Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 29

Sponsored Links

Yau kwana uku dayin sauka misalin karfe 10 na safe mama tabawa fanan kudi taje mata kasuwa tasiyo kayan cafene mikewa suhaima tayi da niyyar rakata mama tace ” wa bafa zaku tafi tare ba nasanku yanzun sekuje kuyi zamanku nikuma ina bukatar aikana da wuri koma kizauna” zama suhaima tayi tanaji tana gani fanan ta tafi. Tafiya takeyi abinta cikin natsuwa tana sanye da dogon riga na material da gyalensa tayi rolling jitayi kamar ana kallonta dagowa tayi taga mutanen anguwa duk sun tsayar da abinda sukeyi suna kallonta sake waigawa baya inda tabari tayi nan ma still idon jamaa nakanta wani irin faduwa gabanta yayi lokaci daya, abin daure mata kai yayi tana tambayar kanta meye damuwarsu dani dasukemin irin wannan kallon kode wani abune ajikina bansaniba can kuma tabasar ta cigaba da tafiyanta tare mai napep tayi yatsaya ganin irin kallon dayake mata ne abin yabata tsoro karfin hali tayi tafada mishi inda ze kaita , sallamarshi tayi tashiga cikin kasuwa nan da nan al umman cikin kasuwar suka fara binta da kallo tsarguwa tayi tafara tafiya sadaf_sadaf kamar wata wacce batada gaskiya wasu mata guda biyu taji suna fadin “itace wallahi kekam dan Allah dubeta a ido kamar wata ta Allah amma fuska fari zuciya baki karuwa kawai” haka suka dinga kus_kus duk da batasan akanme suke magana ba amma ganin kallonta dasukeyi jikinta yabata tabbas da ita sukeyi wani matashi tagani yana kallon jarida seya kalleta seya kalli jaridar wajanshi taje ta fincike jaridar da karfi , Abu nafarko abinda idonta yagane mata shine hotonta itada Mr azaad suna rungume da juna akasan jaridar anyi rubutu kamar haka ” WANNAN DAKUKE GANI SHINE SHAHARARREN DAN KASUWAN NAN WATO AZAAD MUHAMMAD MAINASARA THE BILLIONAIRE, ASHE SHIDIN YAKASANCE MAZINACI NE ME LALATA YARA MATA YAMAIDASU DADIRONSHI SABODA YANADA MAKUDAN KUDADE, ITAKUMA YARINYAR NAN ITACE WACCE TAYI SAUKAN AL QUR’ANI MEGIRMA WACCE TACI KYAUTUTUKA DA DAMA SABODA KOKARI DA HAZAKANTA ASHE ITADIN DADIRON MR AZAAD CE SUNDADE SUNA TARE SAU UKU YANA MATA CIKI ANA ZUBARWA AL UMMAN MUSULMAN DUNIYA SUNA ALLAH WADAI DA WANNAN MUMUNA HALIN NASU”. wani irin dishishi tafara gani nan take tayarda jaridar tare da Jakarta da wayarta hawayene suka fara wanke mata fuska tunani tafarayi meye tayiwa wayan nan mutanen dasuka mata irin wannan sharrin durkusawa kasa tayi tafashe da wani irin marayan kuka kamar ranta zefita babu wanda yakulata awajan suka cigaba da aikin gabansu suna binta da mugayen kalamai da aibatawa gabaki daya tafita acikin hayyacinta since gyalen kanta tayi tasa hannu ta hargitsa gashin kanta kuka takeyi me tsuma zuciya gaba daya taji ta tsani kanta jitakeyi kamar tahau tsakiyar titi babar motar yabi takanta ya murkusheta ta mutu seda tayi kuka ma ishi mikewa tayi tana tafiya tana layi kamar wacce tayi shaye_shaye gashin nan yarufe mata fuska yabazu kamar sabuwar kamun hauka ko gabanta bata gani.

