Kurkukun Kaddara Book 2 Page 9
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E9_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._
Wuraren ƙarfe biyar da rabi na marece, Aneelerh ta fito daga cikin toilet bayanta a goye da baby junaid tayi mashi wanka ta ɗaura mashi towel, A saman Gado ta kawantar da shi fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan zaro mashi ido tayi”Why are u smilling at me”?
“Mommy daɗi nake ji, Angel zata dawo” aɗan ruɗe ta bi shi da kallo”Junaid! Waya faɗa maka Angel zata dawo”? Da yatsan hannun shi ya nuna mata saitin zuciyarshi, murmushi ta saki haɗi da ɗan girgiza kanta”my baby boy nima ina ji araina ƴar uwarka ta kusa bayyana in sha Allahu nan bada jimawa ba, in dai tana numfashi a doron duniyar nan….”tunkan ta rufe baki yace”Mommy Angel tana sona? ɗaga mashi kai ta yi alamar eh”Angel tana sonka junaid tun kafin zuwanka duniya ta ƙwalla fa rai akan son ganin ka,”
Ta yi maganar tare da juyawa ta nufi gaban mirror ta ɗauko Mayukan shafawarshi, a saman mattress ɗin ta ɗaura su, ta soma shafa mashi ajikinshi.
“Aunty Aneelerh,!” muryar zahra ce daga waje take kwaɗa mata kira, A hanzar ce Junaid ya buge hannun Aneelerh data ruƙe shi, ya damƙi towel ɗinshi dake yashe saman katifar, Lamarin yai matuƙar ɗaurewa Aneelerh kai, ganin yadda yake kiciniyar ɗaure qugunshi, duk don saboda zahra kada ta gan shi babu kaya, Kafin zahra ta faɗo ɗakin tuni ya kammala maida towel ɗinshi sai faman haki yake yi, ƙasa ƙasa da murya tace”junaid ban kammala shafa maka man ba”, turo mata baki yai”Ni ae bana sho Aunty zahra ta gane min abuna, idan ta tafi sai ki ƙarasa shafa man….”kumshe dariya Aneelerh tayi abakinta.
“Aunty Aneelerh Abie da daddy suna son Yin magana dake, Na riga na faɗa masu komai game da tada zancen 6acewar su tajuddeen, sun amince da yin hakan” Farin Ciki ne ya bayyana akan fuskar Aneelerh”Zahra, zanje yanzu mu yi magana da su, Ga junaid nan ki cigaba da shafa mashi…” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon toshe mata baki da Junaid yai da tafin hannun shi, Kallon fuskarshi tayi, 6acin rai ta gani akanta.
Ta6e baki zahra tayi idonta akan fuskar Baby junaid,”Kin ga Aunty Aneelerh Ki tashi ki je suna a palour, bana so damar nan ta wuce mu, Ki barni dashi zan ƙarasa gyara mashi jikin” amsa mata ta yi da toh, kafin ta sakko daga saman gadon ta nufi closet ta buɗe ta curo mayafinta bayan fitarta ɗakin, Junaid ya takure kanshi jikin headboard na gadon, lallashinshi ta soma yi”haba habibina meye na 6ata fuska nifa ma mommyn ka ce, zo nan in gyaran maka jikin ka, Maƙe mata kafa ɗa yai”so ki ke ki kalle mun abuna, ni banso, Zan jira mommy ta dawo”
ɗaure fuska tayi ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta haye gadon ta cafko shi, ya dinga kuka yana shure shuren ƙafa, daƙyar ta samu ta shafe mashi jikin tana fadin”ɗan jakar uba, Jiki duk madara, da ace baka da kyau ko kallo baka ishe ni ba” tur6une mata fuska yai hada jifarta da harara, Miƙewa tai daga saman gadon ta sauko ta nufi closet din kayan su ta ɗauko mashi riga da wando, ta dawo ta zauna gefen shi, a tsanake ta zura mashi a jikinsa, tunkan ta kammala Wayar Aneelerh ta soma ringing
“Wayar mommy tana ringing” junaid ne ya sanar da ita
“Ni bana ɗaga wayar mutun idan bashi ya bani izni ba” gatsina mata hanci yai”Angel ce ke kira aunty zahra dan Allah ki ɗaga, kada ta katse” kwantar da kanshi tai saman ƙirjinta, faɗi yake ni ki sake ni, inje in ɗaga kiran Angel” taƙi barin shi ya motsa, suman kanshi take shafawa da hannunta, shiyasa ya ke gudun zahra ta ɗauke shi, kamar ta samu lallausan bready haka take daƙuna shi.
