Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 45

Sponsored Links

Abinda be taba faruwa ba a tarihin agidan yau shine yafaru , ko da wasa basa yiwa iyayensu musu akan duk abinda zasu zartar amma yau ya usman ne da kanshi baba yayi magana yana cewa bazeyuba tabbas yayi nisan da bazeji kira ba soyayya yariga da yarufe mishi ido,yanzu duk abinda zasu fada baze taba sauraran su ba , babban abinda fanan take tsoro kenan dan tasan so mugun abune in mutum ya fada tarkon so tofa komin munin abu baze taba gani ba gaba daya tausayinshi ne yakamasu dan sun san ya daukowa kanshi dala ba gammo ne hakan baze taba faruwa ba bil adama da jinni. Mama kam tsaban takaicin daya cikata ma ka sa magana tayi da wanne zataji, da tafiyar fanan zataji ko kuma da abinda ya usman ya jajibo musu .
Cikin kwantar da murya baba yace ” usman yanzu zaka fara bijire min kenan saboda so ya rufe maka ido ? Kasan bazan taba hanaka duk wani abu ba sede inde yakauce hanya hakan kuma bazan taba lamunta ba daga yau kama fara tunanin cireta aranka dan ba samunta zakayi ba nagama magana ” ya usman dafe setin zuciyarshi yayi da yakeji kamar ana watsa mishi wuta dan bala’in zafin da yake mishi murya na rawa yace ” baba bana fatan ranar da zezo inzama mara biyayya ga iyayena! Amma zanso kuji abinda nakeji wallahi baba in ban samu khairat ba mutuwa zanyi, ku taimakeni kumin wannan alfarman” ya matukar bawa Mr azaad tausayi bama shi kadai ba duk wani wanda yake falon seda ya kashe musu jiki mikewa Mr azaad yayi yarike hannun ya usman suka fita waje.
Sallamar khairatyyy fanan tayi nan take ta bace azuciyar fanan kuwa tana tunanin abinda yakamata tayi dan ceto dan uwanta. Auta kam duk abinda akeyi se binsu da ido takeyi kasancewar takan fahimmci wata maganar wata kuma bata fahimta saboda kananun shekarunta ,ta riga da tagane duk wannan maganar akan khairaty ce da ya usman inde ta ita zaabi khairaty tayi mata kyau sosai, ( kuji auta fah ahhh lallai yaro yarone) fanan da ya al ameen ne suka kwantar wa su mama hankali akan zasuyi iya kokarinsu domin ganin ya usman yacire khairaty a ranshi, kirane yashigo wayar suhaima ganin sunan “my hubby” yabayyana akan screen din ne yasa tabar falon tashige daki.

Haka a bangaren Mr azaad duk da yakasance mara son magana haka yabawa ya usman shawara sosai har yasamu yadawo normal suka dawo falo ko zama ya usman beyi ba ya shiga dakin shi , zama Mr azaad yayi yana shafa lallausan sumar kanshi kafin yace ” baba kuyi hakuri ku mishi uzuri yariga da yayi nisa na lura usman yana matukar sonta , dole muyi kokarinmu domin ganin ya cireta aranshi ” sake baki da hanci fanan tayi tana kare mai kallo jin maganganunshi tunani tafara yaushe Mr azaad yafara damuwa da damuwar mutane amma hakan yamata dadi ganin ya damu da damuwar ahalinta sonshi ne takaraji yashiga cikin zuciyarta, duk maganar nan da Mr azaad yakeyi auta na kwance ajikinshi tayi lamo kamar wata me bacci can kuma ta mike zaune ta kalli Mr azaad tace ” Yaya balarabe kasanme ? ” Kallon fuskanta yayi me kama da na fanan se an nutsu sosai zaa gane kamar tasu saboda skin color dinsu ba daya bane auta farace sol kamar tsada fanan kuma chocolate color ce ,ita kadaice me color skin din agidan , girgiza kai yayi tare da cewa ” cutie bansaniba sekin fada ” cigaba tayi da ” nikam budurwan ya usman tamin kyau sosai especially her eyes that are so big like ball tayi kyau sosai kaima tamaka kyau ko?” Basu taba tsammanin abinda auta zata fada ba kenan amma se sukayi laakari da wayon datake dashi domin basuyi tsammanin harzata fahimci akan abinda ake magana ba kenan , shisa bakowani magana akeso adinga yi agaban yara ba saboda yaran yanzu sun wuce duk yanda kuke tunani , satan kallon fanan yayi yaga se aikin gallawa auta harara takeyi jin tana tambayarsa shima tamasa kyau, murmushi yayi dan yasan akan abinda yasa take hararan auta , lakatar hancin auta yayi yace ” karki kara magana akan abinda manya suke tattaunawa bakyau this is improper” gyada Kai tayi takoma jikinshi ta kwanta .
Sun dan taba hira kafin Mr azaad yakalli agogon diamond dake daure a hannunshi sannan yace ” baba mu zamu wuce dare yayi seda safe ” sallama sukayi ya fita shida ya al ameen fanan ji tayi kamar karta tafi dakinta tashiga ta canza kayan jikinta zuwa riga da wando falazo tasa hijab dinta har kasa dama kayanta duk suna cikin wardrobe dinta,

Haka tanaji tana gani tayiwa su mama sallama, suka fito ita da suhaima tana rike da hannun auta ajikin motar suka samu Mr azaad da ya al ameen suna tattaunawa game da yanda zaa shawo lamarin ya usman bude motar yayi ya dauko fashion bag dake cike da chocolate kala_kala yaba auta karba tayi tana fadin ” thank you yaya balarabe god bless you” murmushi kawai yayi azuciya ya amsa da Ameen motar suka shiga fanan na musu bye-bye.

Back to top button