Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 39-40

Sponsored Links
  1. ❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*39&40*

 

…….. sharif kuwa cikin nishad’i ya shigo cikin d’akin “ko ina yamasa fes kamar yadda yake buk’ata”wanda koda shine da kansa ya gyara d’akin iya haka zai masa”kayan jikinsa yarage ya d’aura towel iya k’ugunsa”can yasaki d’an guntun murmushi daya tuna ranar da amaan tagansa ahaka a wancan gidan”harta tsorata ta fito aguje”yana wannan tunanin yanufi cikin bath room d’in ya shiga….da kayansa data wanke masa ya had’a ido”besan lokacin da y’ar dariya ta sub’uce masa ba dayaga boxer d’insa gefe bata had’a dashiba”hakan ya tabbatar masa da cewa amaan tashi tanada kunya da kawai ci”kuma batada ruk’o”tunda gashi tun kafin yaka mata uzurinsa na dalilin tsakin daya mata har take fushi ta masa wannan kyautatawar..sosai yaji dad’i aransa”yanata wankansa yana murmushi shi kad’ai da tunanin zuci har ya gama wankansa yafito”ganin babu alamar amaan ta shigo cikin d’akin yasaka ya wuce gaban ward rope d’in sbd yaduba kayan da kansa”dama kuma ya tsammaci barata zoba….cikin mintina 35 yafito cikin shirinsa me matuk’ar d’aukar hankalin duk wanda yayi tozali da kyakykyawar surar jikinsa “yayi kyau gwanin burgewa musammun da yau fuskarsa ke cike da walwala”dukda yau yana week end hakan be hanashi niyar fita ba”da yama tashi fitar saiya fita ta k’ofar baya”yana tunanin yau da safe ko jiya da dare period d’in amaan yazo….saidai kuma koda ya iso parking lot sai yaga be kamata yafitaba amaan bata saniba”yasan kan wannan fitar tasa bata sani ba zata iya yin fushi dashi”tunanin hakan yasa yanufi babban parlourn gidan”ammi na zaune a parlourn yashigo”ta kallesa tana fad’in dama ka fita ne?”ah ah ta baya nabi na amshi wani sako”amma yanzun ma zan d’an fita”ya fad’a yana satar kallon k’ofar bed room d’in ammi”yana tsaye shibai zauna ba shibe kuma tafi ba”ammi dai tana kallonsa tace”ni zanyi mgn da iyayenta ko kai?”shiru yayi yana nazari can yace”dake dai ammi zakuyi mgn” yak’are maganar yana nufar bakin k’ofar bed room d’in….ina zakaje shariff??d’an sosa k’eya yayi yak’i yin mgn “ammi ta girgiza kanta kafin tace”shiryawa takeyi shiyasama na fito na bata wuri”kazo ka zauna kajirata ta fito mana”ammi ni sauri nakeyi”yafad’a fuska bbu walwala yanufi k’ofa yanata cin magani yafita”allah ya kyauta maka shariff “da alama ka rage miskilancin naka sbd amaan ko?shine abinda ta fad’a tana maida hankalinta wajen tv”cikin nutsuwa da sanyin jiki amaan ta fito sanye da riga da siket na lace red me zanen golden”ba k’aramin haska farar fatar jikinta kayan sukayiba”tanata zuba sanyayyan k’amshi me dad’i”ammi ta kalleta tana murmushi “ita kuwa ko zama batayi ba tace”ammi hamma yafita?ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa”yafita amaan yanata fushi sbd zai shiga d’aki nace yabari ki fito”ki fita batunsa kije kiyi break fast ina jiranki kizo ki kiramun su hajiyar taku”dato ta amsa jikinta asanyaye ta nufi dining area “zuciyarta na sanar mata idan yadawo ta shareshi”meyasa bazai iya jiran ta fitoba zai tafi?”wannan alamar be damu dake bane….wata zuciyar ta sanar mata”saita tab’e baki tana k’ok’arin yakice tunanin shariff d’in aranta…wata iriyar fad’uwar gaba had’e da bugawar zuciya taji data tuna ko yanada budurwa”tunda tasan beda mata ko a iya zamansu dashi da bata hayyacinta”da