Bayan fitar Aneelerh A palour ta taras da Uncle ɗan Iya tare da abie hada Mommy da Ummi zaune saman Sofa, cikin girmamawa ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe su, A mutunce suka amsa mata, daga ƙasan sofa ɗin da mami da ummi ke azaune ta jingina bayanta, tare da sunnar da kanta tana jiran jin me zasu ce.
Gyaran Murya uncle ɗan Iya ya yi, hakan yasa ta ɗago da ido ta kalle shi, ya ƙwama farin Glass a fuskarshi Ya ɗan sauko har saman karan hancinsa, a halitta baƙi ne wulik, kamar ba jinin Abie ba, yana da Manyan idanuwa hancin shi a wargaje yake, Haka bakin shi manyan la66a ne dashi, wandon shadda ne a jikin shi Daga sama Malun malun ce babi Ƴar Ciki, Ya ƙwama Hula Akanshi Ga uban sanƙo, a saman Kujera mai mazaunin mutun uku suke zaune su Biyu, gyaran murya yai kafin ya soma magana”Zahra ta faɗa min komai, a gaskiya kun kawo shawara mai kyau, Kunyi tunani na hankali” yana magana yana watsa hannayenshi Ɗabi’arsa ce Yin hakan.
“bai kamata don abu ya haura shekaru da faruwa muja baki muyi shiru, tun da har yanzu bamu da tabbacin suna araye ko sun mutu! Idan ko suna araye ba ƙaramin ganganci mu kayi ba, Na watsar da zancen 6acewarsu, wata’ƙil Silar tada zancen Allah Ya bayyanar mana dasu…..” tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Aneelerh ta duƙar Da kanta ƙasa Farin Ciki duk ya cikata, gani take kamar ma har an riga an ganso su.
“In sha Allah zanyi magana da ziyad babban ɗan jarida ne muddin labarin nan ya je gare shi ina mai tabbatar baki da cewa cikin ƙanƙanin Lokaci Duniya zata ɗauka tamkar bai jima da faruwa ba, a manyan Kafafan sada zumunta za’a yaɗa labarinsu, irin su BBc, CNN, and ONt, muma kuma zamu bada gudummuwar mu, wurin Yaɗa hotunansu a social media”
Bayan Uncle ɗan Iya ya takaita da zancen nashi Abie ya ɗaura da cewa”kafin Gobe ki tabbatar kin tattara duk wasu hotunansu Tajudden kin tura mashi, Sannan Adage da addu’a duk danasan kina ƙoƙari wurin yi masu, Mamie ta fadamin kullum sai kin tashi yin nafilfili dare, naji daɗin jin hakan sosai, Allah yayi maki albarka” amsa mashi ta yi da ameen, Mamie tace”Ubangiji Allah ya bayyanar mana dasu, Allah yasa silar tada zancen 6acewarsu da za’ayi su bayyana, mungode sosai” godiya suka hau yiwa Uncle ɗan Iya, kafin daga Bisani Aneelerh ta miƙe tare da yi masu sallama ta Nufi bedroom ɗinta tsabar zumuɗi kamar zata tashi sama, lokacin da ta shiga ɗakin, A kwance ta samu zahra tana fuskantar ceilling hannunta a ruƙe da wayarta, ga dukkan alamu Chatting take Yi, Baby junaid tuni ya jima dayin bacci yana kwance saman ƙirjinta. Jin motsin shigowar Aneelerh Yasa ta ɗan kawar da kanta daga kallon wayar ta take Yi ta kalli Aneelerh tunkan ta ƙarasa shigowa ciki Ta lura da tsantsar farin Cikin dake akan fuskarta
“Yah aunty Aneelerh Ina fatan komai lafiya”tana murmushi tace”abie yace in tura ma Uncle hotunansu tajuddeen wlh bakiji daɗin da naji ba,”Zahra na murmushi tace”Allah yasa Adace sister, nima zan tayaku sharing a instagram page ɗin mu,” Godiya Aneelerh ta yi mata, ringing ɗin wayarta ne Yaja hankalinta ga duban saman pillow, Da sauri ta nufi wayar takai hannu ta dauke ta
“Bansan wanene ke kiranki ba, Tun ɗazu bayan kin fita wayar ke ta ringing ban daga ba”
“Why ba ki ɗaga ba zahra, Surukata ce fa” ta6e baki zahra tayi”matar da ke son ƙwace mana baby junaid ɗinmu ai ƙwara daban ɗaga ba” picking call ɗin Aneelerh tai tare da kanga wayar a kunnanta.
