Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 61-62

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*61&62*

 

……..washe gari misalin k’arfe 6:48 am shariff ya bud’e manyan kyawawan idanuwansa da suka yi d’an ja sbd bacci”ya kalli Amaan dake kwance saman faffadan k’irjinsa tanata baccinta hankali kwance”ta turo lips nata gaba”da Alama sanyi takeji sosai ,sbd ta mak’ale masa sosai Ajiki, ga devut d’in da suka rufa dashi ya janye kusan rabi daga jikinsu….gashin kanta ya gyara mata fuskarsa d’auke da k’ayataccen murmushi yaja dogon hancinta cikin sanyayyar muryarsa yace “salfad Atashi haka nan muyi sallah saiki koma wani baccin ko?”hannunta tasaka ta ture masa hannu tana cigaba da baccinta”yayi y’ar dariya ya matso da fuskarsa yana sauke mata numfashinsa Atsakkiyar fuskarta”Amma ko gezau Amaan bata yiba”ganin batada Alamar tashi daga baccin yasaka ya sumbaci lips nata yana d’an cizan na k’asan “hakan yasa ta bud’e Ido da sauri”Atake idanuwanta suka shige cikin na shariff “wani iri taji sbd kaifin idanuwansa sun rinjayi nata kaifin idon”janye fuskarta tayi da sauri tana k’ok’arin barin jikinsa….madam Abin babu mgn kuma?”kin haye saman bawan Allah kinata bacci me dad’i, kinja mun makara sallar Asuba”yafad’a cikin tsokana yana rik’eta”cizo tasakar masa a gefen yatsu biyu”ya shafi gashin kanta yana fad’in irin wannan good morning d’in zan samu salfad?”nidai hamma ka cikani muyi sallah “idan nak’i fa?”batace komai ta juyo A bazata tafara yimasa chakulkuli tana kauda kanta tana k’yalk’yala dariya”sbd bata son ganinsa bbu riga”kuma yanzun guntun boxer ne kawai yayi saura Ajikin sa”shariff kuwa babu shiri yacikata yana dariya har fararen kyawawan jerarrun hak’oransa suka bayyanah”Amaan tayi wuf ta sauka daga saman bed d’in shima ya duro zai bita”da gudu ta shige bath room ta banko k’ofar ta murza key”ya kalli k’ofar yana murmushi yafita daga cikin d’akin…Agaggauce ta kama ruwa had’e dayin brush da Alwallah ta fito”cire kayan baccin tayi tasaka doguwar riga jallabiya da hijab Ajikinta”tana shimfid’a prayer mate shariff yashigo da farar gogaggiyar jallabiya Ajikinsa”ta kallesa ta turo baki tana fad’in nidai hamma ka koma d’akinka bana gayya ko?”nidai ko salfad?”kanta ta gyad’a masa tana masa gwalo”be kulataba ya matso suka gabatar da sallar”bayan sun shafa Addua ta matso ta Aza kanta saman kafad’arsa Ahankali tace”salfad Ina kwana?”lafiya qlau my salfad”bazavkiyi Azkhar d’in ba?”kayi mana zai wadatar hamma ,ni zanje nad’an gyara kasan ne”d’an murmushi yasaki yana shafa kanta yace”inaga fa tun kafin mu tashi masu Aiki sun gyara down stairs”nan saman kawai zaki dinga gyarawa ko girki kuku ne ze dingayi mana”A week end kawai zaki dinga mun girki Ina tayaki”kai salfad duk Akan me?”sbd bana so ki wahala”kinga gidan yanada girma sosai”part d’in masu Aiki yana daga can waje ba nan ciki yake ba”shima kukun ta k’ofar baya zai dinga bi ya shiga kitchen yafita tacan nama bashi key”sbd bana so yabiyo tanan yana kallemun ke”idan yagama Aikinsa kin shiga ki d’akko warmers d’in Abincin”na sanar musu da babbar murya duk shegiyar data b’ata miki rai bakin Aikinta”su 3 ne,guda share share da goge goge,guda kuma wanki da guga da kulawa da bak’i”guda kuma wanke wanke” ke kuma aikinki kulawa da big baby d’inki ko yakika ce?”ya fad’a yana d’age gira”Amaan ta murd’e masa kunne tana fad’in kaiko salfad?”bazaka dena wannan zafin zuciyar naka ba da saurin fushi?”tu nifa na dena salfad”kawai dai na nuna musu muhinmancinki