Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 46

Sponsored Links

Sun danyi nisa da tafiya se taga yacanza hanya kallonshi tayi tace ” Mr azaad ina zamuje naga nan de ba hanyar gida bane” batare da ya kalleta ba yace ” namanta ban fada miki ba dazun nagama cinikin kanki to yanzu zamuje a fille ne” iya tsorata fanan ta tsorata saboda ko kadan bataga alamar wasa a fuskanshi ba he sounds very serious mazgewa tayi tana turo baki tace ” da ka siyawa kanka rashin kwanciyar hankali dan wallahi nadinga maka fatalwa kenan” tuntsirewa yayi da dariya tare da taka birki motar gudun kar asamu matsala sosai yake dariya kamar ba Mr azaad ba, ya salam wani irin kyau yakara da yake dariyar kyawawan fararen hakoranshi su kansu abin kallo ne zuba mishi ido kawai fanan tayi yayi masifar mata kyau tun daga saninta dashi izuwa yanzu bata taba ganin yayi dariya irin haka ba se yau seta ga ma dariyar yafi mishi kyau ,koda shekara dari zasukai ahaka da wannan dariyar dauke akan fuskanshi bazata taba gajiya da kallonshi ba. hura mata iska yayi a fuska sauke idonta kasa tayi tana wasa da yatsunta jan motar yayi sukaci gaba da tafiya beyi packing a ko ina ba se a ice cream planet zallan ice cream ake siyarwa awajen wajan ya hadu sosai kaff gombe inde wajan da ake siyar da ice cream ne to yafisu kyau da tsaruwa, se fitar da hasken wuta kala_kala yakeyi tunda suka iso gun wajan yadauki hankalin fanan se kallon wajan takeyi tana sakin lallausan murmushi, ” muje ” kawai yace mata ya bude motar ya fito fitowa itama tayi suka shiga ciki , ice cream yazaba yafi kala biyar masu tsada mika mata ledar yayi yabada atm card suka cire kudinsu motar suka koma tun kafin yatada motar fanan tabude roba daya tafara sha se lashe baki takeyi ice cream din yamata dadi bata taba shan ice cream me dadi irin wannan ba , ahaka harta sha roba uku ta bude na hudu kenan zata fara sha yayi karaf yarike hannunta yakarbe ya ajiye kafin yace ” yanzu ke in anbarki se ki tazubasu a cikin ki ko ? Keda yakamata ki hana wani shine ke kikeyi to wayan nan se gobe” yatsina fuska tayi idon nan nata dasuke manya dasu yayi rau_rau kamar me shirin kuka tace ” ayyah Mr azaad kabarni in shanye Allah yanzu in bansha ba kwadayina ze tashi ” kallonta yayi ta gefen ido yaga yanda takoma abin tausayi aranshi yace ” wani abu se yarinta in bahaka ba mutum yata durawa cikin shi sanyi” afili Kuma yace ” idan kwadayin yatashi inada abinda zan bashi ” ganin ya manna mata hauka ne yasa tayi shuru tana bin ledar ice cream din da ido ahaka har suka iso gida.

Gyara packing yakeyi ta faki idonshi tadau roba daya tasa a hijab dinta tafito daga motar da gudu tayi ciki , murmushi kawai yayi dan yaga abinda tayi wato shi zatayiwa wayo , bin bayanta yayi yanda tasamu falon ba kowa shima haka yasamu duk sunshiga sun kwanta dakinshi yashiga yayi wanka ya sauya kaya izuwa sleeping dress ya kwanta.

 

Tana zaune a tsakiyar titi misalin karfe 2 nadare kafa yadauke babu kowa ba alamar koda kafar mutum se haushin karnukan dake tashi , zaman yan bori tayi gashi duk yarufe mata fuska ga mutum kwance agabanta cikin jini dake malala ajikinshi sanadiyar yaga cikinshi datayi kayan cikin duk suna waje itakuma se aikin cin namanshi takeyi zaro dogon hanji tayi tasa abakinta dake dauke da dogayen hakwara duk sun rine da jini , tana janshi kamar yanda akecin indomie harta gama cinyewa tass bata kyaleshi ba seda ta cinye duk wani nama ajikinshi yarage qashi bakinta ta kafa adede wuyanshi tana zuqan jini seda ta tsotse jinin kaff kafin ta dago kanta bakinta yayi dama_dama da jini zaro dogon harshenta tayi ta sude baki hade dayin gyatsa mikewa tayi tsaye tamaida gashinta baya nan take fuskanta ya bayyana ba kowa bace face zeenat Muhammad mainasara……

 

Kuyi hakuri da yanayin read more din yau wallahi yau nidince se a slow.

~Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy ~

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & written by ✍️
MRS ISHAM

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

 

Back to top button