Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 47

Sponsored Links

47
Neman Nisa takeyi cikin tinani da damuwa Akai knocking kofar kafin aka Bude aka shigo.

Masu aiki ne guda biyu suka shigo a tare kowannensu dauke da fararen trays masu kyau dauke da breakfast dinta.

Cikin girmamawa Mai tsananin gaske sukai qasa da kansu suka gaidata.

Shiru tayi Bata dago ba sbd batasan da ita suke ba Dan haka Bata dagoba itama kaman yanda Suma Basu dagoba suka sake gaidata wannan Karan suna Dan dagowa.

Zeenah ce data shigo ta amsa musu tana cewa su Daya a cikinsu yaje ya kawo mata lemon zata ci abinci dashi.

Dayar ce ta fara Jere abincin a gaban Benazir da sai alokacin ta Dan dago ta Gane tin farko da ita suke.

Sake gaidata sukai ta amsa tana Maida musu da gaisuwa itama a sanyaye.

Ana kawowa Zeenah Abinda tace suka fice ta zauna tana kallan benazir data kasa kallan kayan da aka Jere a gabanta qamshinsu na cika hancinta zuwa cikinta.

Chips ne da ketchup da scotch eggs se pepper soup na Kazan da aka cirewa qashi dakuma tea mara Madara me qamshi da zafi sosai.

Bata dauka ita aka kawowa wannan abincin ba saida Zeenah ta sakata cinsa tareda Tayata zuba komai cikin wasu irin plates da suka saka benazir din hankalinta na Neman tashi da wannan rayuwar data samu kanta aciki alhalin mahaifiyarta na can cikin zafaffiyar rayuwa.

Duk yanda Zeenah taso Benazir ta sake taci abincin Bata iya cinsa sosai ba sbd ba cimarta bane irin wannan abincin Dan haka sama sama taci komai taji ya isheta.

Tattara kayan Akai aka fice dasu Mai Aiki ta shigo ta sake gyara dakin ta Kuna humidifier ta fice.

Umme da Zeenah ma shiryawa sukai suka fice zuwa Asibiti dubo dd babba.

Ita kadai aka bari sai Amnah da masu aiki.

Da Rana ma haka masu aiki suka kawo mata abinci aka jera mata
Daqyar ta iya cin kadan tace ta koshi suka dawo suka kwashe.

Kaman mara lafiya haka ta wuni a daki jigum tana renon Amnah duk a sanyaye ba kuzari.

Sai magrib suka dawo har lokacin tana daki zaune ba motsin kirki.

Shigewa sukai kowa yayi wanka suka Dan huta kafin suka fito cin abinci wannan Karan haka aka sakata fitowa zuwa dining Wanda har Akai aka gama Bata iya Sakin jiki ta zauna ko daidaiba bare iya cin abinci a cikinsu.

Dole aka maidata daki aka Kai mata Wani abincin acan Shima Bata iya ci ba saida Umme da kanta ta shigo tace taci.

Yau dinma hakuri Umme ta Bata akan su sake kwana dakin Zeenah kafin gobe.

Wanka sukai kaman yanda Zeenah ta sakata ta shirya ta shirya Amnah suka kwanta.

Yau ma kaman jiya sai kusan hudu ta samu bacci ya Dan dauketa.

Washe garin ranar tana daki masu aiki suka zo aka cire tsadaddin furnitures na dakin dake maqale Dana Zeenah da basuyi komaiba aka saka komai sabo a dakin tareda tsarin abubuwan dakin babys.

Me Aiki aka kawo ranar sabuwa wadda hidiman laluran benazir da Amnah ne kawai aikinta da haka ita aka saka ta Jere kayan lefen Benazir tsaf a closet hakama tarin kayan da aka siyawa Amnah duk ta Jere komai
Duk da babu inda yakeda Wani Abu me suna datti ko qura a dakin Amma Saida Nafisat me aikin ta tsaftace koina ta wanke toilet din da a ranar Shima aka zuba mata toiletries da komai na buqatanta Dana Amnah.

Ac aka kunna tareda qamshin masu Dadi Zeenah ta kawota dakin ta fice sbd wayan da zatayi.

Tinda ta baro gidansu babu Abinda ta dago tayiwa kallan ko sakan uku bare kallan tsaf sai dakin.

Turkish Royal bed ne da set dinsa na komai tareda Wani mahaukacin Katan mirror Daya ci kusan Rabin bangon gefe Daya.

Komai na dakin Ashe ne da fari aka saka sai daukan Idon nuna kudin Dayake cikin siyansa,
A gefen makeken gadon daga qurya gadon Amnah ne fari Mai kyau da tsadan gske Shima hakama da kayan qasan baby a jikinsa,.

Ko beddings dake shimfide a gadon fari ne hakama pillows Akai kusan guda 8 dasuka sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta na mutuwa sosai.

