Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 25

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*25*

Kamar yadda kika sani sunana Amina Abubakar Bakura na kasance y’ar sarkin Borno…” dakata malama, kina nufin ke din y’ar sarki ce? Ikon Allah shine kika dawo kike…” Ki bari na karasa Baki labarin maman Nana kafin ki Yanke hukunci ” gyada Kai mmn nana tayi cike da mamaki inna ta cigaba” mu 8 wajen mahaifinmu nice ta 5 Ina da yayu Maza 2 mata 2 sannan Ina da kanne 3 mata, mu biyu ne wajen mahaifiyata dani da yayata Bilkisu tun Ina y’ar shekara 8 Allah yayiwa maman mu rasuwa daga nan na koma wajen kakarmu yakumbo duk da cewa cikin gidan masarautar tamu take , Yakumbo tana matukar kaunata da duk abunda nake so. Na taso cikin gata da soyayya daga bangaren yakumbo da yayata Bilkisu haka nan mahaifinmu Yana matukar kaunata , nayi makarantar primary da secondary duk cikin Borno daga haka na shiga jami’ar Maiduguri inda na samu gurbin karatu a bangaren Islamic studies, Ina aji 3 a jami’a Allah ya hadani da Sule ta sanadin abokinsa Wani driver dayake kaini makaranta Kuma yake daukana idan na tashi komawa, Sule asalin bafulatanin jahar Adamawa ne Yana aikin direbanci Yana daukan Fasinja daga yola zuwa Borno , wasu lokutan tare suke zuwa da abokin nasa Hashimu daukana a haka har muka saba har yakai idan Hashimu baya Jin dadi ko Yana da Wani uzuri zai turo Sule yaje gida ya daukeni ya ajiyeni makaranta, ana haka har na shiga ajin karshe a jami’a a wannan lokacin mun fara shakuwa da Sule har yakan fadamin matsalolinsa wasu lokutan nakan taimaka masa da Yan kudade saboda jinyar mahaifinsu dake kwance a gida, kwatsam wataran Hashimu yazo da batun cewa zaiyi tafiya zuwa kamaru wajen Yan uwansa a bisa wannan dalilin na roki Sule ya zama permanent driver dina, duk da cewa Ina ajin karshe a jami’a Amma bana kula samari saboda tun tasowata bani da masoyin da ya wuce ya Yusuf Wanda ya kasance dan wan mahaifinmu, Babansu ne yakamata ya gaji karagar mulki saboda shine babba Amma ya nuna baya ra’ayi Hakan yasa aka nada mahaifinmu a matsayin Mai Borno. Ya Yusuf Yana min wata irin soyayya da bazan iya fassarawa ba Wanda duk duniya zan iya cewa shine mutumin da yafi kowa kaunata , tun Ina y’ar karama yake kula dani har zuwa girmana ya tafi masters nashi ne akan idan ya dawo zaa saka mana Rana sai Kuma kaddara ta sauya. Lokacin da na shiga final semester dina ya Yusuf ya shaida min ya kusa dawowa saboda Yana hada PhD program dinsa saura watanni ya kammala, na Maida hankali kan karatuna saboda Muna shirin kamallawa, ranar da na fara rubuta jarabawar karshe a ranar tsautsayi yasa Sule da ya ajiyeni a makaranta yace bari ya dan zagaya da motar Yana fita aka taresa aka masa duka aka kwace mota a hannunsa , na fito ban samesa ba na kira wayarsa Bata shiga daga haka na nemi waje na zauna na share 1hour Bai dawo ba kawai na Yanke Neman abin Hawa, Ina sauka a kofar gida dai dai nan fadawa suna tare da babban yayanmu Ya Mohammed suna Bina da kallo har na karasa cikin gida na wuce bangaren yakumbo dama can na taso can nake zama, ban Dade da shigowa ba sai ga Kiran ya Mohammed a waya yake tambayata meyasa na shiga abin Hawa na haya meya faru da motocin gidan nan na shaida masa driver baije ba Kuma bansamesa a waya ba. Washegari aka hadani da sabon driver da sabuwar mota na fito jarabawa sai ga Kiran Hashimu a waya muka gaisa nan yake shaida min an kama Sulei ana azabtar dashi bisa zargin Sace motata , cike da mamaki nake tambayarsa a Ina yace anmikasa hannun hukuma nan hankalina ya tashi nasan aikin ya Mohammed ne. Na koma gida na shaidawa yakumbo na roketa ta saka Baki don nasan ya Mohammed tace min Babu ruwanta na fara kuka dakyar ta bani izinin zuwa inda aka kulle Sule, aka fito dashi cikin mawuyacin Hali gaba d’aya jikinsa jini don tsabar azaba Ina ganinsa sai da na zubar da hawaye nan ya zayyana min komai nace meyasa baka sanar dani ba da Hakan duk bai faru ba, nan na nemi a bani bail suka Hana sukace an hanasu Bada bail haka na hakura na koma gida na zayyanawa yakumbo komai ta tausaya masa. da yamma ta aika Kiran ya Mohammed yazo ta rokesa akan a sake Sule ba laifinsa bane Yaya yace karya yake sun hada Baki da abokansa ne suka siyar da motar zasu raba kudi, Babu yadda yakumbo batayi ba Amma yaki ya saurareta, a takaice dai har na kammala jarabawa Sule na hannun hukuma yasha azaba iri iri sunki sakinsa daga baya aka hanani zuwa ganinsa na rasa yadda zanyi kullum cikin fargaba da tashin hankali nake na rasa mafita kawai na Yanke hukuncin shaidawa yakumbo cewa Sule zan aura, Hakan kuwa akayi na fada mata cewa mundade Muna soyayya tayi mamaki sosai haka ta shaidawa Yaya yace karya ne ta dinga kuka na daina cin abinci Ganin haka yasa zancen ya Isa gun Mai Martaba da izininsa aka saki Sule, yaje gida ya sameni yayi godiya gaba d’aya ya rame ya lalace nayi ta basa hakuri haka ya shirya ya koma gida jinya bayan na basa Yan kudaden da zaiyi jinyar dasu.
