Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 17-18

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*17&18*

 

……… Ammi dake zaune ta bisu da kallo cike da burgewa”dan gaba d’aya sai taga sun mata kamar ma’aurata irin masu matuk’ar son junansu d’in nan”musammun da shariff ya mik’a ma Amaan ledojin hannunsa “suna kallon cikin idon juna,sannan yaja mata trolley d’in kayanta suka nufi d’akin Ammin”suna shiga ya Ajiye troley d’in gefen mirror yana kallonta cikin cool voice d’insa yake fad’in ga kayanki nan na bada miki wasu d’inki”yafad’a yana duba Agogon dake daure a damtsan hannunsa”yayinda Amaan ta zauna gefen bed tana duba ledojin daya mik’a mata”ice cream ne roba biyu”sai gudar ledar hand bags ne da plate shoes kala biyu”d’ago kanta tayi zata kallesa,yayi saurin janye idanuwansa daga barin kallonta”kukan shagwab’a tasaka tana fad’in ni Ina kayan wasa na to hamma?”ta k’are maganar tana shure shuren k’afafuwa….tunda tafara wannan abun ya kauda kai yana danna waya saida yaji tayi shiru sannan ya kalleta ya tab’e baki cikin taushin muryansa dako beda walwala saita bayyana yace “b’ata miki rai zanyi dake da kayan wasan”nadawo Agajiye bazaki barni na hutaba?shine zaki tsiro da wata rigima ko?ki wuce ki koma parlourn kisha ice cream d’in mana” ni ruwa zanje na watsa”to hamma Ina ice cream d’in Ammi?”kaga wannan nida Abdallah keda shi ko?”tunda wannan yarinyar bbu ruwanmu da ita nida kai”kuma tayita hararata…..oh my god! Amaan meyasa bakya gajiya ne da shirme?”Ammi bata shan Abu me sanyi”bana son kina zancen sakaryar yarinyar can”idan ta miki wani abu kisanar mun bance ki kulataba”to hamma ka rakani parlourn mana”kuma zakaci Abincin ko?”shiru yyi sbd yasan Amaan dai idan yabiye mata sunta faman surutu kenan bazata gajiba”tashi muje”batace komai ta maida hand bags d’in da takalmin cikin ledar”ta d’auki ledar ice cream d’in tanata turo baki”zanyi maganinki Allah”k’azama dake tun safe baki koma wanka ba”yafad’a yana tab’e baki “Amma hamma ba Ammi nah tace saika kamun kayanaba zan koma yin wani wankan”shiru yayi yanufi k’ofa “wai hamma Ina baba ladi?”ko wajenta zaki koma ne?”uhmm uhmm nafison wajen Ammi dan Allah kabarni Anan”bece komai ba saidai kalamanta sun masa sanyi Azuciya”sbd duk me kaunar mahaifiyarsa bayada kamarsa Aduniya”Atare suka fito daga cikin d’akin “ita ta wuce cikin parlourn shi haye upstairs…. Ahankali Amaan ta iso ta duk’a gefen Ammi tace “gashi kisha “Ayya bana shan kayan sanyi Amaan”zoki zauna kisha Abinki”Anty Amaan ni Ina nawa?”cewar Abdallah yana murmushi “batayi mgn ba ta mik’a ma Abdallah roba guda”nifa wasa nakeyi miki”nidai ka Amsa dama nacema hamma zan baka”to shikenan nagode”yafad’a yana Amsa”ita kuma ta zauna gefen Ammi tanasha cikin yanga”Ibtihal na kallonsu”jikinta yagama bata Amaan da shariff soyayya sukeyi tunda harda binta d’aki dayayi….wani irin tsanar Amaan da zafinta taji Azuciyarta….sis bissimillah ko?”cewar fahad batare daya kalletaba”Alhamdulillah! ta furta tana mik’ewa