wuya kamar shariff ace beda budurwa”taji gefen zuciyarta na sanar mata”gaba d’aya sai taji komai yafita aranta “da k’yar ta had’a tea me kauri tasha da zuba chips kad’an taci”daga bisani ta goge hannunta tadawo cikin parlourn “k’asa take k’ok’arin zama”ammi na murmushi tace”dawo nan ki zauna kinjiko?”ta fad’a tana nuna mata gefenta”babu musu amaan tazo ta zauna”wayarta ta mik’o mata batare data yi mgn ba”amaan ta amsa k’irjinta na tsananta bugawa ta saka number d’in mommyn ta tayi dealing…… ab’angaren iyayen amaan”tunda mommy taga har dare yayi salma bata dawo gida ba hankalinta yatashi saidai tarasa meyasa takasa fad’ama wani salma bata dawoba,ko kuma tayi jajenta??”haka shima mahaifinta”saidai washe gari hamma yusuf ,da hamma khalifa suka fara jajen ina salma take? sunsan dai jiya taje gidan kawu bello”daddy da mommy sukace basu san inda take ba”kuma kar wanda yakoma nemanta allah zai maido musu da ita lafiya”sam yusuf da khalifa hankalinsu be amince da hakan ba sai zuwa gidan kawu bellon sukayi akace bata zoba”cikin tashin hankali suka fara nemanta gidajen y’an uwa da abokan arzik’i bbu ita bbu alamar ta”idan ankira wayarta bata shiga”sarai anty zabba’u da yaranta sunsan meke faruwa amma sai suka nuna basu saniba”zuciyarsu fari k’ar”yanxun abinda yarage ma zabba’u shine taje ayi asirin da hankalin nasir zai juyo kan shamsiya yace ita yakeso sai asa musu rana….saida akayi kusan 4 days da b’atan salma sannan y’an uwa suka fara ankara dashi kansa nasir d’in “gefe guda kuma mommy tafi kowa damuwa duk dare sai tayi kukan b’akin ciki”da tazo tayima wani zancen salma ko wani abu daya shafi anemeta sai taji wani abu yataso ya hanata hakan”ko abincin kirki bataci”duk tayi rama”tana k’ok’arin yin nafilfili da gayama allah damuwarta…. ayau yakama juma’a wanda yayi daidai da sati guda kenan da b’atan salma”tunda safe hjy hauwa(mahaifiyar nasir) dashi kansa nasir d’in suka shigo gidan”kasancewar daga anturo get d’in aka zagaya daga can baya tsakar gidan yake”daddy na tsaye gaban window yana gyara hularsa da alama office zai tafi su nasir suka shigo”ya amsa sallamar su”nasir yaduk’a ya gaishesa ya amsa yana kallon hjy hauwa data d’aure fuska tanata y’an harare harare”hjy kune tafebda safe haka?”eh mune kuma ba zama yakawomu ba”wata mgn naji wai salma ta b’ata bakusan inda takeba?”sai yanzun na fahimci zancen zabba’u gaskiya ne bilkisu ta mallakeka”to alhamdulillah na sami labarin salma ta gudu wajen wani saurayinta sbd bata son auren nasir”na kuma yadda sbd inda da gaske b’atan tayi da kazo kamun bayani…… innalillahi wa inna ilaihir raju’un!! haba hjy hauwa wannan wace irin maganar banzace haka kikeyi?”bazaku barmu muji da matsalar data damemuba sai sharri zai biyo baya?”nidai ai haka naji ko?”to shikenan haka kikaji ko?”allah yadawo da ita lafiya”babu ita babu nasir”dole kace haka tunda kasan inda kuka turata”ai dama najima da fahimtar bilkisu so takeyi ta nemi kud’i da salma”mommy ta fito tana kuka tace”k hauwa! kinzo inda bazan iya jureba….ni kike kira da k bilkisu?”eh nace k kisaka alh yasakeni idan kece mahaifiyarsa”aure tsakanin salma da nasir har abada babu shi”kuma insha allah salma zata dawo daban mamaki”na riga na fawwalawa allah lamari nah kome zaku fad’a ku fad’a kuda allah”kinga bilkisu ya isa haka wuce ki shiga ciki”cewar daddy yana kallon ta…..wai hayaniyar menake ji haka tunda safe?”cewar