Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 20

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*20*

Kusan kwana biyu wayar inna a kashe Kuma gaba d’aya kwana biyun walwalar fuskarta ya ragu tana Jin Babu dad’i cikin zuciyarta har tayi nadamar kiransa da tayi a waya, maman Nana ta lura da ita har ta tambayeta meke damunta tace Babu kawai batajin dad’in jikin nata ne, gaba d’aya sana’o’in nata mmn nana ke tafiyar dasu ckn kwana biyun a Rana ta uku ne ta yanke hukuncin kunna wayar ko don samun labarin hajjo tana kunnawa Kiran Ayman ya shigo wayar, murmushi ne ya subuce mata d’agawa tayi tare da sallama daga bangarensa ya amsa ” inna tah ya gida ya aiki” alhmdllh yaron inna ya mutan gida dafatan an samesu lfy ” kowa lfy ya labarin sanyin idaniya ” murmushi inna tayi tare da cewa ” Kai dai baka mantuwa yau Kuma tsokanan akeji koh” murmushi yayi daga bangarensa haka suka dan taba hira ya mata sallama ya kashe wayar, Wani numfashi inna ta sauke gaba d’aya ta rasa tunanin me zatayi ta zauna tayi jugum wayarta ya sake ringing tana kallon layin bugun zuciyarta na dada karuwa da wuri ta kashe wayar gaba d’aya ta jefar da ita cikin jaka ta sulale ta kwanta, Wani hawaye Mai dumi ya fara bin gefen kuncinta tana kefta Ido Batason hawayen ya fito Amma Bata da iKon hanasu fitowa haka ta kasance na tsahon lokaci daga bisani tasa hannu ta share hawayen tana Jin Wani abu na yawo cikin kwanyarta a haka bacci ya saceta.

Al’amarin hajjo kuwa ta Maida hankali sosai ta dage tana karatu ko don saboda ta burge Aman ta tabbata zaiji dadin Ganin ta iya rubutu da karatu ga Kuma turancin da ya fara zama a bakinta saboda ba kasafai suke Hausa ba sai idan suna hostel nan ma ba kowa keyi ba , tayi dace da bunk mate wacce take Ss1 sunanta khairiyya yarinyar tana da hankali ga nitsuwa tana koyawa Hajjo abubuwa da dama ta zame mata kamar uwa ita take nuna mata yadda zata gudanar da komai yadda zata tsabtace jikinta da sauran abubuwa, gaskiya makarantar nasu suna kokari ga Boko ga Kuma addini duk weekend ana musu karatun Qur’an ranar juma’a Kuma malamai ke musu tafsir , Hajjo ta fara wayewa Kuma ba laifi tana Kam mutuncin kanta kamar yadda inna ta fada mata tayi taka tsantsan da kawaye donhaka Bata da kawa daga sister khairiyya sai Blessing d’iyar Mrs Juliet wacce ajinsu d’aya, idan zataje sallah tare suke zuwa da bless sunan da hajjo ta saka mata kenan sai bless ta jirata a kofar Masallacin har ta gama ta fito su tafi sun shaku sosai da Bless gashi ko a aji tare suke zama tare suke cin abinci tare suke komai wajen bacci kadai ke rabasu saboda bless na room 1 Hajjo na room 2, jarabawarsu na gabatowa donhaka suka dukufa da karatu Babu kama hannun yaro duk da cewa idan sunyi Hutu ana summer camp ba kowa ke zuwan gida ba Amma wasu daga cikin daliban suna murna saboda zasuje gida Hutu.

