Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 2

Sponsored Links

_~*✊BOSS LADIES WRITERS✊*~_

*KURKUKUN ƘADDARA*

 

_The Prisoners 2_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

 

Bayin Allah su Batul zullumi da fargabar Halin da Angel zata shiga Ya hana su runtsa a daren ranar, A ɗakin tsohuwa Tamira su ka zazzauna saman floor, zuciyarsu na harbawa da faɗuwar gaba, Sun yi shiru kowa da a bun da ya ke saƙawa acikin ranshi. Deeja ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan su yi mata addu’a. Su ka amsa mata da toh, nan fa kowan nan su ya soma karanto addu’o’in da Angel ta koya ma su.

Dare ya nutsa sosai Azeeza tuni ta koma bacci, a saman ƙirjin Gabriel ta kwantar da kanta, Hannun shi na dafe da bayanta kamar zai mai da ta cikin sa.

Jemimah tana a kwance saman cinyoyin Batul ta ƙi yin bacci, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta runtse idon ta ta yi bacci amma ta kafe akan sai Genie ɗinta ta dawo, a ƙarshe ma da su ka matsa mata sai ta sanya masu kuka, Tsananin tausayinta ne ya kama su, Haris yace ku bita a hankalin ni banga laifin ta ba, saboda ita yarinya ce ta saba kwana rungume da Angel dole taji ba daɗi, Rarrashin ta ya kama ta mu yi, Amsa mashi su ka yi da toh, atare su ka haɗu suna rarrashin jemimah daƙyar su ka shawo kanta.

Parveen sai hammah ta ke yi Ga yunwa ga Bacci, Naufal da ke zaune a gefenta Yace da ita Ki kwanta ki yi bacci mana, Kin ishe ni da hammah” harara ta ɗan jefa mashi tare da cewa”in yi bacci fa ka ce? Sai kace bansan ciwon kaina ba, Ta ya zan iya runtsawa bayan yan uwar mu tana acikin kurkuku….” ta6e la66ansa Yai”Naji daɗi da ki ka yi Hankali” bata tanka mashi ba sai ma ɗaura kanta da ta yi asaman laps ɗinshi.

“Batul mu tashi mu bi Genie mu ɗauko ta” Muryar Jemimah ce ta yi maganar Fuskar ta ta yi sumtum saboda kukan da tasha, Lallashinta Batul ta yi” Ki yi haƙuri kin ji, In sha Allah zata dawo Cikin Mu, Badajimawa ba,” Zumbura ba ki ta ɗanyi “Toh idan ta dawo zamu gudu ko”? gaba ɗaya hankalinsu Haris ya dawo kanta

Murmushi Batul ta sakar mata”Eh mana da zarar ta dawo zamu gudu mubar kurkuku….” tunkan ta kai ƙarshen maganar Jemimah ta katse ta da cewa”Zamu koma gidan daddyn Genie Ko? In da zamu sakata mu wala mu yi rayuwar mu babu takura Allah yasa genie ɗin mu ta dawo da wuri na ƙosa muje inga gidan daddyn ta”

farin cikin da su ka gani akan fuskar jemimah a yayin da ta ke yin maganar yai matuƙar karya masu Zuciya, Har sai da suka ji hawaye sun cika idanuwansu, cikin rauni na murya Deeja tace da ita

“Jemimah Pray for Her! Tana buƙatar addu’ar mu, mu dage da yi mata addu’a har sai ta dawo Cikin mu” jinjina kai jemimah ta yi tare da cewa”tom zan mata addu’a” ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta, acikin zuciyarta tana ambaton Ya Allah ka dawo min da Genie ɗita in dai kana son farin ciki na….”

