Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 28

Sponsored Links

Cike da takaici ya fincikoni ya shiga zare min rigar jikina ina kokarin, kwatar kaina sai da yarabani da kayana ya zuba min ido, zai kai hanunshi kirjina nayi baya tare da jan zanin gadon na kare jikina nace.
“Mi zakayi da sa’ar Yar cikinka, ko zubda kima.”
Fauce bedsheet ɗik yayi ya shiga niman saka min kayana ina tirjiya, nidai banga amfanin saka min kayan ba, dan da wayyo da dabara yagama matseni tass toh ya jima baiyi ba, yau kuma an fake da guzuma an harbi karsana. Ya more watanin hudunshi da bai taɓa ba.

Yana gama shiryani ya fita, abinda nake jira knn nasawa kofar falon key na barshi a jikin kofar, nazo na ciki ma haka. Dama akan abinci rana ne, banyi na dare ba, na kule kaina.

Da yazo yayi bugun duniyar nan naki buɗewa, karshe yace zai kira Umma fitowa falon nayi nace.
“Sai ka faɗa mata kace nayi abu naki kaga indan taxo da kanta zata ga irin uƙubar da kuke gana min kaida Iyalinka idan kuma Mama kakira itama sai tazo taga halin da nake ciki.”

Jin haka ya sauke murya ya shiga rarrashina, har da kawo min misali da halayar mata nagari daga kan Nana Asiya har zuwa kan nana Fatima, yanda nake masa kallon holuko ashe yasan abinda yake, dakyar nafito muka tafi gidan mamie dan acan rahila take, koda muka fito ban kula matanshi ba, da suke jefa min magana ba.

Muna isa gurin motarshi sai ga Mufeeda da gudu, zan buɗe gaba ta bangaje ni yayi kaman bai gani ba, na koma baya na zauna.
Har muka isa kofar gidan su Aman wai yana jiran abuɗe mishi, nayi wuf nafito na rufe mishi kofarshi nayi cikin gidan. Da sanyin jiki na shiga falon Rahipah na zaune ana mata lalle Angon karni ya kasa ya tsare, da ɗanshi a hannu, tun Mamie na magana har ta zubawa Aman ido, dan babu ruwanshi da kunya,

Ganin Rahilah fess da ita yasani jin kwalla ya cika min ido a hankali ta buɗe min hannunta na faɗa ciki ina kuka, sosai Nace.
“Hilah kiyi hakuri bani da waya bani da hanyar da zanzo gurinki, infact komi.”

Sai na kuma cusa kaina a kan cinyarta, ina kuka sosai shiru Aman yayi yana nazarin abinda nace, shigowar mao nasara da Mufeeda yasasu ɗago kai tare da amsa sallamarshi.

Kallona yayi yanda na ke kwance cinyar Rahilah ga Aman ya zuba min, ido yasashi ɗauke wuta. Munafikin kishinsa ya motsa.
D’agani Rahila tayi bayan ta ja hijab ɗinta ta rufe jikinta gaisawa sukayi, sannan ya amshi baby yana hararana.
Buɗa bakin Mufeeda tace.
“Halin munafurcin da aka saba shine akazo a nuna a duniya dan niman suna.”

Shiru falon yayi banyi manakin jin haka ba dan tana tsakiyar manyan mata, dole ta faɗi haka, kuma kalmar da fareeda ta wurgeni da shine kafin mufito shine har ta rike tayi amfani dashi.
Sai ga kunya ta kama shi kamar ya nutse kasa, mikewa Aman yayi yace.
“Yunus muje ina son muyi magana.”
Dan koda Mamie ta dawo ta gaya mishi abinda ta gani ga kuma abinda yarshi tayi min, mika min Yaron yayi tare da take min sawuna lumshe idanuna nayi kawai.
Bayan fitar uban muma muka dasa hiranmu, wanda muka ki ɗago komi dan yarinyar, tsaki tayi ta fara zagina. Kallo ɗaya Rahilah tayi mata, cikeda ɓacin rai tace.
“Kul idan zakiyi rashin kunyarki kije gidanku idan kuma kika ki zan miki shegen duka,, kuma naga Ubanda yaisa ya rama miki, kema Maryam kika kyale wannan yar aban take miki ɗiban albarka kina matar ubanta.”

