Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 27

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*27*

Suna jingine jikin motar tasa kirar Mercedes C300 coupe sanye yake da brown shadda ya murza hula fuskarsa sai sheki yake suna hira da abokin nasa fuskarsa dauke da murmushi yace ” Haba Mansoor kasan bazan taba mantawa da Kai ba, believe me na Dade banzo ba like 3 years I think rabona da gida Amma yanzu insha Allah zamu Dade don akwai auren brother na next month zamu Jira, Kuma na Maka alkawarin weekend zamuzo har gida mu kawo muku ziyara” hmm Allah yasa nidai sai na ganka kawai ” baka yarda ba kenan ” no…I won’t say anything for now ” dariya suke a dai dai wannan lokacin idanunsa suka hango masa kyakkyawar fuskarta tana tafiya a hankali cike da nitsuwa da Kamala , shiru yayi ya zuba mata idanu Yana Jin bugun zuciyarsa na dada karuwa har tazo kusa da inda suke ” good morning sir ” how are you Aisha” am fine thank you sir ” daga haka ta wucesu idanunsa still na kallon direction din da tayi , dariya uncle Mansoor yayi yace ” Kai kallon ya Isa haka ” Wani numfashi ya sauke yace ” kasan Allah, tunda nake ban taba Jin sha’awar Kara aure ba sai yau . Ya ilahi wannan yarinyar ta tafi da imani nah please ya zamuyi na mata magana” ” not possible cos nan skul din sai visiting days Ake barin Baki su gana da students Kuma wannan she is a kid ka mata girma mutumina Ss1 fah take , very brilliant girl wallahi ga hankali ” don Allah yaushe ne visiting day din nasu ” uhmm.. yau me date..ok next 2 weeks haka ” don Allah ka min hanyar magana da ita please aboki ” Kai malam me ka Wani rikice ne haka ” dariya suke haka suka cigaba da hira.
Dake lokacin break ne students suna waje Ummeey tana zaune sai fama Jan tsaki take hajjo ta kalleta tace ” kinfa ishemu malama da wannan tsakin naki ” kanbu…ke kinsan zafin missing na bikin gidanku kuwa, sister na fah nace Miki I mean my blood sis zaayi aurenta Ina skul wannan wace irin rayuwa ce don Allah ” tagumi hajjo tayi tana kallonta sai Kuma tace ” toh ni yanzu me zan Miki ” mtsww…wallahi ke besty kina da kayan takaici ai Koda y’ar dadin baki ne sai kiyi ki dan kwantar min da hankali ” Allah sarki toh sorry besty nah y not ki dauki excuse kije bikin toh ” hmmm…kina magana kamar bakisan skul din nan ban, wallahi ni Aman din ne yaban haushi wai meyasa bazai bari sai ana Hutu ba ” Aman! Hajjo ta furta sunan tare da lumshe Ido tana tuna Aman dinta Allah sarki ko zasu sake haduwa ne oho! hira sukeyi har aka gama break suka koma class.