tsaye tabar parlourn, Ammi na lura da ita Akwai damuwa atattare da ita”Abdallah nata d’anjan Amaan da fira har suka gama bikin shan ice cream d’in su”ta tashi ta wuce d’akin Ammi sbd tayi wanka”ko minti 2 batayiba da barin parlourn shariff yasakko k’asan yaci zazzafan wanka cikin k’ananun kaya “yayi masifar kyau”be tanka kowaba yadai lura da y’ar rigimar tasa bata cikin parlourn”dining area ya wuce ya zauna yazuba Abinci yafara ci”Ahaka kiran fareedah yashigo cikin wayarsa”yaja tsaki yak’i d’auka”yana gab da kammala cin Abincin Amaan ta fito daga cikin d’akin Ammi”tana sanye da riga da wondo na kanti”da mini hijab iya gwaiwar hannu Ajikinta”tanata k’amshi”kai tsaye dining area d’in ta nufa”Assalamu Alaikum hamma”saida ya d’auki kusan second 5 kafin ya Amsa batare daya kalletaba”ita kuma tanata kallonsa sbd yamata kyau sosai”nayi wankan hamma! nagani ai ko?”to yanzun yaushe zan fara sallar?”dama baba ladi tace”saiya d’auke zan fara, kuma ya d’auke”shiru yyi na kusan mintina 3 itadai tana wasa da yatsun hannunta “tamkar bayaso yace”Anjima idan kun shiga d’aki keda Ammi ki tambayeta zaki fara sallah yaya zakiyi?bance ki tambayeta gaban Abdallah ko wani ba kina jina?”dato ta Amsa tayi shiru”da farko haushi tabashi, Amma dayayi wani tunani sai yaji tausayinta”yasan skunyarta”da’a hayyacinta take bazata fad’i haka a gabansa ba duk rashin kunyarta….ji yakeyi da shine mahaifin Amaan idan Asiri yatonu saiya rabu da muguwar matar…..hamma yanzun Ina zakaje?”Amaan ta katse masa tunani da siririyar muryarta” shareta yayi”ta saki kukan shagwab’a “ya mik’e tsaye yana fad’in wuce muje ki zauna ni fita zanyi”hamma zanje dan Allah”bbu inda zanje dake garama ki dena mun wata magiya”batayi mgn ba tamike tsaye ta wuce d’aki”kayanta ta jera cikin ward rope d’in Ammin duka”tana gyara saman bed Ammin ta shigo sbd tayi sallar magrib,yayinda Abdallah na masjeed”Ammi nah! na’am y’ata”kinga hamma ko?”sai tayi shiru”wani abun ya miki ko?”sai tayi k’asa da kanta tace”bbu ruwana dashi”Ammi tayi murmushi batace komai”tana k’ok’arin shiga toilet Amaan tace”dama zan fara salla ya d’auke shine hamma yace na tambayeki”dawowa baya Ammin tayi ta zauna gefen bed d’in Anutse tayima Amaan bayanin yadda zatayi wanka”bbu laifi kuma tad’an fahimta”bayan Ammin ta shiga bathroom d’in ta fito”Amaan d’in ta shiga tayi wankan da Alwallah”bayan ta gama sallah Ammin takoma yimata y’an tambayoyi game da addininta”inda yatadace tayi mata gyara tayi mata…..shariff be dawo gidan ba sai wajen k’arfe 9:11 pm “Ammi da Abdallah na zaune a parlourn”yayinda Amaan na d’aki sbd Abinda Shariff yamata d’azun yasaka batason fitowa ta ganshi” tunda ya shigo ya lura bbu ita Acikin parlourn”bayan ya gaida Ammi ta had’a masa coffee yasha”tun be damu da tambayar Ina Amaan ba”harya yafara tunanin ko tayi bacci”sai kuma yatuna d’azun mus’ab na tsokanarsa da Ina *Amaan shariff* ?ya d’an tab’e baki yana shafa kansa had’e da d’an lumshe idanuwansa”sai kuma ya waresu kansa ak’asa yace”Ammi Ina