Aci Yau Aci Gobe Hausa NovelHausa Novels

Aci Yau Aci Gobe 19-20

Sponsored Links

19 & 20
Sosai Aliyu yayi nadamar gayawa Abba wannan maganar ganin yadda ransa ya ɓace kuma yashiga gidan azuciye komima zai iya faruwa shiyasa yaja gefe ya tsaya yana gaisawa dasu malam Tukur da sauran manyan unguwa suna gaya masa matsa lolin unguwar

Amma gaba ɗaya rabin hankalinsa na can gurin tunanin me Abba zaiyiwa Fateema Allah yasa karya daketa saboda yaga alamun kamar ta kusa fara period kuma hakan zai janyo mata matsala sosai

Doctor mikake tunani ne Tukur ya faɗa da sauri Aliyu yace ba komi sonake na koma gida amma inaso na ƙara yiwa Abban Fateema sallama

Aa Aliyu nifa bangane ba kodai da Fateema za’a yi ne murmushi yayi masa batare dayace masa komi bah tsagora yayi masa zuwa ƙofar gidan inda Aliyu da Tukur suka ja suka tsaya suna rafka sallama

Amma shiru sai suka shiga cikin gidan direct

Tunda Tanimu yashigo gidan yacewa Lantana ina Fateema tace masa tana ɗakinsu ya wuce ɗakin batare dayace mata ƙala ba

Sai ihun Bintalo data ringaji, ta taso a ruɗe tana ɗukan ƙofar amma yaƙi buɗe mata

Koda su Tukur suka shigo gidan Lantana na ihu tana Wayooo Allah Dan Allah ku taimakeni zai kasheta Dan Allah Tanimu ka buɗe ƙofar nan

Karka kashe marainiyar Allah Dan Allah kayi haƙuri kururuwa kawai Lantana keyi

Da sauri Aliyu yaƙaraso idonsa a rufe shida Tukur suma suka shiga ɗukan ƙofar amma yaƙi buɗewa saima ƙarar Fateema dasukeji

Tana wayoo Allah nah Abba kayimin rai karka kasheni Dan Allah kayi haƙuri bazan ƙaraba natuba ka yafemin amma gaba ɗaya zuciya ta rufe Tanimu bayaji baya gani sai dukanta yake kamar yana faɗa da sa’arsa

Wani wawan duka Aliyu ya kaiwa ƙofar da guiwar hannunsa aekuwa nan take ƙofa ta ɓalle, Lantana tayi tsalle ta fada ɗakin tare dasa Bintalo a bayanta tana

Malam mikake shirin yi ne sokake kayi kisan kai muna kallon ka,kowane laifi tayi maka wannan dukan ya Isa haka, Lantana ki ɓacemun dagani idan ba haka ba harke zan iya haɗawa, Ni takeso ta ɓatawa suna nitakeso ta zubarwa da mutunci a idon duniya harta isa yaushe yaushe ne aka haifeta

Yayi kukan kura ya cafko Lantana ya wurgata gefe saida kanta ya daki gefen gado Lantana ya wurgar amma harda Bintalo saida ta faɗi gasa yasa ƙafa ya shuiri Bintalo a ciki

Tasaki ihuuuuu wayooooo nashiga uku Abba cikina zan mutun,Aliyu baisan lokacin da ya shigo ɗakinba yana ɗagota

Malam Tukur yaja hannun Tanimu yana fitar dashi daga ɗakin

A hankali Lantana taja jiki taje gunda Bintalo ke kwance tana girgiza ta a hankali tace Dan Allah ka taimaka mana Aliyu suman zaune yayi ganin Fateema ta zuma gashi tana dafe da mararta ta dunƙule gurin ɗaya

Wani ƙarfi yaji ya zo masa ya dauketa cakk yayi waje da ita, motarsa ya buɗe yasata gidan baya,ya mayar da motar ya rufe yaja motar a tsiyace yana gudu kamar zai tashi sama

City hospital ya kaita kuma anan take aeki sai aka yimata dinki a forehead dinta sai hannun daya kare kuma hannun ɗama sosai Tanimu yaji mata ciwo a jiki

Aliyu yayi shiru yana tunanin Wannan duk laifin sane daya gayawa Abba dayayi shiru da hakan bazata faru, wata zuciyar kuma tace masa ae aekin Alkhairi ne yayi ya ceto rayuwar ta daga faɗawa halaka

Drip aka samata shiyasa yafito daga wajen ɗakin ya zauna yana jiran ta farfado daga sumanda tayi, yacire wayarsa ya kira Raihana

Saida ta gaishe dashi kafin ya tambaye ta Usman na gida tace masa A’a yace Sadeeq fah tace Ehh yana nan

To kice nace ya kawoki City hospital kuma ki dauko set ɗaya cikin kayanki da always (pat) idan kinada idan kuma bakida ita kice nace yatsaya kisiya, Okay to Hamma

