b’ata fuska tayi ta juya masa baya”kallonta kawai yakeyi can yatab’e baki yana fad’in me hakan ke nufi Amaan?kona koma ne?nidai bance ba”to menene kuma kika juyamun baya,kinsan kuma na tsani hakan ko??tanata turo baki da shagwab’e fuska ta juyo saidai tak’i yadda ta had’a Ido dashi”wankan zakije kiyi?”uhmm”fad’amun mekikeso naje na siyo miki yanzun kafin ki gama shiryawa??girgiza kanta tayi Alamar babu”kinsan Allah mgn zakimun kamar yadda na bud’e baki na miki”jiyafa har k’orafin na dinga mgn kikamun….shikenan hamma ! ni bana buk’atar komai,hidimar da kakemun babu dare bbu rana wlh tamun basai ka kamun komai ba”idan nace Ina buk’atar wani abu nayi k’arya”to mema zan buk’ata?”shikenan ni bakya buk’atata ko?”yafad’a cikin wata iriyar muryar dabata sanshi da itaba”tsintar kanta tayi dajin dad’in maganar saidai ta kasa kallonsa”kinji?”nifa hamma koda yaushe Ina buk’atarka kusa dani”Amma dole na hak’ura tunda tafiya zamuyi”kaine dai nake ganin baka damuba da tafiyata”kike gani ai kika ce ko?”shiru tayi”meyasa bakyason kallo nah?”kallon nasa tayi”saidai da sauri ta kawar dakai sbd bata iya jure had’a Ido dashi”hamma! Uhmm Amaan d’ina…sosai taji sanyi Azuciyarta”bara naje nayi wankan ko?”to nima bara naje nadawo”to Allah ya tsare”ya Amsa da Ameen yanata kallonta ya wuce”ta matso ta lek’osa….sai Akayi sa’a yajuyo sai suka had’a Ido hannunta guda ta d’aga masa “sai yasakar mata wani tsadaddan murmushi yayi gaba Abinsa”Aguje Amaan ta fad’a saman bed tana dariya ita kad’ai”madeenah ta shigo cikin d’akin tana fad’in lafiya kike dariya ke d’aya sis?”nida hamma nane”ke ki fad’amun gaskiya wai soyayya kukeyi dashine?”naga kundace sosai da juna wlh ,ga wata iriyar kulawa kina bashi….uhmm! inama zancen naki yazama gaskiya deenah?”tafad’a tana tashi zaune ta kalleta tace”some times idan muna bama juna kulawa bama masoyaba har matsayin ma’aurata za’a iya kallon mu”bana son yaya Nasir musammun dayazo gida shida mahaifiyar sa da mgn marar dad’i game dani”kuma mommy ta gayamun daddy yace”babushi bbu ni”sedai deenah raina na bani Ina yaudarar kaina game da hamma”kamar yaya?”hamma nah ba k’aramin mutum bane”ga kud’i,ga nasaba ,ga d’aukaka,ga girma,ga kyau da aji “inani Ina shi? uhmm salma kenan”to bari kiji babu ruwan SO da wannan”Abinda nakeso kawai dake shine duk wuya duk rintsi karki nuna kina sonsa saidai idan shine ya furta miki”dan tunda na gansa na lura mugun MISKILI NE! kuma yanada izzah had’e da shan k’amshi “kinga nidai Alkhairi yakawoni KD tunda gashi mun jone da wannan yaya sadeeq d’in”wai da gaske kikeyi?”Eh mana”Amaan na k’ok’arin mgn wayarta tayi ringing “taduba k’irjinta na bugawa taga shariff ne”murya Asanyaye tayi masa sallama bayan tayi picking”kinada BVN number?”shine Abinda yafad’a Anutse “Eh hamma ina dashi”okay karantomun”bbu musu ta karanto masa “bayan yagama ji ya yanke wayar”ita kuma ta kalli madeenah tana nuna mata ward rope d’in kayanta da troley d’in da shariff yasiya mata tace”maza had’amun komai kika gani a wannan sashen duk nawane”dato madeenah ta Amsa , yayinda Amaan ta wuce bath room….cikin mintinah 45 Amaan tagama shirya kanta da komai nata”lokacin karfe 11:12 am”gabanta sai