Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 13

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E13_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

Juyawa yai da sauri ya nufi kitchen maimakon ɗakin shi, Yana shiga ya ci karo da zainab tana goge tiles da floor wiper sam bata lura dashi ba, har saida yai mata sallama tukunna ta ɗago suka haɗa ido
Fara’a ta sakar mashi”shuraim tun jiya na ke son yin magana da kai, fargaban Iyayenka ta hanani tunkarar ka” ƙarasa shiga kitchem ɗin yai

“Aunty zainab Ya zamuyi? Uncle musa ya matsa min akan saina bishi abuja, ƙarfe sha biyu zamu bar jos, ” dafe kai ta yi da hannu ɗaya

“Naji takaicin jin haka shureim, Duk plan ɗin da muka shirya ya tashi abanza kenan”

Girgiza mata kai yai”in sha Allah komai zai tafi dai dai aunty zainab, ko da ace bana nan that will not change anything”

Damuwa ce cunkushe akan fuskarta

“How ka ke tunanin komai zai tafi dai dai bayan bamu a wuri ɗaya”?

murmushin gefen fuska ya sakar mata har dimples ɗinsa suka lotsa.

“Kin manta da waya? Ina da ita kina da ita, zamu dinga yin communicating da junanmu, hakan ma zai fi ba tare da wani ya zarge mu ba” ƙayataccen murmushi zainab ta saki

“Allah ya yi maka albarka shureim ni sam na manta da waya, amma fa zan yi missing ɗinka sosai mutumina

Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”Ni kaina zanyi missing ɗin auntyna mai share min hawayena, amma in sha Allah zamu dinga yin waya akai akai, Inaso komai da ke faruwa a gidan nan kidinga sanya min ido, da zarar an samu update ki kirani awaya ki sanar dani, amma fa sai kinyi takatsantsan kinsan Iyayen nawa ba ƙananun mutane bane”

jinjina kai Zainab ta yi don ta gamsu da bayanin shi

“In sha Allah zan kiyaye shureim, kaima ka kula min da kanka, ” idanuwansu duk sun ciko da ƙwalla, don ba ƙaramin ƙaunar juna su ke yi ba, tana jinshi tamkar Ɗanta, shima Yana jinta tamkar mahaifiyarsa, sun jima a kitchen ɗin sunayin magana kafin daga bisani yai mata sallah.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr shureim Ya fara shirye shiryen tafiya abuja, bai canza komai na suturar jikinsa ba, Iya turarurrukansa kaɗai ya feshe jikinsa, sannan ya warware Ɗaurin larabawan dake akanshi, Ya sharce lallausar sumar kanshi Ya gyarata tsaf yabi da mayukansa ya shafe ta, Kafin barinsa ɗakin saida yai Nafila Ya roƙi Allah da ya tsare shi ya kare shi daga sharrin mutun sharrin zuciya da duk wani abun cutarwa, ya kuma roƙi Allah da ya sa silar komawarshi gidan uncle din shi abuja rayuwar shi ta canza ya dawo kamar yadda yake ada, addu’o’i sosai shureim yayiwa kanshi, Bayan ya kammala ya zaro memory ɗinshi da ya 6oye a cikin rigar pillow ya zaura shi awayarsa, Hankalin sa Ya ɗan kwanta zai samu natsuwar cigaba da kallon hotunan Abar ƙaunarsa awayarsa.

A gefen gadon shi ya zauna yana daddana wayar shi, Lokaci ya ke jira ya cika.

