Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 15

Sponsored Links

*15*

 

9:00am Mus’ab ya sauka a garin Abuja lkcn ta gama shirya masa breakfast din a dinning din falon baqi ta koma dakinta tayi wanka ta sheqa kwalliyar ta cikin wani Lagos less purple mai masifar kyau da tsada wanda akayiwa dinkin riga da siket tayi kyau matuqa Mamy ce ta daura mara dankwali ta yafa mayafi purple komai nata purple ne Idan kuka dauke sarqa da dan kunnen azurfar datasa ta dauki zobbanta tasa ta dubi yatsunta wanda Abdul yasa mata ranar da zasu rabu shita zubawa ido tana kallonsa tana tuno kalamansa na rana Samha ki qaddara a ranki yayanki Abdul yana sonki komai nufine na Allah amma inaji a jikina zamu rayu cikin inuwa daya koban aureki yanzu ba wataran zamu kasance tare tabbas alaqata dake bazata tashi a banza ba akwai wani boyayyan abu tsakaninmu damu bamu sani ba”

 

Shigowar Mamy ne yasata janye idonta daga kan zoben ta janyota jikinta tace “dana yana jiranki a parlourn baqi yanzu idan kin tafi shikenan sai munzo Imo State gurinki zanyi missing dinki Pretty amma babu komai watarana ma sainayi watanni banganki ba kinacan gurin mijinki ko?” Ta fada tana dago mata da fuskarta sukayi murmushi lkc daya tare dayiwa juna kiss ta kama hanunta suka fita ita ta yafa mata mayafin sannan tayi murmushi tace “masha Allah kyakkyawata Allah yaci gaba da tsaremin ke kinji ki kula don Allah banason qawance da yayan talakawa da zasu dora miki ciwon kai”

 

Itadai daga kai kawai tayi tarasa meyasa Mamynta bata qaunar talaka bayan tasani har baban Mamy ya rasu wato kakanta a gdan darni suke a Maiduguri sai bayan rasuwarsa Dad ya gyara musu gdansu.
Shiga parlourn tayi da sallamarta ya dago fuskarsa ya zuba mata ido yana murmushi yace “masha Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan mata tawa kyakkyawa” murmushi tayi tayi qasa ta rusuna tace “ina kwana” dariya abin ya bashi sosai wai yau shi Mus’ab shine Samha take yima ladabi haka kamar wani ubanta harda rusunawa ta gaisheshi.

 

Dagota yayi yana murmushi ta zuba masa ido yana da kyau daidai nashi shima yanada haske da manyan idanu saidai bashi da dogon hancin sosai lebensa yanada dan fadi kadan baqi sosai kamar wanda yakeshan sigari amma halitta ce hakan don ko ashana bai taba qartawa ya zuqa ba lumshe idonta tayi tare da janyewa ta koma ta zauna tana hango fuskar Abdul dinta fari tas kyakkyawa me yalwar dogon hanci da qananun lumsassun idanu lebensa jane sosai sai gashin girarsa me gazarzar yanada zara-zaran gashin ido irin nata saidai ita idanunta manya ne.

 

Iskar da taji ya hura mata a idanunta ne yasata dawowa hayyacinta tayi ajiyar zuciya tare da jan flat ta fara zuba masa cheeps din ta hada masa ta zuba masa kunun mardan da Mamy tayi masa ta tura masa ya dauka yakai mata bakinta noqe kafada tayi yayi murmushi ya fara cin abincin yana yabawa da dadinsa shigowar Dad ne yasata miqewa ta nufeshi ya buda mata hanunsa ta shiga yayi kissing tsakiyar kanta yace “zamu tafi saikun taho mu mota zamu hau” ajiyar zuciya tayi tace “shikenan Dad zamu rigaku zuwa yau zakaga My Abdul dina” murmushi yayi ya kalli Mus’ab daya lura mgnr tata batayi masa dadi ba yace “ai yace bazai samu damar zuwa ba munyi waya dashi jiya yayan naki akwai shiririta” yana fadin haka ya fice.