fad’uwa yakeyi”suna zaune itada madeenah Abdallah yashigo da wasu ledoji ya mik’a mata yana fad’in gashi inji Ammi”yaya kuma yana parlourn sa yace”kizo yanzun”dato ta Amsa tana karb’an ledojin”bayan Abdallah yafita ta duba”kayan shafane da kwalliya had’e da turaruka”sunata yaba kayan itada madeenah wacce Aranta take mamakin yadda kowa son Amaan yakeyi Agidan”mayafin bak’ar doguwar rigar dake jikinta ta yafa ta d’auki wayarta ta fita”babu kowa a parlourn sai Abdallah”Ina Ammi?”tana can tare da mommynki”okay ta fad’a tana wucewa saman gabanta na wani irin fad’uwa”jiki Asanyaye ta murd’a handle d’in k’ofar ta shigo”yana tsaye gaban window “da Alama safa da marwa yakeyi cikin parlourn”yana jin sallamarta yasaki Ajiyar zuciya Ab’oye yana basarwa kamar yana duba wani abu ne Ajikin window d’in “hamma kadawo?”uhmm kin gama had’a kayan naki?”uhmm “ta fad’a da k’yar hawaye na cika idonta”gaba d’aya shima wani iri yakeji”zomu zauna”shine Abinda yafad’a iya lab’b’ansa yana zama gefen kujera “Amaan tazo ta zauna bata ce komai ba”fad’amun wane buri kike dashi Arayuwarki?ni bani:dashi”bazai yuyuba Amaan” kowane d’an Adam yanada bururruka wasu suna cikawa,wasu su mutu kafin su samu cikar burin”k’in mgn tayi”wane mataki karatunki yake?”kafa sani hamma saida na fad’a Abaya”shikenan”Akwai driver dazai jaku keda yarinyar nan da securities su rakaku sbd tsaran lafiyarku da kuma suga gidan ku sbd idan zanzo na ganki”naso ace nine zanyi rakkiyar so inada Ayyuka A office”yanzun zamuje ki bani kayanki nakai miki mota ko?”sannan nima inaso ki bani wani abu dazan dinga tunawa dake kullum ko?”shiru tayi tana mamakin yau yayi surutun dabata tab’a zaton zaiyiba”saita d’an kallesa ya harareta”itama ramawa tayi…waye kike harara?”kai mana”yad’an matso dab da ita murya can k’asa yace”fad’amun meye zaki bani?”kaine dai zaka fad’amun hamma”banida Abinda zance maka sai Allah yasaka maka da Alkhairiinsa Ina godiya sosai hamma nah….sai kuma ta fashe masa kuka….kinga Amaan ya Isa haka Ai zanzo bayan ko sati biyu ne naganki”k’ilanma da Ammi zanzo ko?pls Amaan ki dena wannan kukan in kuma kinaso ki b’atamun rai shikenan”yafad’a yana d’aukar tissue dake saman center table yakoma matsowa kusa da ita har tana iya jin hucin numfashinsa yafara goge mata hawayenta ta lumshe Ido”oya bud’e idon kimun murmushi”babu musu ta bud’e idon….tsab suka sark’e da nashi”da sauri tasaka tafikan hannayenta ta b’oye fuskarta tana dariya”shima dariyar yayi suka mik’e tsaye yana duba Time 11:35 am”muje kuyi sallama da Ammi ko?to hamma kamana pics mana”Abinda zance kenan na d’auka ko bakyaso”batace komai ba tana dai tsaye”kina jina?”uhmm”bance ki canza wani sim card ba, sannan ban yarda kisaka number d’in wani k’ato ba Awayarki”sannan yaron can ban Amince bayan gaisuwa ba kimasa wata mgn”tunda last year kike a karatunki zan yiwa daddy mgn ki cigaba da karatu”kanta Ak’asa tana dai Amsawa dato kawai”yazaro wayarsa iphone 14 irinta hannunta ya matso bayanta yana d’an murmushi yafara d’aukar su vedio tana dariya had’e da masa gwalo”daga bisani yamusu pics kala biyu sannan yace”su wuce k’asan”sai yima parlourn kallon ban kwana Amaan keyi”kafin ta zaro xoban Azurfa