**DAULAR OBIE ESTATE**

A Hankali Jigunannun Motocinsu su ke kunno kai saman shantalelen titin obie estete, gaba da baya Sojoji ne ke tafiya akan ƙafafuwansu, Hannayensu ruƙe da bindigu, Motar farko mallakin Sir mubarak ce, motar dake a biye da ita zungureriya ƙirar Navigator limousine wadda cikinta tamkar bedroom ya ke saboda tsabar haɗuwarta, Dattijon arziƙi ne hakimce acikin motar tare da Jikokinsu tagawaye zain da zaid sai Dr Jazz shalelensa, Motar da ke abiye da tasu Danƙareriyar gaske mai numfashi mallakin Senate president Lateef Obinna ce, Yayin da motar ƙarshe Ta pravin Obinna ce, gayu mutanan Allah su kansu motocin da dattaku ake yin driving ɗinsu a tsanake cikin ƙwarewa, sautin karatun kur’ani mai girma ne ya karaɗe ko’ina, Ƙirar Ahmad suleiman mai matuƙar ratsa sassan jiki, daga motar dattijon arziƙi ƙirar ke fitowa, ƙa’ida ne a lokacin da suka fito zasu tafi masallaci sai yasa an kunna masa ƙirar Ahmed suleima haka zalika idan zasu dawo daga masallaci sai an kunna masu karatun wani sa’in Idan ƙirar takai mashi karo har bi yake yi yana lumshe ido, A yanzu haka dawowarsu kenan daga masallacin Juma’a.

Sannu A hankali su ke tunkarar Moto park ɗinsu, kusan atare motocin suka Yi parking at same time, Da azama sojoji su ke bubbuɗe masu mota, A hankali Obie Ya sauko ƙafarshi dake sanye cikin takalma kalar na sarakuna, Jikinsa Jallabiya ce daga sama Ya ɗaura alkebba haɗaɗɗar gaske sai ƙyalli ta ke Yi, ɗaya bayan ɗaya su ke fito daga Cikin motocin, gaba ɗayansu haɗaɗɗun Jallabiyoyi ne a jikin su daga Iyayen Har ƴa’ƴan.

“Mu shiga ciki ko”? Obie ne Yai masu maganar, Zaid da zayn Sai faman sunnar dakai ƙasa suke yi kamar marasa gaskiya, mamakin hakan yasa Mahaifinsu pravin tanka masu

“Lafiya”? Kafin su yi yunƙurin bashi amsa Sir Mubarak ya tari numfashin su

“Zaku ci ƙaniyarku ne, ƙananun Ƴan iska masu kwana da wando, har ni zaku dinga kakkaucema wa? Kun raina ni ko”? Fuskar shi a ɗaure ya ke yi masu magana, sir mubarak mutunne mai fusatacciyar zuciya abu kaɗan ke hasala shi sai da ta wani 6angaren yana da sauƙin kai.

Dr jazz Yana ruƙe da hannun Obie dariya ce ƙumshe abakinsa, ya ƙi bari ta kubce masa gudun kada Ya ji saukar mari daga Sir mubarak, Twins kuwa Duk sun sha jinin jikinsu sai faman noƙe kai suke yi haɗi da sosa ƙeyarsu.

A fusace Ya daka masu tsawa har saida suka ɗan razana atare su ka ɗago da fararen idanuwansu akan fuskarshi” Ina magana kuna kallona? Saboda tsabar fitsara”? Da sauri suka sunnar da kawunansu ƙasa, Alkunyace ta hana Pravin sanya baki, Gyaran murya senate Lateef Ya yi ma ɗan uwan nashi, Ya juya yana duban shi, cikin muryan Manyantaka Ya soma magana
“Aymasu afwa, Yarane su har yanzu, basu mallaki hankalin su ba, Sai ana haƙuri da su”

girgiza kai Sir mubarak yai”Pls ka daina wannan maganar, Yara sun balaga kana faɗin basu mallaki hankalinsu ba”? Juyawa yai tare da kallon su twins muryarshi a kausashe yace”Dagaske baku mallaki hankulan ku ba”? Har suna haɗa baki wurin furta”wlh mun mallaki hankalinmu, pls Ka yi haƙuri Uncle mun gane kuskurenmu zamu gyara in sha Allah, Dan Allah daddy ka bashi haƙuri wlh ba zamu ƙara ba” A marairaice suke kallon Mahaifin nasu pravin, Shi dai Obie bai tanka masu ba, murmushi ne ɗauke akan fuskarshi.