Wannan abunda ya faru ya haddasa gaba tsakanina da Yaya har ya daina min magana sannan yace min na Jira sakamakon tozartashi da nayi, Ban kawo komai a raina ba naci gaba da rayuwa na gama makaranta bana zuwa ko’ina zaman gidan ya gundureni ne yasa na fara Shirin zuwa Abuja wajen yayata Bilkis, bayan sati na shirya nazo Abuja wajen yayata sati na biyu Ina nan ashe yaya Mohammed Yana can Yana shirya min kitimurmura wajen mahaifinmu sai waya akamin akace na gaggauta komawa gida, bayan na koma gida akace lallai lallai na sanarwa Sule ya turo magabatansa na shiga tsananin tashin hankali a wancan lokacin na rasa waye zan tunkara, na shaidawa yakumbo bana son wanna auren ya Yusuf nake Jira tace Mai Martaba da Kansa ya Bada wannan umarni , kuka nake sosai na kira anty Balkis na shaida mata nan take itama hankalinta ya tashi nan ta kira Wani yayan maman mu Wanda yake da kusanci da Mai Martaba, amma duk yadda Ake daukan zancen ya wuce nan nayi kukan nayi rokon amma Basu saurareni ba na rasa me Yaya Mohammed ya fada musu, yayata tazo da kanta ta roki Baba Amma yace Sam wannan auren sai anyi haka ta fara lallabani tana bani hakuri , na kasa sanarwa ya Yusuf don bansan ya zai dauki zancen ba haka na cigaba da rayuwa cike da kunci. A takaice dai haka suka nemi layin Sule aka kirasa yazo har fada nan ya Mohammed ya shaida masa ya turo iyayensa suzo su nema masa auren Amina , ba karamin mamaki yayi ba da Jin wannan batu ya nemi ganawa dani Amma Sam naki fitowa haka ya hakura ya koma yayi ta Kiran Wayana naki dauka daga karshe na kashe wayar gaba d’aya, bayan mako biyu Yan uwansa sukazo ba don suna so ba dama auren gida suke son masa haka sukazo take ya Mohammed ya Bada sadaki aka daura aurena da Sule… sai ynxu ta dakata saboda kukan da yazo mata tana sharewa hawaye mmn nana na Bata hakuri, ta sauke numfashi sannan ta cigaba ” bayan daurin aure da kwana biyu Ina zaune da dare Baba ya aika a kirani Ina zuwa kallo d’aya ya min ya dauke Kai yace” Mamata irin son da nake Miki shine zaki sakamin ta wannan hanyar?” Shiru nayi hawaye na bin kumatu na ” kije ki shirya tunda wannan shine zabinki donhaka kije Amma Ina son ki cire a ranki cewa kina da Uba daga yau, ki dauka cewa Sule shine Uba agareki shine danginki da komai naki” na fshe da kuka Ina son yin magana ya hanani yace na tashi na fita, daga wannan dare har yau ban Kara Sanya kowa nawa a Ido ba sai ya Yusuf da na Gani jiya saboda dokar Baba ne ya Hana kowa zuwa inda nake Kuma ya gargadeni da zuwa inda suke har yayata Bilkis yace mata idan ta nemeni Bai yafe mana ba daga ni har ita, ya Yusuf ya dawo ya samu bana gida ya shiga tashin hankali sosai daga wannan lokacin na koma garinsu Sule da zama har zuwa lokacin da na haifi Hajjo har Kuma dawowarmu Abuja ban sake waiwayar gida ba, wannan shine takaitaccen tarihin rayuwata nida baban hajjo auren kaddara ne Amma Babu digon sonsa cikin zuciyata kawai biyayya nake na sunnar ma’aiki (s.a.w) ” tana share hawaye tana kallon Hajjo wacce har ynxu idonta a kulle yake , maman Nana ta tausay mata tace ” tabbas Kinga kaddarar rayuwa malama Allah ya Baki ladan wannan hakurin da kikayi Allah yasa Hakan ya zama riba a rayuwarki, toh Amma meyasa bakije gun dangin mamanku ba nasan zasu karbeki ” murmushi Mai ciwo tayi ” cewa fa yayi Bai yafemin naje gun Wani nawa ba na zauna da Sule tunda na zabi Hakan ” girgiza kai mmn nana tayi tace” lallai kin Hadu da jarabawa Allah yasa mu dace” Ameen nagode” nidai ki daure ki cika butinku da ya ysuf don Allah kar kice bazaki auresa ba malama”

___________

Sai faman juyi Ayman yake ya kasa bacci gaba d’aya Yana lissafin rayuwarsa ya kusa kammala karatunsa yasan dole zaa bijiro masa da maganar aure Kuma wacce yake so ba yanzu zatayi aure ba, idan har zancen Aman ya tabbata shin Yaya zaiyi kenan? Bai shirya hada soyayyar ta da wata mace ba a rayuwarsa yafi son ya aureta suyi nesa da gida saboda kar a bijiro masa da zancen sarauta yafi son ya rayu like a common man baya son takura da tsanani , Ganin tunanin bazai ficesa ba yasa ya tashi ya shiga toilet yayi alwala ya fito ya kama nafila har gabannin asuba kafin na dan jingina jikin gado har bacci yayi gaba dashi.

Back to top button