Ikraam 84
By Khaleesat Haiydar 84….. Da safe karfe tara saura Ikram na xaune dakin Mami tana rike da Sudais da Mami ta hada ta da tun shigowarta dakin don gaisheta, danne xuciyarta kawae take tana rike da yaron don ji take kmr ta jefar da shi, gashi sae dalala mata yawu yake a jiki wae yana wasa, duk ta wani hade rae tana kallon wani movie da ake a TV, Mami nata harkar gabanta, har Aliyu ya shigo dakin gaida Mami, Ikram bata ko kalli inda yake ba har ya fita daga dakin, Mami ta juya tana kallonta a fusace ta fara mgna “Ikram wnn ba hali me kyau bne kike tsiro kwanan nn, wae ke wace irin yarinya ce ma dae tukunna” shigowar Khaleel yasa Mami ta juya ta ci gaba da abinda take, ya duka kusa da Sudais yana masa wasa yaron sae murmushi yake alamar yana son fara dariya, shi dae yana son yaron ssae gashi sak Babansa, ya daga kai yana kallon Ikram da ta dauke kanta fuskarta a daure tana kallo, yyi murmushi yace “kuna kama da yaron naki ssae” kmr xata yi kuka ta juya da sauri tana kallon Mami ta ga ko tana kallonta kafin ta fara masa masifa, ta ga kallonta kuwa take, hkn ya hanata cewa komai, ya nemi gefen gado ya xauna yana murmushi, mikewa Ikram tayi ta fice daga dakin rike da Sudais, Khaleel yace “Mami xan je Bauchi may b xuwa gobe” Mami ta juya tana kallonsa na kusan Minti biyar shi ko idonsa na kan TV, can ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, bayan kmr minti uku ba tare da ta kallesa ba tace “me xaka je yi a Bauchi?” juyowa yyi yana kallonta yyi shiru bae ce komai ba, jin shirun da yyi yasa ta juya tana kallonsa, ganin kallonta yake yasa ta dauke kai tace “to Allah ya kiyaye Khaleel, amma da Ikram xa ku tafi tunda anyi hutu ko” yace “A’a ba da ita xa ni ba, ae ba dde wa xanyi ba” Mami tace “sbda me? Ae basu san ta ba, don hka dole da ita xaka tafi” ya dan marairaice mata yace “Mami wllh kwana biyu fa kawae xanyi in dawo, ki bari kafin a kare holiday din xan kai ta su ganta, but 4 now ni ba dadewa xanyi ba, kuma ae can gun Amminta tace xata tayi holiday……” Mami ta dakatar da shi ta hanyar masa mugun kallo tace “ban amince da hkn ba, ku shirya ku tafi tare, idan kun dawo sae taje gidan” shiru yyi yana kallonta, daga gani kasan ko kadan bae ji ddin hkn ba, ya mike ba tare da ya kalleta ba yace “to” snn ya fice daga dakin ta bi sa da harara. Da yammacin ranar Aliyu suka bar gidan bayan Mami ta cika Rukayya da Sudais da tsaraba, kiri kiri Ikram ta ki fitowa yi masu sallama, sau uku Mami na kwala mata kira duk tana ji taki sakkowa, sae dae tana jikin window a sama tana kallonsu, har suka bar gidan snn ta sulale kasa ta shiga rera kuka a hankali. Washegari da safe Mami da kanta ta shiga hada ma Ikram kayan sawan ta, Khaleel na xaune dakin yana kallonta, Ikram ko na downstairs dakin Jummai, Mami tace “kai ka gama hada naka kayan ne” ya kauda kansa yace “ni fa kwana biyu nace maki xanyi Mami, sae tula mata kaya kike” Mami ta tsaya kallonsa tace “kaya kala biyar din ne na tula mata, ni fa ban son wlknci, in har baxa ka tafi da Ikram ba to kai ma bbu inda xa ka, don ban ga amfanin xuwan na ka ba” Khaleel ya juya yana kallonta yace “haba Mami xuwa gun yan uwan Mahaifina ne ba shi da Amfani don ban je da Ikram ba” Mami tayi masa mugun kallo tace “to gaya min magana Khaleel” sunkuyar da kansa yyi bae kuma cewa komai ba, Mami tayi kwafa ta dauki wayarta da ke kara ta daga don amsa kiran, Ikram ta shigo dakin Khaleel ya bi ta da harara, bata ma san yana yi ba, ya mike ya fice daga dakin, karfe tara na safiya Khaleel ya shigo dakin Mami yace ya shirya Ikram yake jira, kiri kiri Ikram tace ita bbu inda xata da Mami tace ta shirya xa su yi tafiya da Khaleel, sae da Mami ta bata mata rae snn tana hawaye ta shiga wanka, ko da ta fito Mami bata dakin sae shi, ta dauki kayanta fuskarta a daure ta nufi bathroom xata sa, ya bita da kallo har ta shiga ta rufe kofar, yyi wani irin murmushi hade da kwafa yana gyada kansa ya mike ya fice daga dakin.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar