Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 11

Sponsored Links

Page 1️⃣1️⃣

 

Gaishesu fanan tayi suka amsa Banda zeenat Wanda idonta kurr akanta SE murna takeyi tayi kawa ummi ce tace nikam zeenat tunanin me kikeyi haka murmushi tayi tadawo kusa da FANAN tazauna tarike hannunta tace laaah ummi nayi kawa dariya gaba Daya Yan falon sukayi Ammar ne yace ummi Ina yaseer da azaad suna garden ok garden din yawuce Anan yasamesu suka gaisa yawa azaad yajiki me kula dakai tazo fa mikewa sukayi dukkansu tunaninshi bekawo mishi wannan yarinyar ammar yazo da ita ba shiga falon sukayi harsun haura stairs doctor ammar am FANAN kikaraso mikewa tayi suka haura tare da zeenat shiga sukayi da sallama abakinsu Jin muryantane yasashi yadago Yana kallonta Kara daure fuska yayi ke meya kawoki nan tsayawa tayi haba azaad Meye haka ankawo wacce zata dubaka Kuma kanace mata meyakawota kallon Ammar yayi yace inde wannan ce zata dubani to na hakura yarinyar da itama tana bukatar aduba kwakwalwarta sbd bana tunanin tana da ishashen hankali bayanda baayi ba Amma azaad yace bazatana kula dashi ba kawai aje akawo me hankali fanan kuwa ranta yagama baci saukowa tayi kasa anan tasamu su ummi sallama tamusu ah ah harzaki tafi kingamane ah ah yace wai bazan dubashi ba takarasa magana idonta nakawo ruwa ganin haka yasa ummi tace kyaleshi zoki zauna anan koyanaso ko bayaso sekin dubashi tunda tun farko ke kika fara zama tayi kusada anty Amina, hira anty Amina tafara Janta dashi saboda yarinyar ta burgeta tun bata sake ba harta sake suna hira suna dariya zeenat ma zuwa tayi akaciga ba da hiran da ita ummi tace ai itama wannan naso tayi school of health Amma Taki wai ita law zata karanta dayanzu itama tafara aiki a asibiti dariya FANAN tayi tace Kuma aikinga banisa tsakaninku hira sukasha sosai time din sallah zeenat tace zo muje dakina muyi mikewa sukayi sukabar anty Amina da ummi afalo bayan tafiyansu ne anty Amina tace wlh nikam wannan yarinyar taburgeni baruwanta ga hankali murmushi ummi tayi tace ai kina ganinta Kinga jinin Fulani haka sukaci gaba da hira kafin suka bar falon. Adakin zeenat kuwa FANAN ce tafito daga toilet tadauro alwala dogon hijab zeenat tabata ta tada sallah bayan ta idar ne taninke sallayan ta ajiyeshi a inda tadauka tana karewa dakin kallo yamata kyau sosai komai pink and white zeenat ce tashigo dakin hannunta rike da wayanta iPhone 12pro mika mata tayi samin number ki samata tayi takira taga number atake tamata magana a WhatsApp fitowa falo sukayi a dining sukasamesu Amma Banda yaseer, azaad Ammar su part din Azaad aka kaimusu,
FANAN zoki zauna muci abinci murmushi tayi tace alhamdulillah nakoshi haba kekuwa kizo muci ko kunyarmu kikeji sunkuyar dakai tayi tana murmushi allah nakoshi fawwaz ne yace zamu miki dure fa inbakizo ba dariya akayi bayanda Basu da itaba tace akoshe take komawa falo tayi tazauna Ammar ne yasauko yace FANAN jeki dubashi nizan wuce doctor yace fa bayaso noo karki damu kijeki kawai to shiga dakin tayi fuskanta ahade takarasa syringe tadauka taja ruwan allura ko kallonta beyiba yamika mata hannu yayi yaseer de Dake gefe yazuba musu ido bayan tagama mishi allura Tamika mishi magani sannan tace Kaci abinci ne bece mata kallaba yakai maganin setin bakinshi zesha takara tambayanshi Kaci abinci nikam Ina ruwanki danine konaci ko banci ba gyada Kai tayi tarike kugu tace aikuwa yau inde Bakici abincin nan ba bazakasha magani ba mikewa tsaye yayi ganin yamikene tsoro yakamata Amma bata nuna ba ni saankine dazaki tsaya kinamin rashin kunya cikin i’ina tace ummm nide ai ba rashin kunya namaka ba Gsky nafada maka dama ance Gsky dahci gareta nufota yayi tafara ja baya harta iso jikin bango tsoro taji sosai gashi baa hanya kofa takeba daff da ita yazo yasa hannu yamatse Dan karamin bakinta kafin yace nace ni saankine girgiza Kai tayi ah ah idonta taff da kwallah okay kinsan niba saanki bane Amma kika tsaya kinamin rashin kunya kayi hakuri bazan sake ba idonta yake kallo Wanda yacika da ruwa harwani sheki yakeyi iya karfinta tasa ta tureshi Amma Ina kamar Wanda tature dutse ko motsi beyiba ganin haka ba solution bane yasa tafasa ihu wayyo allah na zekasheni fusata yayi yasaketa yaje dauko belt aikuwa kafin ya Ankara tagudu yaseer kuwa mezeyi inba dariyaba dariya yakeyi harda rike ciki gaskiya dude wannan yarinyar itace Dede dakai mugun kallo yawatsa mishi kafin yaja dogon tsaki ita kuwa kafin taje stairs tagyara tsayuwarta tana aiyana irin muguntar daze mata in yakamata.