“Allah kiyayye daddyna yayi using ɗin wannan karuwar.” Mami da qasu bakinta da suke ɗakinta tare da Rahilah da suke falon duk suka zaro ido waje.
Murmushi yake nayi sannan na mike tare da barin falon, kitchen na nufa nasha ruwa nafito. Mamie da kawayenta sai salati suke suna karawa, fitowa Mamie tayi ta kira Mai wankinsu. Tace.
“Maza kira min Aman.”
…..
“Yunus mi ka ɗauki Maryam har yanzun bata ci darajar iyayenta bane da zaka zauna da ita. Yanzun akan idanunka Yarka take faɗa mata magana babu faɗa balle tsawatarwa.”
. “Ka ga Aman nifa dama bason Maryam nake ba nayi tunani da nazari sai naga ashe kawai sha’awarta nake ji kuma yanzun ina taking drugs Alhamdulillah ai duk matsayinsu ɗaya ne, aurene ya banbantasu da Yaran da na haifa amma ni Maryam bata cikin tsarina dan munyi magana na fahimtar juna dasu Aneesah kuma sun bani shawara, kamata yayi na barta tayita musu aikace aikac..”

Zuciyar Aman ce take bugawa kamar zata fito waje. Sai Sha’ibu mai wanki yace.
“Yallaɓe kazo maza inji Mamie.”
Da sauri suka nufi cikin gidan.
……D’aukar ɗan yaron nayi wanda yake rikici, nasa Hajiya Yabi ta ɗaura minshi a baya na goyeshi ina jijjigashi, Yau gani ɗauke da Yaron Rahilah sai kwalla ke sauka a idanuna, ina ɗan tap ɗinshi har yayi shiru. Ita kuwa mufeeda sai wuliwuli take da idanunta, shigowa su kayi lokacin mi lalle tagama Mamie tq mika mata kuɗinta,

“Lafiya Mamie gamu.”
Nuna mishi Mufeeda tayi tace.
“Haka abokinka ya shahara gurin tarbiya, ku tambayeta mita faɗawa Naryam.”
Kallon Yunus Aman yayi cike da takaici yace.
“Mamie bazan ji mai maici ba, ni ina ganin mi zai hana tunda kece kika musu jagora gidansu Maryam kisashi ya,sake musu Y’a ai babu dole rayuwa tana da zabi wallo kyakyawa ko mummuna, akan mi zaka rike musu Y’a kana cutarwa sai anyi magana kafi kowa shi damuwa watanin baya har zubewa kayi baka da lafiya sabida munce kasaketa mu nemawa yan uwanmu, Yanzun kuma kace tayi yarinya karama. Har shawara kayi da matanka suka ce ka bata aikace aikace ba tsaran aurenka bace, Ka ɗauki Yarka kafita mana a gida Maryam kuma insha Allah gobe zan faɗawa Iyayenta komi, su san halin da take ciki, Ai dama Mami kece kika kaita Zaria,fine gashi nan ta dawo gida. Kuma abinda na fahimta babu Iddarka akanta, Alhamdulillah sakinta baxai gaggara ba.”

Yana gama faɗar haka ya buɗe kofar ta nunawa Yunus da yafitan musu a gida. Kallona Yunus yayi, wanda yake nufin zo mutafi. Shiru nayi narasa makama, “Sunce goyan kibishi.”

