Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 36

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI…..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

PAID BOOK #500

{36}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Sai da nayi dagaske kuma nayi ta maza sannan na samu na tattaro ƴar ragowar juriyar da ta rage min duk da can cikin raina tashin hankali ne danƙare, ɗakin na soma bida kallo sannan na dire kallona kan kyakkyawar matashiyar dake kwance kan gadon da nake kyautata zaton na miji nane, fara ce sol mai ƙiba, babu komai ajikinta haka take kwance tsirara haihuwar uwarta sai ko wani matsiyacin pant wanda dashi gara babu saboda baida maraba da babu ɗin, hannunta riƙe da waya tana latsawa, jin motsina ya sanya ta jan blanket ta ɗan rufe jikinta kaɗan tana kallona sama da ƙasa, ni kuwa uwar kishi tuni naji wani abu ya tokare min maƙoshi haka idanuwana sun kaɗa sun yi jajur kamar gauta,

“Wacece ke kuma wa kike nema?” ta faɗa cikin kallon raini da ƙasƙanci cikin harshen turanci,

“Ke ya dace in yi wa tambayar wacece ke, wanda nake nema kuma wurin mijina na zo” na mayar mata da amsa nima cikin harshen turanci domin duk ƙaryar turancinta nima ina taƙama da nawa,

Wani kallo tayi min kafin ta tashi zaune tana sake kallona,

“Ok you mean kece matar Samz? Wannan jaririyar ”

“Naji daɗin da kika gane hakan tun lokaci bai ƙure miki ba…..”

“Hmmmm…… To ai baki da wani muhimmanci a gareshi, dan da kina dashi da bai ƙyaleki tsawon 2 months yazo yana sheƙe aya dani ba anan… Ohhh wato kin kasa haƙuri kin biyoshi?”

Zazzafan yawu na haɗiye domin zuciyata tafarfasa take yi kamar in je in shaƙeta,

” Kece kike ganin bani da muhimmanci awurinsa amma shi ya san muhimmanci na, zaman sheƙe aya kuma da kika ce kinayi tare da mijina bai dameni ba tun da dama ya jima da bani labarin ki cewa ke ƴar akuya ce kowa ma bi kike, sannan dan na zo wurin mijina ai sai naga kamar banyi laifi ba ko? Sai a tattara a ƙara gaba saboda me wuri yazo, kowanne addini ya girmama mata kuma ya daraja aure sannan ya ƙyamaci fasiƙai…… Ki gaggauta barin gidan nan tun kafin in je in dawo in wulaƙanta ki ”

Ina kaiwa nan na fita, jakata dake falo na fincika na bar gidan zuciyata na wani irin zafi da raɗaɗi, ina fitowa naga mai taxi ɗin da ya kawoni yana ƙoƙarin rufe gaban motarsa da alama gyara ya ɗan yi,

” Ahh hajiya ko dai ba a dace ba? Kar dai ba ayi miki kwatancen daidai ba?”

“Ehh ba nan bane, muje ka sauke ni”

Jakata ya ɗauka yasa aciki sannan nima na shiga yaja muka tafi, gaba ɗaya duhu nake gani bana iya ganin komai, samz ya raina min wayo da hankali ko ɗazu da safe da muka yi waya sai da yayi min daɗin bakin da sai da naji kamar na fi kowacce mace muhimmanci acikin rayuwarsa, harda ce min,

“Gwauruwa….. Ni Kinga ina da mata”

Dariya nayi kafin nace masa “Kaine gwauro nima ina da miji, mijina kuma yafi na kowacce mace, gashi kyakkyawa gashi mai hankali, ma’abocin tsafta da iya kwalliya, ya iya saka kaya, ƙamshinsa kaɗai yana sanyaya raina…. Ina missing ɗinshi over”

Murmushi naji yayi sannan naji yace,

“Kina da miji but you are still virgin…..”

“No, am not” na faɗa cikin shagwaɓa ina turo masa baki,

“Seriously baby…….”

“To kaima saurayi ne sabo fil”

“No, ai ni kin riga da kinyi disvirgin ɗina….” rufe fuskata nayi kamar yana ganina,

“ta yaya? Nida babu ruwana”

“Ohh so kike in faɗa miki?”

“Hajiya ina muka nufa? A ina zan ajiye ki?” muryar mai taxi ce ta katse min dogon tunanin da na faɗa,

“ka kai ni hotel…”

“wanne hajiya?”

