Nasarar Rayuwata 19
*Talented writers forum*
*19*
Sun kammala exams lafiya Ayman ya shirya tafiya Sudan Hutu da Kuma amsa Kiran da sultan ya masa, sunyi sallama da Ammi ta rakasu har airport private jet na masarautar tasu tazo ta daukesa tare da Fauzan suka wuce Birnin Sennar. Fulani na falo ta buga tagumi tana tunanin halin rayuwa guda tajiyo daga waje da busar algaita tabe Baki tayi yau Kuma wane bakon aka samu oho! Jakadiya ce ta shigo cikin kankanin lokaci ta risina tare da cewa ” Allah ya Kara Miki lafiya yanzu na samu labarin isowar yarima Babba , yanzu haka Yana bangaren Sultan ” ware Ido tayi tace ” yarima Kuma? Allah yasa dai lafiya” insha Allah lafiya ne Babu wata matsala don na Hadu da Fauzan yace min Hutu suka samu shine ya kawo mana ziyara ” sauke ajiyar zuciya tayi tare da gyada Kai bayan kaman minti d’aya tace ” aje ayi duk abunda ya dace a can bangaren nasa ”
“angama uwargijiyata ” daga haka ta tashi ta fice Fulani ta kishingide bisa kujera ta lumshe idanun tana son Ganin Ayman batasan halinda ya shiga ba da ya samu labarin sarautar da zaa bawa Aseem . Can bangaren Sultan kuwa Yana tare da Ayman cikin fada tare da manyan fadawa , ya gabatar da gaisuwa cikin girmamawa tattare da nitsuwa Aseem kuwa Yana gefe ya kafesa da idanu daga nan Ayman yace ” na barku lafiya ranka ya dade , ” murmushi ne ya bayyana a fuskar sultan Yana matukar kaunar Ayman yaron bashi da hayaniya ga tsananin biyayya baiga Wani canji tattare dashi ba ko kadan, ficewa yayi daga fadar aka zuba masa idanu kowa da abinda ke ransa shiko baisan suna Yi ba daga haka Fauzan ya mara masa baya suka shige mota Fauzan yace su wuce bangaren Fulani.
Falonta na can ciki take inda Babu Mai zuwa sai na kusa da ita an shirya kayan abinci me rai da lafiya da kayan marmari ga qamshin turare na tashi, bayan kowane dakika sai ta duba kofa , sallama yayi da muryarsa Mai sanyi da Kamala nan da nan fuskarta ya fadada da murmushi ” yaron Amminsa maraba da zuwa ” murmushi yayi ya karasa kusa da ita ya zauna tare da rike tafin hannunta ” barka da warhaka Umma nah dafatan na sameku lafiya” lafiya Alhamdulillah ya mutanen gidan ya exams ” alhamdulillah kowa lafiya exams Kuma mun gama lafiya ” Masha Allah, shiru ne ya biyo baya daga bisani tace ” Bismillah ga abinci ” Umma da dai a bari zuwa anjima yanzu am ok wanka nake son Yi ” ok toh ka karasa bangaren naka idan ka huta kazo ka sameni ” angama ranki shi dade” murmushi sukewa juna nan ya tashi ya wuce part nasa, Gimbiya Suhail kuwa tuni labari ya iso mata cewa Ayman ya shigo nan kuwa ta Kara saka Ido bangaren da Sabreen take tasan karamin aikin ta ne tace zataje ganinsa don har yanzu Babu jituwa tsakaninta da Aseem har yau har gobe tana kukan auren da Ake Shirin daura musu gashi bikin ya gabato saura sati 3 auren nasu, yanzu burinsu shine sultan ya amince a nada Aseem matsayin Yarima me jiran gado Amma har ynxu sultan baice komai dangane da Sarautar ba ga lokacin biki na karatowa .
Bayan sallar Isha sultan ya nemi ganawa da Fulani da Kuma Ayman a can bangarensa, suna zaune su uku kadai a falon nasa Ayman Kansa na kallon kasa Yana sauraron mahaifin nasa inda yake cewa ” dafatan zaka karbi duk abunda nazo Maka dashi da hannu biyu Kuma bazaka bani kunya bah, ka kasance d’a na Mai biyayya a kowane lokacin da Hakan ya taso kana danne naka farin cikin kabi namu ra’ayin , saboda hakane yau na baka dama ka kammala karatunka kafin kayi aure” da sauri ya d’aga Kansa suka hada Ido yayi saurin sunkuyarwa cikin girmamawa yace ” nagode Allah ya Kara girma ranka ya dade ” Wani murmushi ne ya subucewa Fulani Wanda batasan lokacin da ta furta ” nagode nagode sosai Allah ya Kara girma da lafiya ” murmushi me sauti sultan yayi sannan yace ” kayi hakuri bansan yadda kusancinka da Sabreen yake ba Amma koma menene na tabbata ba yin kanta bane saboda na fara fuskantar abubuwan dake faruwa cikin wannan masarautar Amma Babu komai ku cigaba da adua, aurene dai na amincewa Aseem ya aureta Amma kana nan har yanzu a matsayin Yarima…da sauri Ayman ya sake d’aga Kansa a karo na biyu Yana kallonsa cike da mamaki , ya cigaba ” ranar dauren auren a ranar duniya zata shaida matsayinka na yeriman masarautar Sennar insha Allah” ba Ayman kadai har Fulani Saida ta girgiza da Jin furucin nasa . Cikin sanyin murya Fulani tace ” Amma ranka ya dade…. ” Hannu ya d’aga da alama bayason zancen cikin kakkausar murya yace ” bana bukatar shawara da kowa wannan ra’ayi nane , uzurin da na masa akan batun aure dai nayi ne saboda Ganin yanzu ya Maida hankali Yana karatun Amma idan na samu labarin sabanin haka Babu abunda zai hanani nema masa aure ko y’ar waye na aura masa na gama magana zaki iya tafiya Kai yarima ka jirani zamu tattauna ” sunkuyar da Kai Fulani tayi cikin girmamawa ta tashi tsare da cewa ” na barka lafiya Allah ya huci zuciyar ka ” daga haka ta wuce can turakarsa. Ayman dai duk maganganun da mahaifin nasa keyi sai ehh ko aa yake amsawa Yana masa magana ne akan abubuwan da suka shafi masarautar tasu har dare ya fara Nisa kafin ya sallamesa ya tashi ya wuce part nasa.
