Auren Gado 59-60
……………. Ita kanta ta san ya isowa tunbai karaso ba, don haka tuni ta Kara hade fuskar ta tamau domin tayi mugun daukar fushi dashi, tuni ya ji wata natsuwa ta ziyarci zuciyar shi, cikin takun kasaita ya shigo, hade da sallama kasa kasa idanun shi a sama, domin ba Abinda yake buri sama da yayi ido biyu da ita, yayi matukar kewar ta, sai jera Ajiyar zuciya yakeyi tunda ya sauke idanun shi akanta, gangar jikin shi tuni ta amsa gayyatar ganin ta da tayi tank God ma manyan kayane a jikinshi, a bu biyu yanzu zai hanamai rungume ta ya rafe zafi, nafarko Aunty Raliya na biyu momy, don haka ya saita kanshi yayi gyaran murya, tareda gaida Aunty, tamai ya gajiyar hanya da mai jiki, ya Amsa cikeda jin kunyar ta.
Kafin ya matsa gab da gadon, taki ko dago kanta sai bawa momy kunun take tana gogewa, he wants to touch her amma no way, don haka ya waske yana fisgo maganar “momy sannu. Ido ta juyamai Alamar amsawa, fita Aunty Raliya tayi domin amsa waya, yayi Ajiyar zuciya yayi saurin riko hannun ta batareda damuwa da idanun momy ba saboda he can’t help it, tayi saurin dago kyawawan idanun ta masu rikita shi tace ” meye haka agaban momy please stop. Tafada tana karkata kanta, ” why kika ki tafiya gidanki kikatafi na Aunty Raliya? Hannun ta take kokarin kwacewa amma takasa don rai ita tasan kunya, momy Naji Nagani wani irin dadi takeji y’an da yarinyar ta nuna mata kulawa ga kuma Alkunya da zata iya mikewa itama zata basu wuri su zanta da junan su, Amma ko yanzu abun mugun faranta mata rai yakeyi har ya nuna a fuskar ta, “let me go please. Tafada” I want sai kin fada min dalilin da kika tafi gidan Aunty kuma nakiraki kinki daukar wayata kuma kinki kunna taki why?
Dago kanta tayi ta kalle shi cikin fushi tace ka sakarmin hannu idan kai bakajin kunyar idanun momy ni inaji please let go. “Never ever, if I let you go in zauna da wa? “Your second wife da kakeson kasancewa da ita that’s why ka koreni batareda kama bari na duba lafiyar Momy ba jiya that’s why na koma inda dama ka dakko ni kafin mubar kasar nan, ni nasan matsayina banda wani value a wurinka, kuma am not here because of you, nazo saboda nadamu da lafiyar momy tana warkewa shikenan.
Wani irin kallon what is wrong yake mata, momy feels bad saboda itane duk wannan mis understanding din ita tajawowa d’an ta, kallon Naziya tayi taga ita din dai data raina ita tafi dacewa da d’an nata ga hakuri da tarbiya, don haka taji duk duniya ba Abinda takeso yanzu kamar ta warke ta gyaro kuskuren ta,
Mikewa tayi da cup din ya Kara rikota, ” Naziya please stop it, ko so kike ki dagamin hankali um? Dagowa tayi taga momy ta rufe idanun ta, ta ce “I said let go of me. Shima kallon momy yayi kafin ya Kara matsota cikin rage murya sosai dake dauke da damuwa, “meye nayi kike kokarin horani haka please am sorry koda ni bansan laifina ba kiyafe min but I can’t handle your anger on me.
Fisgewa tayi ta yi bathroom domin dauraye cup din da spoon, ya runtse idanun shi tareda dafe kai ” oh my god khaleel ka boni. Yafada tareda binta cikin sauri, tana kokarin fitowa ya maida ita tareda datse kofar, “kallon shi tayi fuskar ta a tamke “meye haka Aunty Raliya zata iya shigowa kuma kasan momy dai Nagani ko? ” Hmm so what? In zaki yi kokarin horani da irin wannan new attitude din ya kikeso ni inyi behaving, tell me? Look am not use to this, and I can’t take it any longer please forgive me if I wrong you.
