Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

Kawali Ne 8

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*8*

 

Hankalin buƙata inyayi dubu yatashi,dan kuɗin sunkai naira miliyan dubu goma,

Ba inda be nemi siyama amma be ganta ba,tuni ya sanar da ƴan sanda inda sukazo akaita bincike baa gantaba dan beda hotonta,wayar ta kuma tabarta agidan bata tafi da ita ba,bata yadda zaayi ayi tracking ɗinta.

Hankali tashe ya kira rayhan,wanda tunda suka tafi american kishinta ke nuƙurƙusarsa koda yaga kiran nashi ya ɗauka sun dawo ne.

Koda ya ɗaga tun kan yay magana habu buƙata ya rigashi da cewa”rayhan dama ƴan damfara ka haɗani da ita,tazo tasace maƙudan kuɗaɗena to wallahi vasu satuba duk inda take ka nemota kubani kuɗina,”

“Alhaji wanne kuɗine kake magana akai,ni bansan mekakeson cewaba”cewar rayhan hankali tashe.

“dan bura ubanka zaka fahimtane in nadawo nigeria ku ƙananun ƴan iskane”yana kaiwa nan ya kashe wayarshi ya kira number shugaban dss.

Bayan dogon bayani yabasa address ɗin gidan rayhan ɗin.

Rayhan hankali atashe yakewa jabeer bayanin abinda yafaru.

“kace matsiyaciyar tazo taja mana masifane,to wallahi sede ajawa juna dan muma ƴan garine dan uwarta”cewar jabeer cikin ɓacin rai.

Shide rayhan shuru yayi yana tunanin mafita,jin an turo ƙofar anshigone yasasu waigawa afirgice dss ne.

Haka suka tafi dasu office ɗinsu su duka batare dasun basu damar kare kansuba.

Koda aka kaisu ajiye su akayi se buƙata yadawo ƙasar,wanda kamin zuwan nashi sunci duka kamar ba gobe.

 

Koda buƙata yazo ya faɗi yawan kuɗin data sace masa ba rayhan ba hatta jabeer seda hankalinshi yatashi.

“dan haka duk inda take ku amsomin kuɗina damuwata kenan inba hakaba wallahi senasa an ɓatar daku”cewar buƙata afusace.

“ranka ya daɗe ksyi haƙuri wallahi bamu da wata masaniya gameda hakan,amma muna neman alfarma zamuyi ƙoƙarin kawo rabin kuɗim, in yaso rabin abarmu mu nemota seta biya mu aware mana namu”cewar jabeer hankali tashe,

 

Rayhan bece komaiba dan yasan suna da kuɗin daya zarce 10b kawai tsananin mamakin siyamar ne yasa yakasa cewa komai.

 

Da ƙyar habu buƙata ya amince da buƙatarsu,take suka tafi gida suka haɗo kuɗin suka kawo masa,sannan aka basu lokacin dazasu kawota.

Bayan sun dawo gida tsabar takaici jabeer ji yake yaganta agabanshi ya shaƙeta

“wallahi rayhan in yarinyar nan ta faɗo komata sena yagalgalata,kaduba fa kagani 5b tasan shekarun da mukayi muna tarasu,tasan saɓon Allah nawa mukayi kan mukai haka,wallahi bazan ƙyaletaba”cewar jabeer yana huci kamar wani zaki.

“jabeer kai kafaɗi ma wani yajika,”cewar rayhan ransa namasa ƙuna dukan datasa akai musu.

tun daga lokacin bayan sun warke daga dukan da akai musu suka baza komar nemanta ta koina.

***********

 

Tun rayhana nasa ran ganin siyama ta dawo harta cire ga shi jikin ummansu ba daɗi kullum tana kwance ba lafiya,rayhanarce ke ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

Tun tana kukan rashin ƴar uwartata har tazo ta daina.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button