Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 53

Sponsored Links

53……
Karfe daya saura Mami ta shigo dakin Khaleel tana kwada ma Ikram kira, farkawarta knn daga bacci bata ga ikram gefenta ba, Khaleel na xaune kan gado yana ta faman solve din mata assignment na Maths, ita kuma tana kwance gefensa duk ta takure kanta sbda sanyin AC tana bacci, Mami tace “Meye hka Khaleel” rufe littafin yyi da sauri yana kallon agogo yace “Mami baki yi bacci ba” tayi masa mugun kallo tace “nan ne wajen kwaciyarta Khaleel, ni fa bana son shashanci da rainin hankali, snn da ka bude mata AC hka kana da maganin da xaka bata ne idan ta tashi tana tari” mikewa yyi da sauri yace “wllh Mami ita ta kunna, kuma ni assignment muke yi tayi bacci” Mami tace “assignment din kke rubuta mata ynxu?” yace “No naga tayi bacci ne….” fixge buk din Mami tayi daga hannunsa tace “kar ka sake yi mata rubutu daga yau tunda bakai ke biya mata kudin mkrntr ba” bae ce komai ba ta isa kusa da Ikram ta dago ta tace “tashi muje ki kwanta Ikram” cikin magagin bacci take cewa “yaya Khaleel ni ka dinga yi min bacci nake ji, anjima xan tashi” Mami tayi tsaki ta shiga tattara sauran buks dinta da sch bag snn tace “ka kai min ita daki idan ka gama tsayuwar” tana kai wa nn ta fice, yyi murmushi ya bi ta da kallo snn ya juya yana kallon Ikram da tayi ruf da ciki tana bacci, ya karasa kusa da ita ya dagota, kwace kanta ta shiga yi ta bude ido a hankali tana cewa “oowh yaya Khaleel ni bacci nake ji wlh” kan kafadarsa ya daurata ya fita daga dakin, ko da ya shiga dakin Mami tana bathroom, ya kwantar da Ita yana kallon dan karamin bakin rashin kunyarta da murgude murgude, hannu yasa ya dan buge bakin ta bude ido da sauri tana kallonsa, ya juya ya fice daga dakin da sauri, murguda masa bakin tayi ta juya ta ci gaba da baccinta. Ranar friday da daddare Ikram na xaune dinnin tana karanta literature book din da suke amfani da a sch mai suna without a silver spoon, Aliyu da Khaleel suka shigo gidan, ta mike da sauri tayi gun Aliyu ta rungumesa tace “yayana nayi missn dinka jiya baka xo ba” yyi peck din goshinta yace “Mami ce ta bar min aiki da yawa a office shiyasa ban xo ba” hanyar stairs Khaleel ya nufa, Aliyu yace “baki gaida Khaleel ba Ikram” ta murguda baki tace “ae nasani” murmushi yyi yace “to me kike yi a dinnin” tace “literature nake karantawa kasan gobe muna da literature” yace “gud, my Ikram je ki ci gaba da karatun ki” ba musu ta koma dinnin din ya haura sama, dakin Mami ya nufa, ya tarda ta xaune tana rubutu Khaleel na kwance kan gadonta, ya xauna ya gaida ta ta amsa snn tace “ya aka yi a Meetn din da kuka je” ya shafa kansa yace “Mami ni ban je ba su Dr Ibrahim ne suka je” tace “ok, Momy ta baka sako ka kawo min” yace “A’a Mujaheed ta ba bani ba” Mami bata kuma cewa komai ba, Aliyu ya dauki remote ya shiga canxa tasha, Khaleel yace “Mami wae fa ran sunday yake son kai Ikram gidansu” Mami ta juya tana kallonsa tace “to shi bae da baki?” Khaleel yyi murmushi yace “to nayi shiru” Aliyu ya juya yana kallonta yace “Mami nayi xaton Momy ta gaya maki ne” Mami tace “to idan ta gaya min fa” ya dan yi shiru snn yace “to kiyi hkuri” bata tanka sa ba, bayan kmr minti biyar tace “da ranar lahadin nake so Khaleel ya kai ta gida, but gobe sae su tafi, ran lahadi sae ka kai ta gidan naku” kai kawae Aliyu ya gyada mata Khaleel ya hade rae ya mike xaune yace “Mami ni wani waje fa xani gobe,” Mami tace “idan ku ka dawo sae ka je inda xaka” bae ce komai ba ya mike ya fita daga dakin, Aliyu ya bi bayansa. Suna xaune daki suna cin abinci Khaleel yace “wae in tambayeka Aliyu” ba tare da Aliyu ya kallesa ba yace “m ol earz” Khaleel yyi murmushi yace “emm dama abinda ka gani jikin Ikram ya burgeka har kke son aurenta nake so ka gaya min” Aliyu ya dago yana kallonsa, Khaleel ya ci gaba da cin abincinsa yana murmushi yace “yes ina jin ka, don ni abun na daure min kai, nd Beside me kaga ta iya, yarinyar da ko hankalin kirki bata da shi, bbu abinda ya cika kanta sae shegen wasa da rashin kunya, common gyaran daki bata iya ba bare shara, uwa uba axo ga girki, ban tsamman ma ta iya kunna gas din ba, wnn burden babba kawae kke son daura ma kanka, yarinyar da bata wuce ka shiga da ita bayi kayi mata wanka ba ka sa ma kaya” dariya ssae Khaleel ya fashe da har da kyakyatawa, Aliyu ya jefa cokalin hannunsa cikin abincin gabansu ya mike yana kallon Khaleel.
[2/25, 08:35] Zjy:

Back to top button