Cikin girmamawa tayi mata sallama”Assalamu akaikum” on the other hand Hajiya adama ta amsa mata da”Wa’alaikum salam daughter In law, ina kika shiga inata kira ba aɗagawa”? aneelerh tamkar tana agabanta tace”Bana akusa da wayar ne bansan kun kira ba” gaisawa sukayi kafin hajiya adama tace”guest what”? ɗan zaro ido Aneelerh ta ɗanyi tana wurwurga eye balls ɗin ta can tace”kun dawo ƙasar”? Sautin dariyar hajiyar adama ne yasa ta saki murmushin farin ciki.
“Mun dawo, in sha Allah end of this month zamu shigo Abuja, two days kin daina kiran layina Why? Ko dan saboda kada na ƙwace maki Yaro”? Cikin Jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, wlh ina ta zucci zuccin in kira ki Allah ne bai nufa ba” Tai maganar a yayin da take kokarin zama saman stool, Ta gaji da tsayuwar, Zahra ta kasa kunne tana sauraron Firarsu.
“Idan ma don saboda dashi ne to ki kwantar da hankalin ki, babu wanda zai raba ki da ɗanki, Munyi magana da abdallah Ya fahimtar dani game da cutuwar da zakiyi idan muka ce zamu raba ki da shi, Ni kaina bazanso Inyi silar sanya ki baƙin ciki ba….” buɗe ido Aneelerh Tayi Wani irin farin cikine tsantsa akan fuskarta, Zahra da ta tsareta da ido tana kallonta, sai faman yi mata mimi da baki takeyi donta fada mata me Hajiya adama ke fada mata wanda yasa ta farin ciki
“Zan kira mamin naki mu yi magana, Sannan akwai wata gagarumar kyauta dana shirya maki idan mun zo zaki gani” Hawayen farin Ciki ne su ka wanke fuskar Aneelerh, kasa jurewa tayi batasan lokacin da kuka ya kubce mata ba. Muryar Hajiya adama a ɗan ruɗe take fadin Aneelerh why? Kuka kuma? Meya faru? cikin shessheƙar kuka tace mata kukan farin Cikine, taji daɗin ƙaunar da take nuna mata, tana alfahari da su, samun surukai irinsu abune mai wuya, Hajiya adama taji daɗin daɗaɗan kalaman da Aneelerh take faɗa mata, tsawon lokaci suna waya Kafin daga bisani Tayi mata sallama, Idanuwanta acike tab da ƙwalla ta wurga su kan fuskar zahra tambayarta ta shiga me suka tattauna da Hajiya adama? Nan Aneelerh ta sanar da ita komai, Fasa ihu zahra Tayi tare da jefar da wayarta gefenta, ta sauke junaid daga saman jikinta a hankali ta kwantar dashi, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi Aneelerh ta rungumeta kamar zata maidata ciki, Farin Ciki duk Ya cikasu, Miƙewa Aneelerh tayi bayan ta ajiye wayar gaban mirrror, Rawa suka soma takawa ita da zahra, hada ɗebo shoki suna kifawa saman goshinsu, Yayin da suke sakin Dariyar murna.
*EVIL FOREST*
A ƙalla yau satin su ɗaya acikin kogon dutsen ba tare da sun motsa ba, saboda marasa lafiyan cikinsu, jikinsu yai tsauri, duk da haka suna ƙoƙarin basu kulawa ta musamman, Danish Ya haɗa masu garin maganin da su ke sha suna samun warakar raɗaɗin ciwonsu, A cikin gorar ruwansu ya ke jiƙa masu maganin, Bayan haka duk in za su yi tsarki da ruwan zafi su ke yin shi, danish ne yai masu dabarar yin hakan, Alhamdulillam Jikinsu Azeeza yayi kyau sauƙi ya samu, ba su rasa ci da sha ba, kullum ne sai sun ci abinci sau uku, Danish ne ke ƙoƙarin yi masu farautar abunda zasu ci wani sa’in zoman daji yake kaso masu ko tsuntsaye hada kayan marmari ya ke samo masu, saboda su ya ke hana idonshi bacci, A zaune yake kwana shi da Angel dinsa, tana ɗebe mashi kewa, shaƙuwace mai ƙarfi a tsakaninsu.