anty zabba’u tana lek’owa daga cikin d’akin ta”hjy hauwa ta tab’e baki tana fad’in zancen b’atan salma mukeyi….wace salmar?”tanan gidan mana”ko kema baki saniba kuna gida guda?”subahanallahi! ni kuwa ina zan sani yaya hauwa?”naga dai kwana 2 bana ganinta”na d’auka ko wani waje taje”to bbu inda taje b’ata tayi sun rufeki….ke koma ciki bana son munafurcin banza da wofi”cewar daddy yana bin anty zabba’u da wani irin mugun kallo “ta tab’e baki tana fad’in ikon allah! daga mgn?”tsaki yaja yafita daga tsakar gidan ya wuce haraban gidan yashiga mota yayi tafiyarsa”hjy hauwa kuwa d’akin anty zabba’u tashiga suka cigaba k’ananun maganganu da gulmace gulmacensu”mommy kuwa batabi ta kansuba”yayinda nasir yabar gidan zuciyarsa na d’aci sbd ya yadda salma wajen saurayi ta tafi sbd karta auresa “tunda dama tuni ya fahimci ba wani sonsa takeyi ba”tanabin umarnin mahaifinta ne kawai wajen kulasa…..wasa wasa tun ana tunanin salma zata dawo gida har aka cire rai”yusuf da khalifa suma kansu sun fara yarda wajen saurayi ta tafi sbd iyayensu sunk’i yarda suyi binciken ina taje?”ko kuma su amince abada cigiyarta a kafafafen sadarwa “mommy da daddy kuwa basu gajiba wajen yin addua”yi sukeyi babu dare bbu rana”ahaka aka ci wata hud’u cif da b’atan salma”ayanzun mutanan anguwa da k’awayenta da dangi kowa da yadda yake fassara b’atan ta”gefe guda kuma anty zabba’u tayi biye biyen malamai sbd ajuyo hankalin nasir yadawo kan shamsiya amma abin ya gagara….. ayau misalin k’arfe 6: da mintinah 8 na yamma”mommy na zaune gaban d’akinta kan kujerah tana azkhar sbd ankusan sallar magrib”sai daddy na tsugunne gaban tape yana alwalla”da gudu anty zabba’u ta fito daga cikin d’akin ta kanta bbu ko d’an kwali zata fita…..gaban mommy yafad’i tace”subahanallahi! ina zakije zabba’u?”banza tamata tayi gaba”alh kamarfa ba lafiya fa dubi ta tafi”tsaki daddy yaja yak’i mgn sbd wata iriyar tsanar anty zabba’un yaji yanaji”macen da tunda ya aureta bbu wata macen dayake gani takai mace sai ita”amma gashi yau da gobe duk asirin datake masa komai ya k’arye. mommy na kok’arin koma mgn sadeeq da khalifa suka shigo rik’e da zabba’u daketa fusge fusge….wai lafiya?”wlh daddy ganinta mukayi zata nufi titi bbu ko d’an kwali da alama kamarfa bata hayyacinta….ihu ta kurma tana fad’in ku barni naje inda salma taje”nice nayi mata asirin kurciya tabar gida”sbd karta auri nasir tafi y’ay’ana hutawa…. innalillahi wa inna ilaihir!! shine abinda mommy ta fad’a tana mik’ewa tsaye arikice, tana jin kamar ancire mata abinda yamata takunkumi game da k’in neman salma”daddy kallon zabba’u yakeyi babu ko k’iftawa”yayinda sadeeq da khalifa suka kasa mgn….wlh dama na jima da zargin akwai saka hannunta aciki”ku cikata duk gidan ubanda zataje taje sakaryar allah ce ai”cewar mommy tana kuka”aikuwa su khalifa suka cikata da gudu ta fita”daddy yabiyota saidai tana isowa bakin titi wata mota da zata wuce aguje tayi ball da ita”saida tayi sama da dawo k’asa”me motar bebi takan taba yabar wajen aguje”kasancewar anata kiran sallar magrib wasuma wajejen har an tada sallar”hakan yasa bakin titin bbu mutane sosai”kuma dama ba babban titi bane cikin layin gidajen anguwar titin yake”wasu mutane biyu da daddy suka rufu kanta”gwiwarta da kanta yabugu sunata jini”dakkota daddy yayi yadawo da gida cikin gidan”ya ajiye ta d’akinta “yasanarwa shamsiya dake zaune ta gama sallah