Cike da tanani Raihana ta tashi ta shirya tana fadin Hamma Aliyu garin taimakon mutane sai yaje ya dauki aljana baisani yanzu haka nasan wata yaga zata haihu ya taimaka mata, Dan karamin tsaki taja mtwww

Kafin tafita zuwa ɗakinsu Sadeeq koda taje yana zaune shima zaman jiranta yake saboda already Hamma Aliyu ya kirasa ya gaya masa

Suna tafiya suna fira yana tambayar ta tasan waye ba lafiya tace a’a, shiyasani ne yace mata shima baisani bah harsuka ƙarasa asibitin

Yana sauketa ya jiuya ya koma gida, saida taje office dinsa taga baya nan kafin ta kirasa yana ɗagawa yayi mata misalin inda zata samesa still suna waya

Har ɗakinda Fateema take taje ta same tana cika ta ganta kwance sai numfashi take saukewa a hankali a hankali, Raihana taji gabanta ya faɗi dummm subhanallah ta faɗa tana ƙarasawa gunta

Aliyu na zaune daga gefe da sauri tace Hamma accident tayi ne kansa ya girgiza mata to miya faru da ita haka waya karya mata hannu

Hmmmm Raihana Abbanta ne ya daketa Abba kuma metayi masa Hamma laifi tayi masane, kinfi kowa sanin metayi Raihana ya faɗa cikin tsawa ya tashi yabar ɗakin yana huci

Cike da magana da alhini Raihana take kallon Aliyu tana girgiza kanta dama idan yana cikin fushi baifiya son yawan magana bah 10:00PM daidai Fateema ta farka tana Wayooo Allah na Abba kayimun rai karka kasheni

Da sauri Raihana ta ƙaraso gunta tana rike mata hannu kafin ta fara magana a hankali tana sannu Fateema bazaki mutuba tana magana tana girgiza mata kai

Saida ta haɗiye wasu yawu kafin ta fara Magana Raihana miyasa kika gayawa Hamma maganar da nagaya miki kinga ya gayawa Abba shiyasa Abba yayimin wannan dukan

Abba baya sona kinga kinga duk jikina ciwo yake mun, Abba da bakinsa yace saiya kasheni Abba bayasona

Shhhhhh kiyi shiru Abba yanason ki kuma bazai taɓa ɗena sonki bah,ke yarsace kuma ki godewa Allah kinadashi a rayuwa wasu nacan basuda uwa basuda uba

Kinga nenan ke saidai kawai kice Alhamdulillah tunda mahaifiyarki ce kawai ta rasu kinada mahaifi rumgume ta Fateema tayi tana sakin wani kuka mai ciwo

Duk wadannan abubuwan dake faru a gaban idon Aliyu kai ya girgiza yana buɗe ƙofar yana shigowa yace Raihana tashi Sadeeq zai mayar dake gida

Kai tashiga girgirza masa tana cewa Hamma ni anan zan kwana, Dan Allah kabarni anan Dan…..bata ƙarasa ba ya daka mata wata tsawa haɗe da cewa karki bari na ƙara maimaita maki cewa ki tashi Raihana aka yiwa tsawar amma har Fateema saida ta tsorata

Jiki na rawa ta tashi tafita tana share hawayen ta

A hankali ya ƙaraso gun Fateema fuska a hade yana cewa akwai abunda keyi miki ciwo ne kai ta girgiza masa,cup ya janyo ya haɗa mata tea yace tasha, ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa ta karɓi cup din tafara sha

Saida ta shanye duka ta mika masa Cup ɗin,ya ƙara tambayar ta babu abunda keyi mata ciwo tace masa Ehhh

Hannuta ya kalla wanda tun ɗazu yake a kan mararta kuma ya tabbata tana jin ciwo a gun kawai kunyarsa takeji shiyasa bazata faɗaba

Ɗagowa yayi ya ƙara kwallon ƙwayar idonta yace kin tabbata babu abunda keyi maki ciwo,cikin ƙaguwa dakuma gajiya da tambayarta dayake tace babu komi kamar zatayi kuka

Unexpected taji yakai hannunsa akan mararta daidai saman hannunta ya ɗora nasa a kai, hade dacewa me hannunki keyi anan idan bakya jin ciwo, bakomi ta fada tana janye hannunta a gun

Okay ya faɗa ya danna hannunsa da ƙarfi wani zillo tayi hade dakai hannunta saman nasa tace Innalillahi wa’ina ilaihiraji’un tana cije lips dinta na ƙasa

Kince babu abunda keyi maki ciwo, karya kenan kike yimin kai ta girgiza masa tana ƙoƙarin ture hannunsa akan mararta saboda bazata iya jurewa ba

Hmmm bakomi zanyi maki ba kuma karma kiyi kalar wannan tunanin akaina, yana magana yana tayar da ita zaune

Hannunsa ya gogi Breast dinta garin tayar da ita zaune aekuwa tace wayoo Allah Hamma zafi yana sane yayi haka Saboda yanaso yayi Noticing wani abu akan period pain dinta……….

*Maman Ekram ce*✍

*ACIYAUACIGOBE*

Back to top button