Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 44

Sponsored Links

My feena nikam yau naga se farin ciki kikeyi meye sirrin ?” rufe fuska tayi tana dariya sannan tace ” ummi Mr azaad ne yace yau zamuje gida ” ummi kanta taji dadin labarin dama tanada niyar mishi magana saboda yakamata ace taje taga gida murmushi ummi tayi tace ” ahhh to lallai wannan Mr azaad din yakyauta! Feena fatan de babu wani abinda yake miki na rashin jin dadi? ” Kwantar da kanta tayi akan kafadar ummi tace ” ummi babu abinda yake mini” ko kadan ummi bata yarda da abinda fanan tafada mata ba , domin kuwa yanayin yanda suke ganinta a yan sattitikan sunsan dole akwai abinda ke faruwa kuma ko sun tambayeta sede tace musu bakomai saboda fanan yarinya ce me hankali taki fa dane gudun fadan dazaa mishi bayan haka kuma bazata iya kai karanshi ba, amma yau ganin yanda take murna yasa ummi tafara tunanin Allah yafara hada kansu, hakan yayima ummi dadi sosai takara jin fanan aranta tare da alfahari da ita. ” Nikam ummi wai ina zeenat da su ya fawwaz ne gidan shuru sun tafi sun barki ke kadai” shafa kanta ummi tayi tace ” ai tun sha daya suka fita sunje gidan daughter! Shine zeenat wai sede taje ta kiraki kutafi tare fawwaz yace shide ba ruwanshi dan yasan son na nan jin haka zeenat dinma tafasa zuwa kiranki ” dariya sukayi atare aranta tana fadin” wato Mr azaad de kowa be bari ba ” haka tayini agun ummi suna hira nan ne ummi ke sanar da ita yaran kannenta nazuwa daga dubai gobe, ba ita tabar part din ummi ba se dataji ana kiran sallah mangrib yasa ta tafi part dinta tayi wanka hade da alwala tazo ta gabatar da sallah.
Shadda lace brown and golding color tasaka Riga da skirt dinkin rigar bubu ne yakawo har guiwa skirt din kuma pencil skirt gashi ta kafa dauri haka tagama shiryawa tsaff bakaramin kyau tayi ba bedroom dinshi tashiga tana adduah Allah yasa ya shirya agaban mirror ta sameshi ya shirya cikin wata hadadden yard white color, ” tsarki yatabbata ga Allah Ubangijin talikai dayayi wannan halittan” abinda ko wannen su yake fada aranshi kenan ta cikin madubi yake kallonta yakasa dauke idonshi akanta juyowa yayi suna facing juna tafiya yakeyi cikin takunshi na jaruman maza ya isa gabanta jan dogon karan hancinta yayi “aucchh Mr azaad hancina ” sake hancin yayi yana cewa ” bana hanaki kallona ba ” murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace ” to aini bakai nake kallo ba kaina nake kallo a madubi” kwaikwayan yanda tayi maganar yayi dariya yabata ganin yanda ya kwaikwayeta in tana magana, tambayar sa tayi ” to yanzu ya kakajin jikin naka ?” Amsa yabata” da sauki” . harsuka fito daga part dinsu inta tuna kwaikwayonta dayayi setayi dariya, girgiza kai yayi dan yaga inta fara dariya batasan bari ba .
Ahankali suke taka staircase din yana rike da hannunta, jin karan takalmi ne yasa dukkansu suka juyo suna kallonsu, hakan ba karamin dadi ya musu ba barinma yanda suka dace sosai tun kafin su karaso fawwaz yafara musu hoto tare da videos batare da sun sani ba, mutsu_mutsu tafarayi da hannunta tana son kwacewa sake rike hannun yayi kam yaki sakewa kunya ne ya cikata kamar ta nitse akasa haka takeji su abba,ummi , fawwaz,areef duk suna falon banda zeenat da zata kwana a gidan anty amina. Dukkansu murmushi ne dauke akan fuskokinsu yanda fanan ke kokarin kwace hannunta gashi Mr azaad yake sakin hannun abin yaso basu dariya sesuka danne, sallama suka musu suka fita tasowa securities sukayi