cewar”ta kira y’an uwanta su kaita asibiti shi bazai iyaba”sosai abin yabata mamaki suka kama kuka itada sauran y’an uwanta”d’akin mommy yanufa yasameta tana kuka tana sanarwa yayanta alh bello komai ta waya”zama yayi gefenta duk su khalifa na zaune”bayan ta gama wayar yace”kiyi hak’uri bilkisu”sai yanzun na fahimci tabbas asirin da zabba’u tayi hardamu tayimawa”tunda bamu nemi y’armuba”amma alhmdllh zuwa gobe zamu fara bada cigiyarta akafafen sadarwa ko k’ilan allah yasa adace”mommy na kuka tace”dama ai ba yau tafara yimun asiri ba”taje itada allah bazan tab’a yafe mata ba”allah ya isa tsakanina da ita”kaima na gama zama dakai da y’ata tadawo zamu bar maka gidanka”adalci kakemun nan gidan?ko kuwa damuwa kayi danine?kasa mgn yayi bece komai ba”khalifa da sadeeq suka tashi jikinsu asanyaye suka bar d’akin “daddy yace”kiyi hak’uri bilkisu wlh bayin kaina bane”muddin nayi bincike itace tayi haka wlh bazan cigaba da zama da itaba”yanzun haka accident tayi”yalabarta mata komai”tsaki taja tana fad’in matsalarta ce”daga haka ta mik’e tsaye ta wuce bed room d’inta”yayinda su shamsiya suka nufi asibiti da mahaifiyarsu….washe garin ranar duk mutanan gidan cikin damuwa suke”sai wajen k’arfe 9:30 am daddy yafara shirin fita shida samarin gidan da nufin afara nuna pics d’in salma gidajen tv da jaridu”mommy na zaune d’akinta tayi tagumi hawaye nata zuba tana tuna salma wayarta tayi ringing”saida taji gabanta ya yanke yafad’i tadai d’aure ta d’auka tana yin sallama…..zumbur ta mik’e tsaye tana zaro ido waje tace”da gaske salma kece?daga d’ayan bangaren amaan na kuka tace”nice mommy”karki tashi hankalinki ina cikin koshin lafiya”sbd allah ya jefani hannun mutanan k’warai”alhamdulillah allah nagode maka! mommy ta fad’a tana fita daga cikin parlourn tasami daddy dasu hamma yusuf tsaitsaye da alama niyar fita suke”alh ga salma ta kirani”ta fad’a daidai lokacin da amaan ke cewa mommy ga ammi mahaifiyar hamma shariff daya tsintseni zata muku bayani”dato mommy ta amsa”bayan ammi ta amshi wayar ta mata sallama kafin su gaisa”mommy tasaka wayar handsfree ammi tafara musu bayani atak’aice”kafin daga k’arshe tace “munaso idan babu damuwa kuzo mu damk’a muku y’arku ga hannu”kuma kuyi mgn da malamin daya bata taimako ta warke”mommy tace”gobe zasuzo” sai godiya mommy ta dinga yiwa ammi da sakama shariff albarka”daga k’arshe daddy ya amshi wayar suka gaisa da ammi da amaan”sannan hamma yusuf ya amsa sukayi mgn da amaan yasanar mata abinda yafaru agidan bayan b’atanta”aciki harda accident d’in da anty zabba’u tayi tana kwance asibiti”damuwar tace allah ya kyauta”anjima idan hamma nah yadawo zan bakushi saiku gaisa”lallai salma kin iya kalar dangi ko?”daga ganin mutum kice yazama yayanki?”k’in mgn tayi yace”ga khalifa da sadeeq ku gaisa …. amaan bata dena wayar dasuba saida katin ammi yak’are duka”sannan ta hak’ura da wayar”ammin tace”ta saka hijab taje bakin titi ta siyo ta dawo taci gaba da wayar”amamakin ammi sai taji tace”ah ah ammi hakanma yayi kar naje na fita hamma be saniba zai mun fad’a”daga haka ta wuce d’aki ta kwanta bbu jumawa bacci yayi awon gaba da ita”sai wajen k’arshe 12 saura ta tashi”kai tsaye toilet ta nufa anan taga bak’on ta yazo”bayan ta fito ta kimtsa ta fito parlourn”ammi na kwance kan 3 seeter “abdallah na zaune yana kallon ball”kin tashi amaan?”eh ammi meye za’a dafa ne?”ah ah ki barsa ki huta