Burinsu marasa lafiyar cikinsu su ƙarasa wartsakewa ko sun samu su cigaba da tafiya.
Yau tun da sanyin safiya ta soma Jin hayaniya acikin kunnuwanta, ƙasa ƙasa take iya jin maganganunsu, Tsantsar mamaki ne ya kamata Jin muryoyin su Batul, tamkar a mafarki, a harzarce ta buɗe idanuwanta tare da miƙewa zaune tana ƙarewa Kogon dutsen kallo, Haris ne kaɗai ya rage a kwance yana bacci, Ya ƙudundune kanshi cikin bargo, ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya ta soma yi, da wata irin kasala ta miƙe tsaye tare da yin hamma, abu biyu ya ɗaure mata kai da farko tayi tsammanin zata ga su Azeeza sai dai bata kowa ba.
Hankalinta A matuƙar tashe ta fito tana ƙarewa Dajin kallo, Kamar daga sama tajiyo muryar Jemimah tana ambaton Sunan da take kiranta dashi”Genie!’ ras taji gabanta Ya faɗi, A ruɗe ta wurga ƙwayar idonta kansu, Gaba ɗayansu ne banda Haris, Yau wata rana sun fito daga kogon dutse jiki yayi kyau, Sai wasa suke Yi suna tsalle tsalle, Farin Ciki duk ya cikasu, Bakunansu awashe kamar gonar auduga, ba ta san lokacin da hawaye suka soma wanke fuskarta ba, Nan ta ke ta zube saman gwiwowinta tare da kifa kanta ƙasa ta yi sujjada tana godewa Allah da ya nuna mata wannan ranar, Haƙiƙa tayi farin ciki mara misaltuwa, kafin ta ɗago daga sujjadar Jemimah ta watso da gudu ta faɗo saman bayanta, sai tiƙar dariya ta ke yi tana fadin”Genie Daɗi kamar zai kashe mu, Wlh daɗi muke ji, wannan wurin mai kyau bamu ta6a ganin irin shi ba, Genie Yau zamuje gidan daddynki ko”? Kasa ɗagowa Angel tai, wani irin yanayi take jin kanta.
Ƙarasowa Azeeza tayi Hannunta ruƙe cikin na Gabriel, Sauran Ƴan uwansu na abiye da bayansu, agaban inda tayi sujjadar suka tsaitsaya suna kallon ta
“Angel muna son yin magana dake”muryar parveen ce ta ratsa kunnanta, daƙyar ta iya haɗiye kukan da ke shirin kubce mata ta ɗago da kanta, tare da zagayo da hanneyenta biyu ta ruƙe Jemimah gudun kada ta faɗo daga bayanta
Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, tun daga kan fuskar Azeeza dake ta sakin murmushi, fatar jikinta tayi haske sosai dama ita can launin skin ɗinta na farar fata ne, da launin gashinta, ta rame sosai ta ƙara komawa ƙarama. ɗauke idon ta tayi daga fuskar Azeeza ta mayar dasu kan fuskar parveen, itama ta faɗa duk sunyi haske kamar fatalwu, Murmushi ta ɗan saki tare da kallon Batul dake a tsaye tana sakar mata murmushin ƙauna.
“Rabin rai kin tashi lafiya, Nasan kinyi mamakin ganin mu awaje muna shan iskar duniya, Danish ne ya fito da mu waje kuma yace da zarar ya sama mana abinci mun ci zamu kama hanya” lumshe ido Angel ta ɗanyi tare da ware su kan fuskar Hannah.