“Gabriel Ka tada azeeza ta tashi Mu haɗu mu duka wurin yi mata addu’a ba yadda za’ae muna acikin tashin hankalin nan ita tana bacci, ko dai jemimah da ta ke ƙarama a cikin mu ta kasa runtsawa balle ita” Rubina ce ta yi maganar, Girgiza mata kai Gabriel yai alamar Bazai tayar da ita ba

“I’m sorry to say I can’t wake her I don’t want to worry her, Just Let her sleep.” ɗaure fuska Rubina ta yi jin a bun da yace, ita haushinta yadda suka tashi hankalin su akan Angel amma ita Azeeza ta lafe jikin shi Hankalin ta kwance ta ke sharar bacci.

“Akwai matsala fa! Dare Yana ƙara nutsawa babu alamun Angel zata dawo” Sarah ce ta yi maganar tana daga zaune Ta jingina bayanta jikin bango, Ta saki dogayen ƙafafuwanta ƙasa.

“Duka yaushe ta tafi da har za ki fara tunanin akwai matsala! Pls mu yi mata fatan Alkhairi, Ni gajan haƙuri ke bana so” acewar Haris.

To jama’a abu fa kamar wasa A ƙalla Angel ta ɗauki tsawon awanni babu ita babu alamarta, Idanuwansu sun kaɗa sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa ga zullumin rashin ta atare da su, sun dage sai addu’a Su ke Yi mata, Ba zato ba tsammani Hasken Ɗakin su ya gauraye ko’ina, ta jikin ƙofar ɗakin tsohuwa da bata ƙarasa datsewa ba su ka hango hasken da ke kurɗaɗowa, Hankalinsu Ba ƙarami tashi yai ba, A kiɗime su ka mimmiƙe tsaye hatta Azeeza da ke bacci sai da ta farka tana faman murza idanuwanta da yatsun hannayenta.

kallon kallo suka shiga jefawa junansu fuskokinsu ɗauke da matsananciya damuwa
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un;’ shine kalmar da ta fara fitowa abakunansu Deeja, Yayin da su ke a tsaitsaye cirko cirko, Bakomai ne ya tayar masu da hankali ba face ganin Safiya ta yi ba tare da Angel ta dawo ba. Nan ta ke ransu ya basu cewar wani abu ya faru da ƴar uwarsu……………..

Shine meke Faruwane ata 6angaren Angel!?

Ai tun lokacin data watsa da gudu ta nufi Cikin kurkuku, Sautin kururuwa
Mai ƙaraji da gurnani ya cika kunnuwanta, ga wani azababben San yi da ya addabe ta, kamar jaura ta gifta Cikin duhu ta ke gudu

Adai dai lokacin da ta ɗaura ƙafarta saman ground floor ɗin nan Inda ke kewaye da dogayen benaye Ba zato Ba tsammani idanuwanta su ka sauka akan ƙafafuwan Tsohuwa Zafreen Lamarin yai matuƙar gigitar da ita, sam Ba ta yi tsammanin Zata ci karo da wani abu ba ita kawai ta sanyawa ranta cewa Danish ne kaɗai mutumin da zata haɗu da shi.

Mummunar faɗuwa gabanta yai, ƙirjinta ya hau bugu da ƙarfi da ƙarfi A firgice ta ɗago da idonta akan tsohuwa zafreen da ke a ruƙe da sanda, Kasancewar Filin Yana da Fitilu masu haske can saman silin ya gauraye ko’ina, daga ƙasa har sama shigar Jajayen kaya ne a jikinta kamar kullum Fuskarta na asanye da takuntumi.

“Ya Allah saida nayi addu’a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar tsohuwar nan Ina lillahi…..” acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani yunƙuri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta ƙwas ƙwas har cikin dodon kunnan Angel, Duk ta ku ɗaya idan ta yi sai gaban Angel Ya faɗi, tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.

Ko da ta ƙaraso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo irin na marasa imani, Shuɗayen idanuwanta sun Ciza launinsu.

“Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da kika fara ƙetare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su ne suka ƙarfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoner ɗin da ya ta6a ƙetare Iyakar shi ba sai Akan Ki”!

Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.

yawu Angel ta haɗiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har ɗiɗɗiga ta ke a ƙasa.