yarinyar nan Amaan?”tana d’aki”shine Abinda Ammi tace”ya mik’e tsaye yamata saida safe”har zai wuce d’akin ya juyo yaga ko Ammi na kallonsa yaga hankalinta na wajen TV “wanda kuma ba haka bane tana kallonsa ta wutsiyar Ido”tura k’ofar d’akin yayi yashigo da sallama cikin k’asaitacciyar muryarsa me dad’in Amo da sauti”Amaan tayi saurin rufe Ido”dan ba bacci takeyiba tunani kawai takeyi”tana kwance Atsakkiyar bed d’in Ammi da kayan bacci Ajikinta”gefen mirror ya tsaya ya kunnah flash light d’in wayarsa ya haske mata fuska”dukda d’akin k’anyar yake da haske”pink lips nata dake motsi da zara zaran eye lashes nata yasaka ya fahimci idonta biyu”saidai beson meyasa ta nuna masa bacci takeyi ba…..ya d’auki kusan second 5 kafin da k’yar yace”kinyi addua ne?”shiru bbu Amsa” *Amaannnn!* saida taji sunan har cikin kanta”Amma ta sharesa”shi kuwa d’age kafad’a yayi Alamar ko Ajikinsa”yanama kok’arin juyawa yafita Ammi ta turo k’ofar d’akin ta shigo, sbd bata son yawan kad’aicewarsu da juna….d’an sosa k’eya yayi yana yin k’asa dakai yace”saida safe Ammi”daga haka yafita daga cikin d’akin “Ammin ta raka bayansa da murmushi ta kalli Amaan data bud’e lumsassun idanuwanta ta juya sbd taga yatafi”Amaan bakiyi bacci ba?”uhmm! ko wani abu kike sone ? Ah Ah Ammi babu komai “to kiyi Addua ki kwanta kinjiko?”dato ta Amsa “Ammin ta shimfid’a katifa k’arama kan carpet ta kwanta…..sharif kuwa Azuciyarsa mamakin Abinda Amaan ta masa yakeyi” *kodai fushi tayi sbd d’azun tace zata bini nace taje ta zauna*?”tsaki yaja daya fahimci Afili yayi maganar”Ahankali yatura k’ofar had’ad’d’en bed room nasa yashiga”kai tsaye gaban ward rope yanufa, ya bud’e ya d’akko towel fari k’ar yanata irin k’amshn jikinsa, ya d’aura ya shiga wanka”bayan yafito ya shirya cikin d’an guntun boxer duk irin sanyin da Akeyi kuwa”kafin ya kwanta yaja devut yarufe jikinsa gaba d’aya,banda fuska”saidai me?”gaba d’aya Amaan ce ta fad’o masa Arai”zuciyarsa na hasaso masa ita time d’in datake masa shagwab’a da shure shuren k’afafuwa wai Ina kayan wasanta?zan siyo miki teddy gobe insha Allah “ya furta in a low voice batare daya shirya furta hakan ba”can kuma yaja tsaki yana jin haushin kansa”tare da shan Alwashin da safe bazai tankataba zaiga iya gudun ruwanta”saime idan tayi fushi dashi ma?”da wannan tunanin bacci me dad’in gaske ya sacesa”Abin mamaki yakoma yin mafarkin gashi nan shida wata yarinya zaune gefen wasu ruwa”k’afafuwansu na ciki suna wasa da ruwan”can saiya fad’a cikin ruwan”yarinyar ta fasa ihu tana fad’in *salfad* karka tafi ka barni?bazan iya rayuwa idan babu kaiba”ta fad’a tana fad’awa cikin ruwan itama ta bishi……iya nan ya farka Anata kiraye kirayen sallar”ya sauke numfashi yana Addu’ar tashi daga bacci”saidai zuciyarsa tak’i mantawa da yadda yayi mafarkin “sai maimaita kalmar sunan *salfad* yakeyi Azuciyarsa”Ahaka ya wuce bath room yayi wanka da Alwallah,yafito yatafi masjeed shida Abdallah……saida gari yafara haske sannan shariff yashigo cikin gidan”wasu daga cikin