Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 30

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*30*

*Birnin Sennar Sudan*

Duk Wanda ya shigo wannan birnin yasan dole akwai bikin da Ake saboda garin ya cika makil da dumbin jama’a sai Busan algaita Ake ana wasan dawakai da wasu al’adun garin , dawowarsu kenan daga daurin auren yarima Ayman tare da gimbiya Failuzaa y’ar sarkin Singa. Gimbiya Suhail ta kulle kanta a d’aki Bata bukatan ganin kowa duk da cewa Yan uwanta sun mata Kara sunzo bikin, gaba d’aya haushi da takaicin sultan da Fulani take ji, wai ita zaa rainawa wayo a ce sultan ya rasa Wanda zai mikawa karaga sai kaninsa waziri Babba, bayan duk tsahon shekarun nan tana jiran wannan Rana ne Amma ashe bahaka abin yake ba, tana da yakinin cewa makircin Fulani ne idan bahaka ba ai mulkin ya Dade da fita gidansu waziri Babba tun bayan rasuwar mahaifinsa, kasancewar mahaifin waziri da mahaifin sultan uwa d’aya Uba d’aya suke bayan rasuwar mahaifin sultan ne aka nada kaninsa mahaifin waziri Babba a matsayin sultan bayan ya rasune aka mikawa sultan sarautar sannan yanzu a ce sultan na da y’aya Maza Amma a tsallake a maidawa waziri Babba gaskiya abin Baiyi armashi ba tana ganin suna da Wani shiri ne nan gaba dole ta dauki mataki tana bukatan nazari da shawarwari sosai, haka ta kasance tana safa da marwa a d’aki a yayinda masarautar ke cigaba da gudanar da bikin auren yarima duk da cewa Bataso auren yarima da y’ar sarkin Singa ba Amma yanzu ba shine agabanta ba wannan karagar dole ta Nemo mafita akansa duk da cewa sultan Yana kan karaga Amma yanzu kowa ya shaida Wanda zai gajeshi tana ganin Hakan zai zubar da kima da darajarta a idon jama’a.
Ammi tana bangaren Fulani suna shirye shiryen karbar amarya saboda Yan Kai lefe da daukar amarya sun shaida musu suna hanya, kuyangi ne ke Kaiwa da komowa tsakanin bangaren da amarya zata tare da bangaren Fulani, turaren wuta kuwa kamar kayi kuka don qamshi duk inda ka gifta kunnasu Ake cikin kaskon zinari da azurfa irin na tarihin masarautar, Yan Nigeria sunyi ayari guda daga Adamawa dangin Fulani sun cika gidan gasu nan kyawawa dasu . Aman Yana tare da abokan ango dayawa dangin mahaifinsa ne sai abokansa da sukayi makaranta tare suna inda Ake wasan dawakai da al’adun garin sai bayan sallar Isha suka koma gida a can sukayi magariba da Isha duka. Karfe 10 na dare angama shirya amarya cikin shiga ta alfarma sai qamshi ke tashi aka samu kuyangi da Kuma Yan uwan sultan biyu sai Ammi sai anty Mami suka rakata zuwa turakar mijinta bisa al’adun garin. Ango kuwa daga shi sai Aman da Kuma Fauzan sauran duk sun koma, suna zaune a falon Ayman akayi sallama aka shigo da amarya, nan Ammi ta musu y’ar nasiha daga haka ta rike hannun amarya zuwa d’akin mijinta sannan kowa ya kama gabansa, ango na zaune Aman ya fara murmushi yace ” uhmm bara na tashi kar amarya ta fara Jin haushi na” murmushi yayi ba tare da yayi magana ba, nan Aman ya tashi Fauzan ya mara masa baya a karo na farko kenan tun bayan tasowarsu Fauzan zai fita yabar Ayman shi kadai , Wani iri yaji a ransa shi Kansa Ayman abin ya fado masa a rai amma Babu yadda ya iya wannan al’adarsu ce a ranar da aka kawo amarya a ranar zata kadaice da mijinta saboda wasu dalilansu na gargajiya. tsaki yaja Yana Jin Wani iri gaba d’aya baya son hada d’aki da kowa he needs privacy Amma yau gashi an wayi gari zai hada d’aki da wata. Failuzaa ta yaye abin lullubin tana karewa d’akin kallo ya Hadu over nan ta Gane ba kayan da iyayenta suka Siya mata bane , tana bin d’akin da kallo sai Wani mayataccen qamshi ke tashi ta lumshe idanu tana shakar qamshin, wata kuyanga ta kwankwasa kofa Ayman Baiyi magana ba ta shigo kanta na kallon kasa ta ajiye Wani golden jug me dauke da Madara Mai sanyi sai kofuna guda biyu, kafin ta tashi wata ta sake shigowa da wata tasa kamar warmer Amma a rufe ta ajiye suka juya tare nan wata ta sake shigowa da katuwar tray shake da fruits tazo ta ajiye , kanta na kallon kasa nan suka koma Mai tsaron kofa yaja ya kulle Aman da Fauzan kuwa suna can bangaren Dake kusa da na yarima dayan guest side nasa. tashi yayi cike da kwalisa ya tura kofar d’akin tare da