Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 25-26

Sponsored Links

2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣

 

Wani ƙululun baƙinciki ne ya zo ya tokarewa yarinyar maƙoshi, jin abin da Inna ta faɗa, gabaɗaya sauran matan suka fara bin ƙirjinta da kallo suna so su gano asalin gaskiyar abin da Innar ta faɗa, aikuwa kowa ya shiga danne dariyar da ke cin sa ganin gaskiya Inna ta faɗa in ma akwai gyara a maganar to kuwa kaɗan ne. Ganin kowa ya zubawa ƙirjinta ido sai ita ma ta shiga kallon ƙirjin nata har da sanya hannu ta ɗan ɗame jikin rigar wai dan ta ga girmansa.

“Duba da kyau dai ɗiyar nan ƙarya zan miki, ai yanzu kya yarda da kika ɗame rigar ai kin ga girmansa bai fi ƙwayar ƙarago ɗan nera biyar ba idan ma ya kai kenan”
Magana yarinyar ke yi ƙasa-ƙasa da baka jin me take faɗa sai yafda bakinta kawai ke motsawa kake gani da alama rashin kunya take yiwa Inna.

“Wa ya ga banza ta kori wofi ai maganar ciki ba magana bace a fito fili a faɗa mana” Cewar Inna ta juya ta nufi ɗaki tana ɗan dudduƙawa dan har zuwa sannan hancinta bai daina zuba ba sosai mira ta mata kamun kazar kuku. Sai kuma wacce ta yi tusa aka cijeta ita ma ta fara magana.

“Aikin banza da wofi duk kin bi kin cije ni, haba wannan wane irin abu ne” Harara kawai ɗayar ta bita da ita ba tare da ta yi magana ba dan idan ta buɗe baki komai ma za ta iya faɗa, saboda yadda ta yi ta ƙwararta da warin tusa sannan ganin Imran ma a wajen ya sa ta ɗaga mata ƙafa.

Inna tana zuwa falo sai ganin Sadiya ta yi kamar an dasa ta a wajen tana tsaye a tsakiyar falon hannunta riƙe da Hassan a siffar miciji har lokacin bai dawo siffar mutum ba. Wani yawu Inna ta haɗiye ba tare da ta cewa Sadiya uffan ba ta nufi inda suka ajiye lalle, kowanne a leda aka kwaɓashi sai mai ƙunshi take ɗauka tana zubawa a cikin kwarkwaron da take ƙunshin. Lalle ne ɗan kwali sajen ne ja da kuma baƙi na fulawa. Da ɗan yawansa a cikin ledar, saboda gabaɗaya ta kwaɓe yadda zai ishe su. Inna baƙin ta ɗauka na fulawar ta ɗauki baƙar leda ta sanya a hannunta ta ƙulle sannan ta juye wannna lallen a kan baƙar leda Sadiya da ke cikin wani haki ko kallon Inna bata yi ba tun shigowar Innar da ta kalleta bata ce komai ba. Dan kawai gabaɗayansu mamaki suke bata na gudun da suke yi, duk da ita ma ta san da a ce Hassan ba ɗanta bane dole ta gudu dan tsoro amma yanzu babu yadda za ta yi ko da tana jin tsoron saboda ya zame mata dole.

Inna sai da ta juye baƙin lallan nan duka sannan ta juyo a dudduƙe ta fito daga ɗakin har lokacin dai kowa na tsaye carko-carko, me ƙunshi ta ɗan juya kenan kafin ta juyo sai ji ta yi an damƙeta an shiga lafta mata wani abu a fuska da ta kasa tantance menene.
Inna kuwa tun da ta damƙi wuyan me ƙunshi ta baya, bata saki ba ta dage sai lafta mata lallen take a fuska kamar wacce take fenti a bango, sai da ta lafce mata shi gabaɗaya a fuska har wuyanta sannan ta sake ta tana ta ihu dan ma dai ta rufe ido da har idanun zai shiga. Imran tun da ya kallesu sau ɗaya ya ɗauke kai dan shi baya son hayaniya kuma ya san da alama yarinyar wani abu ta yiwa Inna dan ba ya raba ɗayan biyu ita ce ta rufeta a freezer.

