Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 11

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E11_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

 

Gaba ɗaya Haris ya fidda rai da rayuwa, tun da halittar nan ta zura ƙafafuwansa cikin wawakeken bakinta, tsabar tsoro da firgici sun hana shi motsawa jini duk ya wanke bakinsa har saman rigar sa, jikinsa yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyaci, Bawan Allah sai sambatu ya ke yi yana ambaton Sunan Danish dana sauran ƴan uwan su don su kawo mashi agaji.

Ba zato ba tsammani ya ji Sautin dirar wani abu daram! tamkar zai fasa kunnansa, tsabar firgitar da yai ne yasa nan take ya sume saman koraren ciyayin.

Wani Gabjejen Bature ne A tsaye cika shigar Kaya na tatattun Ƴan ta’adda babu ɗigon Imani akan fuskarsa, Hannunsa ɗaya ya ruƙe da Bindigar da yai amfani da ita wurin harbin Halittar da ta nannaɗe Jikin Haris, yayin da ɗayan hannun ya ke ruƙe da cigarette.

Hankalin shi a kwance ya ke zuƙar Tabar Cikin ƙwarewa Har ta hanci Hayaƙin Ya ke fita, kwarkwararrun idanuwanshi na akan Haris dake kwance Ya sume, Tuntsirewa Baturen Ya yi da dariya hada ɗan girgiza kanshi, da ƙarƙarfan muryar sa ta Mashaya giya cikin harshen turanci ya ke faɗin

“wani irin ganganci ne ya kawo ka ƙurmin daji da ƙananun shekarun ka, ba ka da hankali ne? Matashi da kai kake son ƙare rayuwarka abanza? Ina iyayen ka su ke”?

kamar zautacce Shi kaɗai ya ke yin maganar shi, sam bai fahimci Yaron Ya sume ba, Sai da Ya gama Magana kafin ya matsa inda Haris yake a kwance, Ya zuƙunna Bayan Ya soke pistol ɗin a qugunsa, Ya sanya hannayensa Biyu Da ƙarfi Yake jan jikin halittar, Har sai da yai nasarar zaro ƙafafuwan Haris daga bakinta, Allah yaso ba ta kai ga Gatsa haƙoranta akan legs ɗinsa ba, da ko ta yi mashi babbar illa, Bayan Ya zame jikin Halittar da karfi Ya jefar da ita gefe ɗaya, yunƙurawa yai ya miƙe tsaye yana kakka6e tafin Hannayensa, Zuƙar Tabar sa Ya ƙara Yi”Bani da zuciyar Imanin da zan Iya taimakon ka, ka gode wa Allah da na raba ka da dabbar nan, da ko yau Ka rasa ƙafar zuwa gidan Iyayen ka” Yana magana yana sakin dariya idanuwansa akan fuskar Haris.

Sautin kururuwar neman a gajin da ya Ji ce Tasa shi Kan ga kunnansa ga iska Don Ya ji da kyau, Muryar Naufal ce Ya ke faman Fasa Ihu, Da gudu Baturen Ya kutsa Cikin Dajin Yana Tunkarar inda sautin Ƙarar ke fitowa, ta wutsiyar idon shi ya hango gifcin mutune sanye da Jajayen kaya, Ta tsakantsakin jibga jibgan Bishiyoyin dake a kewaye da wurin da yake, Cikin Zafin Nama Ya daka uban tsalle ta tsakiyar wasu bishiyoyi, Kamar an jeho shi Ya faɗo Tsakar wurin da Su Naufal su ke, Gaba ɗaya sun fita hayyacin su, Halittun sun kewaye su sai gurnani su ke yi, Naufal da javed sun ƙanƙame Juna, Kuka hada majina fuskokin su jaga jaga da hawaye, wandunansu a jiƙe sharkaf da ruwan fitsarin da suka saki, Ɗan iskan murmushi dangerous terrorist Ya saki kafin Ya zaro bingidar da ke soke a qugunshi, Ya saita Jikin Halittun ɗaya bayan ɗaya yake sakar masu alburushi, duk wadda ya harba nan take Tsakiyar Cikinta yake tarwatsewa Ƴan hanji su fito waje, Sautin harbin bindigar da basu ta6a ji bane Yasa su rikicewa Kusan atare suke yanke jiki saman koraren Ciyayin suka faɗa a sume, Tuntsirewa Baturen yai da dariyar shaƙiyanci Yana faɗin

“Yaran nan kuna da ban dariya, Sai ka ce ba maza ba? Kun iya shiga daji amma ba ku Iya faɗa ba? Zaman gida da sanya buje zaifi da cewa da ku, In yaso kun cigaba da taya iyayen ku shiga kitchen yin girki” acikin harshen turanci ya ke yin maganar.