Inji Mamie. Jikina nane ya ɗauki rawa, haka na kwance yaron ina kallon, Rahilah da take kuka nima nake shirin kuka,
“Amma Mamie.”
“Barshi ba,damuwa duk yana cikin rayuwar aure.”
Ina sauke yaron mamie ta jani zuwa ɗaki, shiru tayi haka ma yan uwanta sukayi shiru, wani bokiti ta ɗauko da wasu tarkace, Wata Yar uwsnta ta mika min wani Humrah mai suna shu’umar Humra na Ha’uwa’u Jidda Aliyu Usman, wanda ake kawo mata daga Sudan. Ta mika min.
Haka suka haɗa min kayan cass na fito nasiha tayi min ta rakoni har jikin mota,

Aman ya rigashi fita, gidan Ahmad yaje, suka shiga tattaunawa, dariya Ahmad yayi yace.
“Ka rabu da shege gobe zamu mishi final, insha Allah xoka rakani.”

Hmmm ai kuwa tsiya suka kula mishi tun a yau dake gobe idan anyi raɗin suna akwai liyafa na maza.

Koda mamie tazo inda yake tace.
“Kaji tsoron Allah.”

Tana faɗar haka jikinshi yayi sanyi muna fita ya kama min masifa ko ina sai na faɗawa kowa sirrin gidanshine, shiru nayi bance komi ba tunda naji abinda ya faɗawa Aman na gane bana tsarin yunus, kaddara da rabon aure ya kawoni gidanshi..
Koda muka isa gida, na fita da kayana. Shima haka dan bazan je sunar gobe ba, dukda monday ne sunan. D’akina na nufa na zauna, ina mai cigaba da zurfafa tunanina mi yasa Yunus ya rena min matsayina na mace.
Haka na gama lalluɓena ban sami komi ba, dan haka nayi kwanciyarta ban fita ba,

Girkin dare kuwa take away yayi musu, ina kwance ya turo mufeeda da nawa tana zuwa ta wurga min, tayi waje yanda ta jefa min haka ya shigo yasamu, kallona yayi a fusace.
“Abincin ne zaki wulakanta min dake baki san darajar nima ba”
“Ni bansan abinci bane, tana zuwa ta cillamin tayi waje, da ni da ita ai kaman Yarane kaga hankali da nutsuwa bai wadaccemu ba amma kayi hakuri tunda kana da matsayin mijina kuma kaman Ubana kake.”
Sauka nayi kan kujeran nayi na ɗauke abincin. Na ajiye akan center table,

Tsaki yayi ya fita daga ɗakin.
**** Washi gari sai gashi sanye da farar shadda, ya shigo ɗakina lokacin har na gama abin karyawa nazo nayi wanka, na gama shafa humran da Kanwar Mamie ta bani knn, ya shigo uwar ɗakin ya ɗauki kamshi humran kallona yayi cikin riga da wando pakistan blue black, mai ratsin whiter flower sai stone, fuskana babu make up kwali na saka kawai, kallona yayi tare da diriri cewa, sabida karfin kamshin humran ɗin, ciki ciki yace min.
“Zan tafi liyafa kika ce baki zuwa sunan ko”
“Eh.” nace mishi,

Yana sauka ya samu Fareeda zata Abuja, maganar kayanta da aka kawo ta can, sai Aneesah da ta sakalo. Jakar aikinta yarama sun fita, Hamshakiya Balkisu tana ɗakinta.

Kwanciya nayi dogon kujeran falona dan nagama da komina hutawa kawai zanyi.

****
An raɗa sunan Yaro da Mahmud Aman Mandara, a masalacin unguwar sai walimar da Angon karni ya shirya wnda su uku sukayi shiga ɗaya,, anci an gyatse, tsakanin Aman da Ahmad akwai mugun kuli, dan dariya suke kawai.

Tunda aka gama walimar a kamfaninsu mutane suka watse Mai nasara ya zuɓe a kujera, jinshi yake a takure baki ɗaya, kallon agogon office ɗin yayi yaga karfe goma da hansin da bakwai, kwanciya yayi, yasaka hularshi Kan fuskarshi yana me ɓoye halin da yake ciki.
Su kuwa sukayi biris dashi, har kusan sha biyu, da ya ga abin na iya shafar lafiyarshi sai ya mike cikin dauriya yace.
“Guys bari naje gida kaina na ciwo.”
“Toh Allah ya sauwaka,” Inji Ahmad dan har lokacin fushi Aman yake dashi.