masu Aiki suna a main parlour sun fara Aikinsu”gaishesa sukayi kamar kullum yad’aga musu hannu ya wuce d’akin Ammi”cikin nagartacciyar muryarsa yayi sallama “yana sanye da jallabiya ya aza jibgegiyar rigar sanyi Asama”Amaan na zaune A tsakkiyar bed d’in Ammi tanata yimata danne danne Awaya”kanta bbu d’an kwali kalbar kanta ta bazo saman bayanta da kafad’unta”yayinda daga cikinta zuwa k’afafuwanta ta rufe da bargo”tunda taji sanyayyar muryarsa ta nutsu,saidai bata kallesaba “shi kuwa yana shigowa batare daya saniba idanuwansa suka sauka kan nata”ya kauda kansa yana d’aure fuska ya duk’a gefen bed d’in inda Ammi ke zaune tana Azkhar ya gaisheta…..batare da Amaan ta kallesaba tace”Ina kwana?”sarai yaji Amma sai yayi kamar ma bejiba”hamma Ina kwana?”ta koma maimaita tawa”Anan ma shirun yayi”har saida Ammi tace”wai bakaji Amaan na gaisheka ne?”yanata cin magani yace”bana son gaisuwar tata, ta rik’e kayanta”yana fad’in hakan da sauri yatashi tsaye yabar d’akin “damma kar Ammi ta masa wata mgn”ita kuwa Amaan bata damuba taci gaba da danne danne Awaya “Shariff kuwa da fushin Amaan yayi shiri yabar gidan batare da kowa yasan fitar tasa ba”……misalin k’arfe 4:37 pm”fahad Shariff ne zaune a lambun gidansu fareedah”ya wanku cikin kananun kaya ya Aza suit caot Asama sbd sanyi”yayi matuk’ar kyau”gabansa kayan motsa bakine dana sha da kayan fruits”wanda kallo basu isheshiba”sai faman duba wristwatch d’in dake d’aure Ahannunsa yakeyi yana jan tsaki”kimanin kusan mintinan sa 7 kenan Azaune fareedah bata isoba”tunani yakeyi in bacin yanada wata manufa kanta ai bata isa har yazo gidansu yamata irin wannan jiran ba….yana wannan tunanin yaji k’was k’was d’in takalminta”ga wani uban turare data fesa over”yatsina fuska yayi yana daidaita fuskarsa”fareedah ta k’araso tana juya idanuwanta da girgiza jiki taja kujera ta zauna tana fad’in yallab’ai sannu da zuwa”da Alama yau naci sa’a tunda ka Amince kazo har gidan mu….tamkar ya mareta haka mutumin naku yaji”yad’an saki fuska Anutse yace”babu wani sa’a kawai ke d’ince ta daban shiyasa”yanzun haka tare nake da mutane nace sai nazo mun gaisa na Amshi sak’o nah”hakane naji dad’in wannan matsayi daka bani”ta fad’a tana zare zobban daga hannunta bbu kunya tana turo k’irjinta da kusan have awaje ta aza masa zobban saman hannunta”har hannunta na gugar nashi”shine kawai yayi kok’arin janye hannunsa yana yiwa mus’ab dake waje tare da driver flashing”dama sun shirya hakan, daya masa flashing zai kira ya nuna ana son ganinsa A d’aya dg cikin gidajen man fetur d’insa cikin gaggawa”hakanne kuwa yafaru”shariff na duba zobban zai mata mgn kenan kiran mus’ab ya shigo cikin wayarsa”Anutse ya d’auka da sallama”fareedah nata kallonsa kamar mayya”tana jin idan ta mallakesa Amatsayin Abokin rayuwa tagama sa’a a duniyarta!