Gabanshi Ne yai mugun faɗuwa Jin ƙarar Jirgi A cikin kunnuwansa, Da sauri Ya kai idanuwansa saitin rassan bishiyoyin da suka lullu6e sararin samaniya, nan ta ke yanayin fuskar shi Ya canza daga annuri zuwa tsantsar baƙin ciki, fargaba da tashin hankali, Juyawa yai da gudun gaske tamkar zai tashi sama Haka ya dinga buga uban tsalle Yana gudun Ceton, ga dukkan alamu bai da gaskiya shiyasa ya ƙe ƙoƙarin gujewa waɗanda suka kawo mashi Hari, tuni Ya jima da jefar da tabar hannun sa, kwata kwata Baya a cikin Hayyacinsa, shi kansa baisan in da ya ke wurga ƙafafuwanshi ba, saboda tabar firgicin da ya shiga, ko ma su wanene su ka biyo shi sun shammace shi bai yi tsammanin za’a gano inda ya 6uya ba.

Sautin Ƙarar danƙareran Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar amurka ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza su ke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, har wani jijjiga ya ke yi tamkar zai fasa dodon kunnan mutun, Shawagi ya ke yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina.

Hot soldiers din da ke a tsaye baƙin ƙofar jirgin zafafan gaske fusatattun sojoji masu ji da ƙarfi, cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Ya ki, Ɗaya daga cikin su Hannayen sa biyu Na ruƙe da Telescope abun hangen nesa, Ya kanga shi saitin idanuwansa, Sojan da ke a gefen shi Yana Ruƙe da Tactical phone wayar da sojoji ke Yin amfani da ita wurin yin sadarwa da Manyansu dake acan headquater, Cikin Harshen turanci Ya ke Sanar da su cewa Sun ƙaraso Dajin ayanzu hake suna kewaye shi domin gano Location ɗin da ɗan Ta’addan Ya 6uya a dajin.

Me ruƙe da abun Hangen nesan ne Ya soma magana Yana ɗaga murya ya ke faɗin A samu wuri a sauke Jirgin Yana zargin me laifin Yana a yankin da su ke, Jin maganar Shi Yasa sojojin dake sarrafa Jirgin su ka Soma ƙoƙarin Samun wurin Da zasu Sauka, A hankali helicopter ɗin Ya ke yin ƙasa tunkafin ya ƙarasa direwa, Sojojin suka soma diddirowa ƙasa Sautin Army boots ɗin dake a kafarsu Yana bugun ƙasa kamar zasu dare ta, Hannayensu ruƙe da Jibga jibgan bindigu, Haka zalika qugunansu na soke da pistols ƙananun bindugu, Sun rufe kawunansu da helmet (hular kwano) Hatta faces ɗin su ba ka Iya gani, Iya idanuwansu ne kaɗai a bayyane, Kusan su shidda ne su ka sauko daga jirgin, Da hannu Commender ɗin su ya rarraba su zuwa gida Uku, kafin ya basu Umarnin shiga Dajin, Da gudun gaske Su ka faɗa cikin zafin nama su ke kurɗaɗawa Cikin ƙurmin Dajin, Babu tsoro ko fargaba suna da ƙwarin gwiwa akan aikin su da ƙwarewar su, kuma suna da tabbacin za su yi nasarar Yin aikin da aka turo su, saboda duhun dajin Da fitilu masu haske su ke yin amfani wurin haska gabansu.

