Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 21

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*21*

*Shatu dambatta ke din ta daban ce Ina matukar kaunar ki har ckn kalbee nah Allah ya barmu tare*

Bayan sallar Isha sultan ya aika a kira masa Ayman sunyi ganawar sirri Wanda ni kaina bansan me suka tattauna bah zaman nasu kwata kwata 1hour ne , duk yadda mukarraban Gimbiya Suhail suka so samun labarin tattaunawar Basu samu ba , ta tara duk masu Kai mata rahoto daga waziri sarkin fada sarkin kofa da sauransu duk Babu labari ta shiga tsananin tashin hankali sosai ta rasa hanyar da zatabi don samun wannan labarin zaman sirri Abu ya gagara a wannan daren kasa bacci tayi . Ayman kuwa Wani murmushi yake faman Yi haka ya kasance cikin nishadi har ya koma bangarensa daga nan suka wuce part din Fulani inda Aman ya gaisa da ita da sauran dangin a tsattsaye saboda cikar mutane Basu zauna ba suka koma part din Ayman.
Washe gari aka fara gudanar da bikinsu na gargajiya Wanda yake al’adunsu na mutanen Sennar, Ayman yasha manyan kayan sarauta yayi kyau sosai baya son zuwa Amma ya kamashi dole yaje haka suka shirya suka hau dawakai harda Aman an bashi kayan sarauta sunyi kyau kamar a gudu dasu Aman kuwa sai faman hotuna yake Niko nace ba sabon ba ..lol, a haka dai aka cigaba da gudanar da bukukuwa har na tsahon kwana 5 kafin aka dugunzuma zuwa masarautar kush a can aka daura auren yarima Aseem tare da Gimbiya Sabreen Wanda dubbannin mutane sun samu halarta an narka dukiya kuwa ba kadan ba dama al’adarsu ne sadaki sai sun hada da sisin gwal ko gwala gwalai, bayan an koma fadar masarautar Sennar ne mutane suka baza kunne suna jiran nadin sarauta yarima Amma shiru kakeji nan koh hankalin Gimbiya Suhail yayi mugun tashi don tasa rai sosai dashi Kansa ango uban gayya , Ayman ko Yana cikin walwala da kwanciyar hnkli ga sauran Yan uwansa sunzo suna tare sai nishadi yake suna can part nasa suna hira . da dare aka kawo Gimbiya Sabreen dama akwai bangaren yarima Aseem a can aka kawata nan zasu zauna, algaita kuwa haka aka kwana ana busa sai gabanin asuba kafin aka watse. da safe aka sake shirya Wasannin dawakai anyi hawa dai iri iri sai bayan azahar aka shirya amarya cikin kaya na alfarma aka wuce da ita gun Gimbiya Suhail anzuba mata kyaututtuka daga zinari da kudi abin baa cewa komai, daga nan suka wuce bangaren Fulani itama ta nuna tata bajintar sai dare sukaje bangaren Sultan kowanne ya Bada gudumawar nasiha Suhail dai karfin hali kawai take kada a gane halinda take ciki amma gaba d’aya batajin dad’i a haka aka gama taro lafiya, Ammi sun tattauna sosai da y’ar uwar tata gameda matsalolin masarautar da Kuma abunda ya shafi Ayman a haka suka Kara sati kafin suka fara Shirin komawa Nigeria.

