Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 57

Sponsored Links

*PAGE* 5⃣7⃣

Ahankali yabud’e idanunsa da gaba d’aya suka canza launi, ji yake kamar yarubuta ma zarah saki sai kuma yaji bazai iya aikata hakanba dan shi kansa ya san idan yasaketa bai mata adalciba.

‘Dago kai yayi yakallesu d’aya bayan d’aya har a lokacin idanunsu suna a kansa,,,Yarima kallonsa yasafke ga memartaba cikin sanyin jiki muryarsa tana rawa yace kagafarceni ranka yadad’e bazan iya rabuwa da matataba.

Gabad’ayansu a firgice suke kallonsa hatta shi kansa memartaba yayi mamakin furucin da yafito daga bakin yarima.

Murmushi memartaba yayi sannan yace suhail idan na fahimceka toh kana nufin ka za6i matarka akanmu ko?

Cike da damuwa yarima yagirgiza kai yace ranka yadad’e ba haka nake nufiba kawai dai… katseshi memartaba yayi yace kawai dai me!!! Toh bara kaji indai har bazaka iya rabuwa da itaba toh mu yazamar mana dole murabu da kai, dan haka kaje kawai na cireka daga cikin masarautata yanzu ka fita daga cikin iyalaina dan haka na baka awa d’aya kaje duk wani abu da kasan mallakinane kaje kakawo min sannan kafita kabarmin masarauta, inkuma ba hakaba zansa a fitar da kai a wulak’ance.

Gabad’aya d’akin shuru sukayi kamar ruwa ya cisu dan sunsan tunda har memartaba yafurta toh tabbas ba wanda ya isa yacanza.

 

Yarima runtse idonsa yayi yana jin yadda maganar memartaba take dukan dodon kunnansa wani irin d’acine yakeji a ransa

Ummi ko rufe fuskarta tayi da alkyabbarta tana goge hawayen da suka taru a idonta, gabad’aya lamarin ya rikitata.

Daddy ma shikad’ai yasan abinda yakeji a ransa game da maganar da mahaifinsa yafurta, kawai dai ya dakene bai nuna ba.

Dada ce takalli memartaba tace ammah ranka yadad’e ba… d’aga mata hannu memartaba yayi yace banason jin maganar kowa daga cikinku dan ni nariga da nagama magana yanzu lokacin da nabaka zai fara aiki.

Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, ahankali yamik’e jiki ba k’wari kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki haka yake tafiya har yafita daga d’akin.

Rahma da Aunty husna ko kuka sukeyi ahankali, inda sumayya take kuka akan mutuwar aurenta.

Yarima ahaka ya isa part d’insu, bakin gadonsa yazauna yadafe kansa shi kad’ai yasan abinda yakeji gashi an hanasa yai magana, tunani yashiga yi shin in ya bar gidansu ina zaije? Tunowa yayi da maganar memartaba da yace ya fara cin lokacin da yabasa, dan haka yajanyo wayarsa yakira wata number bata dad’e tana ringing ba akayi picking,

Yarima k’ok’arin saita nutsuwarsa yayi suka d’an gaisa sama-sama sannan yace Dr Mu’az kana gari?
Daga chan 6angaren wanda aka kira da Dr mu’az yace eh ranka yadad’e.
Ohk, please kaje kasamar min hotel maikyau yanzu zan shigo Abuja.
Cikin jin dad’i Dr mu’az yace angama ranka yadad’e Allah yakawoka lafiya.

Ameen yarima yace sannan yakashe wayar,
Sannan yakira yasa ayankar masa ticket na mutum biyu yace yanzu yakesonta, kasancewar sanannene nan suka amsa masa, bayan sungama wayar yai musu transfer d’in kud’insu, bayan ya gama Dr khalil yalalubo bai wani 6ata lokaciba yai picking

Yarima ko gaisawa bai bari sunyi ba yace Dr khalil kana ina yanzu?

Daga chan 6angaren Dr khalil yace ranka yadad’e ganinan wajejan anguwarku gidan Auntyna.

Ohk, please kazo yanzu akwai inda nakeso kakaini.

To ranka yadad’e ammah ya naji muryarka haka? Lafiya dai ko?

Yarima kashe wayarsa yayi batare da ya bashi amsaba,,,,mik’ewa yayi yaje yafara had’a duk wani abu da yasan ba mallakinsa bane yaware ma daddy da memartaba nasu sannan yad’auki nashi, wajen wardrobe d’insa yaje yabud’e nan yafara fitar da kayansa yana sawa a trolly, cikin trolly guda yazuba duk wani abu da yake buk’ata sannan yajawo,

Tsaye yayi yana k’are ma room d’insa kallo yana jin k’unci a ransa, janyo trollyn yayi yafito cikin sauri guards d’insa suka zo suka kar6a nan yace suwuce masa da shi waje.
Cike da ladabi suka amsa masa.

