Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 24

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to MAMAN TEDDY channel @youtube.
24.
Ya Khalil nifa ƙaramar yarinyace kai ne fa naji kana yi ma Anti Jidder faɗa kan karta fara soyayya! “Yesss”Na sani Ma’eesha, amma tawa soyayyar ba shiririta bane irin nasu . I really……A’a Ya Khalil Anty Maryam fa? Kwanan fa Za’a yi baikon ku . Muryar Ma’eesha ya kuma katse ta wanda har kyarma jikin ta ke yi . Ma’eesha!!! Ya kira sunan ta cikin wani irin Murya wanda bata taɓa jin sa da irin ta ba . Hummmm …. Furzar da Huci yayi kana yace “ Ma’eesha Ni SOJA ne , duk Abinda zai saka Soja ya gurfanar da kan sa da Gwiwowin sa ƙasa ba ƙaramin abu bane ba , babba ne , wanda girmanta ya kai Akira wannan abun da rayuwar sa . Ma’eesha idan na rasaki numfashi na zai dakata da Aiki . Ina nufin zan zaɓi mutuwa da Rayuwa ta”. Dam-dam-dammmm ƙirjin Ta ya buga da ƙarfi ….cikin Muryar matsanancin kuka ta furta “ Sorry Ya Khalil ina Sonka”. Wani irin baya Aliyu yayi da yake jikin ƙofan yana zame hannun sa a hankali duhu duhu na gilma ma idanun sa . Ji yayi jikin sa yayi Wani irin mugun sanyi sam babu ƙarfi a tare dashi bisa ga jin Furucin Ma’eesha na “ Ina Sonka!”. Zazzaƙar Muryar ta ne ya kuma katse shi tana faɗin “ Kar kayi tunanin bana sonka Ya Khalil kome kace nayi maka a shirye nake zan maka shi ”.

“ Cikin Sauri cike da jin Daɗi mara iyaka Khalil ya miƙe daga gurfanen da yake , Hannun sa biyu yasa yana tallabo kuncinta ta tare da saita idanun sa yana Ɗaurawa bisa nata. “Thankyou Ma’eesha , na gode!

Ya Khalil to Anty Maryam fa? Da…..shii ki manta da Wannan maganan zan Auri Maryam a wannan shekarar ke kuma zan cigaba da dakon soyayyar ki har ki girma ki kai lokacin da Daddy zai Aurar dake , A wannan lokacin zamuyi Aure mu gina Rayuwar mu cikin jin daɗi . Kece nake so ki haifa mun ƴaƴa masu kama dake ….ya ƙare maganan yana Ɗaga mata gira tare da Sakin mata murmushi kana ya cigaba da cewa “ Zan Auri Maryam ,amma ba zata haihu ba . Kece zan jira ki zo ki haifa mun masu Albarka ”.

Cike da Yarinta Ma’eesha ta gyaɗa masa kai tare da cewa “ Shikenan Ya Khalil zan yi barci yanzu ”. Alright sweat dream…ya furta yana kama ta tare da nufar Bed ɗin ta sai da ta kwanta sannan ya rufa mata bargo yana takawa tare da rage hasken fitilun Bedroom din yana nufar Ƙofar fita .

Jin takon sa yasa Ali Haidar Saurin barin wurin yana nufa falo .

A wannan dare a taƙaice sam Aliyu ya gaxa rintsawa , zuciyar sa na masa saƙa da Warwara . Inda ya kasa gasgata wani ɓangare ɗaya na Zuciyar sa . Sai dai kafewa da yayi akan cewa “ Khalil na son lalata Ma’eesha ne . Har ya fara tunanin ɗaukar mataki da fushin Zuciyar sa ,sai kuma yace “ A’a ba haka zan yi ba , Ni yanzu da zan tafi tare da ita , ganin ta sai yayi masu duka wuya .bare har ya kawo wani zancen shashanci mtsww .

**
7:35am.
Mami na hango gaban dressing mirror tana gyara gashin kan Ma’eesha da yake fidda Sanyayyar ƙamshi , ga tsawo da cika sunan ta kama mata shi ne wuri ɗaya amma Tudunshi har yayi yawa gashi ya sauko har gadon baya . Ka rantse da Allah Jinin mami ce itama wato fulani . Riga da Wando ne ta jikin ta ,irin suit masu kyau na mata . Sai mami ta ɗaura mata Hijab ƴar ƙarama wanda bai ƙare sauka kafaɗa ba ”. Turare take sa mata tana murmushi tare da cewa “ Yau sai na Lagos . Yessss Mami Ma’eesha tayi maganan tana Wangale mata baki cike da fara’a kaman mai jin daɗin tafiyar ,nan kuwa dole ne yasa ta murmushin . Gyara mata fuska tayi cikin simple make Up Babu Hayaniya. I love my daughter …..Ina sonki Nima Mami ”. Hannu Mami tasa tana rungume Ma’eesha tare da cewa “ ki kula sosai kinji Eaasha na?”…………!