“Ko za ki Iya faɗa min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon ɗakin ku kika fito”? Muryar Angel na rawa ta soma magana”Tsautsayi ne da ƙaddara, dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin ɗan uwana Danish ne shiyasa na fito neman shi…..” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.

Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ƙara kusanta kanta da Angel, A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai

“Tun jiya dana shigo ɗakin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani abu, Unaisah ke ce ƙwarin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne ƙetare Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya ƙwatarki daga hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da ƙarfi zuwa mai rauni……” Zazzare ido Angel ta yi tamkar ƙwayar zata faɗo ƙasa Jikinta sai kerma ya ke yi.

“Kin jama kan ki bala’i da masifa! Not only u! Hatta Ƴan uwan ki da Ki ka baro ɗaki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa farin Cikin da ku ke da shi” Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.

Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani irin rauni na murya ta furta”duk horon da za ki yi mani kada ki haɗa da ƴan uwana, Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta”

Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa “Umarni ki ke Bani? In yi abunda kike so”? A ruɗe Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai ba.

“Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a shaƙar ƙamshin mutuwa ba amma yau zansa ki shaƙeta sosai, waɗannan Idanuwan naki launin ruwan toka yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau ɗin nan zan canza masu kamannin…..” Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.

Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu’umin Murmushin nan nata na tantiran Ƴan duniya waɗanda su ka ga jiya su ka ga yau

Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta

“Ɗan Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan Nasara” Kalmar ƙarshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta ƙasa, Nan ta ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu’a da tazo bakinta, Cikin ƙankanin lokaci ƙurar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta riga ta yanke shawarar komawa ɗakin su gurin ƴan uwanta saboda gudun kada tsohuwa zafreen ta cutar mata dasu kamar yarda ta furta mata cewa zata je gare su, A hautsine Ta juya da niyar tabi hanyar da ta 6ullo don ta koma ɗakin su, Rass gaban yai mugun faɗuwa ganin babu corridor ɗin kwata kwata kamar ba’a ta6a yinta ba, Yawu ta haɗiya zuciyarta na harbawa da sauri da sauri tamkar zata faso ƙirjin ta.

A fujajen ta mayar da dubanta ga dogayen benayen da tsohuwa Zafreen ta faɗa mata cewa ɗan uwanta na anan A hankali ta ke tafiya tana tunkarar benan Yayin da ta ke cigaba da karanta addu’o’in neman tsari a cikin bakinta, firgita ta yi sakamakon Jin sautin shessheƙar kukan Su Azeeza a cikin kunnanta, ta ko’ina sautin kukansu ne kamar zasu zautar da ita, Tunawa da barazanar da aka yi mata acan lokaci na farko data ta6a shigowa prison yasa ta yardarwa kanta cewa ba kukan su bane Anayi ne don a tsoratar da ita, hakan yasa ta samu ƙwarin gwiwa, Watsawa ta yi da gudu ta Haura saman benan Har ta yi tsakiyarshi Taji ya soma motsawa Matakalarshi ta dinga komar da ita baya kamar dai yadda ya faru a jiya, Gudu ta dinga yi tana haurawa, wata uwar zufa ta wanke fuskarta, daƙyar ta samu ta haye saman Second floor.

Numfashi taja tare da fetsar dashi, sai faman yin haki ta ke yi, Tsawon mintuna takwas kafin taci gaba da tafiya tana bin hanyar, wani abu daya ƙara rikitar da ita, Ginin wurin ya dinga canza mata hanyar da take bi, Sai ta yi nisa taga an dawo da ita Baya, hakan ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba. Tarasa ina zata dosa, Tamance ma hanyar da zata bi ta isar da ita hawa na Uku, tana Cikin yin tafiyar kamar zautacciya ita kanta batasan inda ta ke jefa ƙafafuwanta ba, Cikin rashin sa’a ta faɗo cikin wani ɗaki.