dan rakashi hannu yadaga musu kawai packing space yaje yafito da motar kirar BMW baka, shiga tayi me gadi yabude musu gate harsuka iso babu wanda yayiwa dan uwansa magana. Yana yin packing akofar gidan tafito da gudu tundaga bakin gate take kwala kiran ” mama!mama!mama” duk suna zaune afalo suna hira kamar daga sama sukaji muryanta ya karade gidan tagumi baba yayi Yana kallon mama yace ” ohhh mamansu nikam yaushe fanan zata girmane” duka dariya sukasa fitowa ya Usman,ya al ameen sukayi , ya Usman ne yafara fitowa aikuwa tana ganinshi taje da gudu ta rungumeshi tana dariya, dariyar shima yakeyi na farin cikin ganin yar kanwar tashi.
Mr azaad na tsaye abakin gate yashigo yana harde da hannunshi akirji yazuba musu ido fuskan nan ahade kamar wanda akawa mutuwa hada ido sukayi da ya usman dake rungume da fanan ganin yanayin Mr azaad abin yabashi dariya domin babu abinda yake hangowa a kwayar idon Mr azaad daya wuce wutan kishi , kamar ancewa fanan ta kalli bakin gate aikuwa karaff suka hada ido dashi mugun kallo kawai yake watsa mata ba shiri ta raba jikinta dana ya usman, kwafa yayi yawucesu yashiga falon suka gaisa da mama da baba cikin girmamawa sosai suke alfaharin kasancewar Mr azaad a sirkinsu da suna tunanin wani rayuwa yarsu zatayi tare dashi saboda ko fuskanshi kadai mutum ya kalla yasan mutum ne me tsatsauran raayi da rashin magana amma bayan aurensu da kwana biyu yazo gidan kusan duk bayan kwana biyu se yazo gidan gaishesu amma betaba fadawa fanan yaje gidansu ba.
Rungume auta tayi sosai , haka ya al ameen ma sosai yayi murna da ganinta yana tsokananta ” yar kanwa wato seyau kikayi niyar zuwa ko ?” ” Ah ah fah ya al ameen” dariya kawai yayi, sake auta tayi ta cigaba da kwalawa mama kira harta shiga falon fadawa jikin mama tayi ta rungumeta sosai tana fadin ” mama na nayi missing dinki sosai” ” kai!kai fanan kede bazaki taba girma ba mutum kullum ace baya girma dagani karki karya ni” shagwabe fuska tayi ta daga maman tana ” yanzu mama bakiyi kewata ba ” ganin yanzu seta farawa mutane kuka yasa mama tace ” ah nikuwa nayi kewarki shagwababbiyata” dariya tayi ta sake rungumeta yau wani irin annashuwa take cikj na ganin iyayenta, haka taje gun baba tagama mishi shagwaba dariya kawai yaitayi yana kallonta yana jin wani irin daci aranshi babu yanda suka iya dolene seta tafi inde bata tafi ba sede wani ikon Allah shafa kanta yayi yace” Allah yamiki albarka ya kare mana ke da karewarsa ” duka suka amsa da abin. haka suketa hiransu dukda Mr azaad ba wani gwanin magana bane amma yau yadan sake wani yabada amsa wani kuma yayi shuru tashi tayi tashige dakinta dan tasan suhaima na ciki tana wayar jaraba kilama batasan tazo ba , aikuwa kamar yanda tayi hasashe tana ciki tashige bargo ta kashe murya tana waya da masoyinta , tsalle tayi tadira akanta afirgice suhaima tamike ganin fanan yasa tasa ihu suka rungume juna. cire wayar fawwaz yayi daga kunnenshi dan yaji muryan fanan murmushi yayi kasa_kasa yace ” kai matar babban yaya da baby se adduah” lura da yayi suhaima tamanta da suna waya sun baje da hira yasa yakatse kiran.
Shuru_shuru fanan bata fito ba se zuba ido yakeyi yana jiran tafito duk cikin abubuwan tabawa da mama ta kawo mishi drinks da fruit kawai yataba, suma yar hira sukeyi sama_sama da ya usman da ya al ameen kirane yashigo wayar ya usman ya mike yayi waje , picking yayi yanata hello hello bayajin me maganar network ya hana bude gate yayi yafita waje .