*Birnin Sennar*

Saura mako d’aya bikin yarima Aseem da Sabreen yanzu haka Sabreen ta koma masarautarsu saboda shirye shiryen biki, masarautar Sennar ta cika makil da bak’i daga bangaren Sultan da Suhail harma da Yan uwan Fulani saboda Kara ga y’ayan sultan gaba d’aya sun hallara , Fulani sai murna take yau ga Yan uwanta zagaye da ita suna jiran isowar Ammi wacce akaje dakkowa daga Airport. Hanifah ce ta shigo bangaren Fulani tayiwa bakin nasu barka da zuwa , saukin Kai da sanin darajar Dan Adam irin nata yasa suke Shiri da Fulani tana jinta tamkar y’ar cikinta ta juya zata tafine ta Kalli Fulani tace ” Umma Ina Yarima yake tunda nzo bamu Hadu ba? Murmushi tayi tace ” Ina ruwan dan Ammi ai sun tafi airport daukan Amminsa ta iso dazu ” owk kice lallai yau Muna da manyan bak’i tun yaushe rabon Ammi da wannan masarautar, toh madalla Allah bar zumunci” daga haka ta juya ta fice daga bangaren. Motocin fada ne ajere reras guda 5 suka shigo babban kofar da zai sadaka da asalin cikin gidan masarautar suna parking, akayi Maza aka Bude kofofin nan fah aka fara zuba kirari ..takawarka lafiya yariman yau da gobe da jibi, dabino zaki kake a bakin talaka , fatar giwa ka wuce bakin gangan, Allah ya ja zamanin yarima Ayman dan sarki jikan sarki Allah ya…hannu ya d’aga musu Fauzan na biye dashi a baya a yayinda bayi suka karasa suka dauki luggages na Ammi , galala Aman yayi Yana kallo sai yau ya raina Kansa tabbas mulki daban yake da sarauta yau yaga izzar gidan sarauta yaune ya banbanta tsakanin bodyguards da bayi yaune ya gane dalilin dayasa Ayman yake jida Kansa .. “Man let’s go in” muryar Ayman ya katseshi nan ya fara tafiya Yana karewa masarautar kallo yaune karo na farko da ya fara zuwa , Ammi dai tuni tayi ciki tunda ita ba bakuwan gidan bane Aman sai kallon bayin yake duk inda suka wuce sai an sunne Kai cikin girmamawa ana d’aga gaisuwa , bangaren Ayman suka wuce Kai tsaye a nan ya Kara Ganin iKon Allah part din Ayman ya kusa girman duplex din gidan Babansa na Abuja. Bayi ke Kaiwa da komowa ga masu zuba fure ga masu shirya kayan abinci gasu nan dai sunfi 20 kowa na aikinsa , Wani tamfatsetsen falo suka shiga ga wasu royal chairs masu uban kyau da tsada ga qamshin turare masu sanyaya zuciya ga sanyin AC tuni Aman ya samu kujera ya zube tare da karewa falon kallo , ya Saba shiga manyan gidaje a Abuja Kuma yasha zuwa outside country Amma gaskiya wannan falon na musamman ne gashi Babu Wani tarkacen hayaniya Amma ya tsaru ainun, sauke numfashi yayi Yana kallon Ayman yace ” bro u r mad ehn , yanzu wannan rayuwar kake gudu ? Har kafison naija kana zaryar zuwa state uni mtsww baka da lafiya I think” murmushi Ayman yayi yace ” am not after all these..nafison farin ciki da kwanciyar hnkli” hararinsa Aman yayi dai dai nan wasu Yan mata kyawawa sunkai 6 suka shigo a jere kowacce da tray a hannu, suka risina cikin girmamawa tare da ajiye abinda ke hannunsa take suka juya suka fice , ga dogarawa masu gadin kofa nan Fauzan ya d’aga musu hannu suka fita ya rage su uku a falon. Aman tabe Baki yayi yace ” chabb…na samu irin wannan rayuwa Kuma ai sai Allah, wllhi ko wanka sai dai a mini ” “ai zasu Maka idan kana bukata ranka ya dade” Fauzan ya fada in a serious note, bude Baki Aman yayi yace ” are you kidding me, you mean yanzu dude har wanka kana da masu Maka?” hararinsa Ayman yayi yace ” u r not serious am I stupid” wait wait…yanzu da gaske idan Ina bukata akwai Wanda zasu min wanka ?” Me zai Hana idan kana bukata ” gyada Kai yayi yace ” lallai mulki yayi a rayuwa no wonder Ake fada akan sarauta” uhmm …idan ka mutu Kuma Allah na nan Yana jiranka ” mtsw…zaka fara koh, toh dama waye bazai mutu bah, aikowa mutuwa zeyi a duniya naga Kai dai Allah ya bamu duniya da lahiran duka ” tabe Baki