sallama can ciki tamkar baya so tana kwance bisa lallausan gadon tana shakan qamshin turarensa, Kai tsaye bathroom ya shige yayi wanka ya gama ya fito sanye da bathrobe fari da wasu lallausan shoes, gaban dressing mirror ya tsaya Yana taje suman Kansa nan ya dauki body spray nasa ya fesa sunkai kala 4 sannan ya juya zuwa wardrobe ya Bude ya zabi kayan baccin da zai saka. Sai binsa da idanu take ita Batasan inda aka ajiye kayanta ba Kuma bazata iya tambayarsa ba saboda ya shigo Bai mata magana, ya gama duk abunda zaiyi ya haye gado tamkar Babu wata halitta cikin d’akin ya dauki wayarsa Yana duba messages dinsa na social media inda aka watsa hotunansa tare da amaryar tasa nan yayi zooming ya kare mata kallo tana da kyau ba laifi tabe Baki yayi Yana tuna hajjo ko wane Hali take ciki sai Allah , Failuzaa tana ganin iKon Allah lallai wannan sai ta saita mishi zama idan bahaka ba zata Sha wahalan zama dashi . ” Prince wanka zanyi ” ya share minti biyu kafin yace
” Mezan Miki toh , ko wankan zaa maki ne ” ya Bada amsa batare da ya Kalli inda take ba, Wani bakin cki ne ya ziyarci zuciyar ta tace ” kana na nake son dauka ” tabe Baki yayi kafin yace ” toh ki tambayi Wanda suka kawoki don Baki bani ajiyan kaya ba, nan dai d’aki na ne Babu kayan Wani ” kwafa tayi ta tashi nan ta fara cire kayan jikinta ya rage daga ita sai bra da pant , kallo d’aya ya mata ya kauda kai ta shige toilet din Yana Jan tsaki ya cigaba da danna wayarsa. Bayan mintuna goma ta fito daure da toilet ga kananun kitso irin nasu na yan Sudan gashin ya dan jike sai ya kwanta a jikinta ya Kara mata kyau, gaban mirror ta tsaya ta fesa turaruka sannan ta wuce gado ta kwanta kusa dashi Yana satar kallonta, wannan shine karo na farko a rayuwarsa da wata mace ta zauna dab dashi bayan Fulani. “Waya Baki izinin fesa turaruka na , ni bana sharing din abubuwa” a hankali ta juya tana fuskantarsa tace ” ohh.. really hakane, toh ka shirya jiya ba yau bane daga yanzu ka fara sabawa da sharing saboda nan gaba har kaya zamu na sharing nida Kai ” ta juya ta gyara kwanciya. Hararinta yayi Yana Jin he is not comfortable da kwanciya kusa da ita donhaka ta tashi ya fice zuwa parlor, bayansa tabi da kallo tana murmushi tace ” wannan Kuma baka Isa ba wallahi bazaka taba nesanta kanka Dani ba yarima ai ka shigo kenan Babu fita ” nan ta tashi ta gyara daurin towel din ta biyosa zuwa falon, Yana zaune Yana chatting da Aman Yana tsokanarsa da cewa meyake Yi online Ina yabar amarya kafin ya rubuta reply ta fisge wayar ta rike kugu ta tsaya tana kallonsa , mamaki ne a fuskan Ayman ya kasa cewa komai ” ka tashi mu koma ciki, idan Kuma nan kake so mu kwana am ok with that” Wani kallo yake mata shi bayason hayaniya yanzu kansa za fara ciwo Amma wannan tana son sashi yawan magana, nan ta hango abubuwan da aka shirya taje ta Bude kwanon kaza ce aka gasa ta ruwa ruwa ga Wani qamshi na musamman Dake tashi nan ta rufe tasa hannu zata dauki apple caraf ya rike hannayen ” ke Baki da hankali ne kinsan daga Ina ya fito ne?”
“Ba ni aka kawowa ba , gaskiya ni yunwa nake ji” ya fisgota sukayi bedroom yasa key ya kulle yace ” wuce ki kwanta ” ta turo Baki ta haye gado haka yaje ya kwanta ta ajiye wayar tasa a gefe . Baya ya Bata yaja duvet ya rufe tare da kashe wuta yabar bedside lamp d’akin yayi dim haka ga sanyin AC da qamshi na tashi, Failuzaa ta mirgino ta bayansa ta rungumesa nan yaji bugun zuciyarsa na karuwa ta kankameshi kafin ya motsa ta rigasa ta zagaye ta koma gabansa suna kallon juna Baiyi aune ba yaji bakinta cikin nasa gaba d’aya Ayman ya daskare a gadon this is his first kiss , Failuzaa kwararriyace dama can wayayyiya ce nan ta fara sarrafashi tun baya Gane komai har ya fara amsa sakonnin nata masu zafi da wuyar dauka, kidi ya canza dole rawa ma ta canza nan da nan suka Lula sararin samari inda Basusan dashi ba a rayuwarsu gaba d’aya domin kuwa ta kawo mutuncinta, karatu yayi Nisa salo ya canza gimbiya tayi nadamar fara kawo wannan darasin yarima kuwa yace baisan da zancen ba a haka dai aka raya wannan dare me dimbin tarihi a rayuwarsu gaba d’aya sai muce asuba ta gari sabon shiga wai barawo da sallama .

Back to top button