Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 31

Sponsored Links

Page 3️⃣1️⃣

 

 

Dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan San gasgata wani azaad din yake nufi, gyada mata kai me martaba yayi domin tabbatarwa tunani tafarayi taya hakan ze kasance Mr azaad din da bawai sona yakeyi ba zasuce sun mana aure innalillahi wainna ilaijiraji unnn yah Allah Ina rokon ka daka bani iKon cinye wannan jarabawan. Ummi tarasa farin ciki zatayi ko akasin hakan tayi matukar jin dadin wannan labarin domin dama burinta bewuce fanan tazamo surkantan taba gashi Allah ya amsa adduah ta, amma abin tambayan anan shin fanan zata amince da wannan auren kuwa . Mama kam ji takeyi lamarin kamar amafarki cikin awowin dabasu wuce uku zuwa biyu ba har an tabbatar da fanan amatsayin matar aure lallai baa mamaki da iKon Allah me kowa me komai mai tsara komai ayanda yaso kallon fanan kawai takeyi tana tuna zata koma wani gida tayi rayuwa nan take taji wani irin kewarta yakamata, ganin tayi shuru kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta ne yasa baba cewa ” Fatima nasani ke yace me biyayya ga iyayenta bakya taba sabama umarninmu shisa akoda yaushe nake matukar alfahari na kasancewarki ya agaremu , wannan auren da akayi bawai anyishi bane dan kuntatawa daya daga cikinku bane ah ah! Anyi wannan auren ne domin kare mutunci da martabanku dakuma namu gaba daya, zaku iya fitowa duniya kununa musu kudin ma’aurata ne hakan shikadai ne ze wanke sunanku a idon duniya! Kuma iname tabbatar muku da sesun nemi afuwarku, auren nan da akayi yana daga cikin kaddarar rayuwarku Allah yariga daya kaddara azaad shine mijinki kema kece matarsa kiyi hakuri ki rungumi wannan auren in sha Allah zakiga alkharin dake cikinsa Allah yamuku albarka ”
She’s speechless gaba daya kalaman baba sun gama kashe mata jiki tama rasa takamemmen mezatace innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai take iya furtawa acikin ranta ahankali tafara samun nutsuwa.
Gaba daya tausayinta yakamasu Abba ne yace ” Fatima kifada mana shin kin amince da hakan dan bazaa taba miki dole ba munsan dole zakiji wannan lamarin awani iri amma munyi hakan ne saboda wanke sunanku” kanta akasa tana wasa da kyawawan yatsunta dasuka kasance chocolate color with her sweet voice tace ” na amince ” basuyi tsammanin hakan ba amma dasukayi laakari da fanan yarinya ce me biyayya ko da batasan abu bazata taba musawa ba kokuma taki bin umarninsu ba, alhamdulillah sukace atare yaseer ne yace ” yanzu abinda zefaru asamu ashawo kan azaad inyaso zuwa gobe se ashirya hira dasu agidan tv ” jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da maganarshi , cigaba da magana yaseer yayi yana kallon faisal” kashirya appointment da BBC news dakuma NTA domin sun dade sunason hira dashi Allah beyi ba seyanzu da dalili yazo nasan zasuji dadin wannan maganar ” ” to shikenan zanyi hakan yanzu base anjuma ba ” aikuwa yana gama magana ya lalubo wayarsa yayi dialing number customer service na BBC news macece ta daga tace ” hi, am Jenifer thank you for contacting BBC news how can I help you?” Maida mata da amsa yayi ” by the way my name is Faisal adamu I am azaad the billionaire official secretary luckily I want to inform you that your appointment has been approved ” wani irin ihun farin ciki tasa tana ” heyyy thank you jesus ” bama ita kadai ba hatta sauran ma’aikatan dasukaji labarin murna kawai sukeyi dan abinda suka dade suna jira kenan yin hira dashi bakaramin daraja zedagawa gidan tv suba domin he’s the most famous person da kowan ne suke bukatar tattaunawa dashi. Haka faisal yakara kiran NTA yasanar dasu kafin yakashe wayarsa. Duk shuru sukayi suna jiran suji abinda me martaba zece