Daga nan part d’in zarah yawuce kallonta yayi har lokacin tana kwance, ita kanta zarah yanayinsa kawai tagani tasan yana cikin tashin hankali,

Yarima batare da ya janye idonsa akantaba yace tashi kihad’a kayanki,

Zarah saida gabanta yafad’i tace na’am.

Shareta Yarima yayi yawuce wajen wardrobe d’inta yabud’e nan yafara zuba mata a trolly duk abinda yasan zata buk’ata saida yazuba mata a ciki, bayan ya gama juyowa yayi yakalli zarah da tatsaresa da ido yace tashi muje.

Zarah k’wallah ce tacika mata ido tace ina zamuje?

Tsawar da Yarima yadaka matane yasa tamik’e ba shiri tajanyo veil d’inta tayafa nan Yarima yawuce gaba tana biye da shi, wata kuyangarta ce cikin sauri takar6i trollyn da yake hannun Yarima

Zarah tana biye da yarima gabad’aya kanta ya d’aure gashi yarima bai bata fuskar da ma zata iya tambayarsaba ahaka har suka fito harabar gidan, da mamakinta sai gani tayi sun nufi turakar su memartaba.

mamaki bai ida kamataba saida suka shiga d’akin taga gabad’aya family d’in yarima suna a ciki, bata lura da yanayin da suke cikiba, dasauri tatsugunna tagaishesu, gabad’ayansu babu wanda ya amsa mata,

Ta d’auka basujiba nan tak’ara gaishesu, dady da abbah ne kawai sukayi k’arfin halin amsa mata,

‘Dagowa tayi takalli ummi da talullu6e kanta da alkyabba, sai kuma takalli su Aunty husna da rahma da suketa kuka, nan jikinta yak’ara yin sanyi, daganan tamaida kallonta ga sumayya da take gefen dada tana ta rusa kuka, inda dada tabuga uban tagumi, sultana sadiya ko ta cika tayi fam.

gani tayi yarima ya wuce wajen memartaba nan yarussuna yamik’a masa wasu files, a wulak’ance memartaba yakar6a sannan yace ina fata komai ne nan kakawo min.

Ahankali yarima yace eh ranka yadad’e,

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace yarima ka bani mamaki yanzu saboda mace ka amince karabu da kowa naka, inaso kasani dangi basu canzuwa ammah ita mata a kowane lokaci zaka iya canzata, tunda ka za6i mace akan danginka toh sai katashi kutafi.

Zarah cikin sauri tad’ago kai takalli memartaba da yake maganar dan kwata-kwata bata fahimci inda maganarsa tadosaba,

Dada ce cikin damuwa tace ammah har a yanzu suhail idan ka amince zaka rabu da ita toh bismillah dan kasan memartaba yana nan akan bakansa,,,tak’arashe maganar tare da mik’a masa takardar.

girgiza kai yarima yayi yace kugafarceni har yanzu ina akan bakana nima yana fad’in haka yamik’e

Sumayya ce tasake fashewa da kuka tace yanzu saboda waccan jakkar kasakeni saki ukku yarima, wlh bazan yardaba sai ka maidani d’akina, duk inda kaje zaka dawo kataddani.

Zarah sai a lokacin ta fahimci abinda ake tattaunawa gabantane yashiga dukan ukku-ukku a firgice takebin kowa na cikin d’akin da kallo,

Rahma ce tayi saurin mik’ewa dagudu taje tafad’a jikin yarima, cikin kuka tace dan Allah bro kar katafi kabarmu dan Allah ka amince karabu da matarka kazauna cikin danginka.

Yarima idanuwansa ne suka kad’a sukayi jawur kallon daddy yayi da ya janye fuskarsa gefe, a 6angaren abbah ma gefe d’aya yake kallo,

Yarima har ya bud’e baki zaiyi musu magana sai kuma yafasa, janye rahama yayi daga jikinsa, kallon umminsa yayi da taketa k’unshe kukanta, wani iri yaji a ransa gudun kar yaimata magana yaja tayi kuka saisa baice mata komai ba yawuce yanufi inda zarah take tsugunne tana hawaye.

Kallonta yarima yayi yace tashi muje.