Idanuwanta basu sauka a ko’ina ba sai akan wasu tsoffin mata da ke agaban manyan tukwanan girki, An ɗaura su saman murhu Wuta sai Ci ta ke, Hannuwansu ruƙe da ludayi Suna Juya naman da ke a cikin Tukunyar girkinsu, Gabanta ne ya faɗi ganin Naman mutun yatsun hannun da ta gani ne cikin romar miyarsu ya tabbata mata da cewa Naman mutunne su ke yi. farfe sun shi.

Basu lura da ita ba sai da ta daddage ta kwatsa ƙara Mai sautin gaske silar hakan Ya janyo hankulansu ga kallonta, zaro ido waje ta yi ganin sun ganta, a kiɗime ta manne ma bango ɗakin, jikinta sae kerma ya ke yi Tamkar a mafar ki ta ke kallon su.

Halittarsu gwanin ban tsoro Munanan gaske, ga Uban tamoji tamojin akan fatar fuskokin su, kamar jijiyoyin jikin bishiya ƴan rigunan da ke sanye a jikin su launin Ja Kamar yar shara ta maza da su ke sanyawa, Ga uban gashi a hammatocinsu sai ɗoyi suke Yi. a ƙalla sun kai su Shida, uban fason da ke a tafin ƙafafuwan su kamar Kwanannar Fura da ta bushe ta tsastsage.

Kamar mahaukata haka suka fashe da dariya mai sautin gaske Muryoyinsu ne suka Cika mata kannuwanta.

“Laah ga Unaiserh Ta kawo mana ziyara, yau zata sha farfesun Ƴan Ci ki, Zonan Unaisah Yarinyar mu, Zo ki sha roman nama”

La66anta na kerma ta furta”Bazanci ba, Ni ba wurin ku nazo ba, Dan Allah Ku ƙyale ni In tafi….” Tun kan ta ƙarasa maganar ɗa ya daga Cikin tsoffin ta ɗebo farfesun a cikin ludayi hada Yatsun hannun mutun, tunkaro Angel ta yi tare da miƙa mata Ludayi” Kar6i nan ƴata ki sha Roman Farfesun Mutun akwai daɗi” Tashin zuciya ne ya farma mata, a matuƙar firgice ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai kash ƙofar ta ƙi buɗuwa.

Fashewa ta yi da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, da hannu ta dinga Bugun ƙofar kamar zata 6alle ta ko motsi ƙofar ba ta yi ba har sai da tsoffin nan suka cimmata, Ta ƙarfi Suka zaunar da ita tare da rurruƙe mata hannayenta da ƙafafuwanta ta yadda ba za ta Iya ƙwatar kanta ba. Tsohuwar da ke a ruƙe da Ludayin ce ta zuƙunna agabanta tare da tsoma hannayenta masu zaƙo zaƙon akaifa ta ɗebo Ƴan hanjin Cikin sai tiri suke Yi, runtse ido Angel ta yi sosai ta guntse bakinta zucuyarta na tashi kamar zata yi hauka, Bata ta6a ganin masifa ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗa ta da tsoffin nan, Duk yadda tazo ta kufce masu abun ya faskara kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, Ta ƙarfi suka 6are bakinta har saida gefe ya dinga fitar da jini, baiwar Allah taji raɗaɗin azaba, duk ta ciccije la66anta da tsiya su ka dunga tura mata ƴan hanjin abakinta, don dole ta dinga haɗiyarshi da zafinshi harshenta duk ya sale haka la66anta ma sun yi suntum.

Kamar zautacciya haka tsoffin nan su ka maida ta, Sai da su ka gama azabartar da ita kafin suka saketa Anan ƙasa ta shiga kwarara amai suna kallonta suna dariya, kaf saida ta amayar da ƴan hanjin da su ka bata, wani azababben ciwon kai ya farmata, Ga jiri da ta ke gani acikin idanuwanta

“Lami ba ta ƙoshi da farfesun ba, A ƙaro mata wani” maganar su taji a cikin kunnanta, a galabai ce ta miƙe jiki ba ƙwari ta dinga bugun ƙofar ɗakin har sai da ta samu daƙyar ta buɗe ta, gudu ta ke yi jini na wanke rigar Jikinta saboda bakinta da suka sanya ƙarfi wurin 6are shi gefe ya tsage bleeding ya ke kamar jinin jikinta zai ƙare.