Karasowa falon tayi Amma bakowa abakin kofa taga wata mata atsaye tana sanye da abaya Baki Wanda yasha stones fuskanta tamkar bana mutane ba idon yayi Baki kirin bako digon fari aciki fuskanta kuwa ahade kamar Wanda aka aikowa da mutuwa hancinta nafitar da hayaki bakaramin tsorata FANAN tayi ba duk ita atunaninta gamo tayi adduah tafarayi acikin zuciyarta fitowa su ummi sukayi Jin motsine yasa FANAN juyawa dawuri taga su ummi ne ah ah mommyn su kece shigowa mommy tayi tace eh wlh Aysha nice mamakine yakama FANAN ganin atake suffarta yacanza takoma mutum sake sake tafarayi azuciyarta Anya ba idonta bane yamata gizo tana nan atsaye mommy tawuceta zama tayi a kujera fuskanta ba yabo ba fallasa sama sama suka gaisa da ummi kafin anty Amina da zeenat suka gaisheta yatsina fuska tayi kafin ta amsa sannan tace Mansoor ne yazo yaban labari Ashe azaad na lafiya eh wlh lafiyansa KLAu okay yayi kyau haka akeso ai kallon inda fanan take tayi kafin tace wancan Kuma daga Ina anty Amina ce tace nurse din Azaad ce ita take dubashi mugun kallo tawatsawa FANAN atake idonta yajuya ke zonan kasa motsawa tayi domin MATAR nan akwai wani Al amari tattare da ita daka mata tsawa tayi bake nake kiraba karasowa gabanta tayi Meye sunanki fanan okay bar gabana tashi tayi ta koma can gefe har cikin ransu Basu ji dadin abinda mommy tayiwa fanan ba mikewa tayi tace se anjumanku bayan fitan tane ummi tace zo FANAN karasowa tayi jikinta asanyaye kiyi hakuri kinji haka hanlinta yake murmushin yake tayi tace karki damu ummi bakomai yauwa yar albarka dama nasauko zanmuku sallamane SE gobe harzaki tafi eh ummi yamma tayi hakane Abu me aiki ummi takira tace taje daki takira mata areef ko fawwaz dayansu yazo yakaita gida dasauri ta girgiza Kai tace ummi ah ah zanje dakaina meyasa bazaki bari yakaiki ba ummm in baba yaji lbr zamin fada jinjina tarbiyansu tayi kafin tace shikenan pause dinta tadauko Tamika mata 1k gashi kiyi transport ah ah allah akwai kudi ajakata kinganki banason musu kikarba kawai ganin datayi inbata karba ba ummi bazataji dadi bane yasa takarba tamusu sallama zeenat ce tarakota har titi tasamu napep ta tafi.

Abangaren mommy kuwa tana komawa part dinta tafara sambatu ita kadai naje daniyan karasashi da bakin tsafina Amma wannan yarinyar ta wargaza komai dole takarbi hukunci wasu sambatu tayi nan take Takoma wata halitta meban tsoro gashine toko Ina ajikinta wani daki tashiga yakulle zama tayi akasa ta harde kafanta nan take candles suka kawo wuta wasu irin maganganu tafara mara kan gado tun tanayi ahankali harta farayi da karfi wani guguwace ta tashi wani katon basamuden aljanine mara kyan gani yabayyana acikin guguwar Yana wani irin dariya mara dadinji kafin yayi shuru yakalleta yake hafsatu kungiya tabaki umarni Daki saduda da kudurinki akanshi kafin nan dawani lkc kallonshi tayi tace yakai shugabana TANZARZAR Meye yasa kace inbari bayanzuba takarasa magana kanta akasa sbd hakan shine kwanciyar hankalinki itakuma wannan yarinyar tabata bara zanane agunki domin tana dauke da wata irin baiwane atattare da ita Amma bazaki San hakan ba SE rashin hakurinki yakaiki kintabata yagama mgn Yana me dariya kamar mahaukaci kafin batt yabace……….

 

Tofa ana wata ga wata …… SE mun hadu a comment section

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

 

____________________________________________

 

Back to top button