Carpet da table dasu stools harma da sauran kayan dakin kusan tsoro suka Bata saidai batada mafita ko tudun dafawa a wannan rayuwar data tsinci kanta aciki Dan haka ta Tako ahankali ta Kwantar da Amnah ta nufi inda take tinanin toilet ne ta shiga Nan Wani firgicin Yakuma cikata ta ringa saukar da hawaye masu zafin tonowa da Annenta tinanin anan ake nufin zatayi rayuwa Annenta na can cikin halin qaqanikayi.

Sosai tayi Kuka jikinta na sake mutuwa kafin tayo alwala ta fito ta tayarda sallah.

Tana idarwa taga har lokacin Amnah na bacci Dan haka ta koma toilet tayo wanka sbd tinanin al’adar da Dokan gidan ne wanka kafin kwanciya musamman ganin wannan gadan tasan bama zai yiyu ta hau musu gadon ba.

Tana fitowa ta dauko kaya inda Zeenah tace mata ta ringa daukowa ta saka doguwar Rigar jallabiya sbd a kwana Biyun datai dakin Zeenah cikin mawuyacin hali tayi su sbd kayan datake Bata tana sakawa Riga da wando.

Tana gama shiryawa Zeenah ta shigo ta zauna tana Tayata bawa Amnah data farka Madara.

Bayan sun gama Zeenah anan ta kwanta Saida Amnah tayi bacci kafin ta fice musu bayan ta nunawa benazir inda zata Kuna wutar dakin da kashewa kokuma rage hasken.

Zeenah ce ta sakata Hawa gadon kafin ta fice Dan haka tinda ta hau take shiru kaman wadda tayi bacci Amma zuciyarta cike take da tinanin inda ta samu kanta a yanzu.

Baby Amnah kaman tasan sunyi dakin kansu ranar bacci tayi sosai har safe ko madaran Bata farka ta Sha ba.

Suna yin sallar Asuba benazir ta gyara gadan ta sauko da Amnah suka zauna kan tattausan carpet din dake gefen gadon suna gyangyadi.

A gurin bacci ya sake dauketa sai kusan karfe Tara Nafisat ta shigo tafara kokarin gyara dakin ita Kuma benazir tayi toilet da Amnah Dan Yi mata wanka.

Yau ma a jiqe suka gama wankan ta kawota daki ta Kwantar Takoma itama tayo ta fito suka shirya suka zauna jiran tsammani kaman kullum.

Breakfast din na yau a dining aka kirawota a dosane tayisa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.

Suna gamawa ta silale Takoma daki sukuma suka sake ficewa zuwa Asibiti sbd dd babba da zaa wuce dashi Zurich yaga likitan DD.

Dayake tafiyan tareda Dawood din harma da dad kaante zaayi sai Basu Wani tsaya Bata time ba cikin kwanaki 10 aka gama komai suka wuce Kuma tin ranar da aka tafi da dd babba asibiti Dawood Bai dawo kaantes ba sbd kullum a Asibiti yake haduwa da ummensa harma da dad kaante.

******Bayan tafiyarsu dd babba Umme ta samu nutsuwan dawo da hankalinta da kulawanta kan benazir data fara sabo da zaman daki da rayuwar kadaici data sake samun rayuwarta aciki duk da Zeenah na iya kokarinta gurin ganin tana debe mata kewa da Bata kulawa tareda nuna mata wasu abubuwan.

Wata sabuwar meyiwa Amnah wanka aka dauko dattijuwa wadda ita Kuma aikinta kawai na yiwa Amnah wanka ne sbd mura data fara shigarta na ruwan wanka da kullum saita shaqa sbd benazir Bata iya mata wanka toilet.

A jiki Umme tafara Jan benazir sbd lura da akwai tsoron mutane da rashin sabo da mutane sosai a tattare da Bena din,

Mum Khadija ma da bata cika son mutane ba tana ‘dan kaunar Bena din sbd fahimtar zatayi biyayya makan baiwa ita Kuma Daman tanasan Wanda zai Basu girma da biyayya ya nuna su dinne a sama.

Zaman daki da qarfi da yaji Umme da Zeenah suke Hana Bena kullum indai zasu fito sai ankirata ta fito.

A dosane take zama cikinsu Bata iya magana idan ba tambayarta ummen tayiba ko Zeenah.

Ahankali mura Mai qarfi ta shigeta ita da Amnah sbd sanyi da wankan Datake musu so biyu kullum tinda tazo sbd tsoron shafawa Wani Abu ko gidan datti ganin masu gidan da gidan kaman saika wanke hannu zaka taba su.

Boye zazzabinta Mai tsananin karfi tayi ta danne Bata bari ansaniba tinda haka Suka Saba gida,
Na Amnah ne yakasa dannuwa sbd rigimar Datakeyi ba sassauci.,

Ta Dena baccin dare sbd ciwon Amnah ga nata ciwon ga rigimar Amnah ga kadaici ga damuwar mahaifiyarta sai kawai tafara Neman zauncewa ciwo ya Kwantar da ita gadan gadan harda Kuma Qarin sauyin cima da muhalli.