“Wayyo Allah na Allah sa dai ba kashi bane kika lafce min shi a fuska” Cewar me ƙunshin tana ƙololon amai lokacin da Inna ta sake ta.

“Shigiya kudurarriya ni da kashin ma na samu ai da wallahi har haɗiya sai na sa kin yi, har ni zaki garƙame a cikin firinji, sanyin duniyar nan na cikinsa ya ƙare a kaina, hancina banda yoyo babu abin da yake in ba ruwan zafi na yi ba ma masassara ce za ta kama ni, saboda rashin tsoron Allah duk sanyin nan da ake baki tausaya min ba kika rufeni kika kunna firinjin” Cewar Inna tana face hanci tare da sakin wani kuka na tausayin kanta irin yadda ta sha artabu a cikin freezer.
Gabaɗaya dariya suka kwashe dashi Inna da ke shirin magana ta dakata ganin Sadiya ta fito riƙe da micijin a hannunta ba Inna ba su duka ma masu dariyar dakatawa suka yi, Imran da ya fara wani ɗan kakkauda kai yana sosa ƙeya dan ba ya son Sadiya ta zo ta bashi micijin ta kunyata shi a gaban matan nan. Dan haka sai ya shiga muzurai yana ɗan babbasarwa shi a dole ba komai bane. Inna kuwa tun da Sadiya ta fito ta fara tunanin inda za ta garzaya dan ta tsorata da yaron yanzu dan bai taɓa kaiwa kamar haka bai dawo mutum ba amma yau ya yi dogon zango.
Sadiya da take shirin buɗe baki ta yi magana Inna ta katse ta da cewa.

“Ke kuwa Halima baka tausayin yaron nan kika fito dashi da sanyin nan, ko dan kinnga ba a siffar mutum yake ba kike gani kamar baya jin sanyi” Ta faɗa tana wani karya kai gefe dan gabaɗaya ta matsu Sadiyar ta kuya ta koma inda ta fito dan kana kallon micijin duk jarumtarka sai ka ji tsoro saboda yanayin girmansa ma.

“Inna wallahi hannu na ya gaji da riƙonsa kinsan akwai nauyi fa kuma ina son na shiga bayi ne shi ne zan baiwa Abbansa ya riƙe min shi” Cewar Sadiya tana kallon Inna. Imran kuwa jin fitowar Sadiya saboda shi ta fito ta baiwa Hassan sai ya ji wani dammm ƙirjinsa ya buga dan shi yanzu har ga Allah ya tsorata da yanayin yaron.Wani yawu ya haɗiye da bai san lokacin da ya taru ba ya kalli Sadiyar yana shirin magana sai Hajiya da Mama da suka haɗu a ƙofar gidan yanzu suka shigo da sallama.

Ƴan matan nan duk sun sha jinin jikinsu, me ɗinki kuwa da fitowar Sadiya ta mantar da ita abin da Inna ta lafta mata a fuska da wuyanta tsabar tsoro, gabaɗaya ya mata baƙiƙƙirin a fuska kamar ta shafa baƙin gawayi dama ga ta sha uban bilicin sai ta koma kamar wata jimina.

“Yauwa ga kakanninsa nan” Imra n ya yi saurin faɗa ganin su Mama sun shigo. Idanun Mama da na Hajiya ne suka sauka a hannun Sadiya da ke riƙe da miciji, gabaɗaya wani tsoro ne ya rufe su dan su bai taɓa sawaya a gabansu ba, sai dai a basu labari ita kuma Hajiya dama ita ce me cewa ko ya zama miciji babu abin da zai yiwa mutane, sai dai ganinsa yau muraran ya kaɗa mata hantar cikinta, Mama kuwa cikin ficewar hayyacin ganin ƙaton miciji riƙe a hannun ɗiyarta ta buɗe baki ta ce.