Gaba ɗaya sun Yi matuƙar galabaita, tun suna tiƙar gudu Hancin Angel Ya soma bleeding zufa duk ta wanke fuskokinsu da jikinsu, Maƙoshinsu ya bushe ƙamas sai azabar raɗaɗi da ƙaiƙayin da ya ke yi masu

ƙafafuwan su Zogin azaba su ke yi masu, Sun rasa ina zasu tsoma ransu su ji daɗi, Suna a tsaka mai wuya tsakanin mutuwa da rayuwa, Kurar dake a biye dasu Tana gab da zata cimmasu, Wani irin uban tsalla ta daka tana Gurnani Ta takaiwa Ƙafar Angel Cafka da haƙoranta, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa ita da Gabriel a matuƙar razane.

Kurar na ƙoƙarin Gutsire ƙafar Ba zato ba tsammani, Sautin dirar bullet Ya ratsa kunnuwan su, Basu san daga Ina aka harbo bullet ɗin ba, Gaba ɗaya ya tarwatse Kan kurar, Nan take ta saki ƙafar Angel Ta faɗi ƙasa tana birgima, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel Ya sauke Yayin da zufa ke cigaba da wanke fuskarshi, angel kuwa Tsabar firgice ne Yasa ta yanke Jiki Ta faɗi ƙasa a sume tamkar matatta.

Hankalin Gabriel Ba ƙaramin tashi yai ba, Ganin yadda Angel ta zube, Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya gama galabaita muryarsa na kakarwa ya furta sunan ta da ƙarfin”Angel! no!No! Don’t die Angel, Na shiga Uku, Pls Angel ki tashi Ina zansa rai na!”

Fuskarsa sharkaf da hawaye yake yin maganar, Zuciyar shi a karye Ya zube saman gwiwowinsa agaban Angel, Ya dinga kuka yana jijjiga jikinta Da hannayenshi, Sam baya acikin hayyacin sa, shiyasa ma bai yi tunanin Su wanene suka kashe Kurar ba, duk a tunanin shi Angel ta mutu ne, duk yabi ya zauce ya rasa madafa.

Jin Takun Tafiyar Mutanan da ke tunkaro shi ne yasa shi saurin wurga eye balls ɗinsa da suka kaɗa jawur Yana duban su, Sojoji ne Su biyu Hannayen su Ruƙe da Bindugu, duk da baya acikin hayyacinsa saida Ya zabura yana neman guduwa a zaton shi Gianta ne na gidan kurkukun ƙaddara.

Kakkausar Muryar Sojan ce ta ratsa kunnuwanshi”Don’t Move or else i will shoot ur head wit My gun”

Wannan maganar da ya yi ce tasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar ba tare da ya juyo ya kalle su ba, ya soma magana cikin rawar murya

“Just kill me so that I can finally rest, Na rasa ƴan uwana, bani da burin cigaba da yin rayuwa a duniyar nan, ku kashe ni kawai idan ba haka ba ni zan kashe kai na” Yana magana zufa na tsastsafowa ta jikin fatar shi.

Muryar Sojan ce ta kara ratsa kunnanshi cikin harshen turanci yace

“ba zamu kashe ka ba, rayuwarka tana da mahimmanci a wurin mu, Aikin mu shi ne mu shiga tsakanin ku da mugun da ya yi garkuwa da ku Ya kawo ku cikin Dajin nan, Idan ka bamu haɗin kai zamu mai da ku ƙasar ku” tun da Sojan Ya soma Yi mashi magana Cikin kwantar da murya, sai ya ji natsuwarshi ta fara daidaita, kuma ya fahimci ba jami’an kurkukun ƙaddara ba ne.

Da sauri Gabriel Ya waiwayo baya yana dubansu, a jere suke tsaye su biyu, Yawu ya haɗiya Muryarshi still adabarbarce ya furta”idan har dagaske kuna son taimakona, akwai ƴan uwana da suke a cikin dajin, muna acikin mayuwacin hali, wasu mugayen halittune suka biyo mu, ina tsoron su kashe min su” Jin wannan Maganar Yasa ɗaya daga cikin sojojin ya tasa ƙeyar gabriel Gaba, Zuwa Cikin dajin.

