Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 2

Sponsored Links

Page 2️⃣

Tafiya tafarayi cikin nutsuwa tana fito waje kuwa tasauke manyan idanunta akan Khalid Dake wasa a kofar gidansu karasawa tayi kusa dashi tace yaron kirki me yahadaka da auta ka kwace kudi ahannunta. Anty FANAN itace tafara tsokanata shine nafita zan daketa tagudu kudin hannunta yafadi akasa shine nadauka karasa maganar yayi yaname mikawa fanan kudin, sa hannu tayi takarba sanann tace mishi nasan auta da tsokana nan gaba inta Kara kaje gida kafadawa mama kaji ko, to shikenan anty FANAN.
Zuyawa tayi domin taje tayi cafenen da mama tasata bayan takammala siyan abinda yakawota zatabada kudi kawai taji ansa hannu an rufe mata ido dariya tayi tace malama dallah budemin ido angaya miki bazan gane kowaye bane, dariya tabayan nata tayi hhhhh bestie kenan ainadauka bazaki gane bane,zagayowa tayi gabanta tana tambayanta yasu mama, wlh kowa na lfy Amira yau kinje asibiti ne cewar FANAN tana kallon kawarta ta. Amira tace yauwa bestie meya hanaki zuwa yau in charge fah seda yatambayeni ke nace mishi yau kankine yake ciwo shisa bakizoba. Dogon numfashi fanan taja kafin tafara magana kekam yau agajiye nake nasha bacci sosai kawai nace to bari inbari gobe kawai inje, ahh lallai kam kinhuta bestie naga har wani kumatu kikayi dariya dukkansu biyu sukasa.Suna tafiya suna hiransu abin shaawa. FANAN da AMIRA kawayene su tun yarinta kasancewar sunyi makaranta tare Kuma anguwarsu Daya.
Karasowa gida sukayi suka shiga da sallama abakinsu gaida mama Amira tayi ,cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayarta ya mamanki dasu hajiya kowa lfy mama Ina yar auta rigima bangantaba, dariya mama tayi auta rigima kam tana daki wai tana kwalliya dariya Amira tayi tace tom yaukam kwalliyarta fah naga alama semun gudu . Kai autan maman kike fadawa haka cike da zolaya FANAN tayi maganar, murmushi mama tayi tace dukkanku biyu zakuyi bayani. FANAN karasawa tayi kusa da mama Tamika mata kayan miyan tana mata bayanin abinda yahada Khalid da auta girgiza Kai mama tayi tace allah yashiryamin ke auta amsawa sukayi da Ameen.

Daki suka shiga amira natayiwa FANAN hiran abinda yafaru yau a asibiti zama sukayi akan gado sunata hira can Amira tace nikam yau yabanga yaya Usman ba , wlh nima tunda natashi banganshiba maybe bedawo daga aiki ba sbd wani lokacin tare da baba suke dawowa cewar FANAN, cire hijabin jikinta tayi tarage kayan jikinta domin jinta takeyi kamar zata narke Dan zafi, bestie kinaban mamaki juyowa fanan tayi tana kallonta tace nameye kenan bestie, eh mana kamar wacce kaya yake mintsilinki bakya iyazama da manyan kaya ajikinki kina samun sarari Zaki kwabesu dariyarta medauka hankali fanan tayi tace wlh nikaina abin nadamuna inbada kana nan kayaba kwata kwata bana iyazama da kayan daze dameni uhmmm bestie kekam mijinki zega Abu takarasa maganarta cikeda shakiyanci. Amira allah yashiryeki wasa wasa yarinyar nan kinbaci tana magana tana dariya ahaka mama ta kwalawa mata kira zoki dauka muku abincinku fitowa tayi da zani adaure a kirjinta kare mata kallo mama tayi kafin tace nikam fanan lfynki kuwa ace mutum baya kaunar kaya katuwa Dake kina yawo haka cikin shagwaba tafara magana haba mama duka nawa nake dazakicemin katuwa. Takarasa magana tana buga kafa girgiza Kai kawai mama tayi iKon Allah kekam dakece autana dazamuga tabara wlh wuce kibani wuri daukan abincin tayi tana dariyar mama tashiga daki ta ajiye musu abincin kafin sukayi Bismillah suka fara ci. Suna tsaka dacin abinci auta tashigo musu da pure water dago Kai Amira tayi zatama auta magana, zabura tayi fara innalillahi wainna ilaijiraji unnn ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba aikuwa FANAN asukwane tadago Kai takalli inda Amira take kallo kamar tasa gudu dan yau kwalliyar da auta tacaba kamar wata aljana haka Takoma gashi tabude Baki se dariya take musu dukansu zuba mata ido sukayi kafin FANAN ta iya Bude Baki tace auta Dan Allah kiyi hakuri kidena kwalliyar nan Dan inkikayi fita kikeyi daga jinsin bil adama dahaka ake kwalliya Aida anshiga uku Amira Dake bayanta tafashe da dariya, matsowa kusa dasu tayi tace nayi kyau kuwa kokuma inkara janbaki ? Kode kwalli zankara iye anty aikuwa dariya suka Kara fashewa dashi har suna rike ciki ganin hakane yasa auta tabar dakin tana kuka, tsaqaitawa sukayi da dariya Amira nacewa anty ko janbaki zankara, hararanta FANAN tayi cikin wasa tace kinsan allah badan nasan auta nagidaba dazance aljanace. Kai autan mama kenan. Bayan sungama cin abincine sukaji sallaman baba tare da Yaya Usman a fallo saka hijabinsu sukayi atare suka fito Falon suka tsuguna suna gaida baba cikin zolaya yace yau kam bazan amsa gaisuwarku ba domin kutabo yar shalelena inshigo gida taban lbrn irin dariyar dakuka mata Dan tanuna muku kwalliyar data chaba yakarasa magana Yana Dan dariya Suma dariyar sukeyi kafin Yaya Usman yace baba nifa nayi niyyar guduwa Dan nayau abin ya girgizani cikin dariya baba yace daga gudun ai zaka dawoma bawanda yasani kafin yajuyo Yana amsa gaisuwar su Amira yace mata ya gidan naku cikin girmamawa ta amsa da lfy Lau alhmdllh baba yace ta madallah ya asibitin fatan kunayin abinda yakamata kudingayin abinda yakaiku karku biyewa shashanci amsawa sukayi da in sha Allah baba kafin yace Masha Allah allah yataimaka yabaku nasara akan abinda kukasa agaba dukansu amsawa sukayi da Ameen ya Allah. Mikewa sukayi Amira tamusu Sallama zata wuce gida seda safe sukayi kafin taje tasamu mama a kitchen tana hadawasu baba abinci tamata sallama cikin sakin fuska mama tace to Amira kigaida gida kinji ta masa da to mama suka wuce FANAN tarakata har kofar gida sbd Basu da wani nisa.
Bayan tadawo gida tatsaya dasu Yaya Usman a falo sunata hira cike daso da kauna gwanin burgewa.

 

To masu karatu semun hadu gobe, sannan plx kudingamin comment hakan shine zebani karfin gwuiwan cigaba dakawo muku, Amma inna tura Kuna gama karantawa shikenan bazakuce komai haba please Dan Allah mugyara

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story written by (MRS ISHAM )
Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen

 

Wanann littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

__________________________________________

 

Back to top button