guda d’aya tace”hamma gashi”yana murmushi ya Amsa yasaka A k’aramin d’an yatsarsa”sai Akayi sa’a yamasa cif cif”kinga yayi mun cif cif thank you! baza muje gidan baba ladi ba?”babu lokaci Amma wata ran idan kin zoma Ammi hutu sai kije ko?”nok’e kafad’arta tayi tana sakin kukan shagwab’a “ya girgiza kansa yana fad’in muje Amma t k’ofar baya zamu fita”batayi mgn ba suka fito ta k’ofar bayan Ajere suka nufi cikin babban parlourn gidan”gaba d’aya duk suna cikin parlourn da Alama su ake jira”madeenah na rik’e da troley d’in Amaan “gaba d’aya idanuwanta cikowa da k’wallah sukayi da sauri taje ta rungume Ammi tana kuka….dubeta da wani shirme dan Allah”sai kace wacce bazaki koma ganin taba?”cewar mommy duk suna tashi tsaye”shidai shariff na tsaye yayi k’asa da kansa yana jin shashshekar kukan Amaan da yadda Ammi ke rarrashinta tana mata mgn k’asa k’asa bama’ajin me take cewa” shariff muje ka taka mana ko”Hjy mu zamu wuce gida”muna matuk’ar godiya da halaccinku”ubangiji yabiyaku da mafificin Alkhairiinsa”cewar daddy daya mik’e tsaye yana gyara malun malun d’insa”Ammi na murmushi tace”babu komai Alh”Allah yatsare hanya ya saukeku lafiya”Hjy sai munyi waya ko?”ta fad’a tana kallon mommy”Eh insha Allah Ammi”ke kuma saiki cikata mu tafi”Amaan ta cika Ammi tana b’ata fuska ta kalli gefen da shariff yake taga wayam”sai sannan ta lura suna mgn shida daddy yana d’an murmushi”Nasir na binsu da mugun kallo “wata uwar harara ta ban kowa Nasir tana tab’e baki”wanda sarai yana lura da ita”sadeeq kuwa na gefen madeenah suna mgn Ammi data rakosu tana kallon su ta girgiza kanta kawai”har bakin get Ammi ta rakaso”sharif ya bud’e boot yasaka troley d’in Amaan gefen kayan shopping d’in daya mata”yak’i bata ne da hannunsa sbd karta masa godiya kotace bazata Amsaba”sarai tana lura da ledojin daya bud’e boot d’in”bayan ya rufe driver yazo yashiga”madeenah ma ta shiga” sannan Amaan ta kallesa ta shiga”sosai nasir yayi mamakin wai mota daban za’a kai Amaan harda wasu security”daidai gefen inda take zaune shariff ya tsaya ya kalleta Ido cikin Ido”hamma! uhmm Allah yatsare ki kula da kanki”karki koma yin kuka kina jina?”yafad’a cikin cool voice yana jan karan hancinta “tasaki murmushi yarufe k’ofar shima yana sakin d’an tak’aitaccen murmushi”madeenah dai na gefe tana kallon su k’amshin turarensa na kaima hancinta ziyara”Ahaka driver yaja motar yana bin bayan motar daddy”shariff ya sauke Ajiyar zuciya yana bin motar da kallo har suka b’acewa ganinsa…..basufi mintina 20 da fara tafiya ba”text message na first bank yashigo cikin wayarta”da mamaki ta duba saiga sabon acc number ta gani”Atake ranta yabata shariff ne yasaka Aka bud’e mata sabon Acc”bata gama wannan tunanin ba Alert d’in 2million ya shigo cikin wayarta”shiru kawai tayi tana kallon wayar…..daga nan bacci ya kwasheta sai wajen la’asar suka tsaya wani restorant sukaci Abinci sukayi sallar Azahar data la’asar”Amma banda Amaan dake fashin sallah….sai Anata kiraye kirayen sallar magrib suka iso garin Adamawa”basu iso gidaba saida isha’i “driver d’in shariff da body quards nasa suka musu sallama sbd zasu tafi masauki daga nan washe gari da Asuba su koma gida”daddy yaso