Hankali tashe aka kirawo likita har gida yazo ya dubata aka duba Amnah itama.

Wannan ciwon da sukai ya saka jikinta yin sanyi sbd kauna me tsananin dataga Umme nayi mata itada Amnah sai Hakan ya taba zuciyarta akan yaudarar ummen takeyi a matsayin wadda Bilal dinta ke tsananin so.

Wannan tinanin ya sanyayar da zuciyarta daga bushewan da tayi batajin kowane feeling a gidan da mutanen gidan.

Idan zatayiwa Umme adalci Bata cancanta wannan yaudarar da ake mata ba Amma Kuma itama Batada zabi sbd ba itace ta zabarwa kanta wannan rayuwar ba.

A haka dole ta fara sakewa dasu Dan faranta ran Umme Dan Zeenah dasuke nuna mata asalin kauna da kulawa.

Da farko kokarin cin cimar da duk aka Bata tafara tareda daurewa tana cin abincin taredasu a dining kowane lokaci.

Hakama takan daure da kanta ta fito Koda dakin Zeenah ne taje,

Kullum da safe da kanta take zuwa dakin Umme ya gaisheta ta dena Jira sai an Aiko kiranta ta fito.

Hakan data fara ba qaramin faranta ran Umme yafara ba Dan haka suka sake dagewa sosai gurin kulawa da benazir din.

*****dd babba ya samu sauki sosai Amma Dawood ya hanasa dawowa sai ya huta daga tashe tashen hankalin da akaita samu a baya Dan haka sukai zamansu sbd shi Dawood din yanada abubuwan da zaiyi a qasar Kuma ahakan yaqi barin ko so Daya Safnah ta gansa Kuma data kira yace Bai aminta ta samesa ba ta zauna inda take zai nemeta da Kansa.

Wata daya suka share harda sati uku kafin suka fara Shirin dawowa shi dad kaante Daman tini ya dawowarsa yabarsu acan.

*****Acikin wannan watan da satikan rayuwar Benazir a Kaantes ta fara amsa Wani sunan da matsayi na sauyi data fara samu,

Dukiya gaskia ce,hakama rayuwar hutu da daula gaskia ce,

Benazir ta fara samun sauyi na rayuwa Dana fata,
Skin dinta brown ne lafiyayye tin asali,
Su ba maabota yawo bane kullum sune kulle cikin kejin gidansu ahakan suka taso suka girma,

Fara jamiar su kullum jikinsu a rufe yake sbd rashin sitarar arzki da Horan da suka samu
Dan haka fatarta na fara samun hutun kaantes da tsadaddiyar luxury rayuwar da ake Bata yasaka sauyinta fara bayyana a kankanin lokacin.

Cikowar jiki Kuma Daman ita din bamai jikin qiba bace Dan haka bata sauya ba tanan siririyarta Saidai murmurewan data samu.

Umme ta Siya mata waya itada Annenta aka aika mata driver yakai mata Dan haka tana magana da ita idan Ababa Yana gida ya Bata wayar tayi tagama a miqo masa ya aje.

Shima shirun da yayi ya daga qafa ne sbd sanin dd babba da Dawood din Basa qasar shiyasa yayi shiru sai sun dawo an nitsa yafara sanin matsayarsa.

 

******Qarfe uku na yamma jirginsu ya sauka Abbakar ne yaje daukosu
Shikuma DD Naseer ne yaje ya daukosa daga airport gidansa Kai tsaye ya wuce saiya huta zaizo kaantes din.

Yana Isa wanka yayi yayi sallah baya buqatan cin komai sai ya huta tukuna Dan haka kwantawa yayi baccin yamma sai 5 da Rabi ya tashi yasake Yin wanka ya fito Kai tsaye yayi kaantes.

Koda ya Isa zaayi sallan magrib Dan haka tareda dd babba suka shiga sallar suna gamawa ya fito Abbakar na biye dashi Yana sake masa barka da dawowa suka nufo ciko.

Sashen ummensa ya nufa Kai tsaye Shima Abbakar ya koma.

Zaune suke a Palo dukkaninsu daga ummen har Zeenah da benazir dake gefen Zeenah suna bawa Amnah Madara a tare yauma rigimar takeyi.

Qamshinsa yayiwa palon dip Dan haka a tare Umme da Zeenah suka dago kallan kofar daidai shigowansa
Sanye da black Balmain three quarter jean da hoodie sweatshirt hasken qafafunsa dake bayyane na daukan idanuwansu kaman koyaushe fatarsa kaman ta sabon baby sbd hutu da luxury rayuwar daya taso aciki yake aciki.
#MAMUH#
#DBENA
#HOT LOVE
#CRAZY IN LOVE
#ROMANCE

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button