ne Agurinah”Anjima kad’an idan mun sauka k’asan zasuzo su gabatar da kansu wajenki”kukun ma yanzun haka ya shigo yana can yafara Aikinsa”Allah sarki hammanah ! kana bani farin ciki da kulawa ,ga gata kana nunamun da fifitani”Ina sonka sosai dan Allah karka canza hamma pls”ta fad’a cikin raunin murya “kinga ya Isa karkiyi kuka sbd dan na miki d’an wannan Abin”fad’in irin matsayin dakike dashi aguna b’ata bakine Amaan”Allah yabarmun tare sweet heart”yana murmushi yace”Ameen my beuatiful lady”Anjima zan goyaki” da gaske kakeyi salfad?”Eh mana” to shikenan tashi muje kata yani nayi bacci”ta fad’a tana jan hannunsa”Azkhar zamuyi saimu koma baccin….kukan shagwab’a tasaka wai ita bata gama baccinba da rana tayi Azkhar d’in”shidai shariff sauraronta yakeyi yana kuma Aikin kallonta”ta mik’e tsaye ta cire hijab d’in ta ninke ta mayar cikin ward rope ta haye saman bed d’in ta gyara kwanciyarta….harma ta fara bacci taji shariff samanta yana fad’in kin gama tsokanar tawa d’azun?”bud’e Ido tayi tasaki k’aramin kuka tana turashi”shi kuma saiya Aza kansa Atsakkiyar k’irjinta”ta lumshe Ido tana shafa gashin kansa tace”salfad bazaka barni nayi bacci ba?”Eh mana “meyasa?”sbd Ina Ango mana”nidai ka d’agani pls wlh nauyine dakai”kuma kasaka riga mana”bbu wata rigar dazan saka zakijama na cire har boxer d’in babu ruwana”shiru tayi sbd tasan zai iya….hannunsa taji yadora saman k’irjinta hakan yasa ta sauke wani irin nishi babu shiri”pls hamma baccifa kace zamuyi?”uhmmmm! shine Abinda yafad’a yana shafa sassan jikinta ya had’e bakinsu waje guda yana bata zazzafan kiss…..babu yadda Amaan taso haka ta biye masa suna romancing d’in juna”saidai ganin shariff yak’i sarara mata yasaka ta kama yimasa kuka”ga rigarta yacire mata yasameta yanata tumurmusa”gaba d’aya na shanunta da lips nata zunga sukeyi da rad’ad’i”ganin tanata masa raki yasaka ya k’yaleta yana jijjigata kamar jinjira har bacci yayi Awon gaba da ita da busassun hawaye saman fuskarta”sharif kuwa kasa baccin yayi sbd gaba d’aya babban fage yakesan zuwa”daurewa kawai yayi ya nufi side nasa yayi wanka ya shirya cikin sabuwar farar shadda”yayi kyau Abin sai wanda yagani”fuskarsa nata k’yallin Angunci”main parlour ya zauna yana kiran bak’insa yana musu ban gajiya”kafin yakira Ammi”yasanar mata kar Akawo Abin break fast kuku yahad’a musu nasu”dato ta Amsa tana k’ara sanar masa wajen k’arfe 10 dangin Amaan zasuzo suyi mata sallama ,ya sanarwa drivers d’in dazasu kaisu gida su zama cikin shiri…yana gama wayar ya mik’e tsaye ya haye upstairs”Amaan na tsaye gaban mirror tana d’aura d’an kwalin doguwar rigar lace d’in jikinta”da yayi bala’in fidda shape d’in jikinta”shariff na turo k’ofar yayi tozali da bayanta”lumshe Ido yayi ya jingina Ajikin k’ofar yana maida numfashi zuciyarsa nasanar masa da bak’in sunzo sun tafi kawai ya Angwance Abinsa….salfad babu sallama ko?”I’m sorry na bari ki juyo naga kwalliyar sai kizo kiyi hugging d’ina ko?”nidai bazan iyaba bayan d’azun kayitamun….sai kuma tayi shiru”yad’age gira yana fad’in Allah idan baki zoba wancan me gaba d’ayar zan miki yanzun….tun kafin ya rufe baki Amaan ta iso Aguje ta fad’a jikinsa ta rungumesa”salfad dama bakyason abun?”shagwab’e fuska tayi tak’i mgn “yad’ago kanta ya tsura ma fuskarta Ido”tayi masa kyau sosai saidai kawai taji ya cafki lips nata yana sha”gaba d’aya saida ya shanye lips stick d’in data shafa”Amma yak’i cikata sai son k’wacewa takeyi Amma sai k’ara shige mata yakeyi ya matseta Ajikinsa”dataga