“Sadiya me zan gani haka? Hassan ɗin ne ya zama wannan ƙatoton micijin kamar wata mesa? Kuma kika kama shi kika riƙe a hannu, me ye amfanin ubansa da yake tsaye?” Mama da soyayyar ƴa da uwa tasa ta manta cewar Hajiya na wurin ta faɗa tana kallon micijin.

“Haba Mamar Sadiya ai ana barin halak ma dan kunya, kuma uwa ai ita ce tushen ɗa, kuma da ita da Imran ai duk ɗaya ne ma in ta riƙe babu komai” Hajiya ma da son ɗanta ya rufe mata ido ta faɗa ita ma idanunta a kan Hassan ɗin.

“Wai ni kam me yasa kuke haka, ta yaya ma za a ce uwa ce rushen ɗa haba Amina wannan ma ai ba maganar ɗauka bace, uba ai shi ne tushen ɗa, lokacin da ya ɗirkawa ƴar mutane ciki take riƙitu da tsohon ciki baki ce haka ba sai yanzu da take riƙe da miciji aka ce a bashi ya riƙe?” Cewar Inna tana hararar Hajiya Amina da sai yanzu ta ga wautar ta amma ai da gaskiyarta ya za a yi a riƙe miciji da bbau tabbas a kansa.
Hajiya da ke shirin maida martani ta rufe bakinta ruf, ganin wani uban ƙwacewa da micijin ya yi daga hannun Sadiya ya wani zabura ya yi sama kamar wata iska ya bar hannun Sadiya. A tsakiyar mutanen nan ya tsaya tare da fasa kai yana wani wawwaiga idanu. Kowa ya matuƙar razana da yanayin yadda micijin ya yi, Mama kallon ƙofar gidan ta yi amma cikin rashin da’a sai ta ga a kulle dan dama Imran na shigowa sai ya manta bai rufe ba su kuma suna shigowa sai suka maida ƙofar suke rufe jamlock ɗin ya shiga.
Dan haka babu hanyar fita dan yadda jikin kowa ke karkarwa babu inda za su iya buɗewa saboda a tsorace suke gabaɗaya sun gama tsurewa.

Inna kuwa tana ganin hakan sai bakinta ya fara motsi leɓanta na sama ya fara gwaruwa da na ƙasa alamar dai tana rattabo du’ai.

Kowa karkarwa yake kamar sun haɗiyi mazari.

“Wai shin Imirana duk wurin nan fa kai ne namiji, ka yi wani abu mana ” Cewar Inna cikin sarƙewar murya.

” Haba Inna in shi ne namiji ma sai ya kai kansa ga halaka, kar ki manta ni fa shi kaɗai gareni, ga uwar yaro kya ke cewa wai shi namiji ne ai Sadiya ma mace ce me kamar maza kwari ne kawai babu” Hajiya ta faɗa har rana yin in’inna tsabar a ruɗe take.
“Oh ni Azumi na ga abin da ya turewa buzu naɗi wallahi yanzu Amina ƙin gaskiya ƙiri-ƙiri to wallahi ki ji tsoron Allah dan faga ƙin gaskiya sai ɓa…

Wani uban zillo da micijin ya sake yi tare da maida kansa ya kwantar a ƙasan sai kuma ya ɗaga jelar sama, shi ya dakatar da Inna daga maganar da take son ƙarasawa. Kowa ɗif ya yi babu me cewa uffan amma da ka gansu ka san a matuƙar tsorace suke. Imran kuwa sunkuyawa ya yi ya ajiye wayarsa a ƙasa ya ɗago tsaye ya sanya hannunsa na dama a haɓarsa ya shiga shafa haɓar da shi kansa bai san dalili ba, shafawa yake ba ƙaƙƙautawa daga gefe zuwa gefe, bakinsa kuwa sai mismismis yake shi kaɗai ya san me yake faɗa. Inna kuwa hannu ta sanya ta toshe hancinta da ke zubar majina, idanunta a kan me ƙunshi nan da take karkarwa fitsari na biyowa ƙafafunta sai buɗe baki take tana kuka amma marar sauti zuwa lokacin lallan ya gama haɗa mata fuska da baƙi ta yi baƙiƙƙirin da ita.