Ji tayi yakara tunzura ta wato shi baisan laifin shiba, don haka cikin zafi ta dago tareda cewa ” ba Abinda kayimin kawai bana son damuwa leave me alone OK.
“Hhhhh story, rubbish, you are insane Naziya, leave you alone, ni khaleel? You are dreaming wallahi, ban hakura dakeba tuntuni sai yanzu da kika gama shigewa cikin rayuwata kika yimin dalla dalla, hannun shi yasa cikin sauri ya fisgo kugunta ya hade ta da Kirjin shi, Saida yaji kamar ya shekara bai kusance taba saboda shauki da kewar ta, “Ahhhhhh Hmmmm. Yafada tareda kankameta kamar zai mayarda ita cikin jikin shi, kokarin kwacewa takeyi ya hanata dole tayi lakwas tana sauraran bugawar zuciyar shi tareda rawar da jikin shi keyi kamar bai saba rungume taba” baby banyi bacci ba jiya kinsaba min da yin bacci kina saman kirjina bayan kin shayarda ni zumar ki tareda madarar ki mai rikita kwakwal war mutum, why kike fushi dani why kika barni nikadai jiya why kike son ki gujeni bayan kinsan zuciya da gangan jikina bazasu dauka ba?
Samu tayi ta fisge haka kawai taji yanaso ya tayar mata da feelings a Asibiti a banza yabarta da Abin kunya, tana juyawa ya kuma hade jikin shi da bayanta yasa hannu ya rungumo Dukiyar fulanin ta tareda matsawa kadan yana gwama numfashi, “Am honey, kinji let go home yanzu zamu dawo please baby. Yafada yana goga mata jikinshi, she can feel how hard he is, tayi saurin bude kofar domin takai gab ta fisge ta gudu.
Matsawa yayi baya kadan ya dafe bango tareda runtse idanun shi ya dade a wurin kafin ya d’an dawo hayyacin shi,
Ta gyarawa momy kwanciya tareda komawa gefe taja kujera ta zauna, Aunty Raliya tashigo, Wanda har lokacin bai fitoba, tace “ni zantafi nabar yara Allah yakara lafiya Ina khaleel din? ” gani Aunty yafada kanshi kasa domin yasan for sure yadago fuskar shi zata ga canjawar idanun shi, yace “bari muje in sauke ki tom, “Aa Wallahi ga mota nan megidana ya aiko yaron shi Allah ya bata lafiya.
Godiya yayi mata Naziya ta rakata ya zauna tareda bin bayanta da Kallo yana tausaya wa kanshi, Saida Auntyn ta tafi tadawo,
Still fuskar ba walwala, ya kalleta cikin da tausayin kanshi yace ” muje ne? Banza tayi mai ta dauki Jakarta karama ta ciro wayar ta ta kunna.
Tafara game, karkace kai yayi yana kare mata Kallo tundaga fuskar ta har zuwa kirjinta har kafafunta data zame takalmin ta dora daya kan daya, jajur dasu mulmul, ya hadiyi miyau Kut a zuciyar shi yace ” kinada Abinda duk zakija min aji yarinya is your time. Haka suke zaman kurame Wanda har doctor ya shigo tareda duba momy yafita, suka cigaba da zaman haka badon zuciyar shi nasoba sai dan baida yanda zaiyi, idanun ta akan su momyn khaleel din ma kebata tausayi yanzu da tanada baki da ta lallashi Naziya domin ta rikemata yaro hankalin shi ya kwanta,
Sallamar su Shukrah da malam harma da Inna da sadiq ne yasa ta zabura cikin matukar murna ta nufesu, shima mikewa yayi cikin girma mawa ya gaida surukan nashi, malam yace yamai jikin? Sukace Alhamdulillahi.