Yayin da ɗayan Sojan da su ka bari a tsaye gaban Angel ya soma magana ta hanyar yin amfani da tactical phone ɗin hannun shi, Ya sanar da commender game da yaran da suka tsinta a dajin, suna zargin ɗan ta’addan ƙasarsu ne ya gudo dasu cikin dajin yai garkuwa da su don ya kare kanshi daga farmakin da zasu kawo mashi.

Commender ɗin ya ba da Umarnin A tattaro yaran dukansu, a lokacin har sunyi nasarar Cafke ɗan ta’ addan da su ka zo kamawa, Mugun ɗauri suka yi mashi duka jikinshi suka nannaɗe da igiya suka ɗaure shi tamau bayan sun yi mashi allurar kashe ƙwarin Jiki gudun kada ya kubce masu saboda sanin shi da su ka yi, mugun ɗan ta’adda ne mai hatsarin gaske, A cikin jirgin suka wurga shi.

A saman Kafaɗa Sojan Ya ɗaura Angel Ya nufi wurin da suka sauke helicopter ɗinsu, A ciki ya shigar da ita ya kwantar, Bada jimawa ba, sai ga wasu sojojin su biyu ɗauke da Nufal da Javed saman kafaɗin su. bayan sun shigar dasu Cikin jirgin sai ga kira daga Ɗayan Sojan daya tafi da Gabriel gaba ɗaya suna jin muryarshi ta cikin wayarsu, sanar da su yai akwai sauran yaran da zasu nemo acikin Dajin, Yana buƙatar a turo Wasu sojojin da zasu ɗauke su, Umarni commender yaba sauran sojojin da suka dawo akan su je su zaƙulo sauran yaran, Da gudu suka kutsa cikin Dajin.

Gabriel da sojan da ya taso ƙeyar sa suna cikin Tafiya sai faman wurwuga ido gabriel yake yi a ƙoƙarin shi na ya gano inda su Batul su ke, Gabanshi sai faɗuwa ya ke yi tsoron sa kada ace halittar nan ta hanɗame su, Har zasu gifta kwatsam ta wutsiyar ido Soja Ya hango launin jajayen kaya ƙuɗundune cikin koraren ciyayi da sauri ya furta”wait” hakan yasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar, Reverse sojan yai tare da juyar da kanshi Ya wurga ƙwayar idanuwanshi saitin wurin da ya hango jan uniform ɗin, Gabriel na yin tozali da su da ƙarfi ya furta sunan Azeeza, da gudu ya nufi wurin da suke maƙale da juna babu numfashi, Sojan na ganin Ya tunkari wurin shima yabi bayanshi, agabansu Gabriel ya zube saman gwiwonsa Yana Ambaton sunayen su cikin karyayyiyar murya ta wanda ya Sare, kafin sojan Ya motsa Sai ga sauran Sojojin da commender ya turo sun kutsa ta wurin da suke. suna ƙarasowa ba tare da 6ata lokaci ba suka ciccire ƙayoyin da suka sargafe ƙafafuwan Azeeza da jemimah, Kafin su ka ɗauke su saman kafaɗunsu, da hanzari suka juya dasu zuwa cikin jirgin.
Bayan tafiyar su Sojan Ya ce da Gabriel Za su Iya tafiya yanzu? Da sauri ya girzgiza kai, cikin disasshiyar murya ya faɗa mashi”Akwai sauran mutun uku da babu acikin su” Sojan Yace ya tashi su shiga neman su, Ba su buƙatar 6ata lokaci, Akwai Iya adadin da aka basu, Idan har ya cika zasu tafi ne” jin haka yasa Gabriel Miƙewa shi kansa ba ƙoshin lafiya ne dashi ba, ƙarfin haline kawai.
A ƙalla sun shafe tsawin mintuna goma shabiyar suna neman Su Batul, Sai kurɗaɗawa suke Yi cikin dajin babu su babu alamarsu, ganin zasu 6ata lokaci yasa sojan ce mashi”Su tafi kawai, Zai iya yiwuwa sun rasa rayukansu ne” kamar ƙaramin yaro haka Gabriel ya fashe mashi da kuka tare da zubewa saman gwiwowinsa Ya ruƙe ƙafafuwan Sojan Ya dinga kuka Yana roƙonshi akan kada su tafi su bar ƴan uwan shi a dajin, Shi yana ji aranshi suna araye wata’ƙil sun faɗa wani wurin ne sakamakon muggan halittun da suka tsoratar dasu,’ Tsawa Sojan Ya daka mashi a harzuƙe Ya hambare Gabriel da ya ruƙe mashi ƙafa.