Gimbiya Suhail ta kasa zaune ta kasa tsaye daga samun labarin fulani tare da Ayman suna can bangaren Sultan, ita tunda take a rayuwarta na gidan sultan Bai taba nemansu tare da y’ayanta ba Kuma abinda yafi d’aga mata hankali shine har yanzu baice komai dangane da Sarautar ba, waziri da ta tura ya buga ckinsa ma Babu abunda ya tsinta iya kaci sultan yace masa su Jira lokaci. da ace yau kwananta ne da zata bugi cikinsa taji meke faruwa kodai Ayman ya sake yin Wani laifin ne? rike kanta tayi tana safa da Marwa ta kasa zama , agogo ta kalla karfe 10 da Yan mintuna Amma a ce har ynxu suna can bangaren Sultan Kai dole gobe ta nemi labari toh kodai Sabreen zata tura ne yanzu? Wani murmushi tayi daga haka ta wuce bangaren da Sabreen ke zama daga cikin part nata, ta tura kofar tare da sallama tana kwance tana danna waya hada rai tayi da Jin muryar Gimbiya Suhail, kirkiro murmushi tayi ” bakiyi bacci ba Gimbiya sarautar mata, dama nace ko zakije gun masoyin naki yazo yau ” da sauri Sabreen ta d’aga Kai cike da mamaki ” ehh da gaske nake gara kije yanzu Babu Wanda ya sani Amma kinsan da safe idon mutane na kanki, Kuma Aseem idan ya samu labari bazaiji dadi ba, ki tashi kije Kuma kiji me makomarsa shin ya amince da zabinki ne ko Yaya ” idanun Sabreen ya cika da hawaye tace ” bayan Kun rabani dashi me Kuma ya rage , yau auren saura mako 3 yanzu…. ta fashe da kuka , Suhail ta karasa tana rarrashinta tace ” tashi kije idan har ya amince zai aureki ni nasan abun yi don harga Allah tausayi kike bani tashi, kije kar Wani ya ganki ” cike da kwarin guiwa Sabreen ta tashi ta fice. Ayman har 11 ya koma part nasa Fauzan na gaba Yana baya, cike da mamaki fauza yake kallonta Ayman kuwa kallo d’aya ya mata ya kauda Kai ya nufi hanyar bedroom nasa ba tare da b’ata lokaci ba Sabreen ta ruga ta rungumesa tare da fashewa da kuka ” tun dazu nake nan Ina jiranka ” cike da karfin Hali yace ” toh ni me zan Miki” kayi hakuri Ayman kasan har abada bazan daina sonka ba wallahi ba da son ra’ayi na bane aka …shhhh , I don’t need your explanation just tell me yanzu meya kawoki wajena ” ya juya suna fuskantar juna Fauzan ya sulale ya koma d’ayar falon. ” Nazo ne mu nemi mafita saboda ni bana son Aseem Kuma bazan taba sonsa ba, duk duniya Babu …”Sabreen wannan magana ya zama past tense yanzu kiyi hakuri ki dauka cewa ni ba alheri bane agareki shiyasa Allah ya rabani dake” karya ne Ayman kaine alherina Kuma kaine zabina , dama can ba Sona kake bah ” kuka take sosai shiyasa Ayman yayi shiru Bai Kara cewa komai ba ya juya yayi shigewarsa d’aki, kuka take sosai haka ta tashi ta koma bangaren Suhail tana Mai Kara Jin tsanar Aseem da uwarsa, wanka yayi ya kwanta gaba d’aya tausayin yarinyar ya kamasa yasani tabbas Wani abu suka kulla kamar yadda sultan ya fada Amma koma menene shidai yayi murna da Allah yasa ba yanzu zaiyi aure ba Kuma yasa a ransa cewa zai Kara jajircewa yayi karatu sosai saboda fita kunya, ko wacece sultan zai aura masa oho! Ya tabbata Koda nan gaba ne sai sun sake jajubo wata suka hadasu yasan Halin masarautar tasu, Amma Yana burin samun nasara akan abunda zuciyarsa ke muradi, lumshe idanu yayi Yana tuna fuskarta a haka yayi adua ya kwanta