“Shegiyar yarinya ji yadda ta koma kamar bunsurun ɗan akuya, gabaɗaya ta yi baƙi kamar ta shafa baƙin bula, sai ta zama kamar irin baƙin bunsurun nan gemu ne kawai babu” Cewar Inna a zuciyarta tana dariyar ƙeta duk da halin da ake ciki amma fa ka kalli me ƙunshin nan sai ka kai zuciya nesa ne dariya ba za ta ƙwace maka ba. Gurbin idonta kawai ake iya hangowa ita kuwa sai ɓare baki take tana da na sanin zuwa gidan ƙunshin ma gabaɗaya.

Sadiya kwa gaban micijin ta je ta durƙusa tana kallonsa hawaye na zubowa daga idanunta. Mama kuwa so take ta ce Sadiya ta tashi faga gaban micijin sai dai tsoro da fargaba ya hanata magana tana ganin kar ta yi magana micijin ya iyo kanta ya sare ta a banza ta bar duniyar a wufi, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru tana ta lazimi a zuciyarta lazimin da ita kanta da za a sanya mata wuƙa a wuya a ce ta faɗa ko kalma ɗaya ba za ta iya faɗa ba, dan ta kasa banbance ma addu’a take ko karatun qur’ani ko kuwa ƙasida, wani lokacin ma sai ta ji kamar waƙa-waƙa take amma Allah ne kaɗai ya san karatun kurma.

Da baya da baya micijin ya shiga tafiya aikuwa aka dare aka bashi hanya, kowa cikinsa na ɗurar ruwa ga miciji da shegen gudun tsiya idan ka ce za ka gudu idan ya biyoka ba lallai ka tsere masa ba saboda gudun da yake dashi. Dan haka sai kowa ya shiga taitayinsa aka shiga jiran ganin abin da zai yi. Sauran matan kuwa sai kuka suke marar sauti wata ta kama tsantsa wata ta ɗora hannu a ka har da wacce ta ɗaga hannaye sama irin yadda ake addu’a ta baza tafukan hannaye sai wani karkata kai take tana kai kukanta wurin Allah.
Ashrof kuwa ta sanya hannu a fuskarta ta rufe fuskar da tafukan hannayenta tana kallon micijin ta tsakanin yatsada yatsa dan kar ta rufe idanun duka micijin ya iyo wurinta dan ita ganinsa kaɗai ma razana ta yake. Hajiya yadda micijin ya fara ja baya haka ita ma ta shiga ja baya, a hankali har sai da ta ga babu wurin gudu sannan tana tsoron ta zuba da gudu micijin ya tsallakr kowa ya biyo ta haka ta jure tana cewa a zuciyarta.

“Allah ka dubemu ka kawo mana mafita”

“Allah ka kawo me cetonmu, a wannan gida da muke ciki a rufe ga kuma ajalinmu a tare da mu” Cewar Inna a ɗan hankali kamar tana tsoron faɗa.
A hankali micijin ya shiga kanannaɗewa har sai da ya kanannaɗe duka jikinsa, sai kuma cikin hanzari da zafin nama ya zura da gudu, ya shiga zagaye gefen da mutanen ke tsaye kowa kallonsa kawai yake sai da ya zagaya kusan sau uku, sannan cikin tafiya ɗaya biyu ya yi sai gashi a gaban Imran yana zuwa ya fasa kai ya dakata a wurin ba tare da ya matsa ba.