Matsawa tayi zata rungume Inna tace ” ke bani wuri ingaida mai jinya mara kunya. Shukrah tayi dariya tace Aunty nidai Rungume ni nayi kewar ki. Suka rungume juna yana kallon duk wani motsinta kamar ya sace ta ya gudu yakeji, ganin ta yakeyi kamar ma bai taba Rayuwa da itaba,
Komawa sukayi gefe itada Shukrah su kuma suka matsa jikin gadon suka fara gaida ita, “Sannu Hajiya Allah yasa kaffara ne. Inji Inna da sai yau suka hadu da juna ido da ido, kallon iyayen Naziya takeyi tana hango tsantsar datti jantaka a fuskokin su, malam yace “kulu ciromin Ruwan zam zam din nan da kunnen magaryar. Yafada yana zama gaban gadon, a wurin ya balle Y’ar Karamar robar Inna tabashi cup ya juye ya fara Addu’a a ciki tareda mutsika ganyen magarya yace Naziya zo ki karba ki juye a gora kuna shafa mata a hannu da kafafun ta har fuska sau uku a yau.
Malam ya dade da sanin wasu mutane basuda yadda shiyasa bai hado komai ba yayi wannan agabanta idan taji sauki bakinta ya bude zai iya bata wani, a take Naziya ta yi y’an da malam yace Wanda tunda ake shafa mata a kafafun takejin wani irin sanyi hade da jin jikinta na rage nauyi kamar tace kar Naziya tadaina, a ranta nadama takeyi mara Amfani wasu hawaye take fitarwa na rashin bakin da zatayi godiya,
Khaleel kamar ya goya su yakeji y’an suka nunamai karamci da kulawa, yana Kara godiya da Allah ya hadashi da surukai nagari, basu dade ba suka tafi, yarage daga shi sai ita, matsowa yayi yace “am hungry madam in baza abani Abincin cikin rigaba abani Abincin da zanci. Yafada yana rage murya tareda kashe mata ido, mikewa tayi ba musu ta zubamai Wanda su Inna suka kawo shinkafa da naman zabbi,
Ta hado mai da ruwa mai sanyi domin akwai dispenser a dakin ta Ajiye ta juya.
“Kinsan tun jiya banci komai ba kuma kinsan bana iya cin Abinci nikadai yanzu kizo muci. “Ni ba wannan nakeso ba. Tafada tana tura baki. “Oh lobster or crabs? Yafada cikin mamakin y’an da ta juya cin wainnan Abubuwan. “Ni shrimps nakeso. Iyakar gaskiyar ta tafada, ya fara cin Abincin shi Saida yayi kat yasha ruwa, ya gyara zama, zuwa tayi tadaga plate din ta saka a, basket tadawo tareda tsayamai akai, “yunwa nakeji nima. Tafada cikin fushi domin yasan sarai me takeso, ” bude idanun shi yayi yace ga Abinci nan kici in kuma nine muje sai kin koshi.
Komawa tayi can kusa da momy ta zauna, Abinta ta share shi, tashi yayi ya fita, Wanda yana fita y’an uwan shi suka shigo daga gidan kawun shi. Haka tayi ta karbar baki bayanan har zuwa magrib ta rage ita kadai, ta kuma shafewa momy jiki da ruwan Addu’ar, anan take shinfida dadduma tayi sallah domin kayanta a yalwace suke, bai shigo ba sai bayan isha’i.
Ya matsa tareda gaida momy kafin ya ce ta tashi lokacin tafiya yayi su tafi gida don ba akwana anan. “Ba inda zanje inbarta ita kadai intana bukatar wani Abu fa? ” nurse na nan. “Am not going nama fadawa doctor zantsaya kuma ga ruwan maganin ta Anjima zankara shafa mata, kai katafi.