_________
*Sennar city Sudan*

Bushe bushen algaita da akeyi a masarautar ne yasa kowa ya shaida cewa akwai abunda ke faruwa, isowar yarima Ayman kenan Yana gaban sultan bayan ya gabatar da gaisuwa fuskar sultan na dauke da murmushi me kayatarwa Yana Jin Wani sanyi na ziyartar zuciyarsa yau Ayman ne Zaune agabansa a matsayin graduate ashe zaiga wannan Rana alhamdulillah Alhamdulillah, hamadala yakeyi a boye tabbas soyayyar da yakewa Ayman daban ne shi Kansa baisan dalilin dayasa yake fifita son yaron ba ko saboda hakuri da Halin dattakun da Allah ya bashi, ko saboda riko da addini da yake dashi da sanin darajar dan Adam. ” Ina tayaka murna yarima Allah ya sanyawa rayuwa albarka” Ameen ya rabbi nagode ranka ya dade Allah ya Kara girma ”
” Yanzu me shirinka na gaba, wane mataki ka shiryawa rayuwar ka tunda gashi Allah yasa ka kammala karatun naka ” sunkuyar da Kai yayi cikin girmamawa yace ” Ina Neman izinin sultan zanyi bautar kasa a can Nigeria a jahar Lagos sannan Ina son fara kasuwanci, idan na gama zan wuce Saudiya nayi degree na biyu daga nan sai abunda kace Allah ya Kara Maka lafiya ” gyada Kai sultan yayi cikin gamsuwa yace ” shikenan zanyi tunani akan haka, Tashi kaje ka huta ” na barka lafiya ranka ya dade” idan ka fita ka turomin Fauzan ” angama ranka ya dade” daga haka ya tashi ya fice dogarawa na zuba masa kirari yana d’aga musu hannu. Bayan fitarsa da kamar minti 5 Fauzan ya shigo dama d’akin ganawarsa ta sirrine donhaka Babu kowa daga sultan sai Fauzan, ya gabatar da gaisuwa nan sultan ya kama masa wasu tambayoyi game da Ayman da alama dai maganar ta sirri ce sun tattauna sosai da Fauzan dangane da yarima Ayman din daga karshe sultan ya sallamesa ya tafi. Waziri karami duk ya rikice Yana son sanin ganawar ta mecece Amma Babu inda zai samu bayanai haka ya wuni cike da zulumi Yana Neman daman da zai samu suje su zanta da uwar dakinsa gimbiya Suhail . Ayman na shiga part nasa anhada masa ruwan wanka sai da ya gama shiryawa cikin manyan kaya yayi tsananin kyau cikinsu don idan Yana gida baya saka kananun kaya ko al’adar masarautar tasuce oho! qamshi ke tashi ko’ina nan ya shirya zuwa gaida Fulani dogarawa suka rufa masa baya har zuwa can part nata inda aka masa iso cikin falon da take ganawa da Baki na musamman Wanda ba kowa ke shiga ba, tana nan kishingide da littafin tarihin annabawa tana karantawa ya shigo da sallama ta rufe littafin fuskarta dauke da murmushi ta sauke Wani boyayyen ajiyar zuciya tana Mai hamdala ckn tsananin farin ciki tace ” lale marhaban dan gidan Amminsa Masha Allah angama karatu Alhamdulillah Allah yayi albarka” zama yayi kusa da ita ya dora hannunsa bisa nata ” na sameki lafiya gimbiya Fulani y’ar lamidon Adamawa” murmushi tayi tace ” yau Kuma da sabon salon da zakazo min dashi kenan, toh yayi kyau ya ka baro Ammin da sauran Yan uwa ” kowa na lafiya suna gaisheki dafatan na sameku lafiya Babu wata matsala koh ” lafiya Alhamdulillah Muna cikin tsananin farin ciki at least dai yanzu ka tsaida hankali waje d’aya kayi karatu ka kammala lafiya sai godiya” aduar ki ne yake aiki Kuma Ina fatan zaki cigaba dayi saboda nan Bada dadewa ba zan cigaba da karatun har sai na cika Miki dukkan Wani buri da kika Dade kina nema awajena insha Allah ” sauke numfashi tayi” Alhamdulillah Allah abin godiya Allah ya Maka albarka yayi jagora, akoda yaushe nafison ka gina rayuwar ka nafison ka nisanci kanka da wannan masarautar ” insha Allah burinki zai cika Umma nah, ni kaina bana kaunar zama cikin wannan masarautar” abinci aka shigo masa dashi aka shirya da y’ayan itatuwa da ababen Sha nan kuwa ya zube a kasa Yana ci suna taba hira da mahaifiyar tasa daga ganin fuskarta kasan tana ckin tsananin farin ciki, Bai bar part din ba sai da aka kira sallah kafin ya mata sallama ya tafi.
A can bangaren Suhail kuwa labarin zuwan Ayman ya risketa da Kuma labarin kammala karatunsa gaba d’aya hankalinta ya tashi saboda yanzu Asim ya samu aikin gomnati Yana zuwa kullum Kuma har yau sultan baice komai ba dangane da nadin sarauta , shiyasa yanzu da ta samu labarin zuwan Ayman da Kuma ganawar sirri da sukayi da sultan hankalinta ya tashi sosai gashi ta rasa Ina zata samu labarin. da dare sultan na tare da Fulani a turakarsa lokacin dare ya raba sosai suna fuskantar juna yace ” na Dade Banga wannan murmushin ba a fuskarki Fulani wannan ya Kara tabbatar min da cewa hankalinki a kwance yake yau Kuma kina cikin tsananin farin ciki” hakane Allah ya taimakeka tabbas Ina cikin farin ciki saboda ban taba tunanin cewa wannan yaron zai Maida hankali yayi karatu har ya kammala ba , sai gashi cikin iKon Allah yau ya gama ya dawo Harma Yana neman zuwa gaba ” adua Babu abunda ya bari Fulani, karfin aduan da muke masa ne insha Allah nasan nan gaba sai ya zama abin kwatance a nan yankin namu inajin Hakan a jikina ” Allah yasa ” Ameen Fulani Ina Neman shawara ne dangane da nadin sarautar ” sauke numfashi tayi daga bisani tace ” ni shawarar da zan baka ba lallai kayi aiki da ita ba ” saboda me, ki fadamin koma menene ” ” ranka ya dade kafini sanin meke faruwa cikin wannan masarautar kasan dayawa Basu son yaron nan da wannan mukamin sannan daga shi har yarima Asim Basu gama mallakan hankalinsu ba , ni da zakabi tawa mezai Hana ka bawa Wanda yafi cancanta ” ya kura mata Ido Yana mamakin kalaman nata don Bai taba kawo Hakan a ransa ba ” waye kenan kike nufi ” murmushi tayi ta juya ta gyara kwanciya tace ” kayi nazari zaka samu amsa da kanka ” murmushi yayi Yana girgiza kai ” Fulani kenan”.