ni nayi musu abincin ranar”dan allah kar muyi jayayya ammi indai ina gidan nan bazan bari kiyi aikin komai ba”pls anty amaan kimana me dad’i kamar na d’azun “cewar abdallah yana kallonta”tayi murmushi batace komai ba “ammi tace”to shikenan y’ata duk abinda kikaga yadace ki aza “jummai da laure na kitchen d’in zasu d’an kama miki wani abun dan kuyi sauri ko?”dato ta amsa ta wuce kitchen”suna aikin jefi jefi shariff na fad’o mata arai”sai wajen k’arfe 2 ta gama”su jummai suka jere komai a dining area “ita kuma sbd ba salla takeyiba ta wuce d’aki tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa”lokacin da fito zataci abinci har ukku ta wuce amma shariff shiru be dawo ba……da yamma suna zaune a parlourn”da abdul da sadeeq da abdallah da amaan”mazan nata fira ita kuma tana duniyar tunani”abdul nata satar kallonta “sai yawan sakota cikin firan tasu yakeyi ita kuma tana sharesa”ahaka shariff yashigo cikin parlourn da sallama cikin tattausan muryansa”yana rik’e da wasu fararen ledoji irin na shopping”fuska bbu yabo bbu fallasa yashigo amma yana ganin amaan zaune atare da samarin atake ya had’e rai ya kauda kansa “adak’ile ya amsa sannun da suke masa”ita kuwa saida taji gabanta yafad’i tayi saurin tashi tsaye tana nufosa ahanakali tace “hamma sannu da zuwa”yauwa”ya amsa da k’yar yana juyowa suka had’a ido”ta sunkuyyar dakai “beyi mgn ba yamik’a mata ledojin hannunsa”k’in amsa tayi “hakan yasa yad’ago kansa ya zuba mata manyan idanuwansa.…..da sauri ta kawar dakai ahankali tace”hamma ni bazan amsaba sai d’aure fuska kakeyi ko?”beyi mgn ba yamatso dab da ita yakama hannunta guda yasaka mata ledojin…..yanayin yadda taji taushin hannunsa saida takusan sakin ledojin”tamkar bayaso yace”meye amfanin kije kiyi zaune cikinsu?”to hamma yazanyi?kaifa na zauna jiran dawowarka”bayanma ka fita bansani ba”ta fad’a cikin shagwab’a “ya kauda kansa yana fad’in muje sarkin k’orafi”yayi maganar suna jerawa ahankali suka nufi dining area “taja masa kujerah ya zauna”abinda tasan zai buk’ata ta zuba masa “sannan ta matsa gefen fridge d’in dake wajen ta d’akko ruwa da kwalin lemo tazo ta ajiye masa”thank you! babu godiya tsakaninmu hamma”ta fad’a tana kok’arin tafiya…ina zakije?”zan mayar da ledojin d’aki”zoki zauna kiduba su anan ki bani labarin yadda kukayi da y’an gida”sosai taji dad’in tambayar tasa”gefen sa ta zauna tana duba ledar farko”kwalin waya ce k’irar iphone14 pro max, sai ledar pads…da sauri ta d’ago kanta akunyace tana kallon sa”ashe ita yake kallo sai suka had’a ido”gira guda ya d’age mata yana fad’in yaya dai ?”kauda kanta tayi tana duba gudar ledar”sweets ne da manyan chacoolates”ta turo baki ta kauda kanta”uhmm !sbd dan na siyo miki da pad kike wannan faman turomun bakin”very soon zanyi maganunku keda bakin naki….toni dama nace ka siyo mun itane hamma?”tab’e baki yayi tamkar ba zaiyi mgn ba sai kuma yace”nasan yau ko jiya jinin naki zaizo shiyasa naka miki”kokin manta time d’in da kike tambayata jinin ya d’auke yaya zakiyi?? yak’are maganar ko ajikinsa yana ci gaba da cin abincin sa dayayi masa masifar d’adi”ya tabbatar amaan gwanace wajen iya girki dan yasan itace tayi girkin “sbd yasan kalar girkin ammi da d’and’anonsa…. amaan kuwa….✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
vip grp 1000
via 2230373842 nabila aliyu uba bank

ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button