Ni da Patient Dina Book 1 Page 6
Page 6️⃣
Yadauko faro water ya shafa mata afuska ajiyar zuciya tasauke ahankali tafara Bude idonta, kamar amafarki kawai taga mutum na kallonta dasauri tamike zauna tana tariyo abinda yafaru, juyawa tayi takalli kan gadon nashi taga bayanan sannan tasake dawo da kallonta kanshi karfin halin qirqiro murmushi tayi ta tashi tsaye kafin tace yajikin naka shuru yamata bece mata komai ba ganin datayi bece komai bane yasa tayi tunanin to kode baya magana ne kokuma brain nashi yatabu Kara magana tayi tace tashi kaje kwanta indubaka da sauri yadago Yana kallonta daga sama har kasa wannan yar karamar yarinyar ce take mishi magana kamar wata mamarshi Mikewa yayi yaje gadon yakwanta yazuba mata ido Yana San ganin abinda zatayi fara dubashi tayi taga komai normal Amma tarasa gane abinda yahanashi magana sunkuyowa tayi da kanta gabb danashi kan tace meya hanaka magana shuru yamata bece komai ba takaracewa to kode Kai kurmane nanma shuru tofa alamu sun nuna kamarma bakajin abinda nake fada to shikenan yanzu de bari in kawo maka peper da pen karubutamin sunanka shide yazuba mata ido Yana jinjina surutu irin nata afuska kamar bazatayi yawan magana ba Amma kamar wata parrot duk tacika mishi kunne yama rasa meze ce mata. Zata Kara magana cikin tsawa yace shut up your mouth kinbi kindameni komawa gefe tayi tana kallonshi kafin tawani fashe da dariya harda rike ciki. Shikam yau yaga takanshi dama mahaukaciya akabawa kula dashi ohhhh kome tamishi lokacin dayake cikin coma oho. Tsaqaitawa tayi da dariyar tace walahi banyi tunanin zakayi magana ba tom yanzu de yakake yajikin naka sezuba takeyi shikuwa daure fuska yayi beko Kara kallon inda take ba, fita tayi daga dakin tawuce office din doctor ammar aikuwa tayi saa tasameshi da sallama abakinta tashiga tanata murmushi dagowa yayi yakalleta yace ah ah Fatima kece eh dama nazo fada maka patient Dina ya farfado ai tun kafin tagama rufe Baki yafita a office din suka shiga dakin abakin gado suka sameshi Yana zaune kanshi akasa . Karasowa kusa dashi doctor ammar yayi yace barka de be dago ba SE bayan 3mint yace yawwa bekara cewa komai ba. Yanzu meyake damunka dago ido yayi ya kalli doctor ammar , waro ido doctor ammar yayi yace AZAAD MUHAMMAD MAINASARA jiki narawa yace dama kaine dama kana Raye tsaki azaad yayi yace please banasan dogon magana nan wani garine domin kuwa tun kallo Daya dayawa Ammar yaganeshi, azaad nan garinkane garin gombe state ok yace,FANAN Dake tsaye abakin kofa tazuba musu ido tana kallonsu dago Kai yayi yaga tana kallonshi harara yawurga mata dasauri tadauke kanta. Sake dubashi doctor ammar yayi yace yanzu meyake maka ciwo ahankali yace babu kawai ciwon kaine okay dama shi SE ahankali zesake ka. Cewa yaushe zaaban sallama eh zaa sallameka Amma gaskiya zekai nanda 1week sbd kagama discovery ok yanzu de wannan kayan jikin nawa sun damameni am so exhausted to shikenan doctor ammar yace yafita dasauri. Karasowa dakin FANAN tayi taje tadauki glucose tahada mishi a cup Tamika mishi gashi batare dayakalla ba yamika hannu yakarba yakai Baki yayi yasha asukwane yatofar dashi ke Meye wannan Baki da hankali ne Zaki ban glucose, narai narai tayi da ido kamar zatayi kuka tace yanada kyau kadingasha hararanta yayi yace to bazansha ba din yanda yake mata tsawa ne yasa tafashe mishi da kuka dago Kai yayi ya Salam malama kimin shuru natsani Jin kuka Meye namiki dazakimin kuka , cikin muryan kuka tace meyasa kamin tsawa nibaamin tsawa agidanmu, shikam takaicine kamar yakasheshi yama rasa yanda zeyi da ita , to shikenan kimin shuru banason kuka share hawayenta tayi kafin taje kan kujera tazauna ahaka Sega doctor ammar yashigo shida wani security Yana rike da leda Niki Niki ya ajiye yafita doctor ammar dawo da kallonsa yayi kan AZAAD yace ga komai da komai Wanda zakayi amfani dashi fito masa dakomai ammar yayi yajerasu tsaff a wardrobe din dakin fito mishi da kaya yayi marasa nauyi Bakin wando dakuma Riga fari dasu brush tooth paste da takalmi da etc. Karba yayi bece mishi komai ba yawuce toilet yafara wanka. Fanan yanaga kinyi shuru kode bakyajin dadine inji doctor ammar lfy na KLAu doctor okay yace kafin yakara dacewa kinsan wayene azaad kuwa girgiza Kai tayi yace bakyajin sunanshi agari bama iya gariba har kasashen waje tace bantabajiba shuru yayi kafin yayi tunani okay Amma kintabajin sunan AZAAD THE BILLIONAIRE eh tabbas natabaji Amma ai Kwanan nan naji labarin ai yarasu ah ah berasu ba shine wannan ai zaro ido tayi tace dama shine eh mana kafin sukarasa magana yabude kofar toilet fitowa yayi tsarki yatabbata ga allah dukansu idonsu nakanshi FANAN kam suman zaune tayi kyaunshi yakara fitowa dogo ne sosai yanada jiki amurde irin wanyanda suke daga karfe yanada farfadan kirji kanshi kuwa gashine atare yagyarashi ga sajenshi mejan hankali yanada manyan ido dara dara sexy eyes ga dongon hanci bakinshi Dan karami Yana dauke da pink libs dawo da kallona nayi hannunshi dogayen fingers ne dashi masu dauke dagashi ya Allah azaad kota Ina yamatukar haduwa kamar shi yayi kanshi. AZAAD MUHAMMAD MAINASARA kenan shahararren Dan kasuwan da ake tunkaho dashi a Nigeria da kasashen waje saurayi Dan kimanin shekara 33yrs aduniya Wanda yakasance half cast mahaifiyarshi balarabiya ce mahaifinshi bafulatane Kuma babban Dan kasuwa Kuma Dan siyasa……
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
Story Written by (MRS ISHAM )
Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen
Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci
___________________________________________