su sauka Anan Amma sukace bbu damuwa sunada masauki…..sune da kansu suka bud’e get d’in gidan sbd babu kowa cikin gidan”zabba’u da family nata suna can Asibiti An bata gado”ciwo yayi k’amari dole Aka kwantar da ita”Nasir be shiga cikin gidan ba daga waje ya musu sallama yayi tafiyarsa”Amaan da madeenah suka kwashe kayan Amaan suka wuce cikin gidan”bayan sun shigar da komi itama madeenah bata zaunah ba Abbansu tabi suka wuce gida”daddy kuwa part nasa yanufa….mommy tabi kayan dake Ajiye tsakkiyar parlourn da kallo tace” wa’annan ledojin fa na meye salma?wlh mommy hamma shariff ne yamun shopping”dayake hankali ya miki yawa shine kika Amsa ko?”kina ganin irin hidimar da mutanan sukeyi damu ko?”ah ah wlh Ammi nima sai yanzun driver d’insa yabani yace injishi”yanzun haka yabud’e mun sabon acc yasaka mun million 2 ciki”million biyufa kikace? Amaan na kok’arin mgn wayarta tayi ringing”da sauri ta duba k’irjinta na bugawa”saita mik’e tsaye ta wuce bed room sbd ganin sharif ne ke kiranta”itadai mommy da kallo tabita tana mamakin wasu Abubuwan “saita d’auki baby Nokia d’inta ta lalubo number d’in Ammi tayi dealing sbd ta sanar mata sun sauka lfy…..cikin sanyin murya Amaan ta masa sallama”ya gyara zamansa yana shafa kansa yace”yanaji muryarki wani iri ko iskan mota kika shak’a ne?”uhmm uhmm”Ina wuni?”lafiya qlau da fatan kun sauka lafiya?”Alhmdllh “d’an shiru na second 5 yaratsa”can yace”menene kikayi shiru bayan nasan idan kina tare dani kinamun surutu?”yanzun dan Allah hamma Abinda kayi ka kyauta?”so kakeyi ka k’arar da dukiyarka akaina ko?”dama wannan shine k’orafin?”Eh mana”mommy sai fad’a takemun….kinga ya Isa haka “yanzun kinyi wanka?”ah ah”sai yaushe?”yanzun zanyi nad’an kwanta”okay kina Ina yanzun?”Ina d’akin mommy a bed room “idan kin gama shirin kwanciya ki kirani”dato ta Amsa shi kuma ya yanke wayar “tashi tsaye Amaan tayi ta bud’e ward rope ta haska kayanta da flash light d’in wayarta tana kallo ta sauke Ajiyar zuciya ta zaro farin towel ta d’aura ta shiga wanka”duk da sanyi Akeyi hakan be hanata yiba sbd Akwai heater a toilet d’in “tana wankan tana tunanin Shariff harta idar ta fito”shiryawa tayi cikin riga da wondo na bacci”kafin ta fito parlourn sbd jin muryar yayun nata”sadeeq, yusuf,khalifa”sallama ta musu ta zauna suka gaisa suna murnan ganinta”yayi da sadeeq keta tsokanarta “mommy dake zaune ta kalleta tace”kije ki kwashe indomie na nan dana sauke na d’iba”dato ta Amsa ta fita daga cikin parlourn “bata jimaba ta dawo ta zauna tana cin Abincin tana tuna gidan Ammi”Ahaka daddy ya shigo da jallabiya Ajikinsa da farin glass ya zauna”duk mazan suka masa sannu”yayinda mommy be isheta kalloba sbd har yanzun fushi takeyi dashi”gyaran murya yayi yace”yanzun na gama waya da shamsiya”tace mun Aiki za’a yiwa zabba’u a k’wak’walwa sbd buguwar datayi Akai ya shafi cikin k’wak’walwarta”Ana buk’ata kud’i nera dubu d’ari shidda da hamsin”ta kumayi mun complaine d’in zabba’u ta koma kamar k’aramar yarinya”sannan likita yace”idan ba’ayi gaggawar yin Aikin ba zata iya samun tab’in hankali….yusuf yace “subahanallahi !kai meye kace musu daddy??…..✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button