Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 7

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na bakwai_

 

INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY

MAZA KU GARZAYO “UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN “TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.

KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE……

CONTACT ME ON

09035390383

____________

…….“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”.
“Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”.
Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma’auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba…

★★★…..

“Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma’a”.
Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata.
“Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta…”
Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”.
Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera.
“Taauuu!!”.
Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”.
“An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”.
“Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”.
“Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai…” fuuu ya fice kamar zai tashi sama.
Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama’a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya…..

(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).

★★★……

Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu.
Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala’in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa….
Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu.
A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi’ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba…..

( Uncle JJ badai kuma ka haukace ba).

…★…★…★….

Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”.
Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”..
“A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf……”
Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko’a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”.
“A’a ai ba’ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta.
“Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”.
“Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa….

A cikin abinda bai wuce mintinan arba’in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo Kainaat ke masa wani irin shu’umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za’ayi ba. Sai dai fa duk da wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da’a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago. Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A’a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka wani abu ne na sace ka”.
Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”.
“Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”.
Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta.
“Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi…..”
Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba. Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za’ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a’a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi……….✍️

_Na rasa mima zance akanki Kainaat_.

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button