Muryar Gabriel ce ta janyo hankalinta ga kallon shi”Muna so muyi maki godiyane akan irin ƙoƙarin da kikayi mana, Angel kin cancanci ayaba maki, babu wasu kalmomi da zamu Iya yin amfani da su wurin yi maki godiya ke da Danish, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku” Cikin sanyin murya tace”Allah shine abun godiya Gabriel, Alhamdulillah ala kullu halin, ina taya ku murnar Samun ƴanci arayuwarku, Kuma inayi mana fatan Allah ya bamu sa’a adukkannin abunda muka sa agaba, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalar mu ce tazo….” addu’o’i ta dinga jera masu suna amsa mata da ameen, Sai da ta kai ƙarshen maganarta, muryar jemimah ta katse ta”Genie ba zamu ƙara komawa kurkuku ba ko?” Batul tace”har abada mu da kurkukun ƙaddara, Daga nan sai Gidan daddyn Genie, ko kina son komawa ne”? Zaro ido tai tare da girgiza kanta”banso, Allah ya tsinema su da tsohuwa zafreen, muguwa idan mu ka yi ƙarfi sai mun kashe su, damu da daddyn Genie, zamu rugurguza kurkukun kowa ya huta, Kuma zamu ƙwato ƴan uwanmu da ke a wurinsu” ranta a6ace ta ke yin magana, kumatunta sunyi jawur da su.
Angel tace”In sha Allah Jemimah mune zamu kawo ƙarshensu, Allah sai ya saka mata cin zalunmu da su ka yi, haƙƙin mu ba zai ta6a barinsu ba, tun agidan duniya zasu fara gir6an abunda suka shuka” tana magana hawaye nabin fuskarta.
“Angel Ba ki faɗa mana ina ne nan ba? Munga wasu abubuwa da su ka ɗaure mana kai waɗanda bamu ta6a ganinsu ba ko a mafarki,” Javed ne yai mata maganar fuskarshi da alamun ruɗu.
“Angel munga kalar ganyan da ake kawo mana muna ci a kurkuku,” still fuskarta da murmushi ta yunƙura ta miƙe hannunta ruƙe da Jemimah, Gabriel ta kalla”meyasa baka yi masu bayani ba”? Ta6e la66ansa yai”sun fi so suji daga bakin ki,” Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa”Okey, Ku jira Danish Ya dawo, idan muka kammala cin abinci, muka kama hanya zanyi maku bayanin komai” amsa mata su ka yi da toh. Kafin wani ya ƙara cewa wani abu, Motsin tafiyar Danish ta janyo hankulansu ga dubanshi.
A tsanake ya ke yin tafiya yana tunkaro su, hannun shi ɗaya a ruƙe da kwandon da ya haɗa masu saboda ajiyar kayan abincin su, tunkan ya ƙaraso Jemimah ta sauko daga bayan Angel, da gudu suka nufe shi ita da Azeeza da parveen, atare suka faɗa mashi tare da ƙanƙame shi suna sakin dariyar farin ciki.
Ganin shi suke yi tamkar mahaifinsu, saboda kyautatawar da ya ke yi masu wurin yin jinyarsu, nufo wurin su Angel tayi tana faɗin”Sannu da dawowa My Man, Na farka ban gan ka, meyasa baka tada ni mun tafi atare ba” ta yi maganar tare da kai hannu ta ruƙo hannun Kwandon da ya ruƙo, sakar mata yai ta kar6a tana leƙa cikinsa Kayan marmari ne ashaƙe cikin kwandon.
Da sauri ta ɗago suka haɗa ido da juna, murmushi ta sakar mashi”sannu da ƙoƙari, duk namu ne wannan,” ɗaga mata gira yai alamar eh, “mun gode Danish, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka,” lumshe mata ido yai kafin ahankali ya ware su akan fuskarta.
Su Parveen sun ƙi sakin jikin shi tun da su ka rungume shi ba su ɗago ba, faffaɗan tafin hannun shi ya ɗaura asaman kawunan su a hankali ya ke shafa sumarsu kan su, sai ƙara ƙanƙame shi suke Yi, a hankali ya furta masu”Ya Jikin naku”? Jemimah da Azeeza suka haɗa baki”Ai mun warke, Gidan daddyn Genie zamu je yau”
Ganin sunƙi sakin shi yasa Angel yi masu magana”ku sake shi mana, Ko mun samu muyi sauri muci mu tafi, idan har ba barin Dajin nan mukayi ba Hankalina ba zai kwanta ba” Jin maganarta yasa suka sake shi, Ya ruƙo hannun Azeeza dana Jemimah suka jera atare suna tafiya, Cikin Kogon dutsen su ka koma gaba ɗayansu, suna shiga suka tarar da Haris zaune shi kaɗai, bai jima da farkawa daga bacci ba, A ƙasa kowanansu ya zauna, Angel ta curo kayan marmarin ta rarrabamasu, A tsanake suke sha suna kallon Juna, bayan sun kammala sha, Suka fara shirin tafiya, Ba tare da 6ata lokaci ba, Angel Ta goya jemimah abayanta da mayafi ta ɗaureta, Gabriel Ya goya Azeeza abayanshi, sai daɗi suke ji an goyasu har gwalo suke Yima Parveen, Batul kuma ta Goya Back pack ɗin Unaiza abayanta, Javed Ya ruƙe masu akwatin kayansu, basu bar komai acikin kogon ba, Hatta Gorar ruwansu acikin kwandon kayan marmarinsu su ka sanyata, Parveen ce ta ruƙe kwandon a hannun ta.
