Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 41-42

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*41&42*

 

……… Amaan kuwa tunda yafara maganar ta sunkuyyar dakai k’asa tana jin kamar k’asa ta tsage ta shige ciki sbd kunyar da kalamansa suka bata” Azuciyarta kuma gulmarsa takeyi wai wannan hamman bashida kunya”saidai kuma k’asan ranta farin ciki ne da mamakin kamarta zata rik’e wannan wayar me tsananin tsadar gaske?”tama fahimci irin wayarsa ce yasiya mata…idan kin gama tunanin gulman tawa kije kisaka phone d’in naki chargy”yafad’a cikin cool voice d’insa yana cigaba da cin abincin sa”saidai haka nan yaji kunyarta ta burgesa….ganin ta mik’e tsaye tak’i yadda ta kallesaba yasaka shi cewa”akwai sim card zuwa dare zai hau”bance kisaka contact d’in saurayinki Aciki ba”yafad’a cikin hura hanci yana yatsina fuska”Amaan dai batayi mgn ba “tana kuma mamakin meyasa yatsani yaya nasir wai??”tana wannan tunanin ta wuce daga wajen batare data koma tankashiba”shi kuma yatab’e baki yana fad’in nafiki miskilanci yarinya mu zuba mu gani”daga haka yaci gaba dacin Abincin sa”koda ya idar bebi takan taba ya wuce shashensa yayi wankansa yafice ta k’ofar baya”Amaan kuwa cikin farin ciki ta nunama Ammi wayar sannan tasakata chargy”ta zauna tana duba chacoolates d’in”can kuma ta Ajiye ta d’auki ledar pad d’in ta wuce bath room….wasa wasa tun Amaan na zaman jiran dawowar shariff harta hak’ura ta wuce d’aki wajen k’arfe 9: 30 pm ta d’auki wayar ta bud’e taga sim d’in ya hau”tana duba balance nata taga tanada credit kusan na 10k”shiru tayi tana d’an tunani”can tace”lallai hamma wato shi kud’i ba matsalarsa bace”kodai fushi yakeyi danine?”tafad’a tana mik’ewa tsaye k’irjinta na tsananta bugawa sbd Amon jarumar muryansa dataji”da sauri ta saka hijab ta bud’e k’ofar ta fito…..wlh da gaske nakeyi Abokinah tazo tamun rantsuwar idan har zaka Aureta zata dena komai…wani irin tsinkewa zuciyar Amaan keyi, taji kamar zata faso k’irjinta ta fito”da sauri tayi baya”adaidai lokacin dataji shariff na fad’in look mus’ab! kasan babu Abinda na tsana sama da wata tace tana sona ko?”to pls muma Ajiye wannan zancen sbd na tsaneta bana k’aunarta”Allah yasa ta mutu sbd ni”Abinda take Aikatawa kar Allah yasa ta dena”yafad’a cikin zafin rai yana huci…pls calm down shariff meyayi zafi haka? nifa turoni tayi bayan ta had’ani da girman Allah da monzonsa”shiyasama har na maka mgn”ni kaina nasan fareedah bata dace dakai”pls mus’ab dan Allah kaje mun had’u da safe office “cewar shariff yana mik’ewa tsaye”da sauri Amaan ta koma ciki sbd sautin takun takalminsa sawu ciki dataji”shi kuma tama gaban d’akin ya wuce bebi takan jin Amaan d’in tayi bacci ba ko batayiba”sbd har itama haushinta yaji yanaji…. Amaan kuwa wata wawuyar Ajiyar zuciya tasaki me k’arfi tana rintse ido ta fad’a saman bed”k’asan zuciyarta tana jin sanyi sbd kalaman da shariff yafad’a Akan yarinyar…..tana Ahaka Aka turo k’ofar d’akin”saida k’irjinta yabuga tama d’auka ko shine sai taga Ammi ce”baki kwan taba Amaan?”eh Ammi zan kira mommy ne”dato ta Amsa ta fita”d’aukar wayar Ammi tayi tana dubawa”can ta gano number d’in shariff ta d’auka”bayan ta Ajiye ma Ammi waya ta saka number d’in mommy ta kira….sai wajen k’arfe goma da wasu mintinah ta gama wayar”bayan mommy ta sanar mata gobe insha Allah zasuzo ta turo cikakken ful Address d’in gidan Ammi”yadda dasun iso garin zasu zo nan….koda ta kwanta tunanin shariff ne yamata sallama”wanda zuciyarta ke ganin bala’in kirkinsa da mutuncinsa”ta fahimci yana k’ok’arin kyautata mata fiye da tunanin me tunani”idan Abaya yamata haka yanzun Aita dawo hayyacinta ko?”saima kyautatawar taci gaba”saidai ranta yabata yanada saurin fushi”zatayi k’ok’arin ganin yarage wannan yawan saurin fushin kafin tabar gidan….da wannan tunanin bacci me dad’i yayi Awon gaba da ita….. shariff kuwa sai bayan yayi wanka da shirin bacci zuciyarsa ta bujuro masa da tunanin Amaan”sai jan tsaki yakeyi yana juyi saman bed”ko coffee d’in dayake sha yau be nemaba, sbd mus’ab yabashi haushi daya kamasa zancen fareedah “yarinyar daya san y’ar lesbian ce meye zaiyi da ita ko mata sun k’are a duniya??