____ ” alhamdulillah abu nagaba danakeso infada duk da kunsani kuma shine! duk yarinyar da aka daura aurenta tana tarewane agidan mijinta a ranar inbawai akwai wani kwakwaran dalili bane zehanata tarewa” yajuwa ga su ummi yacigaba” Aysha yau base gobe ba ku fara shirin daukan amarya banyan sallah isha ” daf!daf!daf gaban fanan yatsinke ta shiga uku yanzu ana nufin bazata kwana agidansu ba wani irin rayuwa zatayi atare da Mr azaad. Abinda baba yake tunani yazo daya da abinda mama da su ya Usman suke tunani taya zaayi amarya ta tare batare da iyayenta sun mata kayan daki daduk wani abinda ake bukata ba, suna bukatar abasu ko nan da gobe ne saboda bawai basu dashi bane Allah ya hore musu abinda zasu mata irin na yar gata ma kuwa.
Baba ne ya nisa kafin yace ” me martaba agafarceni, banqi ta taka ba domin kai amarya aranar da aka daura aurenta izuwa dakin mijinta bakaramin lada zata samu ba da albarkan aure saboda hakan shine ka’ida ! amma abamu daga yau zuwa gobe wannan auren yazo mana baa kan shiri ba bamu tanadi komai ba in sha Allah daga yau zuwa gobe inyaso se azo adauketa” murmushi irin tasu ta manya me martaba yayi yana kallon yan falon gaba dayansu sannan yace ” shin awani ayah ko hadisi kukaji ance kayan dakin mace dakuma duk wani abinda zata bukata agidan aurenta yarataya aka wuyan iyayenta ? To bari kuji abinda kuka manta a musulunce muddin mutum ya auro mata komai yanakanshi daga abinda yakama gida wato muhalli, kayan amfanin gida, tufafinta, shanta da ciyar da ita duk ya tattara akan wuyanka amatsayinka na shugaba agareta! Yanzu ne da zamani yake juyawa yakoma juyi_juyi iyaye suka fara kai yayansu da kayan su gado su setin daki dasauransu amma badole bane wannan kuma yin hakan shike Kara sangarta mazan sukeyin duk abinda suka gadama gadaransu yanzu shine kawai sadaki zasu bada da kayan lefe se gida shikenan amma da su sukeyin komai da komai dakansu bazasu taba kuskuren sakin matansu ba dan haka babu abinda fatima zata tafi dashi gidan mijinta koda kuwa cokali ne ” babu yanda su baba suka iya tabbas maganar me martaba gaskiya yafada amma yanzu anawa mata hakane domin gudun reni ko kana nan maganganu.
Abba da ummi kuwa sunji dadin maganar da me martaba yafada domin suma abinda zasu fada kenan yarigasu domin sune da matukar godiya da baba yabasu auren fanan yarinya me hankali da tarbiya babu gidan da bazaayi farin cikin samun yah Kamar taba .
Karfe 5:00 saura Adduah me martaba yayi sosai taro yakare, mikewa yayi rike da sandar shi yana musu sallama su fulani da galadima suma sukabi bayanshi suka tafi, su abba ma fitowa sukayi zasu tafi suka rako su har bakin gate suna musu se anjuma insunzo daukan amarya tare da musu godiya sosai ahaka sukayi sallama . Komawa cikin gida sukayi suna jinjina iKon Allah babu wanda yayi zaton haka awannan lokacin zama sukayi suna dan maida magana mikewa fanan tayi tabarsu afalon bin bayanta sukayi da kallo gaba daya jikinsu babu laka bin bayanta suhaima da amira sukayi dakin akwance suka sameta kanta na kallon saman celling kamar wata me tunani zama sukayi akusa da ita.
Baba ma dakinshi yashiga bayanshi mama tabi dan tanason jin yanda sukayi dangane da fanan.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & Written by..
MRS ISHAM

Back to top button