Baiwar Allah ga zazza6i mai zafi daya rufar mata, Jikinta sai kakarwa ya ke yi, ta gama fita hayyacinta, Neman hanyar da zata koma cikin ƴan uwanta ta ke yi saboda ta riga da ta sare da kurkukun, mutuwa ka ɗai ta ke gani acikin idanuwanta gashi ba ta son ta mutu ba tare da ta yi bankwana da ƴan uwanta ba.

Tsabar raɗaɗin da bakin ta ke yi mata ne ya jaza mata rauni da rashin kuzari a jikinta Ƙaffuwanta suka harɗe Gaba ɗaya ta kife saman floor, kanta ya daki ƙasa sosai, runtse idanuwanta ta yi yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta miryarta babu sauti take ambaton sunan ƴan uwanta tana neman taimakon su akan su zo su taimake ta, kada ta mutu ba tare da sun gana da junan su ba, Babu alamun hankali atattare da ita, sai sambatu ta ke yi ita kaɗai, Addu’o’in da ta ke ƙokarin yi yanzu sun kufce mata……

Sautin tafiya ta soma Ji kamar motsi motsi saman jikinta, a daddafe ta miƙe tana faman yin nishi, Ras taji gabanta Ya faɗi ganin wasu Girgizo kwafta kwafta a kewaye da ita, Tashin hankalin da ta shiga ne yasa ta fasa ƙara tare da yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta miƙi hanya tana gudu tana waiwayon su gaba ɗaya sumar kanta mai tarin yawa ta rufe mata idanuwanta, Cikin rashin sa’a Ta 6urma cikin wani ɗaki tare da Jan ƙofa ta datse, ba tare da ta ankara da inda ta faɗo ba, Jikinta sai kerma ya ke Yi.

“Barka da zuwa Ɗakin Fiɗa, Ga dukkan Alamu mun samu wata sabuwar ma’aikaciyar” Muryar matashin saurayi taji acikin kunnanta, Tun kafin ta juya ta kalle su Jikinta ya hau tsuma, A furgice ta waiwaya tare da sanya hannu ta nannaɗe sumar kanta da ta rufe mata idanuwanta, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un bakomai ne yasa ta ambaton hakan ba face Matasan ƴan matan da ta gani kwance saman gadaje kalar na marasa lafiya, zindir babu kaya a jikin su hada masu Ɗauke da juna Biyu, gwanin ban tausayi, Giants ne tsaitsaye akansu Hannayensu ruƙe da kayan theater suna acikin shigarsu ta baƙaƙen Kaya.

“Ƴar uwa dan Allah ki taimake ni, ki fitar dani daga wurin nan kada su kashe ni” waro ido sosai Angel ta yi akan matar da ta yi mata magana, Ita ce mai ɗauke da juna biyu Daga ganin cikinta tsoho ne Ya shiga wata na tara. Sun tu6e mata kaya tsiraicinsu duk abayyane, Wannan wata irin masifa ce? Hasbunallahu wa’ni e mal wakeel Lahaula wala ƙuwata Illa Billah, Allahumma ajirni fil musibati wa aklif ni khairan min ha,’ adabarbarce Angel ta ke ambaton hakan. Matar sai kuka take yi tana rokonta akan ta taimake ta ko dan saboda yaron da ke a cikinta, rushewa Angel ta yi da kuka ba tare da ta Iya furta magana ba.

Ɗaya daga Cikin Giant ɗin dake a ɗakin tiyatar ne Ya tunkarota Hannun shi ruƙe da wuƙa, Tunkan yai magana ta fahimci abinda ya ke nufi, aiko Jiki na 6ari ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai ina kafin ta yi hakan ta ji Ya damƙi hannunta, ruƙo bana wasa ba, ta ƙarfi ya dinga janta har sai da ya kai ta bakin gadon da matar nan me ciki take kwance.

