Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 22

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

22
*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya kudin littafin ba . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 yan Niger katin Artel zaku tura na 500f*

Tana cikin Bedroom dina….yayi Maganan hankalin sa ƙwance tamkar bai yi wani Abu ba . Baya Mami da ƙafarta da take shirin bin wata hanya da ban tana juyowa a fusace tare da jifan sa da Wani irin kallo , sai kuma ta nufi hanyar Bedroom din nasa cikin sauri tana kiran Sunan Ma’eesha ”. Dariya ne ya kusa kama shi ganin yanda duka mami ta ruɗe tamkar wanda yayi ma Ma’eesha wani mugun horo , gashi daga can Ma’eesha sai ƙwaɗa kiran Mami take itama mami na kiran sunan ta. “Mtswwww”. Jidder ta ja wani dogon tsaki tana hararan ɓangaren da take jiyo Ihun Ma’eesha kana tace “ Shashancin Banza da wofi ɗan riƙo yafi Ɗan gida . Yanda Mami ke kulawa da Wannan yarinyar dukan mu yayan ta bata kulawa damu haka ”. Duk maganan da take yi Aliyu zuba mata ido yayi fuskar sa yana nan yanda yake baka fahimtar cikin sa bare ka gane meyake nufi .

Motsin tahowar Mami yasa su duka kallon direction ɗin nasu . Rungume take da Ma’eesha da gaba ɗaya ta narke a jikin ta , ƙafarta kuwa Ɗingisa ta take yi fuskar Ma’eesha duka ya kacame da Hawaye , kumatunta har girma suka ƙara suɓu-suɓu gashi sunyi jah na tsaban dirjan hawaye . Wallahi Ali duk abun da kake yi kanka kake mawa! Sannan nasha faɗa maka ka daina kula mun Ma’eesha babu ruwan ka da ita , tun da baka da imani gaba ɗaya ka zama irin mugayen sojojin nan wanda basa tausaya ma mata ko kaɗan suna ma mata kallon maza ne . Wallahi har tausaya mawa matar ka nake Haidar don zata axabtu.

Kalli kalli yanda a yini ɗaya ka sukurkuta mun yarinya ka fitar mun ita daga Hayyacin ta . Aliyu Are You out of your mind? Baka da hankali ne ? She is small baby girl kawai saurin girma tayi?. Kallon Ma’eesha Aliyu yayi yana bin ta da wani irin kallon ƙasa-ƙasa kana yace “ Mami I’m sorry, raina ne ya ɓaci da lamarin Ma’eesha, Mami ko fa girki bata iya ba . Nasata tayi mun indomie kin ga Haukar da tayi mun wai ta kawo mun tana tunanin na iya cin sa . Ai Ya Aliyu sam ba laifin ta bane ba , Baka ji mene Mami ke cewa yanzu ba? She’s small baby girl means all what she did wrong bata isa hukunci ba , babu mai hukunta ta tun da ƙaramar yarinya ce , to Mami yaushe zata girma don Allah kullum Kice yarinya ce yarinya ce ….aaaaa haba ! Shiyasa take tsiyar da take so . Har takai ma idan tayi laifi ita da kanta cewa take wai saurin girma tayi ayi haƙuri ….Mami ne ta katse Jidder ta hanyar ɗaga mata hannu kana tace “ Ba karamar yarinyar Bace hala shekarun ku ɗaya ne da ita ? Kin ba Ma’eesha kyawawan shekaru takwas ko ma nace fiye , don haka ku kama kan ku babu ruwan ku da yarinya ta. Aiki kuma daga yau na cire maku kusa mun ita bare har tayi ɓarna kuce tace maku ita yarinya yanzu kowa ya samata ido . Nafi san haka kawai .

Kai kuma Ali kar ka ƙara saka mun yarinya knee down har ƙafafunta su kumbura irin haka! Fatan ka jini da kyau?. Gyaɗa kai yayi tare da cewa “ Yess mami ”. Juyawa tayi tana dafa Ma’eesha tare da cewa “ Lets go baby”. Fuska a narke don har a lokacin kuka take yi sosai don ƙafarta zugi yake mata zugin da bata taɓa jin irin sa ba .

Mami anya babu kuskure anan? Muryar jidder ya katse su tana kwantar da murya a makirce kana ta cigaba da cewa “ Common thing indomie Ma’eesha Bata iya girkawa ba ,aƙwai matsala fa a ƙasa ”. Aure zan mata! Nace Aure zan yi mata da zan damu ta iya indomie ko bata iya ba . Bare yanzu fa take ɗagawa wannan duk mai sauƙine nasan zata iya nan gaba .