Girgiza kai zarah tashiga yi dak’yar tabud’e baki muryarta tana rawa tace please yarima kar karabu da danginka ni yafi dacewa karabu da ni dan danginka sune komai naka, mik’ewa tayi tare da fashewa da kuka had’e hannuwanta tayi waje guda tace dan Allah yarima na rok’eka kacika umurnin memartaba kasakeni kawai, cikin sauri taje takar6o takardar hannun dada tadawo inda yake tsaye tamik’a mashi tace please karubuta min sakina, kar katafi kabar su ummi, neman tura mashi tankarda tayi a hannunsa ganin ya k’i kar6a yasa tawuce inda ummi take zaune tatsugunna cikin kuka tace please ummi kisa baki yarima yarubuta min sakina bana son yasamu matsala da kowa dan ku kune farin cikinsa.

Ummi kasa 6oye kukanta tayi nan tafara sheshek’ar kuka, zarah ganin ummi batada niyar cewa komai yasa tamik’e takoma wajen yarima tace kaduba kaga ummi da ‘yan uwanka kuka suke yanzu ka amince katafi kabarsu cikin….wani gigitacce mari yarima yakwad’a mata wanda gabad’aya ‘yan cikin parlourn saida suka kallosu, yarima cikin 6acin rai yace zarah kidawo hayyacinki.

Nan zarah tashiga hankalinta tare da kife kanta a k’irjin yarima tarushe da wani sabon kukan, yarima jin kukan nata yake har cikin ransa, janyeta yayi daga jikinsa nan yarik’e mata hannu suka fara tafiya, memartaba janye idonsa yayi daga kallonsa inda su daddy daman basu d’ago ba dama.

Aunty husna ce cikin sheshek’ar kuka tace yarima na rok’eka kar ka aikata hakan dan Allah kadawo,

Jan hannun zarah yayi suka ficce daga parlourn Aunty husna har ta mik’e zata bi bayansa nan taji muryar memartaba ya ce kar wanda yasaki yabi bayansa.

kan dole takoma tazauna.

Yarima yana fita nan yatarar da Dr khalil tsaye yana jiransa, wajen motar dr khalil yanufa.

Cikin sauri Dr khalil ya iso inda yake yace yarima ya naganku haka?

Yarima kallon guards d’in yayi yace susaka masa kayansa a boot, cikin sauri suka cika umurninsa.

Nan suka bud’e masa motar yashiga, zarah da take tsaye fuskarta rufe da mayafi itama aka bud’e mata baya tashiga.

Dr khalil da yake tsaye zuwa yayi yashiga motar tare da kallon yarima yace ranka yadad’e ina muka nufa?

Yarima batare da ya kallesaba yace airport.

Cikin sauri Dr khalil yatayar da motar, lokacin da zai fita daga masarautar yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri a cikin ransa,

Tafiya suke ammah gabad’aya babu wanda yayi magana,

Dr khalil juyowa yayi yakalli yarima da yazuba ma titi ido cike da damuwa yace ranka yadad’e wace irin tafiya ce ta gaugawa takamaka haka? Ina zakaje?

Yarima batare da ya juyo ya kallesaba yace Doctor ga amanar hospital d’ina nan na damk’a a hannunka domin nasan zaka kularmin da shi kamar yadda zan kula da shi ammah ban saniba ko nan gaba za’a kawo wanda zai maye gurbina, koma mekenan nidai na aminta da kai.

 

Kiiittt yaja burki yatsaya tare da juyowa yakalli yarima, cike da damuwa yace please yarima kaimin bayani yadda zan fahimta dan gabad’aya ka d’aure min kai, wace irin tafiya ce zakayi haka? Ina zakaje please kafad’a min.

 

Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace please kayi sauri flight d’in da zamu bi ya kusan safka.

Tada motar Dr khalil yayi dagudu yafigi motar.

Yarima ta mirror yakalli zarah da tabuga uban tagumi, jingine kansa yayi a kujeyar da yake zaune tare da k’ura mata ido ta mirror d’in, zarah ko bata ma san yanayiba dan gabad’aya ta yi zurfi cikin tunani.

Suna isa flight d’in yana safka, Dr khalil cikin sanyin jiki yakalli yarima yace Dr toh yanzu sai yaushe zaka dawo?

Murmushin k’arfin hali yarima yayi sannan yace kar kadamu ba wani dad’ewa zanyiba.

Jinjina kai Dr khalil yayi sannan yace ammah zanyi kewarka dayawa,

Yarima kallon abokin nasa yayi yace nidai fatana karik’e min amanata kacigaba da tafiyar da komai daidai kamar ina nan.

