Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 23

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

23

Barkan mu da dawowa wannan tafiya da muka ɗan jinkirta wurin kawo maku shi ,hakan ya faru ne Sakamakon ɗan rashin lafiya da nayi ,amma yanzu jiki alhmdlh komai normal ina sauraren sharhin ku tare da fatan Alheri ina kuma godiya sosai . Taku Ayshatu Mrs Usm…(Maman-teddy).

*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya kudin littafin ba . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 yan Niger katin Artel zaku tura na 500f*

Wani irin zafi Zuciyar Aliyu keyi ganin yanda Khalil yasa hannayen sa biyu yana rungume Ma’eesha cike da kulawa . A hankali Zuciyar sa ta fara tambayar sa da “ Me yasa kake jin zafi a duk lokacin da kaga Ma’eesha da Wani ɗa namiji bayan kai koda kuwa jinin ka ne? . Ɗan lumshe dulu-dulun idanun sa yayi yana ba kansa amsa da cewa “ Saboda ina son kare mutuncinta ne ,don babu wanda yasan darajarta da ya wuce Ni . Su duka sauran ganin ta suke kamar kowacce ƴa , Ni kuma a jinin jiki na ke jin ta . Wannan shine banbancina da su . Shi kuma yasa nake jin zafi a duk lokacin da na ganta tare da Wasu maza . Saboda maza basu da tabbas.

Ma’eesha ya kamata kiyi barci yau da Wuri kar gobe kiyi mun barcin mota . Don NDA zamu fara zuwa daga can mu wuce Aviation .

Muryar Aliyu ya katse su , yana mai zuba idanun sa zuwa inda Ma’eesha take zaune a jikin Khalil suna magana ƙasa ƙasa wanda babu mai jiyo su . Wato yarinyar nan har Tasan ta rinƙa irin wannan maganan amma bata iya girki ba? Zata sani ne? Duk wani kalan girki sai kin iya shi haka Aikin cikin gida , don ko Bedroom baki iya gyaran shi ba . Wannan ɗabi’un naki duka basu yi mun ba dole na sauyaki zuwa yanda nake SO .

Duka maganan yake a zuciyar sa , yana yi yana ɗaura yatsunsa bisa pillows din dake Daga saman Cushine ɗin da yake zaune ,yana matsasu ji yake tamkar bakin Ma’eesha yake matsawa da ƙarfi haka don ya ɗau Aniyar ganin ya saita ta yanda yake So, don a ganin sa Sangarta ta Mami tayi ba tarbiyya ta bata ba . Muryar Mami ne ya katse su inda take cewa “ my baby A tashi haka nan , nasan ki da son barci kinji tun yanzu sharuɗan da ya fara yi Miki . Nifa Ali indai wannan tafiyar taka da Ma’eesha da takura wahalar mun da ƴarinya zaka yi Tom a haƙura , Nima ba SO nake nayi nisa da ita ba ” . Mami ta ƙare maganan tare da Watsa ma Haidar kallon uku saura ƙwata .

Cike da Ƙwantar da kai da murya Ya furta “ Mami please ki daina tunanin komai fa , Ma’eesha tawace! ….gigif Khalil yayi yana miƙewa daga kishingiɗen da yake bisa ga jin Furucin Ali Haidar …Muryar Aliyu ne ya cigaba da cewa “ Ba zan Wahalar Miki da ita ba , cool your mind please ” . Hummmm … Mami ta sauke wani gauron numfashi kana tace “ Alright ga Amanata nann” . Uhmm Mami kenan . Nifa mamaki kike bani wallahi …Haidar ne zaki ba Ma’eesha wai kuma kike tunanin ba zai wahalar da ita ba? Ai kima bar wannan tunanin Allah dai ya bata ikon cinye jarabawa ”.

Dariyar Mugunta ne ya kusa kama Jidder don ita a rayuwar ta bata da Burin da ya wuce Taga Ma’eesha cikin mawuyacin hali . Amma sai ta dake tana cigaba da latsa Wayar ta tare da karƙaɗa ƙafa ɗaya .

Buɗe baki Mami tayi tana shirin magana Muryar General Saleh Yelwa ya katsesu da cewa “ Ya kamata yanzu fa kusan kun girma haka nan. Khalil Haidar , wai yaushe saɓani ya fara shiga tsakanin ku? Ƙwata² babu jituwa kaman ba kaine Ali haidar mai tausayin Yayan ka ba . Mai kuma haƙuri da masa biyayya….Kai kuma Khalil kamar ba kaine babban Yaya ba , Wanda koda ya ɓata maka kake dannewa Bama kason mu sani . Please ku cigaba da yanda kuke a da baya . Abun naku yana neman zama sakarci kuma na rasa gane menene ya kawo maku wannan rikicin haka!

