Nasarar Rayuwata 28
*Talented writers forum*
*28*
*Masu tura min mssgs da masu kira Ina godiya Allah ya barmu tare Ina yinku irin sosai din nan*
Ayman ne Zaune gaban sultan Kansa na kallon kasa sultan yayi gyaran murya yace ” Kai nake saurare yarima wanne ka zaba ” bugun zuciyarsa ya tsananta gaba d’aya Gani yake tamkar a mafarki abubuwan ke faruwa Amma har abada bashi da ra’ayin mulki donhaka gwara d’ayan zabin duk da cewa baya bukatan hakan amma bazai iya jayayya da siltan ba yasan ya d’aga masa kafa donhaka dole wannan karon ya amince da bukatarsa , muryar sultan ne ya katse masa tunani da cewa ” kasan bazai yiwu a ce na zuba Maka Ido haka nan bah ga can kaninka ya ajiye iyali har Yana Neman haihuwa na biyu donhaka lallai ka zabi d’aya daga cikin sharudan da na gindaya Maka ” sauke numfashi yayi tare da cewa ” Allah ya Kara Maka lafiya na amince da auren ” mamaki ne karara a fuskar Sultan lallai yanzu ya gaskta cewa sarauta baya gaban d’an nasa , wato ya gwammace yayi auren akan sarautar abin baiyiwa mahaifin nasa dad’i ba Amma Kuma Babu yadda ya iya ya amince da shawarar Fulani yanzu ne Kuma yaga amfanin Hakan , murmushi yayi irin tasu ta manya yace ” shikenan kaje Allah ya Maka albarka yasa Hakan shine Mafi alheri a rayuwarka gaba d’aya” Ameen ya rabbi nagode Allah ya Kara girma ”
“Zaka iya tafiya sannan ka fara shirye shirye saboda Rana ita yau an daura insha Allah ” ” na barka lafiya ranka ya dade ” daga haka Ayman ya tashi ya fice abin mamaki baiji digon bacin rai ba dangane da wannan magana har abin ya basa mamaki cikin zuciyarsa yace maybe alheri ne shiyasa, daga nan bangaren Fulani yaje aka shaida masa Bata fito ba donhaka ya koma part nasa Fauzan na biye dashi a baya, a falo suka zube kowa da tunanin da yake Abu kamar almara shida yazo Hutu Kuma shine zai koma da mata iKon Allah kenan matar mutum kabarinsa haka kurum yayi murmushi da ya tuna da baby da irin reaction din da zatayi idan ta gansa da wata a matsayin matarsa , ko a banza dai ya rabu da alakakai duk da cewa baisan wacce zaa aura masa ba Amma ya gwammace zabin iyayensa akan zabin Ammin nasa saboda yasan me irin halinta zata kwasa. Fauzan yace ” yarima yanzu me shirinka , akwai Wanda zamu gayyato bikin ne daga Nigeria?” Murmushi yayi yace ” inna tah kadai zaa gayyata bayan ita bana bukatar kowa, sannan Ina son bayani akan yarinyar da Kuma halayenta ” “angama ranka shi dade Ina zuwa ” daga haka Fauzan ya tashi ya fice dogarawa suka rufe kofa nan yarima kuwa ya tashi ya koma bedroom nasa Yana bukatar kadaici zaiyi tunani.
A can fada kuwa Sultan ya kira Sarkin fada sukayi ganawar sirri bayan ya sallameshi ya kira Waziri babba suka gana nan take aka rubuta takarda izuwa fadar Singa na neman auren gimbiya Failuzaa , Babu b’ata lokaci aka tada Yan aika suka shirya tafiya don isar da sakon Sultan. Waziri karami ne a falon gimbiya Suhail sai safa da marwa yake a yayinda Suhail ta buga uban tagumi , numfashi ya furzar a iska yace ” na gama iya lissafina na kasa gane meke Shirin faruwa a wannan fadar , Amma na tabbata akwai abunda Sultan ke kullawa don sau biyu Yana ganawa da yarima Ayman ga Kuma waziri Babba ga sarkin Fada na tabbata akwai wata a kasa amma gaskiya na tsorata don Ina Gani tamkar gagarumin Abu Ake shiryawa saboda an gayyato masu gyaran fada ” Suhail ta buga kirji tace ” na shiga uku ni Suhailat ya zanyi Ida akace nadin sarautar wancan yaron me uban taurin kan Ake shiryawa, da kuwa sai na kwanta jinya don bazan jure ganin wannan ranar bah ya Allah ka kawomin mafita ” ta dunkule hannu ta tashi tsaye tana Jin Wani radadi cikin zuciyarta.