“Za ku Yi bayanine, muddin Owais ya dawo ƙasar nan zan sanya shi Ya ba ku horon isod, Ni dama can ban Goyi bayan aikin Company da ku ke zuwa yi ba, saboda ba ku iya komai ba” Zaro ido waje su ka yi jin abunda yace Hankalinsu ya tashi matuƙa, saboda suna mugun tsoron training ɗin Isod har ƙwara abasu horon aikin Soja, tuni sun raina kansu, Muryoyinsu tamkar zasu fashe da kuka su ke kallon Kakansu obinna don ya sa baki akan maganar
Pravin na murmushi yace”dama kun daina wahalar da kan ku, kunsan wanene Kawun na ku mubarak, Idan ya yanke hukunci babu wanda Ya isa ya dakatar dashi, Ni ma kuma na goyi bayan hukuncin da ya yanke”

Ransu ya 6aci jin abunda daddyn su Yace, juyawa su ka yi afusace suka nufi gidan.

Girgiza Kai Sir mubarak yai”kun ga irinta ko? Ana magana sun juya sun tafi saboda rashin ganin girman nagaba da su, duk izzar Owais ba ka ta6a yi mashi magana Ya juya maka ƙeya duk mun rashin daɗinta, natsuwa ya ke yi ya saurareta, Ai duk laifinka ne Pravin da kai da Saratun Kun sangartasu duk cikin Ƴa’ƴanmu babu sangartattu irin twins, Zanyi maganinsu ne” Maganar Sir mubarak ta ta6a zuciyar Pravin, yana ɗaya daga Cikin abunda ya tsana, ya ji an kushe ƴa’ƴan shi an yabi na wasu, Musamman owais, gani yake kamar don saboda Shi ba Jinin family ɗin bane Shiyasa suke nuna ma ƴa’ƴan shi wariya.

Tuni yanayin fuskarsa ya canza sam babu annuri, Ba tare da ya kalli fuskokinsu ba Ya furta”Ni zan Shiga ciki Sai kun ƙaraso” Yana faɗin hakan Ya zura hannayenshi cikin aljihun jallabiyar shi ya nufi gidan.

Gaba ɗaya sun fahimci canzawar da yai, Senate Lateef ya girgiza kai Yana bin bayan pravin da kallo

“Narasa gane kan mutumin can, ƙaranci Hankali nadamun shi, meye aciki don Anyi maganar ƴa’ƴan shi sangartattune? Ƙarya aka yi ne”? ran sir mubarak Yafi na kowa 6aci”Ka barni dashi, zan koya mashi hankaline, Maganar horon Isod da za’a ba ƴa’ƴan shi ba fashi ko da zuciyarshi zata buga ne ɗan rainin wayau”

gyaran murya Obie Yai masu hakan Ya janyo hankulansu ga kallon shi, ya ɗan jingina bayan shi jikin motarshi su kaɗai suka rage a harabar ajiye motocin, tun bayan isowar su gidan sojojin da ke take masu baya suka watse zuwa 6angaren da suke kula da shi na gidan.

“Sai kuna Yi mashi uziri, Pravin yana da raunin zuciya, ga shi dai a ido kamar Namiji sai dai a zuciya baida mararraba da mace, shima auta ne kamar saratun, mijin auta ai auta ne shima inda kara”

ƙumshe dariya Dr jazz yai jin sharrin da Obinna ke yiwa Pravin

Fuskar senate Lateef ɗauke da murmushi yace”A’a, baba ai ko saratun dakakkiyar zuciyace da ita, kaima ka sani gaba ɗayanmu Jinin ka muka Biyo, babu ragwantaka atare damu, shi dai ne macen Mijin tace, ita kanta saratun Juya shi take yi son ranta, Ina ji ran nan mun shigo gidan tana yi mashi masifa akan Ya zari kuɗi a account ɗinta ba tare da ya nemi iznin ta ba, sai lalla6ata ya ke yi kamar zai yi mata sujjada”

Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, daga obinna har shi Sir mubarak ɗin.

Dr Jazz ya saki baki yana tiƙar dariya kamar wani babba ya shige cikinsu, sai da suka kammala Yin dariyar, Sir mubarak Ya lura dashi, sam ya manta da dr Jazz a cikinsu, Ɗaure fuska Yai”kai! Me ka ke wa dariya? Akwai tsaranka ne acikin mu”? Da sauri Dr jazz Ya shanye dariyarshi, Hada la6ewa bayan Obinna.