**
Dinning room
Tun da Aliyu da Khalil suka zauna babu abin da suke yi ma juna face auna ma juna kallon banza . Duk da shi Khalil na kai Zuciyar sa nesa . Sannan duk abin da suke yi babu wanda ya gane daga gare su .

Keeee Da Allah kici a hankali ….kaman Ƴar matsiyata wanda suka fito da ga fari? . Muryar jidder ya katse su inda take doka mawa ma’eesha Tsawa cikin Faɗa da hantara . A hankali Ma’eesha ta janye Fork ɗin da take cin Irish tana Ajewa a gyefe….inda cikin Faɗa Mami ta katse jidder da cewa “ Akan ki take ne? Masifaffiyar banza kawai , Ai sauri take kada Ali ya fara Mata nashi sababin…..ku kiyaye ni duka ”.

Gummm Jidder tayi tana cigaba da Kai Cuscus bakin ta , ranta a ɓace don bata son tayi ma Ma’eesha faɗa Mami ko Daddy su katse ta .

Muryar General Saleh ne ta katse su inda yake furta “ Kici a hankali Ma’eesha ba zaki bishi ba sai kin ƙoshi kinyi nakkkk sannan .

Gyaɗa masa kai tayi kana ya cigaba da cewa “ Kai kuma Ali ina so nan da 1 mount to 2 mount kafin bikin Khalil ka fidda wacce kake so ka Aura yanda muna gama nashi sai naka . Saboda dukan ku kun isa aje iyali kuna da Abunyi da ƙarfin ku haka da Arziƙin ku ka fahimce ni?.

Shiru Haidar yayi na yan sakanni don a yanzu shi babu lissafin aure a rayuwar sa , a cewar sa Abin da ake yi ma Auren yana Samun na bati a banza a waje . Kuɗin sa nayi masa komai don haka baya sha’awar aure a yanzu .

Aliyu da kai nake yi …..Muryar Daddy ya katse shi inda cikin sauri Aliyu ya furta “ Okay Daddy inshallah kamin lokacin ma , Abun da yasa har yanzu kuka ji shiru saboda Ni ina so na Auri SOJA ce . Ma’ana matar da zan Aura ta kasace SOJA kama na ” .

SOJA…!!!!

Duka suka haɗa baki wurin furta kalmar ciki har da Daddy da abun bai masa ba sam . Ita kuwa Mami buɗan bakin ta cewa tayi “ wow that’s very good, Hakan yayi sosai Haidar Nima zan so ganin hakan . Ai hadin yayi ko Janar? . Ta ƙare Maganan tana duban inda Daddy yake ya saki baki yana kallon ta .

Kamin Daddy yayi magana ne Khalil ya amshe da cewa “ No Mami Sam baiyi ba . Ni fa babu Abin da na tsana irin naga mace wai SOJA abun ba burgewa sam .

Hahahaha!
Wani irin dariya Aliyu yasa wanda duka sai da suka tsaya suna binsa da kallo . Kana ya tsagaita yana kallon Khalil tare da cewa “ I found the solution, Ma’eesha taho mu wuce ”.

Cikin Sauri Ma’eesha ta miƙe tana ma su Mami waving tare da furta “ Dad Byebye! Mami anti jidder sai na dawo ”. Banza jidder tayi mata a haka ita dai ta wuce Daddy suna biyo bayan su har farfajiyar gidan sai da suka fice daga gidan ne sannan suka koma ciki ” .

Kaduna ya ɗau hanyar nufa inda tun shigar ta tayi shiru ta koma kamar marainiya .

Aammm Ma’eesha me kike son ki karanta nan gaba? .

Muryar Aliyu ya katse ta inda cikin sauri ta kalli inda yake , amma sam idanun sa baya ma akan ta . Cikin sakin fara’a irin nata ta furta “ I want to be a nurse ”. Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa na kan hanya cikin bada umarni ya furta “ Ba zakiyi ba , SOJA zaki zama wannan tafiyar da zamuyi za’a fara baki horon atisayen zama soja……………………!

*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya Ni ba . Gama su buƙatar wannan littafin regular group suna biyan ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.©Maman-teddy….. YouTube channel@MAMAN TEDDY.* *https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS*

Back to top button