_____zaune yake afalon ummi yana duba wasu files gasu fawwaz dukansu suna zaune zeenat kuma takwanta tadaura kanta akan cinyar ummi Abba ne yashigo dasauri ganinshi a irin wannan yanayin daya shigone yasa suka tashi suna tambayarsa meyafaru kasa magana yayi kawai yadauki remote yadanna yashiga BBC news aikuwa suma yanzu suka fara bada labarin ganin hoton azaad rungume da fanan ne yasa suka shiga tashin hankali jin irin mugayen kalaman dasuke fada akansu harda wai yasha zubar mata da ciki kuka ummi tasa itada zeenat sun shiga cikin matsanancin tashin hankali babu abinda suke furtawa banda allahumma ajirni fi musibhati da innalillahi wainna ilaijiraji unn, azaad dake zaune fuskan nan yayi jajir idonshi yakoma kamar gaushi inbanda tsuma da karkarwa babu abinda ilahirin jikinshi yakeyi afusace yamike aikuwa dasauri Abba da fawwaz suka rikeshi dansun san inya fita zaayi bacecciya ne dan inranshi yabaci ba abinda baya aikatawa wani irin mugun zuciya ne dashi shisa ahar kullum basa kaunar suga abinda ze bata mishi rai dan asamu ashawo kanshima babban wahala ne fuske hannunshi yayi daga rikon dasuka mishi kara rikoshi sukayi da karfi harda areef azaad din bana wasa bane ahakama ji sukeyi yafi karfinsu ummi inbanda kuka ba abinda sukeyi anbata musu suna yaro da sunan family ga fanan baiwar Allah yarinyar dabataji ba bata gani ba sun bata mata suna innalillahi wainna ilaijiraji unnn wannan wani irin mugunta ne. Shigowa yaseer yayi shida doctor ammar dukkansu suna cikin tashin hankali dasauri Ammar yahada allura yazo zema azaad dagowa yayi yakalleshi da idonshi dasuka rine tsabar bacin rai cikin wata irin murya ta bosawa dabantaba tunanin yanadashi ba yace ” don’t you dare inject me ” ja baya ammar yayi yana shakkan tunkararshi yaseer ne yaje yarikoshi ” please dude calm down kabari abi komai asannu yanzu haka nasa ana investigation akan lamarin duk wanda yakeda sa hannu akai seyayi dana sani” mugun kallo yakebin yaseer dashi kafin yace” are you telling me to calm down!? After they ruin my reputation and you’re telling me to calm down impossible ” yafada da karfi cikin dabara doctor ammar yazagaya ta baya yaseta injection din yamishi a hannu ganin alluran ba abinda yamishine yakara musu damuwa yau inde azaad beyi bacci ba basusan yazasuyi dashi ba , lumshewa idonshi yafara slowly_slowly rikoshi yaseer yayi yakwantar dashi akan sofa nan take bacci yatafi dashi , duk shuru sukayi sunma rasa abinda zasuce duk sun shiga cikin alhini, daga waya Abba yayi yakira dpo yabashi umarni akan kar asake sako abinda yadanganci haka a gidan kowani TV sannan amishi binciken suwaye suka aikata hakan yakatse kiran, Abba ne yace ” yanzu kowani irin hali gidansu fatima suke ciki se Allah! Wannnan aikin yan adawan azaad ne gashi sun batama yarinyar da babu ruwan suna wannan wani irin bala I ne ” haka Abba yadinga fada.