…….k’arfe 10:38 pm ya sakko k’asan yana sanye da jallabiya fara gogaggiya yanata zabga k’amshi fuskarsa ad’aure tamau”hakan kuma be hanashi yin kyau ba…..wani iri yaji sakamakon hango Ammi da yayi zata shiga d’akinta”Anutse yace “Ammi”juyowa tayi suka had’a ido “ya kauda kai da k’yar yace”dama zansha coffee ne Aturo Amaan ta kamun….dakatar dashi tayi da cewa”y’ata tayi bacci”koma bata yiba bbu inda zataje”dama kana buk’atar coffee d’in kak’iyin mgn tun d’azun??”bece komai ba yana dai tsaye gefen up stars d’in “sanin ba mgn zaiyiba yasaka ta wuce d’aki tana murmushi domin tagama fahimtar shariff yagama mutuwa a soyayyar Amaan”Amma zata k’yalesa taga zai Ajiye miskilancinsa yasanar mata ko kuwa??”dukda Amaan d’in tasan An kawo kud’in gaisuwarta kuma bata son yaron”hakan bazai saka su fidda rai ba”zata cigaba da addu’ar zab’in Alkhairi”koda bataga iyayen Amaan ba ta fahimci yarinya ce ita me tarbiya da sanin yaka mata”kuma tanaso bayan iyayen sunzo zata saka Acan Adamawar Amata bincike sbd Akwai k’aninta Acan”har cikin zuciyarta tana yiwa shariff kwad’ayin ya mallaki Amaan Amatsayin matar Aurensa”dukda tasan nema cikin nema haramunne Amma Addua itace maganin komai”da wannan tunanin itama Ammin ta kwanta bacci”shi kuwa shariff ya k’ule sosai da hanashi ganin Amaan da Ammi tayi”dama kuma babu wani coffee d’in dazai sha , kawai ita yakeson gani”da k’yar yasamu yayi bacci….washe gari yana dawowa daga masjeed ya wuce d’akin Ammi sbd yaga Amaan”saidai koda yashiga suka gaisa bbu ita”gadai teddy d’in ta da wayarta saman bed yana gani”duk Ammi na lura dashi”ya mik’e tsaye ya rasa ta ina zaice tana ina?”sai kawai yafita ransa na bashi tana kitchen” tunda ga Ammi nan zaune tana Azkhar yasan kuma bata barin Ammi tayi Aiki da kanta”tunanin hakan yasaka yanufi kitchen kai tsaye”koda yatashi shiga cikin sand’a ya shigo Amaan na tsaye gaban gas cooker tana fera dankali”tana sanye da doguwar riga fara k’al y’ar kanti irin ta y’an k’asar turkish”tayi Acuci da gashin kanta data saka red d’in veil ta yane”sosai ta masa kyau yabi bayan ta da kallo”ya kawar da kansa yana d’an sakin jikinsa ta yadda zataji motsin mutum”da sauri kuwa ta juyo”had’a ido sukayi”gabansu yafad’i Atare”Amaan tafara kauda kanta tana cigaba da Aikinta…wai yarinyar nan tana nufin tafi k’arfin tamun mgn ne kome? yafad’a Acikin zuciyarsa yana nufar gaban fridge yabud’e ya d’auki goran ruwa”sai wani d’aure fuska had’e da shan k’amshi yakeyi”yasha Alwashin bazai tanka taba”harya kai k’ofa yaji siririyar sanyayyar muryarta tace”hamma ina kwana?”bana so! nace bana so Amaan!! ki rik’e gaisuwarki”sbd kinga kin samu lafiya zaki bar hannuna shine zaki tsiro da haka?to yayi kyau na gode…. yafad’a cikin kakkausar murya yana fita daga cikin kitchen d’in batare daya kalletaba… innalillahi wa inna ilaihir raju’un! fassarani zaiyi ni salma?ta girgiza kanta idanuwanta na cikowa da k’wallah sbd ta tsani Arayuwarta Atuhumeta da laifin da bata san ta Aikataba”sosai tasha kukanta cikin kitchen d’in tana Aikinta harta gama”Abinka da farar mace duk fuskarta tayi