Muryarshi a kausashe yace “Get up and let’s go. Otherwise, we’ll leave you here in the forest.” Hawaye na bin kuncin Gabriel, Ya girgiza mashi kai yana faɗin”bazan Iya tafiya nabar su ba, Atare muka sha wahala, bai kamata mu tsira mu ƙyale su ba, ni banga gawarwakinsu ba, Tayaya zan yadda sun mutu,” numfashi yaja kafin ya ɗaura da cewa”Zaku iya tafiya da waɗanda kuka ɗauka, Ni ku barni anan zanje na nemo ƴan uwana ko da ace zan rasa raina ne” Juyawa Sojan Yai a fusace Ya soma tafiya, Sai da yai nisa zuciyarshi ta soma tariyo masa kalaman Gabriel, Dakatawa ya ɗanyi yana wani tunani, ga dukkan alamu kalaman sun ta6a zuciyarshi, A hankali ya ɗan waigo Baya yana dubanshi, Bawan Allah Ya kifa kansa saman ciyayi, Sai kuka yake yi kamar ranshi zai fita, takaicine ya ishe shi ga samu ga rashi, Yasan muddin sojojin suka tafi shida barin dajin har bada, a ƙarshe ma ya rasa ranshi, sai dai baya jin zai Iya binsu alhalin sauran ƴan uwanshi da suka sha wahala suna acikin dajin! ya zasuji idan suka dawo hayyacinsu suka taras babu su? Me zai biyo baya?

A lokacin da Gabriel baiyi tsammani ba, muryar Sojan Ta ratsa kunnanshi

“Yaro ka ci albarkacin sarƙar cross ɗin da ke a wuyan ka, A karo na biyu zan Taimake ka, mu gano sauran Ƴan uwan naka” wani irin farin Cikine ya lullu6e Gabriel Jiki na rawa ya yunƙura Ya miƙe, kafin su fara tafiya sai ga sauran Sojojin da su ka je kai su Azeeza hada ƙarin wasu kusan su shidda suka nufi Dajin neman sauran Yaran, Marece ya nutsa abun da sojojin suke gudu dare ya yi masu a dajin saboda Sanin hatsarin dake gare shi, Daƙyar Gabriel Ya samu Ya gano masu hanyar wurin da suka yi shimfiɗarsu, da gudu Ya nufi Danish da ke a kwance yana sharar baccin shi.

Tun kafin sojojin su ƙarasa Gabansu yai wani irin faɗuwa saboda razanar da su ka yi da ganin shi, Wani abu ya ɗaure masu kai, har saida su ka kalli junansu da alamun ruɗu akan fuskokin su, Ba Iya kyawun Fuskar Danish bane Ya girgiza su, Zazzafar surar Jikinshi Ta yi matuƙar rikitar dasu, Kaf a cikinsu babu mai kalar ƙirar ƙarfin shi, Hakan ba ƙaramin kokwanto Ya saka masu ba acikin zuciyoyin su, har sun fara kokwanton Anya kuwa ɗan ta’addan da suka Biyo ne yai garkuwa da yaran? Ta ya ya za’ai ɗan ta’addan Ya iya sato wannan jibgegen ƙaton mai ƙirar sadaukan Yaƙi, a ganin su ko shi ɗan ta’addan bai kama ƙafar Matashin yaron ba wurin zubin halittarshi.