Magana yakeyi da yaron shagonshi idonshi ne ya sauka akan khairatyyy dake tsaye ta bashi baya iska se kada kayan jikinta yakeyi da dogon gashinta dayake sharan kasa, yanayin de abin tsoro in bil adama yagani amma ya usman de kara burgeshi tayi babu wani fargaba ko tsoro ya nufeta yatsaya abayanta tun fitowarshi a gida take sane dashi awajen amma batayi tsammanin har yanada karfin guiwan tunkaranta ba domin duk wani bil adama dayayi gamo da ita mugun firgita yakeyi amma shi meya taka haka , batare da ta juyo da gangan jikinta ba tajuyo da kanta kadai fuskanta ba alamun dariya ko wasa idon nan manya_manya dasu tace ” meya kawo ka nan kazo ka tsareni da ido babu ko tsoro a tattare dakai ” dariya ya usman yayi ganin tadage ita adole seta tsoratar dashi bata san son dayake mata ya kore duk wani tsoro da firgici ba , ganin yaki ce mata komai yakafeta da ido yana murmushi ne yasa ta murguda mishi baki tace ” kabari banaso kadena kallona kokuma in hukuntaka” shi komai tayi kyau take mishi dakara burgeshi ” kin taba kallon wanda yaji tsoron abinda yakeso ?” yamata tambayar yana kallon cikin manyan idonta dasuka zarce na bil adama, kara zaro su waje tayi tajuya ta kalli gaba daya arean dan tabbatar da babu wani jinni kana nan yaran aljanune kawai suke wajan suna wasa , kasa kasa tayi da murya tace ” baka da hankali ne? kokayi hauka ne? kode bakasan nidin wacece bace kakemin irin wannan banzan maganar to koda wasa kar kasake insake jin irin wannan maganar abakinka in bahaka kuwa ze iya yuwa inyi ajalinka ” tunda tafara magana yake kallonta sake matsowa daff da ita yayi yace” to aini hakan zezamo abin alfahari agareni ace wacce nakeso ce ta kasheni! balle ma nasan ke ba muguwa me cutarwa bace khairatyyy kiji tausayina kisoni kamar yanda nake sanki dan Allah ” yafada yana hade hannunshi duka biyu yana rokonta , dafe kai khairaty tayi yau taga takanta duk iya yanda zatayi ta fahimtar da ya usman kancewa babu maganar soyayya tsakaninsu saboda sudin ba jinsi daya bane amma yaki fahimtarta .
Sosai yabata tausayi tabbas ta yarda da irin son da yake mata amma dolene tunkafin yayi nisar da bazeji kira ba ta dakatar dashi , godiyarta daya tasan duk abinda suka tattauna sarauniya taji.
_____ zuruf fanan dake hira da suhaima tamike domin duk maganganun da ya usman da khairaty suka tattauna akan kunnenta tana jinsu fitowa tayi daga dakin ganin haka yasa suhaima tabi bayanta ,suna zaune afalo sukaga tafito da mugun sauri kamar zata tashi sama hannu daya Mr azaad yasa yariko ta dan sun lura ba lafiya ba irin yanda tafiton nan duk tunanin su wani abunne yake faruwa, Mr azaad ne yafara magana ” lafiya fanannnn ina zakije kike wannan saurin haka?” Ajiyar zuciya tasauke seyanzu ta lura a irin yanayin da tafito ko dankwali babu akanta gashi sun fara tunanin wani abu rike hannunshi tayi suka zauna akan kujera batare da tace musu komai ba ta daga kai ta kalli sama tace ” khairat kizo keda ya usman yanzun nan ” gaba daya lamarin yadaure mata kai taya akayi har ya usman yafada soyayya da jinsin daba tashi ba, ana haka yayi sallama yashigo yazauna kallonshi kawai fanan takeyi tama rasa mezata ce mishi ” kallon bakin kofa tayi tace” kishigo kema ” bayyana khairaty tayi taxube akan guiwowinta tagaida sarauniya,umarni fanan tabata data zauna itama, zama khairaty tayi tana satan kallon sarauniya sude da basu san meke faruwa ba sun kasa kunne da sunji abinda fanan zata fada.
Gyara murya tayi kafin tace ” khairat meye hadinki da ya usman danaji zancen soyayya natashi ” dafe kirji mama tayi tace ” so me? Kamar de kunne na ne beji dede bako?” alama baba yamata da tayi shuru su gama jin me fanan zata fada sukansu abinda yabasu mamaki amma banda ya al ameen daya san dama zaa rina.
______ kanta na kallon kasa tace” yake sarauniya bantaba sanin da wannan labarin ba se dazun yake sanar dani babu irin fahimtar dashi da banyi ba amma yakasa fahimtar babu wani soyayya atsakanin mu saboda mun kasance jinsi daban daban” sun gamsu da maganar khairatyyy . maida kallonta fanan tayi kan ya usman da har time din idonshi na akan habibiyarshi khairaty ” ya usman kabar wannan maganar saboda babu aure tsakaninka da khairaty kai bil adama ne itakuma jinnu ce hakan baze taba yiwuwa ba ” hararanta yayi yace” fanan wallahi inasonta ni ahakan na amince zan aureta ” daka mishi tsawa baba yayi kafin yadaura da ” usman ina maka kallon me hankali ashe babu taya zaka fara tunanin fara son abinda kasan bazaka taba samuba ko so kake ka lalata rayuwarka yar uwarka tafada maka illan hakan amma kai har kana wani cewa zaka aureta ahaka ” ” nooooo bazeyuba ba Ina san khairaty babu abinda ze rabani da ita se mutuwa! wallahi ba ni na daurawa kaina son taba Allah ne yadaura min bazan iya rayuwa ba in babu ita aciki dan Allah kutaimakamin ku auramin ita ” …………

 

Tofa ana wata ga wata.

Masu comment Allah yabar kauna ina godiya sosai Allah yamuku albarka.

Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy .

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & written by ✍️
MRS ISHAM

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

 

 

Back to top button