“koma wannene kawai kai ni” na bashi amsa kaina na jikin window ina kallon yanda rayuwa ke gudana agarin,

Gaba ɗaya bana cikin hayyacina, hankalina duk baya tare dani danma inata karanta addu’a acikin raina shine sauƙin da na ɗan samu. Ba zan iya gane hotel ɗin da ya ajiye ni ba nan na bashi kuɗinsa duk da banma san ko nawa na bashi ba nayi gaba ina jin sa yana cewa ga canji amma na wuce kawai,

Ɗaki na kama na biya kuɗi sannan aka kaini, ina shiga na zame na zauna a ƙasa jikin gado, gaskiya samz yayi mugun yaudarata dan ko a first night ɗinmu haka ya rinƙa nuna min kamar bai taɓa sanin wata mace ba sai ni, ashe duk salon yaudara ne, wayata na ɗauka ina hawaye na rubuta masa saƙo kamar haka,

_Ka jima kana cin amanata ban sani ba, ashe dama karuwa ka ajiye agidanka shiyasa kayi watsi dani ka ƙi zuwa inda nake to yau Allah ya nuna min da idona na gani, Allah ya isa tsakanina da kai, kuma sai Allah ya saka min, sannan ko Kaine autan maza to na haƙura da kai, ka aiko min da sakina ko ta waya ne._

Ina gama rubutawa na tura masa na kashe wayata zuciyata na cigaba da yi min zafi, wannan sirrin bai cancanci in sanar da kowa ba dan duniya sai tayi min dariya, idan na fallasa wannan sirrin to fa kamar na ɗauki wuƙa na burmawa kaina ne, ko ƴan gidan mu da ƙawalli ba zan iya faɗawa ba, kuka na fara yi cikin ƙunar zuci.

Ina fita daga ɗakin Felicia ta lashi lips ɗinta abin ka da ƴar neman mata take ta ji sha’awata ta yi mata dirar mikiya,

“Wow…. This beb is beautiful….. Shege samz dama wannan Fulani girl ɗin ya samu, ya samu fine girl yana ta morewa abin shi….. To wallahi nima sai na ɗana, i most taste that girl, ko Samz yana so ko baya so sai munyi shearing ɗinta tare”

“Haba no wonder naji yana faɗawa friend ɗinshi wai he’s eager yaje wurinta dan rabonshi da ita it’s almost 2 months”

Kwanciya tayi ta rungume pillow tana lasar baki a idon zucinta tana hangoni tare da ita muna aikata masha’a amma cikin ranta alƙawari take yi wa kanta na dole sai tayi amfani dani koma me zai faru sai dai ya faru dan ita bata ganin macen da tayi mata ta ƙyale.

A ɓangaren samz kuwa yana bacci lokacin da saƙona ya shiga wayarsa, misalin ƙarfe biyu da wani abu ya farka kuma da tunani na ya farka dan alla alla yake yayi salla sai ya kirani amma me? Koda yazo kirana bayan ya idar da sallar sai yaga saƙon da na tura masa, dafe goshinsa yayi hankalinsa a tashe dan duk tashin hankalin da nake ciki nasa ya ninka nawa, tunawa yayi da zuwan Felicia jiya da yamma wai tazo yi masa weekend kuma tana da interview da zata yi da wani company sun yi magana da mommynshi tace ya bata Accomodation, babu yadda zai yi shiyasa ya bar mata gidan shi kuma ya koma gidan Ahmad ya kwana dan shi dai ba zai kwana wuri ɗaya da ita ba kuma tunda ya baro gidan bai koma ba har yanzun nan, ko ɗazu sai da ya gama yi wa Ahmad hira ta wai so yake yaje ya ganni ya ganni a video call na ƙara girma kuma nace banda ciki, dariya Ahmad yayi yace,

“Allah sarki ni wallahi tausayi ma take bani, haka kawai kana tarawa ƴar mutane gajiya, akan ka auro babbar budurwa ka tashi ka ɗauko ƴar yarinya wacce zaka yi ta cin zalinta….. Wai dan Allah tana iyawa da kai?”

Dariya yayi ya kwanta harda jan blanket ya rufe jikinsa,

” Idan tazo ka tambayeta… Da ina cin zalinta ai da ba zata rinƙa kuka idan zan taho ba….. ”

Tashi yayi domin zama bai kamashi ba ya san duk yanda aka yi na zo Abuja ne idan ba haka ba ta yaya zan san cewa Felicia tana gidansa? Yanzu dole yaje ya nemoni duk inda nake sannan ya zama dole yaje ya kori Felicia daga gidansa korar kare koda hakan na nufin fushin mommy akansa,

“Wai in saketa…. Am sorry baby, ai babu saki a auren mu insha Allah…. In sakeki ki auri wani kenan? Ohh my God idan hakan ta faru zan samu heart attack….. No my sweet baby” ya faɗa yana sauya kayan jikinsa, ko rufewa Ahmad gidan bai yi ba ya fita nemana, shine har su tasha, airport kasuwa da duk inda ya san zai iya samu na yasan da ace Anty na gari da gidanta zan nufa kai tsaye, waya ya kikkira Kano amma daga yanda suke gaisawa da ƴan gidan mu ya fahimci cewa ban sanarwa da kowa abin da yake faruwa ba, har magariba tayi yana nemana amma shiru ga waya a kashe wanda ya kira yafi sau ɗari,