Muryar Gabriel da sassarfa yake Ambaton sunan danish Hannayenshi duka biyu akan jikinsa sai jijjigashi yake yi yana faɗin”Danish ka tashi, mun samu taimako za’a fidda mu daga cikin daji, Har ma an tafi dasu Angel, pls ka tashi, Bana so mu tafi mu bar ka”

Ko motsi Danish bai yi ba, ganin haka yasa shi juyawa yana kallon Sojojin, Sun ƙame a tsaye suna kallon Abun al’ajabi kusan suman tsaye sukayi yayin da suke kallon Danish
“Dan Allah ku taimake ni, ɗan uwanmu ne, haka Allah ya halicce idan Yana yin bacci yakan ɗauki tsawon awanni bai farka ba,” a ruɗe yake kora masu bayani, duk don ya samu su tafi da Danish kada suce zasu barshi anan, don ya fahinci tashin shi ba yanzu ba

Daƙyar ɗaya daga cikin sojojin ya iya shanye mamakin shi ya sarrafa kanshi wurin furta” bai da lafiya ne? Ko ya suma ne”?

“A’a, bacci ya ke yi, kuma ba zai Iya farkawa yanzu ba, ….”tun kan ya ƙarasa maganar ɗaya daga cikin soldiers ɗin Ya zaro penlight ya zuƙunna agaban shimfidarsa, da yatsun hannayensa yai amfani wurin gwale idanuwan Danish ya haskasu ya tabbatar da yana araye ga numfahi na fita a tsanake, Kallon sauran sojoji yai”he’s alive” jin haka yasa suka gasgata maganar Gabriel, mutun Biyu suka ranƙwafa tare da ɗaura hannayensu da nufin su cuccu6i Danish sai dai wani abun ɗaure kai ko motsi baiyi ba, saboda tsabar nauyin sa duk irin ƙarfin da Allah ya yi ma sojojin na halitta da kuma na horon aikin da suka samu baisa sun Iya cuccu6ar Danish ba, A ƙarshe suka Yanke shawarar zuwa ɗauko stretcher domin ɗaukar shi, zaifi Yi masu sauƙi, abun ɗaukar Majinyatane da ake amfani dashi, Yana da maruƙi a jikin sa, saman shi faɗine dashi kamar allo, bayan sun ɗauko stretcher ɗin Saida suka haɗa ƙarfi su huɗu tukunna su ka iya cuccu6ar Danish tare da ɗaura shi saman abun ɗaukar, su ka ɗaga shi har zuwa Bakin helicopter din kafin suka samu damar shigar dashi ciki, Bayan sun tafi da danish Ɗaya daga Cikin Sojoji biyu da suka rage Ya ɗauki Back pack ɗinsu da ya gani a jikin bishiya, don suna buƙatar duk wasu shaidu da za su zamar masu hujja.

da hannu ɗaya ya ruƙo jakar ɗayan hannun kuma ya ruƙe hannun akwatin kayansu Yaja shi zuwa Bakin jirgin.

A can Cikin Dajin Gabriel ne Ya rage tare da Sojan nan, Suka kuma kutsawa cikin dajin Don ya sanar mashi akwai sauran Ƴan uwanshi, Abun dai ya ɗaurewa Sojan kai, Su fa duk a tsammaninsu ɗan ta’addanne ya yi garkuwa da su daga ƙasar su america Ya shigo da su Dajin, Saboda Yaran sunyi kama da mutanan ƙasarsu, Hasken fatarsu da Doguwar sumar kawunansu, a hasashensu kenan, sai dai duk da haka sun ɗanyi mamakin wasu abubuwa da suka sanyasu yin al’ajabi, tayaya har ɗan ta’addan ya iya guduwa dasu bayan ƙasarsu tana da mugun tsaron da babu wani shege da ya isa Ya ƙetare ta cikin Salama, Abu na biyu Ta ya ya Ɗan ta’addan Ya iya ɗaukar mutun mai mugun Nauyi irin matashin saurayin da suka gaza ɗagawa? Abu na uku da ya ɗaure masu kai Uniform ɗin Jikin yaran masu ɗauke da numbobi sunyi mamakin hakan.

Suna Cikin yin tafiya, Zuciyar Gabriel na dakan uku uku tamkar zata faso kirjinshi ga kishirwa da ya ke ji, babban tashin hankalin shi Ina Su Batul suka kutsane a cikin Dajin? Ga dare yana shirin yi masu adajin, fargabansa kada sojojin su ce zasu tafi.