…..what?? yafad’a da k’arfi yana ware manyan fararen kyawawan idanuwansa”saida fareedah taji tsikar jikinta ta tashi”tana jin koda kafin suyi Aure ne zata iya bashi kanta idan zai so hakan…. subahanallahi! gani nan zuwa yanzun”yafad’a yana yanke wayar”fareedah na kashe masa idanuwa tace”lafiya meya faru?”karki damu baby zamuyi waya Anjima”kiran gaggawa akemun Awani gidan maina “yafad’a yana d’aukar duka wayoyinsa kafin tayi mgn yabar wajen a hanzarce”saida yafito daga cikin get yatab’e baki had’e dajan tsaki”tun kafin ya iso driver yatashi motar”shi kuma yabude back sit yashiga ya zauna gefen mus’ab”Abokinah kamar kana cikin k’aya”hmm! daka san yadda na tsani yarinyar nan mus’ab daba da k’aya zaka misiltaba”daga haka yayi shiru yana duba zobban”indai munyi nassara can ta matse mata”cewar mus’ab”ko munyi ko bamuyi ba na gama da babinta saidai Abi kuma ta wata hanyar”kai Abokinah kana fire wlh”kasan kuwa meenal nata tambayata kai?”had’e rai Shariff yayi yaja tsaki bece komai ba”Ina y’ar rigimarka Amaan shariff?”wlh d’azun baba ladi ke sanar mun ta waya irin Abin Arzik’in daka mata”da komawar Amaan hannun Ammi”Ina fatan dai batun magungunan ta tana Amfani dasu ko?”shiru na wasu y’an few minutes shariff yayi can yace”yau nakeso nayima Ammin bayani”rubutu kuma zan tura Abdallah yadinga Amsowa”ni Ai fushi takeyi dani y’ar rainin wayo”wai Amaan d’in Abokinah?”banza shariff yamasa sbd yasan mus’ab dason jin gulma….mus’ab kuwa mamaki ya dingayi da Abinda shariff yafad’a “saidai kawai yabar wani tunanin sai yau da gobe zata tabbar masa da Abinda yake tunani inhar Allah yanufa”duk yadda yaso suyi firan Amaan da shariff k’in Amincewa uban gayyar yayi yamasa banza”bayan sun iso office”suka saita duk Abinda ke cikin zoben yakoma kan laptop d’insu”sannan suka kunnah suna gani”Abin tashin hankali Ashe faridah y’ar lesbian ce”sannan kuma Alh isah tafashiya shine shugaban masu shigowa da miyagun k’wayoyi”saiga fuskar Alh yahaya mijin Ammi tare dasu”kuma yadda suka fahimta Alh isah tafashiya deputy governor shine ya had’a baki da Amintaccen likitan me girma governor yasaka aka masa Alluran b’atar da mutum hayyacinsa”sbd yana so ya haye kan kujerarsa ta mulki…. Abubuwa sosai naban mamaki suka gani”wanda mus’ab ne kawai ke mamakin Amma uban gayyar wato miskilin namiji ko Ajikinsa”bayan sun gama ganin komai “mus’ab yace”yanzun dole yaka mata ka zauna ka nutsu ka had’a duk wasu baya nai da vedios ka tura can sama”nasan ta hakane iyalan governor zasuyi k’ararsa”Shariff beyi mgn sbd kiran fareedah daya gani”rejecting d’in kiran yayi ya zare layin ya karya” dama sbd ita yasaka shi”sai wajen 6 pm yatashi daga office “har zai bar laptop d’insa Anan sai yayi wani tunani yafasa”Ahanya suka tsaya wata super market shariff ya shiga da kansa yazab’oma Amaan wata jibgegiyar teddy”bayan yabiya kud’in sannan yafito driver yakawosa gida”yana rik’e da ledar da teddy d’in keciki ya wuce cikin gidan Anutse….hango Amaan yayi itada Abdallah sunata guje guje yabiyota”kanta bbu ko d’an kwali gaba d’aya jikinta bbu inda baya juyawa”sbd gwont d’in jikinta ta kamata kuma robber ce…..✍️

Adinga sharhi

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button