Zura mata wuƙar ya yi a cikin hannunta Ya damƙe shi da nashi hannun, Ta ƙarfi ya soma ƙoƙari sanyata farke cikin matar, Kamar zata zauce saboda tsabar kiɗima har Allah ta dinga roƙo akan ya ɗauki ranta kafin faruwar hakan, Bata ta6a danasanin zuwanta duniya ba sai yau, ta yi fatan ace bata ta6a wanzuwa acikinta ba, ta yi kuka kamar ranta zai fita tayi haukan tayi borin duk abanza, ta ƙarfi giant din nan ya ɗaura hannunta saman cikin matar nan da ke ta kuka tana roƙonta akan ta taimake ta, Saboda rashin imani Ya yi amfani da hannun Angel wurin farke cikinta Kamar an fasa pipe ɗin ruwa Haka jini yadinga tsastsafowa yana wanke fuskar Angel har ta cikin bakinta ya dinga fallasa yana shiga.

Hatta jaririn da ke acikinta bai tsiri ba, Biyu suka raba shi da wuƙar, Allah sarki Angel Gani ta yi kamar ita ta aikata kisan kan, Wata irin kururuwa ta saki da iya ƙarfinta na karshe ta bangaje giant ɗin da ke a ruƙe da ta ita Amakance ta dinga Tafiya tana neman Hanyar fita, muryarta da sautin kuka ta ke faɗin.

“Nashiga Uku na bani na lalace Inalillah wa’inna ilaihirraji’in Na aikata kisan kai! na yi kisa da hannayena Shikanen Na mutu, nasan Allah ba zai ƙyale ni ba, Na kashe mashi baiwarshi da bata ji ba bata gani ba, Wayyo Allah Na……”

Yatsun hannayenta ta ɗaura asaman kanta kamar Aljanna Jinin matar duk ya canza mata kamanninta, duhu ya mamaye idanuwanta da zuciyarta.

Giants ɗin da ke Yin aikin fiɗar sai tiƙar dariya su ke Yi, Hankalinsu kwance su ke Cigaba da gudanar da aikin su, yadda su ke farke cikin mutun kamar dabba babu imani ko misƙala Zarratin.

Da wata irin raunatacciyar murya ta ke faɗin”Allah ba zai ta6a barin ku ba, Mugaye Azzalumai, Tun agidan duniya za ku fara gir6ar abunda ku ka shuka ƴan iska fasiƙai masu zuciya irin ta kafuran farko, In sha Allah Ni ce Ajalin ku, Sai kun ɗanɗani kuɗar ku sai kun gane ba ku da wayau, kamar yarda kuka sa na zubar da hawaye na in sha Allah kuma za ku zubar da naku hawayen Na jini ma, Yadda ku ka cutar dani ku ka sa na aikata kisa kuma sai an yi maku mafiyin shi……” ƙululun baƙin Cikine ya tokare maƙoshinta, silar hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar.

Hannayen ta biyu ta sanya saman wuyanta, ta shaƙe shi sosai cikin fitar hayyaci kamar zata kashe kanta, tsabar raɗaɗin da ƙunar da zuciyarta ke yi mata ne yasa ta ke ƙokarin aikata hakan, tana a cikin wannan mawuyacin halin taji An sunkuce ta kamar Ɗiyar roba haka aka ɗauke ta sama, wani gabjejen giant ne yai mata wannan ɗaukar, fucewa yai da ita daga Cikin ɗakin Ɗauke saman kafaɗarshi bai nufi ko’ina da ita ba sai cikin wannan Ƙaton palourn Da taron matsafa su ke gudanar da Bautar su, Wasu dogayen mutane masu sanye da jajayen kaya ko’ina na jikin su arufe ya ke, sun kai su talatin, Agaban dodon tsafin su, Anan Ya sauke ta saman floor, a durƙushe ta kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, Hatta numfashinta a hargitse yake fita Jikinta yai zafi rau kamar wadda aka tsomo daga cikin wuta.