 

Suna gama cin abincin suka miqe driver yakaisu airport suka hau jirgi sai Kanon dabo suna zuwa driven gdansu Dr Mus’ab yazo ya daukesu suka nufi cikin makarantar kamar hadin baki shima Abdul sun shigo shida Manson shine yake driving din zuciyarsa tana cike da farin cikin ganin Samhar saboda mugun kewarta yakeyi da tarin maganganu a bakinsa da shikadai yasan irinsu lkc daya motocin sukayi parking hakanan yaji gabansa yana faduwa ya zuba idanunsa kan motar da tayi parking kusa da tasu Dr Mus’ab ya bude ya fito yana dariya ya zagaya ta saitin inda Samha take ya bude mata gaban Abdul ya qara bada wani rass yana kallon qafarta data fara zurowa kafin daga bisani ta fito gaba dayanta wata uwar zabura yayi yace “Sam…Samha itace wlh Samha ce Mansoor da gaske auren mutumin nan zatayi?” Wani uban tsaki Manson yaja yace.

 

“To Ina ruwanka da wanda zata aura tunda dai bakai bane Mainah Abdu kace bakaso ta hqr ta cireka daga zuciyarta har ta bawa wanda yake sonta dama ya fito zasuyi auransu na qauna don Allah dubesu fah kai salon bai burgeka ba da gani kasan Allah yayi mawa yarinyar nan sauyi….” Wani uban mari ya zafga masa yace “zanci durun uwarka Mansoor ficemin daga mota ka fice nace….” Dariya sosai Manson yake ya bude motar ya rufe masa ya leqa ta window yace “kadai bi a sannu matar wani ce tariga tayi maka nisa” kifa kansa yayi a sitiyarin yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji’un oh my God” yana mgnr zuciyarsa na wani irin tiriri gashin jikinsa ya wani miqe saboda bala’in kishi nandanan qananun idanunsa suka qara qanqancewa suka kada sukayi jawur jikinsa har wani rawa yakeyi.

 

Ita kuwa Samha tunda ta dira a farfajiyar B.U.K take rarraba ido taga ta inda Abdul zai bullo amma babushi babu alamarshi wata sabuwar qaddara lkcn dataje amsar posting letter dinta saitaga an turata Katsina daga ita har Rahmah sosai iyayenta da masoyinta Mus’ab da Rahmah sukayi murna da sauyin da aka samu saboda dama bason zuwa kudun sukeyi ba amma ita haka kawai tunda tagani gabanta yake faduwa ta rasa dalili daga qarshe dai ta alaqanta hakan da cewa saboda asalinta ne da bata sani ba sannan garin masoyinta ne “shi ko Ina aka kaishi?” Tambayar data yiwa kanta kenan amma batada amsa hakanan ta yini raba ido domin ganinsa amma yaqi bari tagansa ta wucce ta gaban motarsa yakai sau uku yana kallonta haushin ganinta da wani ya hanashi yimata mgn yasan da alqawarin da yayi mata na idan sunzo zaije su gaisa da Dad dinta saboda yanda ta nuna tanason hakan amma kishi ya hanashi cika Mata wannan alqawarin ta kirashi a waya yakai sau goma amma bai daga ba da haushi ya ishetama jifa tayi da wayar ta koma ta kwanta jikin Dad dinta tace “yaqi dagawa Dad yaqi zuwa ku gaisa Dad kace zaka Saudi don Allah kayimin dawafi Allah ya mantar dani Abdul a rayuwata kowacce alfarma na nema a gurinsa bayayimin saboda ya tsaneni” Mamy ce tace “inda kinsan yanda na tsani yaron nan Samha dakin daina mgnrsa a gabana bantabajin kince yasaki farin ciki ba kullum quntata miki yake amma dake bakida hankali kinqi mantawa dashi”

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Back to top button