Muryar Haidar ne ya katse su yana saƙo da maganar sa cikin hikima da dabara “ eh zata iya don datayi na farkon baiyi dadi amma na biyu yayi daɗi sosai kamar kar ya ƙare. Shiyasa ma nake so gobe mu tafi Lagos tare tayi hutun ta Acan.

Buɗe baki Mami tayi tana waro manyan idanun ta wanda Aliyu ya ɗebo su waje kana tace“ Wannan dai yarinyar tawa Ma’eesha ce zan baka ita Ali ka tafi da ita kake nufi? ”. Kallon Mami yayi yana gyaɗa mata kai Alamun eh jikin sa yana dan sanyi don dama yasan za’a kai ruwa rana wurin Amincewar Wannan tafiyar nasa da Ma’eesha ”…To baka isa ba, Ba zan yarda da Wannan tafiyar ba . Mami ita ce take so , Ma’eesha bakya so mu tafi tare ? Yayi maganan yana sauke Muryar sa tamkar ba shine mai bata horon nan ba ”.

Ɗago da ido Ma’eesha tayi tana kallon Mami kana ta kalle shi tsoron gargaɗin da yayi mata ne ya dawo mata ka….Wannan yasa ta gyaɗa kai hawaye na kwanciya a idanun ta kana tace “ Mami ina so zan bi Uncle ”. Nasan zai kula dani sosai ’. Hummmmmmmm ….. Numfasawa Mami tayi kana ta rungume Ma’eesha tsammm tana furta “ Allah sarki Aiiiii na . A’isha na Ma’eesha . Yau zamu fara shiri ,amma yanzu zan fara gasa ƙafarki ne ya saki sai kiyi barci gobe sai ayi shirin tafiya da Uncle . Aliyu…..!!! Mami ta kira sunan sa har sau uku kana tace “ Ka kula da Ma’eesha tana budadden zuciya tana jin ka sosai a ranta da zuciyar ta . Ma’eesha ƙanwa ce a gare ka .

“Ohhh Mami ” ki daina faɗin haka , Ma’eesha ba ƙanwata Bace mami nine fa Aliyu , Ai Ma’eesha ƴa ce a gare Ni . Wanda na ɗauke ta da hannu na kuma na Raine ta . Mashaallh Uban san girma , na baka Ma’eesha a yanzu ma …. Ma’eesha na! Ta kira sunan ma’eesha da ta zuba mata lumsassun idanun ta kamin tace “ Na’ma Mami”.

Kin shirya Uncle Haidar ya ƙara Miki RAINON SOJA a karo na biyu?. Zai kula dake sosai ina da yarda dashi da amincewa da zai kula mun dake . Cike da Yarinta ta saki Murmushi tana gyaɗa kan ta tace da cewa “ Eh mami nasan Uncle zai kula dani sosai . Muje fara shirin tafiya nidai kam sai da ɗan hawaye ya tsillo daga ido na don na tausaya ma Ma’eesha a hannun Ali haidar a wannan karon ”.

Tana Rungume a jikin mami suka nufi bedroom din ta suna barin falon . Jidder taso hana wannan tafiyar amma kuma bata da yanda zatayi saboda Tafi son taga ta raba Mami da Ma’eesha kamin ta dawo ta ɓanɓareta ta da Haidar,amma ita har a yau so take taga Ta bude ido Ma’eesha ta bar cikin gidan .
**
7:00pm.
Zaune suke duka a falon Daddy kowa da Abin da yake yi. Ma’eesha na gani daga ƙasa inda Ƙafar Daddy yake tana rungume da yar teddy din ta Pink mai kyau tana murmushi alamun Daddy wani maganan yake faɗa mata . Ɗagowa tayi tana kallon Khalil da shima ita yake kallo . Sosai yake tsintar kansa cikin yanayin jin daɗi a duk lokacin da yaga murmushi a tare da Ma’eesha ”. Ya Khalil i will miss you ”. Ta furta tana kallon sa . Murmushi yayi yana danne abun dake taso mata kamin yace “ i will miss you too Ma’eesha na”…Da Sauri Ma’eesha ta miƙe tana nufar inda Khalil yake tare da rungume shi…. Rungume ta yayi yana murmushi tare da cewa “nan kusa zaki dawo ai . Wani irin zafi Aliyu…………….!

 

 

*Ban yarda ki karanta mun baki biyani ba . Wanda ya karanta shi da Allah . Masu ɓukatar regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank*

Back to top button