Matafiya sun shirya tsaf saura tafiya ta rage masu, kafin fitarsu daga kogon dutsen saida Angel ta yi masu addu’o’i tabi kowan nan su ta tofe shi tun daga ƙasa har sama ko da ta zo kan Danish sai ce wa yai me take yi haka? ta daina watsa mashi yawu baiso, dariya tayi batare da tace mashi komai ba, Danish ne ke ruƙe da Haris saboda rashin ƙwarin Jikin shi.
Suna tafiya suna fira a dokar dajin, Su parveen sunga abubuwan da suka ɗaure masu kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta ƙwalo Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo, Angel sai ƙoƙarin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya kashe masu idanuwan su.
Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al’ajabi, su fa duk ɗaukarsu Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling ɗin ɗakin su na kurkuku Yake, Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta faɗa mata tayaya akai har aka ɗaura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba,” Dariya Angel tasaki tare da cewa”Kai parveen Nafa ta6a faɗa maku saboda gudun haka, Rana ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya ɗaurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai daƙyar ta samu suka fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya tunawa, A ƙalla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko’ina acunkushe yake da tsirrai.
Gaba ɗaya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance Har bacci ya ɗauke su a goye sai daga bisani suka farka,
“Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? Ƙafafuwana duk sun rurruƙe, Ga yunwa inaji” Parveen ce tayi maganar,
“Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba zamu ƙare acikin Dajin nan ne,” fuskar Angel ayamutse ta yi maganar,
Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ruƙe.
Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada tsokanarta”ƙatuwa dake dole sai an maki goya irin namu” Harara parveen ta watsa mata. Ba tare da tace komai ba.
Zogin da ƙafafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata ƙatuwar bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan tasha ta miƙa ma Naufal yasha ya miƙa ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu suna faman lumshe idanuwansu,
“karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido,” Angel ce tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace”kaɗan zamuyi, ” batul Ta natsu tana kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu,
“Angel Su waɗannan basu gajiya da tsayuwa ne”!? Fuskar ta aɗaure tayi maganar babu alamun wasa
“Su wa kike nufi” Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata Bishiyoyin dake fuskantarsu, Ɗan zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a kwance taci gaba da cewa”tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne”? Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, daƙyar ta iya cewa”Haka Allah ya Halicce su Batul”
Gabriel da ya ƙumshe dariya abakin shi yace da ita”ke yanzu idan waɗannan bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa”? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka ɗanyi na wani lokaci, Har bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take ji, Ɗaukarta Angel tayi tare da miƙewa ta kalli Danish”Zanje nakaita tayi fitsari,”lumshe mata ido yai tare da cewa”No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko abayan bishiya ne” Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita, bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan, Miƙewa su kayi jiki duk ba ƙwari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya azeezarshi suka dasa da tafiya.
Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta faɗo wurinsu kamar an jehota, a matuƙar figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da su ka yi.
Hankalinsu Danish ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse waɗanda suka rage Danish ne sai haris shima saboda Ya ruƙe shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da Haris jikin bishiya da gudun gaske ya faɗa Cikin Dajin don Ya tattarosu.
Jemimah ta ƙanƙame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar baki, Ciyawar dake awurin take Ci,
Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya karaɗe kunnuwansu
“Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, ƴan nonuwanta azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko”? shiru Angel bata tanka mata, Damuwace ƙarara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba adawo dasu Batul ba.
Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta faɗo wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita, Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma ya ɗaureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah kaɗai yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro.
“Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne” Gabriel yai maganar, da sauri tace”A’a, Kada kaje ko’ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka shiga Danish zai nemo su”
Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin ƴan uwansu, suka soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke maza, Batul na aruƙe da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su ƙaraso Angel ta fashe da dariya hada dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba ƙaramin ƙona ransu yai ba.
Ko da su ka ƙaraso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne suka sani,’ Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta ɗaura da nata faɗan akan dariyar da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, Ruƙo haris danish yai tare da taimaka mashi ya miƙe tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta daji gwanin ban sha’awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu shimfiɗa, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya haɗa masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su kaɗai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu ɗaya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya ɗaga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya ke ɗaukar su Ya nutsa dasu Cikin dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya sauƙaƙa masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani baƙon Yanayin a jikin shi, fargabarshi kada Giant’s heart ɗinshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.
*PRISONERS*
Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiɗarsu, Sai faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ƙoƙarin fuskarshi.
Angel da ke a kudundune cikin bargo taƙi runtsawa duk don saboda shi, ta kasa samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta miƙe tana miƙa ta nufi inda yake zaune, Tunkan ta ƙarasa taga yana gyangyaɗi Ƙiris Ya rage ya kifa kanshi Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ƙarasa tare da zubewa gefen shi saman gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya gaza buɗe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta, idanuwanta suka ciko tab da ƙwalla, tsananin tausayinshi take ji.
“Danish muje mu kwanta,” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”bazan iya bacci ba Angel idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta silar rauni na” ƙara ƙanƙame shi tayi a jikinta”In sha Allah ba abunda zai same mu Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu’a, Kada kaji komai kazo mu kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata” A hankali ya zagayo da hannayenshi saman waist ɗinta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai ƙara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya ɗauke shi ne, Kiran sunanshi tayi”Danish” amsa mata yai”Na’am” cikin kulawa tace dashi”nayi tsammanin ka fara baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala” daɗin murya yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi mashi surutu.
“Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba”? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna taji yace”Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce ƙwarin gwiwar da nike da shi Angel ” murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
“Faɗamin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake ƙaunata? Ta yi maganar tare da Ɗaura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi a Namijin shi.
“Nikaina bansani ba” amsar daya bata kenan,
Ɗagowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haɗe jikin na juna, Hasken wutar dake cine ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faɗuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha jinin jikinta, ƙwarjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe ɗaya
“Abu ɗaya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za’a raba ni da ke!” Dawo da dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai”Zan iya komai a wannan lokacin,”
“Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne, mutuwace kaɗai zata Iya raba ƙaunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani da madadinka” kalamanta sun ɗan sanyaya zuciyarshi,
“Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai Iya ƙwace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina” Muryarshi araunace yai maganar.
Ɗaure mashi fuska ta yi “Danish zaka Iya bari wani ya ƙwace maka ni”? Girgiza mata kai yai alamar a’a, ya ƙara da cewa”Sai inda ƙarfi na Ya ƙare, ”
Lumshe ido ta ɗan yi calmly ta furta “Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake so Mu ji daɗi atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faɗin duniyar nan, Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka? Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene Iyayenka ba, amma inaji araina ba ƙananun mutane bane yadda kake da kyan nan da izza ɗabi’unka sak Irin na ƴa’ƴan Hamshaƙan masu kuɗi ne, Ni ko ka ga ba ƴar kowa bace, Mahaifina ɗan Jarida ne kuma ya rasu ma, ” Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi maganar, ƙwallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.
“Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani buƙatar kowa,” muryarshi a kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi mashi.
“Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faɗamin tun kana jariri aka sadaukar dakai, Naji raɗaɗi jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun ƙaddara ba dole sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata’ƙil ma basu da masaniyar kana araye….” bai bari ta taƙarasa maganar ba yai saurin toshe mata bakinta da tafin hannun shi”Is ok, Kije ki kwanta dare Yana ƙara yi,” maƙe mashi kafaɗa tayi”Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne,”kafiya ta sanya mashi ya rasa ya zaiyi da ita, A ƙarshe dole Ya haƙura Ya ƙyaleta, kwantar dakanshi yai saman ƙirjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya ɗauke su saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na farko da ya fara runtsawa Acikin Dajin❗❗❗
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*