___________
Bayan kwana biyu masarautar Sennar ta kasance cikin zulumi saboda kowa na son sanin meke faruwa sai gyara akewa fadar ana canza abubuwa zuwa sababbi Kuma har yanzu sultan baice komai ba jama’a duk an baza kunnuwa ana jiran labari Amma shiru kakeji, bangaren yarima Ayman kuwa an zuba masa komai sabo nan jama’a suka fara yada jita jitan cewa zaa nada Ayman yarima nan Bada dadewa ba , hankalin Suhail da yarima Asim ya tashi sosai sun kasa zama kullum da zulumi suke kwana ga matar Asim ciki ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe. Yau da safe sultan da Kansa yayiwa Ayman magana akan zaije masarautar Singa gabatar da gaisuwa, aka shirya manyan fadawa Yan rakiya waziri Babba ne jagora sai wasu manyan fadawa masu fada aji , aka shirya motocin na alfarma motoci goma manyan Prados bakake wuluk dasu sai sheki suke. Yarim Ayman ya fito cikin shiga ta alfarma ta manyan kaya da wasu irin kayan kasar Sudan tamkar alkyabba haka sai qamshi ke tashi, Fauzan na gaba Yana baya aka Bude masa mota ya shiga a dai dai wannan lokacin mutum uku suna gindin window suna hangosa da Fulani da gimbiya Suhail sai Sabrina nan da nan tsohon faminta ya tashi ta fara zubar da kwalla tabbas ta rasa miji har abada bazata taba samun madadin Ayman ba saboda yakai duk inda akeson namiji yakai, ta shafa katon cikin nata ta juya ta koma bisa gado ta kwanta tana Jin Wani irin yananyi cikin zuciyarta. Tafiyar awa 3 sukayi suka shigo birnin Singa Kai tsaye suka wuce masarautar garin inda aka musu kyakkyawan tarba da kayan bushe bushe na ban girma saboda birnin Singa tana karkashin iKon masarautar Sennar ne , fada a cake makil da jama’a nan aka fara gaisuwa yarima Ayman dai Kansa na kallon kasa ya gaisa da Sarkin Singa daga nan ya koma gefe ya zauna , bayan kamar minti talatin aka Bada izinin a shigo da yarima zuwa d’akin ganawa ta musamman nan Fauzan ya tashi yarima ya biyo bayansa tare da wasu hadimai aka nuna musu hanya zuwa Wani dankareren falo na alfarma inda bayi ne birjik sunfi goma sun shirya kayan motsa Baki da abincinsu na gargajiya, turaren wuta kowace kusurwa a kunne ga manyan dardumar da throw pillows na alfarma abin dai gwanin sha’awa. Fauzan na tsaye a yayinda Ayman ya zauna Yana kallon wayarsa dai dai nan Wani hadimi ya sanar dasu isowar gimbiya Failuzaa take falon ya dauki Wani qamshi na musamman, Fauzan ya d’aga Ido nan ya hangota cikin kaya na alfarma doguwar Riga tana Jan kasa fara sol sai kwalliya da aka mata a fuska fara ce Amma ba sosai ba tana da kyau ba laifi , kuyangi na zagaye da ita bayan ta nemi waje can nesa da yarima amma suna fuskantar juna ta zauna nan da nan duk suka watse d’akin ya rage daga yarima sai Fauzan sai ita, ganin haka Fauzan ya juya ya fice zuwa bakin kofa ta waje don Basu damar ganawa.
Sun share mintuna goma Babu Wanda yayi magana cikinsu , yarima Ayman Yana pressing phone nasa chatting yake da Aman Yana fada masa batun aurensa next week, Aman ko gani yake tamkar wasa yake masa . Failuzaa ta d’aga Ido tana kallonsa hankalinsa gaba d’aya Yana kan waya haka ta kare masa kallo tana Jin Wani farin ciki a zuciyarta dama irin mijin da take mafarkin samu kenan a rayuwa ya Hadu over. Ganin bashi da niyyan mata magana yasa ta sauke nata girman kan a hankali ta taka zuwa inda yake ya zaune bisa kujerar dake next to him , ya cigaba da abunda yake ta lumshe idanu tare da furta ” barka da zuwa my prince” thanks ” ya amsa daga haka ya cigaba da abunda yake, ta rasa me zata ce masa ita ba gwanar surutu bace batasan me zata fada ba donhaka ta dauko tray din fruits tace ” Bismillah ” ya dan kalleta yace” no ..karki damu am ok ” ta ajiye tray din tana wasa da bangles nata , sun share 10 minutes a haka still sannan ya ajiye wayar ya dan kalleta yace” akwai abinda kike bukata ne ?” ” Kamar me kenan ?” Like anything.. I mean uhmm.. komai ma ” ta juya idanu tace ” not really thanks maybe you should tell me about yourself ” guntun murmushi yayi” am Ayman from Sennar ” murmushi tayi tana kallonsa cikin Ido ta rausayar da Kai tace ” I know that, I mean tarihin rayuwarka ” Sauke numfashi yayi tare da cewa” am not good in that , ban iya Bada labari ba ” ” well…sunana Failuzaa na gama skul dina a MAAU Khartoum na karanta Bsc Microbiology, Kuma ban taba soyayya ba you are my first love dafatan zan samu karbuwa duk da nasan cewa baza’a rasa wacce kake so ba” murmushi yayi yace ” really..kamar kinsani kuwa akwai wacce nake so Kuma Ina saka ran aurenta nan gaba insha Allah ” dakyar ta kirkiro murmushi tace ” that’s good ” shiru sukayi daga haka Ayman ya tashi Yana gyara rigarsa ” am going ” ya furta tare da juya sexy eyes nashi Wanda Hakan ya Kara narkar da zuciyar Failuzaa ta rausayar da Kai tace ” thanks for the visit, Allah ya tsare ” “Ameen thanks ” daga haka ya juya ya fice ta bisa da idanu tamkar ta biyoshi ta rungumesa lallai tayi sa’a Kuma sai ta samawa kanta matsuguni cikin zuciyarsa , tana tsaye kuyanginta suka fara shigowa da kaya cikin akwatuna kyauta ce ta musamman daga masarautar Sennar zuwaga gimbiya, nan murna ya sake mamaye Failuzaa tabbas tayi dace daga haka ta wuce bangaren mahaifiyarta tana labarta mata yadda sukayi da alama Yana da saukin Kai zasu zauna lafiya nan suka cigaba da tattauna yadda bikin zata kasance.
Waziri babba ya gana sosai da Sarkin Singa inda sarkin ya nuna masa farin cikinsa a fili game da auren y’ayan nasu da Ake Shirin daurawa sannan sun amince da ranar da aka saka wato juma’a Mai zuwa , daga haka sukayi sallama tawagar birnin Sennar suka shige motocinsu suka kama hanyar gida da kyakkyawan labari.
*Muje zuwa wasa farin girki*