Aman yayi Yana mikewa kafin yace ” bari na watsa ruwa na dan kwanta I need some rest sai dare muje gun Umma ku gaisa ” ji mana malam, karka maidani dan iska mana ka tafi ka barni da ubanwa? ” Lumshe idanu yayi kafin yace ” Fauzan is here duk abunda kake bukata ” tsaki yaja tare da cewa” why am I even saying dis kamar mun Saba zama tare ” murmushi Ayman yayi daga haka ya wuce wata kofa da zai sadashi da bedroom nasa, Aman ya Kalli Fauzan yace ” Kai dai ka shiga uku da aka hadaka da wannan uban Yan girman kan” murmushi Fauzan yayi yace ” he is simple kawai baka Gane halinsa bane, kaga ni tun Muna yara muke tare nafi kowa sanin halayensa Yana da kyakkyawar zuciya kawai bashi da hayaniya ne Kuma bashi da saurin sabo but am sure idan Kun Saba wataran Kai da bakinka zaka Yaba halayensa” cike da mamaki Aman yace ” Kai kuwa tunda ka taso kake bauta masa har ynxu? Shin baka da Wani abu a rayuwa bayan wannan?” Murmushi yayi yace ” mahaifina y’antaccen bawa ne ga Sultan haka mahaifiyata ta kasance Mai hidima ga Gimbiya Fulani, tun Ina karamin take shigowa dani tana aikinta a bangaren Fulani har zuwa lokacin da na fara girma, Ina da shekaru 8 Allah ya dauki ranta daga nan Fulani ta daukeni ta damkawa jakadiya ta cigaba da kula dani a nan na fara zama da yarima a matsayin Mai debe masa kewa, tun a wannan lokacin har izuwa yanzu ban taba rabuwa da yarima Ayman ba Kuma har abada bana fatan rabuwa dashi, Fulani ta zame min uwa tana bani duk wata kulawa tamkar dan da ta Haifa tare mukayi primary da secondary da yarima daga nan nace karatun ya isheni Amma duk inda yake Ina tare dashi a matsayin Mai kula dashi , bani da abunda zan biya Fulani dashi sai kula da yarima har karshen rayuwata ” nan hawaye ya cika idanunsa . Jikin Aman yayi sanyi yace ” Kuma baka da burin aurene ko Wani abu haka na rayuwa?” Murmushi yayi yace ” sai yadda Fulani tayi duk hukuncin da ta yanke a rayuwata a shirye nake da na amince donhaka wannan ba hurumina bane ” gyada Kai Aman yayi cikin gamsuwa , daga nan yabi kayan da aka jera masa da kallo nan yasa hannu ya dauki apple guda d’aya ya fara gutsirawa yadauki wayarsa Yana dannawa. ” Idan kana bukatar Hutu muje na nuna maka d’akinka ranka ya dade ” “no am ok! Maybe later ” daga haka ya cigaba da danna wayarsa.
Gimbiya Suhail ce tare da jakadiya can kuryar d’aki suna tattaunawa ” jakadiya jikina ya fara mutuwa da lamarin auren nan, Kinga fa har yanzu sultan yaki ce mana komai game da nadin sarautar naga Yan uwan Fulani suna ta tururuwa a gidan nan kodai sunji Wani abu ne, Anya bikin nan ne ya kawosu haka jakadiya Anya..” ta karasa maganar cikin damuwa, “kwantar da hankalinki uwardaki nah kinsan haka Fulani suke da gayyar biki kedai ki zuba Ido ki Jira ranar daurin aure nice nan zan fara kawo Miki kyakkyawan labarin idan Allah ya yarda, ki saki ranki ga bak’i cike kar su gane halinda muke cki ” sauke numfashi tayi ” toh shikenan yanzu naji dan dama Amma gaskiya shirun yayi yawa, na kira waziri karami yace ba labari haka nan sarkin fada yace ko maganar baayi nace toh Allah yasa an d’aga nadin ne sai nan gaba Kinga kafin nan idan Sabreen ta haihu shikenan dole a nada Aseem matsayin Yarima tunda wancan Yana karatu gashi beyi aure bah ” Hakan ma yayi Allah yasa dai Muji alheri” “Ameen, naji ance wannan munafukar y’ar uwar tata Amina tazo koh, na tsani matar ita takemin kasalandan cikin lamurana duk abunda na shirya sai ta warware shi shegiya ” karki damu da kowa kedai kije kiji da jama’a ranki shi dade na barki lafiya bara naje na duba abincin bak’in namu da na abokanan yarima me jiran gado ” murmushi Suhail tayi tana matukar kaunar jakadiya don ta yarda da ita Sosai ta iya Bada shawara ga Kuma kula da duk shiga da fitan lamuran bangaren nata.

Back to top button