ja”hakama idanuwanta”tana gab da kammalawa Ammi ta shigo cikin kitchen d’in tana fad’in sannu da Aiki Amaan”su mommy d’in sun kai kusan la’asar kafin su iso ko?”k’ilanma har biyar sai sunkai kinsan da nisa…kallonta Ammi tayi sosai dukda ta juya fuska gefe”gabanta yafad’i tace”Amaan lafiya naga kamar kinyi kuka?”babu komai Ammi kawai ina kukan zanyi kewarku ne”kinga idan sunzo yau gobe zamu juya mu tafi shine fa”batare da Ammin ta yardaba tace”karki koma kuka ga waya Amaan”bayan ita kuma nima Ai zanzo ko shariff yaje ya d’akko mun ke ko?”hakane kuma”to karki koma yin kuka “idan kin idar kizo kiyi wanka ki huta”dato ta Amsa Ammi ta fita daga cikin kitchen d’in “kai tsaye sashen shariff ta nufa sbd ranta yabata shine dalilin kukan Amaan”kawai dai ta b’oye mata ne”hakan kuma yatabbatar mata da cewar Amaan nada hankali da sanin yaka mata…. shariff kuwa ya d’auka zata biyosa ta tayita masa shagwab’a da bashi hak’uri sai yaga Akasin hakan”har cikin main parlour ya zauna yana danna wayar k’arya kodan k’ilan ta fito” Amma sai yaga Amaan shiru”daga bisani ya wuce samansa”sai haushin kansa yakeji wai Akan me zai damu da ita wai?”yana wanka yana jan tsaki “harya fito ya shirya zuciyarsa Acunkushe take….yana zaune a parlourn sa ya Aza k’afa d’aya kan d’aya yana waya da mus’ab”Ahaka Ammi ta shigo”saidai yadda yaga fuskarta yasaka yaji fad’uwar gaba”yada dai dake sbd namijin duniya ne shi”sallama yayima mus’ab kafin yasaci kallon Ammin…..sannu ishashshe me walkin sa! wai yaushe zaka dena wannan zafin zuciyar taka ne shariff?”me kuma nayi Ammi?”tsaki taja tace”me kayiwa y’ar mutane take kuka?”k’arata ta kawo?”ko d’aya”Amaan nada hankali koda na tambayeta b’oyemun tayi”saidai tace mun……ta masa bayani”kafin ta d’ora da cewa”hakan yatabbatar mun wani abu kamata”yau iyayenta zasu zo kuma gobe nake tunanin zasu juya da y’arsu “me makon ka sakata farin ciki shine zaka sakata kuka ko?”shiru yayi yak’iyin mgn “ta juya ta fita daga cikin parlourn”gaba d’aya sai yaga be kyautaba”yasan kawai rashin fahimta suka samu Amma ya lura Amaan nada sauk’in kai”jikinsa Asanyaye ya fito daga cikin parlourn yanufo down stairs “hangota yayi tana jera warmers Asaman dining table”kallon cikin parlourn yayi yaga babu kowa”cikin sand’a ya iso gab da ita yasaki ihu daidai kunnanta…..ta saki k’ara Atsorace ta juyo suka had’a ido”saura kiris ta fad’a saman k’irjinsa”kusancinsu yayi yawa har hannunta na shafo nasa”saita turo baki tad’an ja da baya tana neman barin wajen….dama ke matsoraciya ce bansani ba?”yafad’a yanata kallonta sbd shima ya lura da tayi kuka d’azun….kabani hanya na wuce! shine Abinda ta fad’a kanta Ak’asa”idan nak’i fa?”yafad’a cikin taushin muryansa yana koma fake wajen ta yadda bazata iya wucewa ba”Allah koka matsa kona had’aka da Ammi?? Amaan! yakirata cikin wata iriyar murya har saida taji gabanta yafad’i”uhmm! meyasa jiya muna zaune inata mgn kika mun shiru?”kunyafa nakeji hamma shiyasa”Amma kai kana ganin laifina kana fushi dani damun zaton Abinda ba haka nake nufi ba ko?”tayaya sbd na warke zan maka Abinda be kamata ba hamma??sai kuma ta saki kuka”kinga ya Isa zoki zauna muyi mgn “yafad’a yana matsowa yaja mata kujerah murya can k’asa yace”zoki zauna ki dena kukan”batayi mgn ba ta zauna kan kujerah “shima zama yayi gefen tata kujerar ya ciri tissue dake Ajiye gefe ya matso dab da ita har tana jin hucin numfashinsa “bazaki dena hawayen ba?”saida ta kwab’e baki kafin tace”toka hak’ura?”kina kallon wani wajen bani ba shine zan hak’ura”to Ai basai ka kalleniba zan kalleka ka yarda?”ah ah “yafad’a yana saka dogon hannunsa dake rik’e da