Ayman kuwa a dai wannan lokacin ya rufe Qur’an yayi adua ya shafa ya tashi ya nade dardumar sallah ya gama Shirin bacci ya haye lafiyayyan gadon nasa ya kwanta , wayarsa ya dauka ya Bude Whatsapp nan yaga message din Aman Yana ce masa ya kira wayarsa a kashe nan ya masa reply ashe Yana online suka fara chatting Aman ke basa labarin cewa baby kamar zatayi kuka da taji yayi tafiya, tabe Baki yayi yace taji dashi I don’t have her time, Aman ya tura emojis na dariya yace bro me farin jini yanzu kaga da Shirin aurenka Ake tare da my zee ” kaga ka taimaki kanka da ka yarda zaka aureta ” na taimaka mata dai don ni bawai Ina sonta har can ba, Ina nan Ina jiran hajjo y’ar fillo nah kwanan biyu bankaiwa inna ziyara ba zanje naji labarinta ” zuciyar Ayman sai da ya Bada sauti Amma ya share ya rubuta masa ” that’s good ” kasan me bro few months fah naga wata me kama da ita wallahi nayi mamaki ” Ayman ya rubuta ” ayya ” haka suka cigaba da char sama sama yawanci hiran na hajjo ne Ayman da abin ya ishesa ya masa sallama da cewa bacci zaiyi Saida safe nan ya kashe data yayi adua ya kwanta, hajjo ce ta fado masa a rai bugun zuciyarsa ya karu Yana lumshe Ido shi baisan yaushe yayi Nisa cikin kogin sonta ba sai yanzu har mamakin Kansa yake yadda yake jinta cikin zuciyarsa, Yana imagination ranar da Allah ya kaddara ya aureta toh shin zata so shi kuwa? ta manta da Aman kodai har yanzu Yana cikin zuciyarta? Haka dai ya cigaba da tunani har bacci yayi awon gaba dashi asuba ta gari yarima Ayman.

Back to top button