Senate lateef yace”Ni zan wuce gida Baba, In sha Allah zan samu lokaci in shigo ciki mu ƙara gaisawa” obie yace”kada ka ta kura kanka, Ai kuna ƙoƙari ma, Ko awaya ne munyi magana, Idan ka shiga gidan ka gaishe min da hajiyar taka, Ina nan ina jiranta ta zo ta same ni agida mu gaisa”

Amsa mashi yai da toh, kafin Ya kalli ɗan uwan nashi”Ni zan wuce Mubarak agaishe min da Turai,” amsa mashi yai da toh”Nima a isar min da saƙon gaisuwa zuwa ga madam ɗin taka” A mutunce sukayiwa junansu sallama,

“Baba nima zan shiga ciki, amma kafin nan zan raba ka da wannan mata mazan” yai maganar yana ƙoƙarin damƙo hannun Dr jazz, Ƙanƙame obie yai, Sir mubarak yace” So ka ke ka karyamana Uban namu, Fito nan, Ni ba wani abu zanyi maka ba, Inaso ne mu shiga ciki, ka gaida mahaifiyar taka, nasan saboda ni ya sa ka daina leƙowa wurinta, tsakaninka da sai kira awaya sai kuma idan ta shigo gaida baba”

Jin abunda yace ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin jin shakkar Uncle mubarak ya ke yi ba, ruƙo hannun shi mubarak Yai

“Zaka rabani da sanyin idaniyata” acewar dattijon arziƙi.

Dr jazz yace”kada ka damu kakana, Ba zan jima ba, zan shigo gidan, pls Ka kwanta ka huta,” lumshe ido obie yai idonshi akansu har saida suka 6ace ma ganinshi, tukunna Ya ruƙe sandarshi Ya nufi cikin gidan.

Hajiya saratu ce zaune gefen gadonta cikin shiga ta bubu gown anyi mata kaftan style, kanta babu mayafi, Ta natsu tana kallon screen ɗin laptop ɗinta dake ajiye a gabanta saman round table, fuskarta ɗauke da murmushi, Video call ta ke Yi da ƴar autarta Faryat dake zaune gidan Yayanta Hateem na ƙasar canada

Matashiyar budurwace launin fatarta kalar na mahafiyarta ne, tana a zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru dake a kewaye da table, agaban tafkeken swimming pool, gefen laptop ɗinta Cup ɗin coffee ne ajiye, ta ɗauki wankan short gown ajikinta launin pink tabi shape ɗin jikinta.

“Yaushe zaki dawo gida ne? Na yi missing ɗin ki daughter”
Fuskar Faryat ta cika screen ɗin laptop ɗinta, faɗaɗa murmushin fuskar ta tayi da zazzaƙar muryarta ta furta

“I’ll come home as soon as we have a school break because I can’t wait to see you, my first love.”

“Canada ta kar6e ki daughter, kinyi haske kinyi kyau abunki, faɗamin dame dame ki ke yi a lokacin da ba ki yin komai”?

Farfari Faryat tayi mata da ido kafin ta soma jera mata

“Going to the movies, beach, club, playing games… ”

tunkan ta ƙarasa maganar Hajiya saratu ta dakatar da ita, Fuskarta a ɗaure tace”Faryat! Kina zuwa club? Da beach..? waro ido Faryat tayi batasan tayi su6ul da baka ba, da sauri ta toshe bakinta da tafin hannuwanta

“Mom, I was just joking. You know Uncle Hateem would never let me go to those places. Also Yazrin and Nazli keep an eye on me, even when there’s no school, they keep me company. I’m too busy to waste time.”
Hankalin saratu har ya ɗan kwanta

“Dama nasan ƙarya kike yi min, Na yadda da yayana Hateem nasan duk wani shige da fucen ki Yana a tafin hannun shi, duk da yana busy hakan bazai hana shi sanya jami’an da zasu dinga kula da motsinki ba, shiyasa tun farko na tura ki can don su gyaramin natsuwarki, kuma Alhamdulillah naga canji” Dariya Faryat ta saki jin abunda mommyn nata tace, Tsawon mintuna talatin sunayin wayar kafin daga bisani sukayi sallama da juna.

Layin Landline na kitchen Hajiya sarah ta kira Safa ce ta ɗaga kiran.