Fita yayi cikik rashin kuzari ya fita,

…….Ina fama haɗa abincin rana, naji dirin motarshi, har shigowarshi gidan, ɗakin balkisu ya nufa nan ya zube akan gadonta tare da zuba mata ido, matsawa yayi jikinta ta wani zabura tace.
“Wai Lafiyarka Yunus nifa bazan iya da matsalarka ba, kaje kayi hakuri yanda kasa ba plss am not in mood.”

Zaro ido yayi cikin damuwa kafin ya karya wuya ya shiga rokonta, Allah da Annabi amma fir taki gashi yanayinda yake ciki kara tu’azara yake, cikin masifa yace.
“Zina kuke son na fara ko mi? Ni da hakkina sai nazo ina rokonku, Kee nazo gurinki sukuma sauran basa nan gurin wa zanje.”

“Oho dai ni kan bana ma Sallah kaje inda kasan zaka samu amma ba dai nan ba.”

Takaicine ya kusan sanyashi fasa ihu haka ya sauko daga sama ko kallon gabanshi bayayi, ina tsaye na kure Mp 3 wanda yake ɗauke da Karatun alkur’ani,

Ina bitan suratun nisa’i, tsayawa yayi yana kallona cike da sabon tashin hankali, “Maryam Sajida.”
A tsorace na juya da cewa.
“Na’am!!!”

Iska ya fesar tare da juyawa yace.
“Ki same ni a ɗakina.”
“Wayyo Allah ni Maryama mi kuma nayi mishi.” na faɗa,

Kashe wutar girkin nayi na wucce dakinshi, tsayawa nayi a bakin kofa, tare da jan zuciya na murɗa hannun kofar na shiga ɗakin, na tsaya a bakin kofar ina jin saukar ruwa, tuna lokacin da nake shigowa ɗakin domin yin gyaran cikinsu yanzun kƴwa ɗakin ya koma Matattaran datti, tsince kayashi nayi na kasa, na gyara kasan fitowa nayi na ɗauki tsintsiya da parker na koma na shiga sharewa, ina cikin sharan yana fitowa daga ban ɗakin, ɗaure da towel.
Sunkuyar da kaina nayi na cigaba da aikina, ga baki ɗaya tsigar jikinshi mikewa yake, wai a hakan yaki yake da zuciyarshi dan kar ya kaishi inda zai baroshi.
Har ta inda yake na share, na fitar waje zuwa korido ina faman haɗa, sharan sai ji nayi anyi sama dani, ihu na kwala, tsabar tsoro dan bansan mi nayi mishi ba, abu ɗaya kawai yake ji yasami nutsuwa ko wacce irice ya rabuda abinda ke damunshi.

Gadon ɗakinshi ya kaini, ya ajiye ni, tare da rufa min, a tsorace na mike ya maidani ya tara min karfinshi, ada can ai ba haka yake min ba tunda yana ɓata lokacinshi gurin taɓe taɓe, yau kuma babu haka shi kawai abinda zai fiaheshi yake nima, ni kuma, na gaza fahimtar haka na shuga kokarin kwace kaina………. Heyyyy Ku cixan ta inda Zan warke…….

*Alhamdulillah na gama Book 1 Yau tohfa Anya Maryam Zata kawo gyara Gidan Yunus? Shin Mi yake shirin faruwa ga Tsarin Yunus na aqidarshi? Ya Gidan Aman Tsakanin Hindu da Rahilah? shin wani irin zama suke? Ya zata bar kazamta da hidimar social media ta rungumi mijinta kamar Rahila? Ya batun Ahmad da Hafsa tunda yace bazai saketa ba ba shin zata saduda a zauna lafiya da ita? Ya batun ɗabi’ar Mufeeda, shin taya mai nasara zai tankwas mufeeda*

Back to top button