tissue d’in ya share mata hawayenta”ya yar da tissue d’in yana fad’in yanzun zakiyi break fast d’in?”uhmm uhmm! ta fad’a Ad’arare sbd jin Alamar idanuwansa na yawo a Akanta”gaba d’aya kunyarsa da wani irin kwarjininsa takeji….kusan mintina biyu bbu wanda ke mgn cikinsu”can ta saci kallon sa caraf suka had’a Ido”da sauri ta rintse Idonta yasaki d’an guntun murmushi yana fad’in kunyar gulmace “ni yanzun na hak’ura kema kin hak’ura ko?”girgiza kanta tayi “cikin sanyin murya tace”nidai idan kanaso na hak’ura saika dena wannan rashin maganar dakakeyi ka kuma dena d’aure fuska da saurin fushi ko?”uhhmm Amaan kenan! kinsan Ance hali zanan dutse”haka Allah ya yini saidai kiyi hak’uri kawai”kuma Alhmdllh keda y’an gidan nan Ai Ina mgn daku ko?”Allah komu wani time d’in sai Ayita maka mgn kayi shiru ko?”shikenan d’iyar Amminta”d’an murmushi tayi ta mik’e tsaye yanata kallonta ta zuba masa komai kafin ta zauna tafara had’a masa tea”hamma! uhmm”wai miye Aikin ka?”y’ar jarida kika koma ko?”nidai kasanar mun”to nidai talakane Ina kasuwanci”sannan ni d’an CID ne”nasan Baki manta sadda aka sacekuba keda matar mus’ab ko?”d’an jim tayi Alamar tunani”can tace Eh natuna”kawai dai kafad’a ne nice talaka bakai ba”duk wanda ke rayuwa Anan ya wuce Ace masa haka”ta fad’a tana turo masa cup d’in tea Agabansa”nifa Amaan sai 12 nake break fast “jiyama sbd wasu dalilai nayi 8 am”to Ai yauma sai kayi sbd wasu dalilai d’in ko?”Amma ni wlh sai kayi yanzun”ta fad’a cikin shagwab’a “cikin wata murya yace”to kema kin yarda zakiyi?”uhmm uhmm wanka zanje nayi”ta fad’a tana nok’e kafad’arta “sosai yaji ta burgesa”dama bakiyi wanka ba?”idan nace miki k’azama ki musamun ko?”nafayi wanka da Asuba hamma”okay karawa zakiyi sbd kina period ko? innalillahi! dan Allah kadena mun haka”shareta yayi ya d’auki cup d’in tea d’in yasha rabi sannan yanufi bakinta dashi”ta kurb’a ta kallesa sukayi murmushi Atare”Hakan yafaru kan idon Ammi”har fork d’in daya saka yafara bata chips duk ta gani”saidai tada fahimci basu lura da itaba sai tabar wajen”Aranta tace duk zafin kan namiji idan yazo hannun wacce yake so dole ya Ajiye sa”ita inda badan ta ganiba zata d’auka bazai iya bama mace kulawaba irin haka”dubi Amaan y’ar yarinya da ita Amma yamace kanta….hamma kaifa baka san ci nice kawai kaketa lodamawa ko?”beyi mgn ba shima yafara ci”suna a haka sukaji k’amshin turaren sadeeq abayansu”kallo d’aya ya musu yaji sunyi bala’in burgesa”gaba d’aya sai yaji Aure yakeso…babban yaya da babynsa sannunku”sosai kalmar baby ta tsaya Aran Amaan”tana jin kunyar sadeeq ya samesu Ahaka “fatanta Allah yasa kar Ammi ta fito”shariff kuwa ko Ajikinsa yabasar”bayan sadeeq ya zauna yana zuba Abinda yakeso Abdallah shima yazo ya zauna yanata kallonsu”badan Amaan ta k’oshiba tace masa ita ta k’oshi”hakan yasa ya k’yaleta”daya ga tana k’ok’arin tashi saiya kalleta ya girgiza kansa”Alamar karta tafi”da Ido ta rok’esa Amma saiya share ta”hamma zanje wajen Ammi pls”kansa kawai ya gyad’a mata”tana baro dining area d’in Ammi na fitowa daga cikin bed room d’inta”Ammi yanzun zakiyi karin? Eh Amaan “to bara naje nayi wanka”dato ta Amsa ta wuce d’aki”shariff na break d’in yana jin zuciyarsa wasai”saidai wani bangaren na zuciyarsa yana fargaban Amaan ta tafi garinsu tabarsa”sbd Aganinsa shak’uwa yayi da ita”ni kuwa nace mgn zakayi”be bar gidan ba saida Amaan ta fito da zazzafan wankanta”Ammi na kallonsu ta d’aukar masa jakarsa da farin kayansa irin na police a jikinsa tarakashi bakin get tadawo…..sai wajen k’arfe biyar y’an Adamawa suka iso KD…..✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button