“Assalamu alaikum” Sarah ce tai sallama, Hajiya sarah bata tsaya amsa sallamarma ta ce”Jira ake sai nace akawo min abinci? Ko so ake in taƙo da ƙafafuwana in zo kitchen ɗin in ɗiba”? Muryar safa adabarbace ta furta”Ba haka bane Hajiya, duk laifin abla ne, itace take da aiki apart dinki, amma in sha Allah yanzu zata ƙaraso” yatsina fuska Hajiya saratu tayi fuskar ta babu annuri ko misƙala zarratin

“Okey, ina buƙatar dambun nama, A haɗo mun da fresh fruit, kada amanta da farfesu…” a ƙalla ta lissafa kusan abu takwas da za’a kawota don tayi breakfast….tunkafin Ta yi rejecting kiran muryar Pravin ta ratsa kunnata

Ranshi a6ace ya shigo yana zazzaga masifa”wannan wani irin wulakanci da cin fusk ne, Nifa nagaji da aibata ƴa’ƴana da ake Yi” yana huci ya ƙarasa maganar tare da goya hannayensa saman ƙirjinsa, idon saratu akanshi bayan ta katse kiran ta ɗaura wayar saman nightstand
A tsanake ta soma yin magana”wanene ya ta6a min romeo ɗin nawa”? ko sallama babu ka shigo kana ta zazzaga masifa? Tell me meya faru”? Aƙagare tayi maganar, tare da yunƙurawa ta miƙe tana fuskantar shi
Zuciyarshi A harzuƙe ya furta”Yayyanki mana, Akan me zasu dinga kushe ƴa’ƴana suna yabon nasu? sai yaushe ne zasu daina nuna min wariyar launin fata? Saboda kawai ni bani da alaƙa daku shine zasu dinga kushe min ƴa’ƴana”? Idan da kara ƴa’ƴana ai nasu ne’ Tsabar fusata yana magana facial muscles ɗinsa na kerma.
Matsawa tayi kusa dashi, fuskarta a ɗaure ta furta”what? Wanenen acikinsu yai maganar”? Da alama ranta ya 6aci hakan ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba

“Lateef ne da Mubarak, Agaban obie da sangartaccen Yaron nan dr jazz suke kushe Twins, har faɗi sukeyi wai sangartattune basu Iya komai ba irin na maza, zaifi kyau su ajiye aikin da sukeyi na company su koma ɗaura zani” Baki asake saratu ke kallon shi hada ruƙe qugu, muryarta akausashe tace”Pravin dagaske sune suka furta hakan? Kuma agaban Baba shine bai tsawatar masu ba”? Kwa6e fuska pravin yai”ae abunda zai baki haushi, baisanya baki amaganar ba, saima murmushi da yake saki, hada wannan munafukin Yaron, Shi da ba ɗan kowa ba agidan face ɗan mai aikin, wama ya sani ko shege ne, dani da uwarshi duk ɗaya muke ai, yadda bani da alaƙa da ku, itama haka har ƙwarani mun samu ƙaruwa ta ƴa’ƴa har uku”

Ran Hajiya saratu ya 6aci matuƙa, sai faman jinjina kai take yi tana fadin”bari naje wurin baban, yanzu har takai ga ƴa’ƴana aka kushewa agaban sakaran yaron nan jazz? suma waɗanda suka yi maganar zasu fuskanci 6acin raina wlh, zasu san dani suke magana” takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana neman mayafin da zata yafa, Pravin hada saurin rigata ƙarasawa gaban closet ɗin kayansu Ya buɗe ya ɗauko mata mayafi da kanshi ya ɗaura mata shi asaman kanta, A fujajen ta fuce daga cikin ɗakin, fitarta keda wuya pravin ya soma sakin shu’umin murmushi, ba tun yau ba ya saba haɗata faɗa da ƴan uwanta, mugun munafuki ne na bugawa a jarida, A zubin halitta idan ka kalle shi tamkar Namiji.

Bayan fitar Hajiya saratu da ƴan mintuna, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin zame jallabiyar jikin shi da niyar canza kaya, Sallamar Abla ta ratsa kunnuwanshi, Jimm ya ɗanyi kamar bazai amsa mata ba, daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”shigo daga Ciki” a hankali ta turo ƙofar, Hannunta biyu ruƙe da faffaɗan tray na Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu.