Kamar ya dora hannun shi a kai ya buga ihu yakeji, “look kinga banason musu kitashi mutafi. Momy naji kuma tana gani so takeyi tayi magana ba dama,
Tashi ma tayi ta haye gadon dake dakin extra ta kwanta tareda jan net bayan ta saukewa momy nata, tabashi baya.
Abun ya matukar konamai rai don haka a zuciye yabar Asibitin, yayi gida.
Inba haka tayi ba bazai taba barinta ta Kwana da Momy ba ita kuma so take ta kula da ita saboda tasan a duniya batada ya’ya sama da Ahmed da shi gas hi ba Ahmed Khaleel kuma namiji ne, kuma bai kamata wata nurse na wani kula da itaba,
Don haka ta zamo mata ya’ koda bazata godeba zatayi domin Allah.
Wani irin farin ciki momy keji ganin y’an da Naziya ta jajurce wuni guda tana bata kulawa. Sai dai rashin jituwar su yasa abun ya taba mata zuciya, ba Abinda take buri yanzu sama da ganin farin cikin khaleel da Naziya.
Gida yatafi kai tsaye badon yasan zai iya bacci ba, ya kwanta yanata fushi a kujera ga gidan bakowa cikin shi sai masu aikin shi tsoffi da yadawo dasu, harma da mai gadi bayan ya kora Wanda suka kawo.
Har karfe goma na dare yakasa natsuwa haka ya canja zuwa kanan kaya ya dauki key din motar shi ya kuma barin gidan.
Naziya Saida ta kuma shafe momy tsab da ruwan Addu’ar ta kunna musu waya tasa kira’ar sudais cikin suratul bakara tareda Ajiyewa kusa da gadon momy ta koma nata ta kwanta bayan taja mata bargo, murmushi kawai momy keyi najin dadi ya’ daga sama wadda tafi ma d’an ta damuwa da ita, haka tayi baccin ta mai nauyi cikin salama tareda jin duk wasu igiyoyin da suka daure jikin ta suna kwancewa a hankali. Ita kanta Naziya tana bukatar hutawar domin d’an baccin ma da takeyi na rana yau bai samuba don haka tana kwanciya yayi awon gaba da ita,
Kamar a mafarki takejin hannun mutum a Kirjin ta tareda jin nishi kasa kasa, wai don ma yana controling kanshi karya samata ihu a Asibiti. Jin jikinta na canjawa yasa tayi saurin bude idanun ta, dayake akwai d’an duhu sai hasken dake shigowa kadan daga window domin tayi switching light din, mugun tsorata tayi jin mutum laulaye da ita gaba daya hannayen shi damke da kirjinta gam, sanin zata iya samai ihu yayi saurin rife bakinta yana rage murya tareda cewa ” it’s me baby.
“Hmmmm tayi saurin dafe kirjin ta ta zabura tana sauke rigar ta daya kwashe mata. Matsowa yayi ya janyota tareda zaunar da ita saman kafafun shi ” hey relaxed, kinga fushina ba inda zaije nadawo because I can’t sleep, the house is too big for me, please baby I really needs you kinsan bazan iya hakurin da nayi a bayaba, karki yimin irin wannan horon.
Y’an da yake magana ya mugun bata tausayi don haka ta d’an natsu a jikinshi,
“Kai wai bakajin kunyar idanun momy ne in taganka fa? Ni dai kayi hakuri inna dawo gida kabari momy ta warke.
“I said I can’t why don’t you understand?
Yafada cikin tsawa da fada, “you are my wife ya zaki rika garani saikace ba halalina ba how many times kikeso in lallaba ki?