“Ka min daidai Hassan, gwara da ka je gun ubanka da kan ka yau za mu ga ƙarshn ƙarya” Cewar Inna a zuciyarta tana ƙwafa.

“Wayyo Allah ɗana, ɗana guda ɗaya da nake da shi duk duniya yau ya haifi abin da zai zama ajalinmu” Cewar Hajiya a zuciyarta tana tana share hawaye.

“Gwara da ka je wurinsa tun da ba ita kaɗai ta haifeka ba da za take jigilarka ita kaɗai” Cewar Mama a zuciyarta a fili kuma sai ta dakata da motsin bakinta ta danne gefen keɓenta da haƙori, irin ka min daidai ɗin nan.
Imran kuwa wasu hawaye ne masu kamar an musu dole su fito suka shiga surnano masa a fuska, sai na ido ɗaya ya gama gangarowa sannan na ɗaya idon ma ya gangaro.

“Alwudu’u, alwala, kaifa tatawadda’u, yaya za ka yi alwala” Cewar Imran yana sakin kuka dan yau ya sadaƙar sai dai gawarsa tun da har kicijin ya je gabansa da kansa.

“Ɗan karan uwa ɗan gwafar uba da baka karanci yadda ake alwalar ba sai yau, to duk sallaolinka na baya aradu ka yi su a wofi tun da sanda ka yi baka iya ba alwala, sai yau da ka ji uwar bari, ka fara tuna karatun alwala ai bari ba shegiya bace da ubanta” Cewar Inna a zuciyarta.

Sauke kai micijin ya yi daga fasa kan da ya yi, ya wani kaiwa ƙasa sara sau biyu da mugun ƙarfi.

Imran idanu ya ƙwalalo tare da ɗauke numfashinsa ganin micijin ya sari ƙasa kusa da ƙafarsa, duk tunaninsa ma shi ya sara sai da ya zare idanu da kyau sannan ya gane ƙasa ya sara, sai dai yana rayawa a ransa shi ma ana daf da saransa. Ƙafafu ya ƙame a wuri ɗaya yadda sojoji ke ƙamewa, ya ɗaga hannu biyun duka ya ka gefen kansa yadda sojoji ko ƴan sanda ke yi idan za su sarawa oganninsu, amma shi da hannu biyu ya yi, a wannan ƙamen ya shiga jero taken Nigeri’a ba ƙaƙƙautawa, shi kansa ya tsinci kansa ne yana faɗa ba tare da niyyar hakan ba saboda gabaɗaya ya rasa me zai ce ma.

“Kai jama’a yau ake yinta, lallai gulma yau ya ƙare tun da uwar gulma ta yi cikin shege, wato saboda ɗaurewa Nigeri’a da harshen nasara tsantsa kaima yadsa abokinka sojojo ya yiwa Nigeri’a baitika kaima hakan take” Cewar Inna a ranta tana tuno yadda aka kwashe da soja da Hassan ranar nan.

Kamar wanda aka faɗawa micijin sau saurin barin wurin Imran ya yi ya tafi wurin Hajiya yana zuwa ya tsaya a gabanta. Ai da sauri ta gyara tsayuwarta tana ɗaga hannaye yadda Imran ya yi ra sanya su a gefen kanta yadda sojoji ke yi ta buɗe baki kuka na neman ƙwace mata sai dai tana tsoron sakin kukan dan kar micijin ya sareta ta ɗan ɗaga murya amma kuma ƙasa-ƙasa ta ce.