A lokacin ta kai maƙura bata iya ta6uka komai, motsin hannun mutun ta ji ajikinta, saboda duhun da idanuwanta su ka yi mata yasa ta makance, bata ganin komai, kayan Jikinta suka cire mata gaba ɗaya iya pant ɗin ta su ka bar mata, duk da bata acikin hayyacinta sai da ta shiga matsanancin tashin hankali tunawa da robar ruwan zamzam ɗin da ke a cikin wandonta, rarrafe ta dinga tana laluban suturarta don ta mayar dasu a jikinta sai dai kash bata samu damar ganin inda aka jefa mata kayanta ba. Kukan zuci ta dinga yi, duk wani motsinta akan idon matsafan, ita damuwarta ba akan tsiraicinta da suke kallo ba, robar ruwan Zam zam ce damuwar ta, Ya za ta yi idan ta rasa ta? Ita kaɗai ce damar da suke da ita.

Kunnuwata ne suka soma Jiyo mata Sautin muryoyinsu Marasa daɗin ji magana su ke yi da yaren su na matsafa gur6ataccen yare mara daɗin ji, kamar zata haukace, Lallai yau Angel ta shaida tana acikin kurkukun ƙaddara.

Ƙwaryoyin ne ruƙe a hannun matsafan masu ɗauke Da zallar Jinin mutane mai ƙarni, Layi suka jera agabanta suka tsaya tare da Kwarara mata Jinin A saman kanta, Wa’iya zubillah Numfashinta ya gauraye da Ƙarnin Jinin Nan ta ke Ta ƙara sa faɗuwa ƙasa tana fitar da numfashi sama sama, basu ƙyale ta ba sai da su ka yi mata wankan tsarki da jinin da ke a hannunsu, wani kalar Jini mai wari da ƙarni daga gani sun tsuma shi sosai, ba ƙaramin zautar da ita su ka yi ba, Kwakwalwarta bazata Iya jure abinda suke yi mata ba, Tana jin motsin hannayensu a jikinta saƙo da lungu su ke cuccuɗata kamar suna yi mata wanka, Sun goga mata najasa a jikinta sun wulaƙanta Martabar jikinta. Allah ne bai nufa Angel zata mutu ba da tuni ta jima da mutuwa lokacinta ne bai yi ba, domin kuwa warin jinin da suka yi mata wanka dashi kaɗai ya isa ya halakar da ɗan adam. Bayan sun kammala yi mata wankan tsarkin nasu na matsafa, Giant ɗin da ya kawota Ya sanya hannu tare da tattareta kamar tsumma Ya ɗauke ta, Ya fito da ita daga Cikin Falon Ya nufi Hawa Na uku da ita, ba tare da sun mayar mata da uniform ɗin ta ba, ko yatsun hannunta bata Iya motsawa, Sautin tafiyar shi ka ɗai ta ke iya ji acikin kunnuwanta, ƙofar Wani ɗaki Ya tura da ƙafarshi Ya shigar da ita, Katafaren bedroom ne na zamani kamar ba’a cikin kurkukun Ya ke ba, Da jinin jikinta da komai Ya jefar da ita saman gadon tare da Juyawa Ya buɗe ƙofar Ya fuce.

Kaɗan daga Cikin Abunda ya faru da Angel kenan A cikin Daren ranar, Shin me kuke Tunani zai biyo Baya? Bayan gaba ɗaya Shirinsu Ya tarwatse Babu alamun zata haɗu da Danish, Ko da ta haɗu dashi daƙyar ma Ta iya gane shi saboda bata a cikin hayyacinta babbar matsalar babu ruwan zamzam ɗin da zata Iya shawo kanshi, saboda kwalbar tana a cikin aljihun uniform ɗinta, Ya salam!! Wannan wace irin mummunar ƙaddarar rayuwace!!! Me zai faru da su Azeeza? Me tsohuwa zafreen zata yi masu

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button