Momy Saida ta farka saboda tsawar da ya bugawa Naziya, cikin ikon Allah ta bude bakinta tace “khaleel! Kamar daga sama sukaji muryar ta duk da maganar bawai ta bude sosai bane, da gudunsu suka matsa kusa da ita, Naziya tayi saurin gyara kanta ta kunna wutar dakin suka ganta tana kokarin mikewa, wani irin farin ciki ne yasa ya ji duk wani bacin ranshi ya kau ya rikota tareda cewa “momy you talk, kuna kintashi zaune? Cikin so much excitement, itama ta matso kusa da ita tace “sannu momy tana boye hawayen idanun ta domin tsoro biyu ne ya hadu mata, ga fushin khaleel ga tsoron Abinda Momy zata yimata tunda kuma daga gani sauki yazo, kallon ta tayi kafin ta kalli khaleel dayayi kicin kicin tace “meya miki kike kuka? Khaleel meyasa bakada hakuri da daren nan kana yiwa yarinya ihu duk da gajiyar da tayi..
Wani irin hawayen farin ciki ne ya Kara shatatowa daga idanun ta, batayi zaton haka daga momy ba, shikan shi yaji mugun dadi don haka yace ” tanbaye ta ni ba Abinda nayi mata impact in kukane ma nine yakamata inyi ba itaba, do you know momy tundazu nake lallabata muje gida ta nace ita nan zata Kwana tare dake saboda taurin kai.
Hannun ta datakeji ya saku sosai guda daya ta mika tareda riko hannun Naziya zuwa kusa da ita, ” Zo kinji daina kuka inbakya son zuwa ba mai matsa miki kinji, Amma in saboda nine kitafi gida ki huta kinga am OK zan iya gyara kwanciya ta zan iya tashi hannu na dayan nan ne da kafar hagun nan nakejin su a rike, Alhamdulillah nagode wa Allah nagode miki keda iyayen ki Naziya Allah yasa ki gama da duniya lafiya. “Amen Amen Sukace, farin cikin su baya misaltuwa a wannan lokacin, tace “in kina son binshi kije da safe kya dawo.
“Banason zuwa momy ni ina nan. Tafada batareda ta kalli khaleel ba,
Fuskar shi ya tamke yayi banza da ita,
Tace “kije kiyi kwanciyarki kinji kibarni dashi nasan kin gaji.
Wannan canjin na momy yafi komai faranta mata zuciya don haka bataso tayi Abinda zata bata mata rai har su koma Y’ar gidan jiya don haka ba musu ta wuce Abinta, momy tace ya tashi ya kashe hasken ya kunna musu na wayar shi magana zata yi dashi kar hasken ya damu Naziya zatayi bacci. “Ya tashi cikin murnar ganin momy taji sauki ga kuma canjin hali da ya lura tayi tuni ya goge mai duk wani fushi da yakeyi ya hakura da Abin da ya kawoshi ya zauna tareda gyara mata zama don tace ta gaji da kwanciyar jikinta na ciwo,
“Khaleel bansan ta ina zanfara magana ba. Tafada tana dukar da kanta tareda share hawayen ta da hannun ta mai lafiya, yayi saurin rikewa tareda girgiza kai ya share mata hawaye tareda cewa “don’t say anything momy kinga jikin ki bai gama dawo wa dai dai ba, banaso kiyi tunanin kinyi mana ba sai dai ba, ke mahaifiyar muce dole mubi Abinda kikeso, am sorry for everything momy. Shafa fuskar shi tayi tareda murmushi “nice zan baku hakuri banzamo muku uwa tagari b…. Rufe mata baki yayi ” enough for all this talk momy ki huta, komai ya wuce kawai lafiyar ki itace damuwa ta. “Khaleel Salifa….. “Leave everything to me momy am here don’t worry yourself. “Akwai Abinda nakeso infada maka akan Salifa. “Nasan komai momy ki kyalesu I will handle everything. “Hmmm tom don Allah karka kai Naziya cikin gidan nan su cutar da ita……. 🖊
*Jumu’at kareem to All my fans Allah ya sadamu da Alkharin dake cikin wnn ranar Amen *