yak’i cikata saita fara masa chakulkuli”da sauri yacikata tana k’ok’arin guduwa yakoma ruk’ota yabita jikin bango ya rik’e hannayen nata duka guda biyun “sai kawar da fuska takeyi Amma be fasa bintaba saida yayi nassara koma kissing nata….saida yagaji dan kansa sannan ya k’yaleta idanuwansa sunyi jajir…ta sunkuyar da kanta lips nata nata rad’ad’i”kinga nayi maganin bakin shagwab’ar ko?”shiru tayi tak’i mgn saima k’ok’arin barin wajen tayi ta zauna saman bed”yabita da kallo yana nufo inda take ya zauna”menene salfad?”kanta ak’asa tace”babu komai”shiru yad’an yi sai kuma ya kalleta yace”bakya son Ina tab’aki ko?”ta girgiza kanta”to menene duk kinyi wani iri?”babu komai “be koma mgn yakama hannunta suka sakko k’asan”dining area suka nufa sbd ganin Anjera musu komai da zasu buk’ata wajen break fast “Amaan ta mik’e tsaye tafara duba komai kafin tafara serving d’insu”shidai yanata kallonta”Aransa yace”da kinsan yadda nakeji salfad da bazakiyi fushiba sbd kawai nayi kissing naki….. bissimillah! kin gama fushin ne?”kallonsa tayi ta maka masa harara”yayi murmushi yana fad’in thanks matsoraciya”idanma zaki saba garama ki saba yarinya sbd Ina son romance da sex sosai….kasa mgn Amaan tayi gabanta na fad’uwa Aranta tace”dama hamma ya wuce yadda nake tunani”irin wannan rashin ta Ido haka….zan hukunta zuciyarki tunda take mgn ta”taji Amon muryarsa”k’in mgn tayi ta d’auki cup d’in tea”ya rik’e da sauri”kallonsa tayi yad’age mata gira guda”saman cinyata zaki dawo muyi break fast d’in “kinsan kuma ba’a yiwa muji gaddama”batace komai ba tadawo saman cinyoyinsa ta zauna Ad’arare “hannayensa yasaka ya zagaye cikinta dasu yana Aza kansa saman kafad’arta ta rintse Ido sbd saukar sajensa gefen wuyanta”guduna kikeyi ko salfad sbd kinga jiya da d’azun ban miki komai ba sbd Ina jin tausayin ki ko?”bafa haka bane”ta fad’a cikin shagwab’a”to fad’amun menene?”sai tak’i yin mgn”sai sinsinarta yakeyi yana manna mata kiss”saida yagaji dan kansa kafin su fara break fast d’in”suna gab da kammalawa k’ofar glass ta shigowa cikin parlourn tayi k’ara Alamar Akwai bak’o ko bak’i dake san shigowa”Agogon dake d’aure Adamtsan hannunsa yaduba yaga 10:11am”ransa yabashi dangin Amaan ne sukazo yimata sallama”hakan yasa ya Ajiye fork d’in hannunsa ya shafi fuskarta Anutse yace”salfad k’inyi bak’i fa”zanje na bud’e musu nad’an fita”kai hamma baka d’auki hutu ba?”kuma ni Abarni ni kad’ai kuma”na d’auki hutu mana sbd na kasance tare da sahibata “kawai Akwai Abinda zanyine idan naje office”sannan kuma zanje mu gaisa da Ammi”zanje pls”murmushi yasaki yana d’aukar ta suka mik’e tsaye”ta shige masa tanata zuba shagwab’a”murya Akasale yace”bazan wuce Awa gudaba zan dawo tare dasu mus’ab suci dubulan”to shikenan kuma Allah ni karka dinga fara’a”kumtunta yaja ya sumbaci lips nata yana fad’in salfad kin kasa yadda bana kula ko wace mace ko?…. k’arar k’ofar yasaka yacikata yakama hannunta suka nufi k’ofar”wasu malatsai ya danna k’ofar ta bud’e”da sauri yaja baya yana sunkuyar dakai k’asa batare daya cika hannun Amaan ba”duk matan suka shigo”shamsiya da Fatima na gefe suna k’are ma parlourn kallo”shamsiya Aranta tace”lallai salma tagama samun duniya” Amutunce shariff ya gaidasu kafin yaja hannun Amaan suka fito wajen barandar dake bakin shiga parlournya kalleta ya marairaice murya wajen cewa “salfad kissing d’ina fa zakiyi Asaman lips d’ina saina tafi ko?”….✍️

Ayi hak’uri da kad’an banida chargy

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button