“Kana tunanin ƴan uwanka zamu same su? Lokaci Yana ƙure mana” Sojan ne yai mashi maganar, gabriel bai samu damar amsa mashi ba saboda tashin hankalin da ya ke aciki, Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansa ya ke yi akan bishiyoyin dake a kewaye dasu, Suna Cikin yin tafiya suka ƙaraso gaban wannan ramin mai ɗauke da ta6o, har zasu gifta shi Kwatsam Sojan Yaji ya taka wani abu, Da sauri Ya ɗage ƙafarshi yana kallon Warin Slipper ɗin dake asaman ciyayin, Gabriel na ganin takalmin Ya zuƙunna tare da kai hannu ya ɗauke shi, Gabansa ne ya faɗi A gigice ya kalli sojan tare da furta”Takalman Ƴar uwata ne!” Ya gane slippers ɗinsu ne Da tsohuwa Tamira tai masu kyautarsu, dama tunda suka shigo Dajin da takalmansu suke yawo a ƙafafuwansu, shiyasa ko ƙaya ba ta ta6a shigarsu ba.
“Dan Allah ka taimaka mun, wlh takalmansu Batul ne ƴan uwana” Muryarshi na rawa yake maganar, cikin ƙagara.
Waige-waige Sojan ya ke yi yana bin ko’ina Na dajin da kallo, Kafin ya sauke idonshi akan Ramin ta6on, kasancewar Sojoji suna da ƙwarewa wurin sanin takan Daji, Nan take ranshi ya bashi cewar Ta6on da ke a wurin Ramine, mutun zai Iya rubzawa cikinsa, musamman wanda ke gudu cikin fitar hayyaci.

Matsawa yai gaban ramin, Bayan ya soke bingidar hannun shi a ƙugun shi, Ya ɗan zuƙunna saman ƙafarshi, a tsanake Ya tura hannun shi Cikin ramin ta6o, Cikin sa’a Ya damƙo gashin ɗaya daga Cikin su, matsar da hannun shi yai ya ruƙo Hannunta, Ya ɗago da ita gaba ɗaya jikinta ya 6aci kaca kaca da ta6on baka Iya ganin komai na fuskarta, hatta Gabriel bai gane wacece a cikin su ba, A ƙasa sojan ya kwantar da ita tare da ƙara zura hannun shi Ya ƙara cafko hannun wata ya curo ta, bayan ya kammala zaraso duka ukun Gabriel Yace mashi suke nan babu saura, Jin haka yasa Sojan Zaro wayarshi Ya sanar ma sojojin dake a bakin helicopter din cewa sun ƙara samu Yara Uku azo da stretcher a ɗauke su, Cikin ƙanƙanin Lokaci sai ga sojoji sunzo da abun ɗaukar, duka ukun suka ɗaurasu saman shi kamar tsummokarai haka suka nannaɗe.

Sojoji biyu ne suka tafi dasu zuwa Inda jirgin ya ke, Hankalin Gabriel Ya ɗan kwanta sam ya manta da Haris saida suka kamo Hanya zasu Nufi jirgin ba zato ba tsammani su ka ci karo da haris a sume, Ba tare da 6ata lokaci ba, Sojan da suke atare Ya sa6e shi saman kafaɗa, suka nufi Jirgin Bayan sun Shiga su dukansu. Matuƙar jirgin suka Tada shi, Da wata irin jijjiga tayoyin jirgin su ka soma motsawa suna yin tafiya sannu a hankali, Gabriel da ya kasance shi kaɗai idon shi biyu, farin Ciki duk ya cika shi, sam baiyi tunanin wace ƙasa za’a kaisu ba, hankalin shi bai kai nan ba, fatan shi su bar dajin Cikin ƙoshin lafiya.

Bayan tashin jirgin sama Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin ne Ya kanga Tactical phone ɗin hannunsa jikin kunnansa Yana magana Cikin Harshen turancin muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest.” (Munyi nasarar cafke mai laifin, yanzu muna akan hanyar mu ta dawowa U.s, tare da yara goma sha ɗaya da mu ka samu a dajin)

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito.

*Alhamdulillah Finally Ex-prisoners sun Bar Evil forest Fatan Nasara*

Back to top button