“Imran karanto min taken Nigeri’ar sai in ke faɗa idan ka faɗa ka san ni ba iyawa na yi ba, amma idan kana karantowa sai in ke bita, tun da gashi a gabana layi ya zo kaina” Hajiya ta faɗa idanunta a kan Imran da har lokacin bai saki hannayensa ba haka zalika ƙafafunsa na nan yadsa suke a haɗe, bakinsa kuwa sai jerawa Nigeri’a kirari yake, kamar wanda aka ce Nigeri’ar za ta watse idan ya dakata da yi.Sara ya fara a gabanta ko ƙaƙƙautawa babu, kuma babu alamar zai dakata, dan haka Hajiya sai ta fara kuka, kuka kawai take wiwi dan ta rasa ma yadda za ta yi. Cikin ikon Allah sai ya bar gabanta amma bata bar yin kukan ba, gaban Inna ya nufa yana zuwa ya tsaya. Kallon kallo suka fara da Inna wacce majina ta taru cikin tafukan hannayenta da ta rufe bakin da su, ganin micijin a gabanta sai ta ce a zuciyarta.

“Yau na tabbatar kai ba mutum bane, ɗan ruwa ne, in ba ɗan ruwa ba a ce jariri da kai amma har ka aan ka je gaban wannan ka je gaban wancan”

Ganin yana shirin kaiwa ƙasa sara sai Inna ta yi karaf ta fara masa waƙa.

“Haba Hasanunu, ɗan aljanna, haba hasanunu ƙaton kirki, haba Hasanuna ɗan Imirana, haba Hasanunu me sauya kala” Ta faɗa tana wani rausaya kai ita a dole ya bar gabanta, ai sai gani ta yi ya kai wani sara me ƙarfi.

“Lanjeriya ƙasar ƴan baiwa, lanjeriya ƙasar talakawa, lanjeriya ƙasar Bahari ɗan daura” Ta faɗa tana kuka hawaye shaɓe-shaɓe.

Wani saran ya kai wanda ya kusa samun ƙafarta ta janye da sauri, cikin kuka ta ce.

“Wallahi tallahi, ƙur’ani ban iya yaren nasaraba (Turanci) Dan Allah tun da dai Nigeri’a ƙasar hausawa ce ka barni hakan dan wallahi ban iya irin wanda Imirana da sojojo ke yi ba” Kamar wanda aka tsikara ya fara tahowa, gabaɗaya matan nan suka sha jinin jikinsu.
Kowacce ta shiga addu’a tana fatan kar ya zo wajenta, zagayasu ya yi sau ɗaya Mama da Hajiya da ke gefe, suka ƙara matsawa kusa da sauran kowa yana jin matsanancin tsoro.Gafe ɗaya ya koma ya tsaya yana ƙare musu kallo har Sadiya da ke tsugunne a wajen, Ashrof kwa hawaye sam basa tsayawa ga tausayin kanta da na ƴar uwarta da ma mahaifiyarta.

“Sahuuuu” Cewar Inna cikin tsoro, kowa da ido ya bita alamar tambaya.

“Yo jama’a ba dole na ce sahu ba tun da haka Allah ya ƙaddara mana yau, zama inuwa ɗaya da miciji, kuma miciji me son taken Nigeri’a to tun da Imirana ne ya fi iyawa sai mu bi ayari mu yi sahu, mu bi bayansa idan ya faɗa sai mu ke masa amshi da dai mu tsaya micijin nan ya mana ɗauki ɗai ɗai, dan ni kuma ban shirya mutuwa yanzu ba in barwa Tasalla Malam” Cewar Inna tana kuka abin tausayi abin dariya.
Gabaɗaya kowa sai ya fahimci maganar Inna haka take dan suna ganin kamar micijin ya fi son national anthem dan haka sai suka fara yin lafi a bayan Imran banda Sadiya da ke tsugunne a tsakiyar wurin, Imran da har lokacin yake a ƙame bakinsa bao huta ba da taken Nigeri’a yana kaiwa ƙarshe sai ya dawo farko. Yana faɗa su ma suna faɗa duk da ba kowa ke faɗa daidai ba irin su Inna da su Mama su ma sauran matan tsoro ya mantar da su cewa sun iya national anthem sai suka dawo kamar wasu ƴan koyo dan suna ganin kamar Imran ne ya fi iya wanda micijin ke so.