Gidanshi ya koma yayi wa Felicia kaca kaca amma taƙi tafiya sai da taga dagaske haukansa yafi nata sannan ta tattara ta fita, shi kam rasa inda zai sa kansa yaji daɗi yayi daga ƙarshe shaiɗan ya fara raya masa ya ɗanje night club ya ɗan sha abin da zai kwantar masa da hankali, girgiza kai yayi domin ko ada lokacin da yake Christian baya shan giya bare yanzu da ya musulunta, giya da neman mata tun asali dama bai san daɗinshi ba bare yanzu,

Yanda na kwana banyi bacci ba haka shima ya kwana cikin damuwa da tunanin inda zai samoni, washe gari har asibiti yaje ya dudduba amma babu labari, gida ya koma ya zauna yayi tagumi yana saƙawa da warwarewa kan inda ya dace yaje, to ko Kano zai koma? Ji yayi gabansa ya faɗi kansa ya fara ciwo, zuwa can ya tuna da wani abu cikin sauri ya tashi ya ɗauko system ɗinsa ya buɗe text massage ɗin da nayi masa ya soma bin diddigi zuwa wani lokaci yaga daga inda na tura masa text ɗin, kai samz jaraba ne a harkar na’ura, kai tsaye hotel ɗin da nake ya nufa, har ɗakin da nake lokacin naci kukana na ƙoshi har hawayen sun ƙafe. Ina yashe ƙasan tiles kamar wata gawa dan ko ruwa da ƙyar na iya sha, abinci kuwa rabona dashi tun jiya, tabbas naji alamun shigowar mutum amma sai nayi zaton ma’aikatan hotel ɗinne sam ban kawo a raina cewa shine ba saboda ban taɓa zaton zai gano nan har yazo ba saboda wayata a kashe take, da yake acikin duhu nake ban kunna wuta ba amma duk da haka ƙamshin turaren black oud da naji sai da na ji ƙirjina ya rirriƙe domin sak irin ƙamshin da mijina keyi wanda nice da kaina na zaɓa masa wannan turaren kuma ni na fara siya masa,

Kamar acikin mafarki naji muryarsa,

“Baby” ai tuni naji wani gagarumin ƙarfi ya zo min, kishin da ya lafa ya motsa nan na rufe ido na fara zazzaga masa masifar da ta jima tana ciciyar raina,

“Mayaudari me ya kawo ka? Ka zo ka sake yi min daɗin baki ne? Watanni biyu ka tafi ka bar ni ashe kana nan kana tare da karuwarka….. Wallahi ban yafe ba cin amana ta da kayi, kuma wallahi sai ka sake ni…..”

“Am very sorry baby…… Pleas….”

Tun kafin ya ƙarasa na katse shi na fara tura shi waje dan bana son ganin shi zuciya ta zafi take yi,

“Ni ka fice….. Ka tafi bana son ganin ka….. I hate you….”

Har bakin ƙofa muka je ina tura shi wanda na san kawai ya ƙyaleni ne amma banda ƙarfin fitar dashi daga wuri indai ba yaso ba,

“Am so sorry baby… Pls allowed me to explain……”

“Ni babu abin da zan ji….. Bayan abin da idona ya gane min? Har fa gori tayi min da bakinta cewa ka bar ni a Kano ita kuma ka tare awurinta…. Wallahi ba zan zauna da kai ba sai ka sake ni”

Ƙofar ya riƙe yana center shi ba awaje ba kuma ba aciki ba, idan baka sani ba ka ganmu zaka yi zaton ko irin saurayi da budurwar nan ne suke hira, ƙoƙari nake ta yi na in rufe Ƙofar amma na gagara, tureshi nake yi da iya ƙarfina amma na kasa gashi naƙi barinsa yayi magana sai masifa nake yi masa ina dukansa, rabuwa yayi dani har nayi na gaji na sake zubewa a ƙasa ina kuka, kuka nayi mai isa ta kuma naƙi barinsa ya matso kusa dani bare har ya rarrasheni, haka muka kasance har dare, order ɗin abinci yayi mana amma ko kallonsa banyi ba ni dai bani da aiki sai kuka. Da yake ba acin bashin bacci ban san lokacin da ya kwashe ni ba, ƙarfe 6 na tashi, yana zaune kan kujera ya ɗan kishingida duk ya kakkama jikinsa amma ban kula shi ba, zuwa can na ga ya tashi ya nufo gadon yana haɗa hanya kamar wani wanda ya sha abin maye……….. ✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Back to top button