Ganin Pravin shi kaɗai a ɗakin Yasa ta ɗanji faɗuwar gaba, miryarta na rawa ta furta”umm..amm dama Kayan breakfast ne na kawoma Aunty saratu” lumshe idon shi Ya ɗanyi, tare da tunkarota Ya ruƙe tray din hannuta”bari na ƙarasa shigar maki da shi ciki,” kar6a yai tare da juyawa ya ɗaura tray ɗin saman table, kafin Ya juya ta yi saurin kai hannu zata tura ƙofar ɗakin saboda sanin halin shi, sai dai kafin ta kaiga ƙarasawa ga ƙofar yai saurin damƙota ya janyota zuwa jikinshi, Hankalin abla Ba ƙaramin tashi yai ba tsananin tsorone da fargaba duk ya cikata, ƙamshin turarensa ya addabi hancinsa, cikin shessheƙar murya take faɗin”pls ka sake ni dan Allah, na roƙe ka kada kaja min bala’e,” kwantar da kanshi yai saman kafaɗarta dogon hancin shi na gogar fatar wuyanta, yayin da hannayensa ke asaman ƙirjinta ahankali yake matsasu, kamar zatayi hauka ƙoƙarin kwace kanta take yi saida ya hanata yin haka saboda ƙarfine dashi kamar doki, fashewa tayi da matsanancin kuka tana yakushin hannunshi da akaifun hannunta kamar zatayi hauka.
“Nashiga uku, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Ya Allah ka kawo min ɗauki,” hankalin shi kwance yake cigaba da ƙoƙarin tura hannayenshi cikin rigarta

“Daddy!” muryar Zayn ce tasa shi saurin sakin Abla, ɗaure mata fuska yai

“Don’t you dare tell anyone what happened. Wipe ur tears off your face right now.” Jinjina mashi kai tayi da sauri ta sanya ƙasan rigarta ta share hawayenta, shu’umin murmushi pravin ya saki’Good zaki Iya tafiya sai mun haɗu wani lokacin” wani irin ɗaci taji acikin zuciyarta, Tana buɗe ƙofar ɗakin taci karo da twins, ko kallonsu batayi ba da sauri tabi ta gefensu ta wuce, awata ƴar corner ta la6e ita kaɗai ta zuƙunna tana cigaba da yin kuka haƙika pravin ba ƙaramin cin zarafinsu yake yi ba, shiyasa suke gudun zuwa su tarar da shi a ɗakin Hajiya saratu musamman idan bata nan, Romancing ɗinsu yake yi tamkar zai kashesu, halinshi ne bunsuranci, har ƙwara Ƴa’ƴan shi twins duk iskancinsu babu ruwansu da masu aikin gidan, amma shi uban nasu baya iya kauda idonshi akansu, Ya maidasu kayan biyan buƙatar shi, Kuma ba su isa su ce zasu hana shi ba, saboda barazanar da yake yi masu, hakan yasa suke mugun jin shakkar fallasa shi awurin masu gidan, kuma hada ƙarin basu son yayi masu silar barinsu aiki gidan, ba don kudin da ake biyansu da dollar ba, sai don sabon da sukayi da mutanan gidan sannan da yawansu Iyayensu masu ƙaramin hali ne, wasu ma babu Iyayen neman na kansu suke yi don su rufawa kansu asiri.

Ex-prisoners Meya hwaru Bayan jirginsu Ya ɗaga daga Cikin Dajin Evil forest shin sun sauka lafiya ko kuwa akasin hakan”?

*SAN ANTONIO-TEXAS*

*UNITED STATES OF AMERICA*

San antonio texas babban birni ne da ke a cikin jihar Texas ta america Yana ɗaya daga cikin jigunannun manyan biranan America Masu matuƙar ƙayatarwa Manya manyan gine gine na tarihi dana zamani, abubuwan more rayuwa masu ban sha’awa na musamman da kuma wadatar arziki, Hadaddiyar daula ce a U.s tsayawa suffanta kyawun birnin 6ata baki ne, balle ni da nake da abunyi.