Suna cikin yi sai micijin ganin sun tattaru a waje ɗaya sai kawai ya shiga zagaye su, a mugun guje yake zagaye su har wani tsalle-tsalle yake, ganin hakan ya sanya suka ƙara tsorata, cikin tsoro da ruɗewa suka dunƙule a waje ɗaya, kowa ƙoƙarinsa ya samu mafaka a jikin ɗan uwansa, dan gani suke kamar in kana kusa da wani micijin ba zai zo wurinka ba. Imran da Mama sun ƙanƙame juna cikin rashin sani dan ita bata san shi bane shi ma bai san ita bace an haka kowa ya ƙwamusu baka jin komai sai sautin koke -koke.

Sai da ya gaji dan kansa ya koma waje ɗaya ya tsaya, kowa ya ɗan fara sakin ajiyar zuciya, Mama da Imran sai lokacin suka ankare sa sauri suka saki juna Mama na saurin juyawa ta dafe haɓa tana zabga salati a ranta, idan ba larura ba ya za a yi a ce sun rungume juna ita da Imran mijin ƴarta Sadiya. Kafin kowa ya gama tantancewa micijin ya buga wani uban tsalle ya hau kan bishiyar da ke tsakar gidan gabaɗaya kallo ne ya koma sama, kowa na kallon micijin da mamaki har da Sadiya ma da ta rasa bakin magana sai kuka, jelar ya kanannaɗe a jikin reshien bishiyar ya zaro kan sa yana kallon kowa da kowa, ganin haka sai kowa ya fara neman inda zai fake idan an sakko micijin ya dawo mutum sa fito.
Imran da gudu ya nufi wajen tukunyar dafa ruwan wankan jego da ke ɗore a kan murhun sai dai ba a kunna wutar ba, a ka Inna ke barinta saboda wahalar ɗorawa sai dai wani lokacin ta kan bar ruwa kaɗan a ciki. Yana zuwa bai yi wata-wata ba ya gotar da murfin tukunyar da yake babbace sai ya samu ya shiga ba tare da ya cire murfin duka ba, yana shiga ya ringisa a ciki, ya miƙo hannu ɗaya ya ja murfin ya rufe kamar me rufe ƙofa.

Matan nan sai gasu suna tseren shiga kicin da Inna, Inna ce a kan gaba, tana shiga ra sauke idanunta a kan freezer da sauri ta ɗauke idanunta dan ko ƙaunar ganin freezer bata yi.

Wasu lokarsu ta ɗazu suka ƙara komawa bayan sun garƙamawa ƙofar kicin ɗin sakata. Me fulawa da Hajiya da Mama suka shige ɗaki Hajiya ta shiga ƙasan gado dakyar tana kukkujewa amma ba damuwarra bace hakan mafaka kawai take nema. Mama cikin wardrobe ɗin Imran ta shige ta rufe, tana kallon yadda ta zaune kayan sirikinta har da gajerunan wandunansa. Me ƙunshi kuwa kayan wankin da ta gani a ƙulle a zanen gado masu yawa su ta sunce cikin sauri ta kwasa ta libgawa kanta.Sai wani zarnin fitsari take ji a hancinta ashe wandon Imran ne da ya jabgawa fitsari ranar da Inna ta rufe shi a ɗaki a ranar farko da Hassan ya zama miciji. Amma bata damu da warinnba tun da ta samu mafaka.

Ashrof kuwa bayi ta koma, ta banke ta aka bar Sadiya kawai a tsakar gidan tana kallon Hassan rataye a sama.

Inna da ke ƙasan wani dogon benci da da ake ɗora kayan abinci a kai ta rufa buhhuna kusan goma a kanta ta daddage ƙarfinta ta ce.

“Halima in ce dai kin samu mafaka, dan na ga Imirana tuni ya yi hanyar murhu, in kuwa tukunyar da nake dafa ruwa ya shiga dan na ji ƙaran murfin ina samun kaina wuta zan galgala masa sai na dafashi luguf ya dahu…
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

 

Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

Back to top button