Su baba duk sun dawo gida sunga abinda yafaru a gidan TV gaba daya basa cikin nutsuwarsu mama kam kukan zuci takeyi suhaima ce ma ta iyayin kuka itada Amira ganin suna kukane yasa auta kuka itama baba yana zaune yakasa cewa uffan duk sunyi cirko_cirko abun tausayi babu abinda suke tunani kamar ya fanan zataji intaji wannan mummunar labarin duk suna zaune suna jiran dawowarta daga kasuwa cikin sanyin murya ya al ameen yace ” kota dawo kar mu nuna mata wani abu saboda karta fahimmci akwai damuwa ” dukkansu sunyarda da shawaranshi domin kuwa su sunfi kowa sanin halin fanan bazata taba aikata abinda zezubar musu da mutunci ba yarinyar da tunda tazo duniya inbanda yan uwanta maza babu wani namijin data taba kulawa Allah isanta, tun karfe 4 suna tajiran dawuwarta amma shuru 5 tayi nanma shuru hankalinsu be kara tashi ba se dasukaji anan Kiran sallah mangrib a masallaci ringing wayar baba yayi yaduba yaga sunan alhaji mainasara ne dagawa yayi suka gaisa suna jajanta abinda yafaru tambayar baba Ina fanan Abba yayi yace tun 3 mamarta ta aiketa amma haryanzu shuru bata dawo ba yanzu haka fita zamuyi mudubota, sallati Abba yake ta nanatawa aranshi sannan yacewa baba bari yasa sojoji da polisawa su duba kaff cikin garin gombe anemota ahaka sukayi sallama fita su baba sukayi kowa yashiga motarshi nemanta sukeyi kamar zasuyi hauka amma ko me kama da ita basu gani ba, acikin daren haka suka shiga cikin kasuwar da babu kowa da torchlight dede wajan yan takalma sukagano jakarta da wayanta aciki dauka ya usman yayi yanunawa ya al ameen cigaba sukayi da nemanta amma shuru, haka suma jami’ar tsaron suketa nemanta har karfe 12 nadare babu fanan babu labarinta zuciyarsu cikeda rauni suka koma gida .
Atsakar gida suka tadda su mama se safa da marwa takeyi harda hajiyarsu amira da Amira ganin su baba sundawo batare da fanan bane yasa zuciyoyinsu karyewa jirine yafara diban mama kamar zata fadi ya usman yayi saurin tarota jikinshi yazaunar da ita , tashin hankali iya tashin hankali yaukam sunganshi yau yakasance bakar rana agaresu har karfe 1 nadare basu runtsaba suna filin gida suna zaune cikeda jimami, haka zalika su ummi suma suna at the same condition babban damuwarsu rashin ganin fanan dabaayi ba azaad har a time din alluran bata sakeshi ba , cike da damuwa ummi tace ” yakamata muje gidansu yarinyar nan ” ajiyar zuciya Abba yayi yace” inasane Aysha yanzu kinga dare yayi sosai mubari gobe da safe ko ” ahaka Suma suke zaune afalo . Sa kafarta kawai takeyi aduk inda tabi domin bata cikin hayyacinta shigowa cikin gidan tayi gaba dayanta tafirgice kamar ba fanan ba , jin motsine yasasu dagowa ganin itace yasa suka mike suna Kiran sunanta atare ko kallonsu batayi ba magana suke mata amma gaba daya bata jinsu falo tashiga direct tawuce dakinsu tana shiga tasaka key tako Ina rufe windows din tayi tasauke labule, dan batasan magana da kowa kuma batasan ganin kowa can karshen gefen gado taje tazauna akasa tahade kai da guiwa kamar wata me bacci , hamdala sukeyi dukda sunga irin yanayin data dawo wannan yatabbatar musu da taji abinda yafaru bubbuga kofar dakin sukeyi dantabude musu kofar amma ina abu kamar wasa har karfe biyar 5 idonsu biyu babu Wanda yaruntsa har time din bata bude kofar ba tunda takifa kanta akan guiwanta bata sake dagowa ba. , Mama kam kamar zatayi hauka haka takeji tarasa inda zatasa kanta daga karshe kuka tasaka musu tana rokonsu dasu fasa kofar kar yarta tamutu kiraye_kirayen sallah asubane yasata dagowa idon nan sunyi luhu_luhu sunyi ja fuskanta yakumbura Sosai, mikewa taje tayi alwala tayi sallah, tunda ta idar da sallah bata tashi akan daddumar ba tana zaune gaba daya jitayi tatsani duniyar ma dakuma kanta, dawowa sukayi daga masallaci baba yabasu umarni dasu fasa kofar dakin nata kawai aikuwa haka akayi suka fara kokarin fasawa jin zasu fasa kofar ne yasa takalli jikin key din da bangon dakin takomar da kanta kan guiwanta har karfe 10 na safe fanan bata bude kofar ba gashi kofa yaki fasuwa babu yanda suka iya haka suka zauna shuru ko breakfast basu samu nutsuwar yiba ahaka su Abba da ummi se yaseer da doctor ammar sukazo gidan suka samesu suma babu yanda basuyi ba amma fanan taki bude kofar….

 

Ina godiya masuyin comment dakumin adduah nagode sosai Ina nan inata ganin wayanda sukemin comment, innaga comment dinki nada yawa zansaki a dayan group din.

 

Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & Written by (MRS ISHAM )

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

Alhamdulillah munzo karshen book 1 se mun hadu a book 2 inda rai da lafiya zamu tafi hutu kamar 1week ko 2weeks,in andawone zaa daura da book 2 inme duka yakaimu da Rai da lfy.

 

A gaskiya Ina matukar alfahari daku sosai da sosai da yanda kuke bani ruwan comment Lodi lodi dakuma adduah nasara arayuwa Ina me matukar godiya sosai.

Musamman…!

 

Maman shurem
Sherteen gayu
Eysher raj
Maman junior
Maman yazeed
Umamah Abbas
Snacks craving
Pinky darling
Hauwa’u illiyasu
Oumu Maryam
jiddah
Nana farida
Maarufa Ahmad
Mum basma
Maman widad
Mami
Maman junior
Anty rukkaya
Fatima Hassan umar
Diamond sarah
Maman faruq
Yar mamanta
Ummu amal
Ummu suhaima
Mhizz deejerh
Zainab magarya
Anam
Anty ummi mulki
Maryam said
Khareema
Man munawwara
Etc Dade sauran ku

Yesterday you guys gave me unforgettable hot comments I really appreciate allah yabar kauna inasonku sosai

Wannan last page din sadaukarwa ne gareku.

 

 

Free book

 

꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁

&_______________________________________&

Last page

Back to top button