Murmushi Dr khalil yayi yace karkadamu insha Allahu zanyi kamar yarda kace,
Nagode sosai abokina,,, yarima yafad’i hakan cikin jin dad’i, sannan yabud’e k’ofar yafita,

Nan shima Dr khalil yafita, yarima dakansa yabud’e ma zarah k’ofan, dak’yar tasafko k’afanta tafito, nan yarima yana rik’e da ita yai waya akazo aka kawo masa komai nasa, kayansu aka fitar aka saka a cikin flight d’in.

Dr khalil har wajen jirgin yarakasu nan suka k’ara sallama da yarima cikin rashin jin dad’in nisan da zasuyi da juna.

Zarah ko saboda tashin hankalin da take ciki baisa tayi murnaba koda wannan shine karo na farko da tafara shiga jirgi.

Daga gefen yarima take zaune har jirgin yatashi, wani irin kunci da bak’in ciki yaziyarci zuciyan yarima a lokacin da suka fara tafiya, bak’in space d’insa yajanyo yadad’e idonsa, zarah cikin rashin k’arfin jiki takwantar da kanta a saman k’irjin yarima.

Rungumeta yayi cike da tausayinta, ahaka zarah tayi bacci.

Cikin k’ank’anin lokaci suka isa garin abuja.

Jirginsu na dira yarima yakira Dr mu’az yace gamu mun safka.

Dr mu’az cewa yayi ranka yadad’e ai gani nan tun d’azu nake jiran safkarku.

Tada zarah yayi da take bacci nan suka fito.

Wani mutum ne wanda bazai wuce tsaran yarima ba koda ma zai girmi yarima toh dakad’an ne, nan ya iso inda suke fuskarsa d’auke da fara’a.

Yarima koda yana cikin damuwa ammah hakan baihana sa nuna jin dad’in ganin abokin nasaba,

Dr mu’az cike da jin dad’i yace sannu da zuwa prince suhail.

jinjina kai kawai yarima yayi sannan yamik’a masa hannu sukayi musabaha.

kallon zarah yayi yace sannu madam.
Zarah batare da ta kallesaba tagaishesa, daga nan yace prince zamu iya tafiya.

Murmushi kawai yarima yayi nan yaruk’o hannun zarah, inda Dr mu’az yasa aka d’aukar musu kayan aka saka bayan boot.

Koda suka kama hanya Dr mu’az kallon yarima yayi yana murmushi yace prince ka kwana biyu bakazo garin nan ba yau ma ji nake kamar a mafarki naganka.

Murmushi yarima yayi yace kaima kasan yanayin aikinmu ne yake 6oyemu tunda kaima kakwana biyu baka lek’aniba.

Dariya Dr mu’az yayi yace wlh abokina nima naso inzo abubuwan ne sukaimin yawa kowane lokaci busy nake ammah da badan hakaba ai da ba abinda zai hanani zuwa dan kaima ka san banda aboki sama da kai dan kaimin *HALARCI* a rayuwata wanda bazan ta6a mantawaba.

Murmushi yarima yayi yace kadaina magana akan abinda yariga da yawuce.

Hmm ai duk zuciya mai adalci bazata ta6a mance alkhairin da akayi mataba,,,daidai lokacin Dr mu’az yashawo kwanar gidansa.

Kallonsa yarima yayi cike da mamaki yace ni da zaka kai hotel ya naga ka kawomu gidanka?

Murmushi Dr mu’az yayi yace taya kake tunani zan iya barinka kazauna a hotel alhali ina cikin garin nan, ai kaima kasan hakan bai daceba.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonsa sannan yace kar kadamu ni nasan fiye da hakan ma zaka iya yimin ammah ni nafi buk’atan son zama a hotel d’in.

Doctor Mu’az tsayar da motar yayi yajuyo yakalli yarima cike da damuwa yace ranka yadad’e kayi hak’uri da inbarka kazauna a hotel na k’wammace ni inbar maka gidana kazauna inje inkama haya,
Yarima shuru yayi baice komai ba.
cike da damuwa Dr mu’az yace dan Allah ka amince muje gidana.

Zarah da take zaune baya tana saurarensu ita kanta cikin ranta bata son suje hotel.

Murmushi yarima yayi yace shikenan na amince Dr.

Cike da jin dad’i Dr mu’az yace nagode sosai doctor.

Nan yatada motar, a bakin gate d’in gidansa yayi horn, cikin sauri megadi yazo yabud’e masa gate nan yacinna motarsa cikin makeken gidan.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Ummu Zainab tsakanina da ke saidai addu’a dan banda abinda zan biyaki da shi, Allah yak’ara lafiya, Allah yasa ciwon zakkar jikine, Allah yatashi kafad’unki, Nagode, Nagode, Nagode sosai Allah yabiyaki abinda kikayi min_

Back to top button