Tsit…!!
Falourn yayi har Daddy yayi maganan sa ya gama , sai Muryar Mami da ta furta “ Suma dai yi , Ni nawa ido , zasu daina ,abin da basuyi farkon shi ba ai baxasu yi ƙarshen sa ba. Ma’eesha na taho muje kiyi barci .

“Da sauri Ma’eesha ta miƙe tana kallon Mami kana ta saki Murmushin nan nata tana cewa “ No mami zan ƙwanta ba sai kinzo ba . Wankan kuma fa? .

Muryar mami ya katse ta , wanda jin haka yasa ta saurin juyawa tana kallon inda Ali Haidar yake , gabanta na bugun uku² , a Zuciyar ta tana cewa “ Na shiga uku kar Fa Uncle yace Har Wankan ma ban iya ba naja ma kaina ”. Shagwaɓe fuska Ma’eesha tayi tana cuno ɗan mitsulun bakin ta tare da cewa “ Mami nifa ba kya mun wanka tuntuni Ni nake yin abu na ”. Dariya Daddy da mami suka saka harda Khalil …..Wannan yasa Ma’eesha juyawa tana barin falourn , Don sun fahimci Ma’eesha ba son zancen wanka take yi ba a gaban su Khalil da Haidar .

Kaman mintuna biyu Khalil ji yake tamkar ana tsingulunsa , Abubuwa da yawa na cunkushe a cikin Zuciyar sa . A hankali yakai hannun sa yana dafe ɓarayi guda na Zuciyar sa kana ya rintse idanun sa …. lokaci guda Idanun sa sun sauya kala sunyi jah….miƙewa yayi yana kallon Su mami kana yace “ Ammmm Bara na duba Ma’eesha ta ƙwanta kuwa! . Uhmmmm aifa duba mun ita , don kwana biyu bata barci sai Game a laptop ɗinta tun da suka samu Hutu itama take Hutawa abinta. Mami tayi maganan tana bin bayan Khalil da kallo don tuni ya nufi hanyar da zai kaishi zuwa Bedroom ɗin Ma’eesha ”.

Ɓangaren Aliyu kuwa tun da Khalil ya miƙe yaji jikin sa bai basa ba , wannan yasa shi Oga ne bai tsaya yi ma kowa magana ba yayi gaba yana nufar Bedroom ɗin kansa tsaye.

Hannun sa yasa a Handle Door din yana ƙoƙarin murɗawa yaji furucin Khalil daga ciki wanda sai da Ƙirjin sa ya buga da ƙarfi . Wannan yasa shi dakatawa yana Sauraren kalaman Ma’eesha ”.

Ya Khalil Menene? Meke faruwa ya Khalil? Tana maganan Muryar ta na rawa alamun kuka ….Muryar ta ne ya cigaba da Amon cewa “ Ya Khalil ƙwallah ne fa nagani ko nace hawaye a ƙwance a idanunka . Hummmmmmmm Jan Ajiyar zuciya yayi yana saukewa kana yace “ Yessss Ma’eesha hawaye ne wannan sannan kar kiyi mamakin ganin su” .

Ya Khalil menene ya saka ka kuka? Mene ya faru? Kukan……Shiiiii ɗaura yatsarsa yayi bisa laɓɓanta yana katse zancen nata kana yace “ Sorry dear Kece kike saka zuciyata wannan kukan tuntuni wanda a yanzu ta kasa daurewa da jurewa har idanuna sun fara zubda Ƙwallah ” .

Jikin ma’eesha ne ya hau Rawa , ƙwallah na ciko idanun ta . Cikin kuka ta fara furta “ Ya Khalil me nayi maka Ni? Ka faɗa mun na baka haƙuri ”.

Numfasawa yayi kana cikin wani irin sarƙaƙƙiyar murya ya furta “ I love You Ma’eesha…. Nasani ya Khalil nasan kana so na , nima ina Sonka. No! Ba Wannan soyayyar ba. Son ki nake Don Allah Ki Aure Ni mu rayu tare A matsayin miji da mata yayi maganan yana zubewa Gwiwowin sa ƙasa a gaban ta . Wani irin bugawa ƙirjin ma’eesha keyi ….cikin Muryar kuka ta furta…………………….!

 

 

*Ban yarda ki karanta mun wannan labarin ba tare da kin biyani ba . Don Allah kar a soma ayi hakan . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 ƴan niger katin Artel 500f zaku turo.*

Back to top button