*San Antonio International Airport*

Katafaren Airport ne na tashi da safkar jirage dake a cikin birnin san antonio, ƙayataccen gaske, sanarwa ce ta soma fitowa daga muryar na’urar computer (PA announcement) Kunnuwan Ma’aitakan Airport ɗin da fasinjojin dake zirga zirga a cikinsa gaba daya sun natsu suna sauraron sanarwar kwamfutar

“Attention, passengers. A UH-60 Black Hawk helicopter is scheduled to land at San Antonio International Airport in approximately 10 minutes. We appreciate your patience and understanding.” (“Amaida hankali, fasinjoji. Jirgin sama mai saukar ungulu na UH-60 Black Hawk yana shirin sauka a filin jirgin saman San Antonio a cikin kusan mintuna 10. Muna godiya da haƙuri da fahimtar ku.”)

Tunkafin ƙarasowar Helicopter ɗin nasu tuni Daga can headquater na sojoji an kira Emmergency Number ta Asibitin University Hospital Domin zuwa ɗaukar Marasa lafiyan da Jami’an su suka ɗauko, Da wata irin jiniya Jibga jibgan Ambulances din suke zuba uban gudu saman titin da dai sadaka da airpot din, jiniyarsu ta karaɗe ko’ina duk inda suka bi darewa akeyi abasu Hanya tunkafin su ƙaraso saboda sanin aikinsu na agaji, kowace ambulance tana ɗauke da tambarin sunan asibitin UHS which means (University Health System) daga gefen rubutun Zanan white cross ne backround dinsa launin Ja,Kusan su uku ne Motocin suka jera, a Airport helipad ambulances ɗin suka Yi parking, helipad yanki ne na musamman da aka tanada domin safka da tashin helicopter.

Mintuna goma na cika cuf cuf A gogon birnin San antonio ya buga ƙarfe 5 na safe, adai dai Wannan lokacin sautin Danƙareran Jirgin Da ke shawagi Saman iska Ya karaɗe kunnuwan kowa dake a yankin airport ɗin ga dukkan alamu Matafiya sun ƙaraso .

Sannu Ahankali Helicoptern Ya sauke tayoyin shi yayin da ya ke yin ƙasa ƙasa, Slowly yake tafiya har yakai ga inda zai dakata a filin helipad, Sojoji ne Kewaye da Jirgin waɗanɗa suka zo tarbarsu daga headquater, Motocinsu na ajere dana ɗaukar marasa lafiyan.
Buɗe Bayan Ambulances ɗin akayi at same time, Ma’aikan Jinyane waɗanda ake kira EMTs (emergency medical technicians) suka soma diddirowa daga bayan motar, mata da maza turawa cikin shigar fararen kaya masu ɗauke da tambarin Lafiya Hannayensu da ƙafafuwansu duk safunane haka zalika Sun toshe rabin fuskokinsu da face mask.

Saukowa Sojojin helicopter ɗin suka soma Yi daga cikin shi, Biyu daga cikinsu ruƙe da ɗan ta’addan da su ka damƙo a evil forest, Kaitsaye suka nufi motar ƴan uwansu sojoji da suka zo daga headquater, Abayan Kanta suka wurga shi tare da datse ƙofar,
Dawowa su ka yi wurin ƴan uwansu, nan fa aka fara rungume juna, ƴan uwan nasu nayi masu jinjina ta ban girma, akan Nasarar cafke ɗan ta’addan da su ka yi.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Emts suka Curo stretcher daga motarsu kusan guda Takwas, agaban Helicopter ɗin suka ƙarasa da shi ɗauke a hannunsu, Da taimakon sojoji suka dinga Jigilar ɗaukar su Angel suna miƙa su cikin motar, da aka zo kan Danish Sai dai sojojin suka kar6i stretcher ɗin suka shigar dashi ambulance ɗin, Bayan sun kammala kwasarsu, Motar sojoji gaba da baya a yayin da motocin Ambulances ɗin ke a tsakiya, da wata irin Jiniya suka haura saman titi da gudun gaske, sauran sojojin dake acikin motar da ɗan ta’addar yake tuni sun raba hanya sun nufi headquater ɗinsu da shi.

 

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button