*Abuja Nigeria*
Rayuwa yaci gaba da gudana inna ta kasance cikin rashin kwanciyar hnkli a Halin yanzu Bata cika barin wayarta a kunne ba yawanci sai dai ta kunna ta kira Mrs Juliet ko Ayman ta Kara kashewa haka ta cigaba da lamuranta na yau da kullum hajjo sungama exams zasuyi summer inna ta roki Mrs Juliet akan tazo tayi Koda sati guda ne a gida Mrs Juliet ta Bata shawara akan tayi hakuri ta kyaleta summer din Yana da matukar amfani Yana taimakawa dalibai Kuma anriga anbiya mata kudin kowane summer har zuwa lokacin da zata gama jss3 ,inna ta nuna bazata Hana hajjo ba amma tana bukatar ganinta na Yan kwanaki kalilan Babu musu Mrs Juliet ta amince nan inna ta shirya da kanta taje daukan hajjo, sun rungumi juna cike da tsananin farin ciki inna harda hawaye tana kallon Hajjon ta Kara haske tayi fresh jikinta ya murmure alamar hutu ya bayyana sosai a jikinta duk da cewa batayi Wani kiba ba amma tayi kyau matuka. Cikin mota sai labari take bawa inna ita dai murmushi kawai take tana Jin Wani sanyi na ratsa zuciyarta tabbas Hajjo sanyin idaniyarta ce Allah ne kadai iya adadin son da takewa tilon y’ar tata a haka suka sauka maraba last bus stop daga nan suka nemi bike zuwa gida. Suna shiga gidan da sallama maman Nana ta ruga aguje ta rungumi Hajjo ” oyoyo ga Yan makaranta oyoyo ” bayan sun zauna ne mmn nana tana kallon Hajjo cike da zolaya tace ” Kai Masha Allah anzama Yan matan habuja Yan birni kin zama big girl fah ” murmushi hajjo tayi ta d’aga mata gaisuwa tana tambayar Ina Nana take ” ana can maraba kin wuceta a kasuwa ” a nan suka zauna suna ta zuba hira can sai ga Wani yaro ya shigo da sallama ” wai ana sallama da inna ” cike da mamaki inna tace ” iKon Allah waye Kuma” yaron ya juya yayi ficewarsa , hijabi ta saka ta tashi tana fitowa sukayi Ido hudu da Aman Yana jingine jikin motarsa ran inna ya baci Amma ta daure tace ” au dama kaine sannu da zuwa ” ya dan risina ” Ina wuni inna ya gida ya aiki” lafiya Alhamdulillah ya mutan gida ” lafiya kalau inna dama nazone mu dan gaisa nace ya labarin hajjo tana lafiya koh ” lafiya kalau tana can yola ” Allah sarki nace ko akwai number waya da zan sameta ” toh dayake boarding ne Basu amfani da waya ” shiru yayi sai Kuma yace ” toh shikenan zan tafi sai na sake zuwa nagode inna ” daga haka ta juya ta shige ko zama batayi ba Wani yaro ya shigo da manyan ledojin Sahad ” ance a kawowa inna ” ya diresu inna ta tashi da wuri ta Maida hijabi tana bin bayan yaron tana fitowa ta hango motarsa na barin layin nasu , Wani ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ciki. ” Malama waye haka da wannan dawainiyar” tsaki taja tace ” kedai bari anjima mayi maganar ashe abunda Ayman ke gudu kenan , idan ba raini ba har zai Wani turo a kirani tamkar wata sa’arsa, yanzu Yan unguwar nan Basu ga haka ba ma ya nake fama da kanakun maganganu bare ya faramin sintiri a kofar gida irin haka” nan da nan mmn nana tagane kan zaren wato Aman ne yazo, Satan kallon Hajjo tayi taga hankalinta baya kan zancen nasu tana game da wayar mmn nana, zama inna tayi cike da bacin rai ko kadan Aman Bai mata ba bashi da hali irin Ayman dole ta Kara nisantashi da Hajjo bazata taba barin alaka ta kullu tsakaninsu bah. Bayan sallar Isha ta kunna wayarta ta fara Neman Ayman ringing 2 ya katse ya kirata nan suka gaisa yake ce mata ” wllhi dama kina raina inna jiya na dawo Ina ta Neman layinki off ” Allah sarki wayar ne a kashe , kana jina ” ehh Ina ji inna meya faru?” dama mostly idan tace masa kana jina toh ya tabbata magana me muhimmanci zasuyi donhaka ya tattara hankalinsa ya Mika mata ” kayi hakuri jiya naje na dauki yarinyar nan dama wai so nake tazo tayi Koda sati ne…” Haba inna meyasa, nafa gaya miki bana son tazo gida har sai ta gama idan Muna raye but why ..” hmm ai nayi kuskure gashi jiyan kuwa dan uwanka yazo nan ” shiru yayi ya kasa magana sai da tace ” hello..” inna Ina Jin ki toh ya kukayi dashi ?” Na fada masa tana makarantar dai ” shiru sukayi can yace ” shikenan gobe zanzo insha Allah dama Ina son zuwa wajenki ” ah ah ba sai kazo ba, bana son mutane su fara min Wani kallo daban kasan unguwar namu sai a hankali ” shiru yayi daga karshe ya mata sallama ya kashe call din, jikin inna yayi sanyi harga Allah Batason masu mota suna zaryar kawo mata ziyara tana gudun magana da duk Wani abu da zai zubar da kimarta a idon mutanen unguwar, tagumi tayi tana tunanin Kodai kawai gobe ta shirya ta Maida hajjo skul ne toh Amma me zata ce musu? haka dai taci gaba da sake saken kafin ta fita tsakar gidan inda sukayi shimfidi suna Shan iska .
karfe 10am inna tana shigar da zobo cikin firji kamar a mafarki taji sallamarsa da sauri ta d’aga kanta don tabbatar da abinda kunnenta ya jiye mata ya sake maimaitawa nan ta sheda donhaka ta dauki hijabi ta rufe firjin Yana tsaye kofar gida ta amsa tare da masa izinin shigowa tabarma ta shimfida ta dora dardumar sallah a Kai , gidan nasu fes yake mmn nana ta tafi kasuwa cefane hajjo kuwa bacci take a d’aki , da mamaki take kallonsa murmushi yake ” waya nuna maka gidan ” Ina kwana innarmu ” lafiya ya gida ya hanya ” lafiya Alhamdulillah ya sanyin idaniya ” murmushi tayi kafin ta amsa ” tana ciki bacci take ” Allah sarki tana baccin gajiya koh ” uhmm Wani gajiya taje ta samu Hutu ta canza ” really..! baisan lokacin da ya furta Hakan na, murmushi inna tayi daga haka ta tashi ta shige d’akin tana tashin Hajjo. Sanye take da doguwar Riga me guntun hannu Wanda sister khairiyya ta Bata jikinta na qamshin turaren emergency kunsan Yan boarding ta gayu lol.. kitson kalba ne a kanta manya manya ya matukar Kara mata kyau Wani siririn gyale ta yafa bayan inna tace mata ta fito su gaisa , Kansa a sunkuye yaji qamshin turaren nata cike da mamaki yayi saurin d’aga Kai suka hada Ido ta sauke nata tana Mai risinawa gefen inna a hankali tace ” Ina kwana ” lafiya ya skul ” alhmdllh ” daga haka sukayi shiru inna tace ” tashi ki dakko masa zobo da kunu bansan wanne yake so ba ” ta tashi cikin nutsuwa ta koma d’akin bayan minti d’aya ta fito da zobo me sanyi da kunun aya ta dora kan plastic plate ta ajiye kusa dashi daga nan ta koma d’aki ta gefen Ido yake kallonta har ta shige. Inna tace ” Bismillah kasha ruwa ” nagode inna” shiru sukayi sai can tace ” ya zancen auren naka ” murmushi yayi yace” Allah ya amsa aduata anfasa auren ” toh me abin murna a cki Allah dai ya Maka zabi Mafi alheri” zabin kenan ai inna ” murmushi tayi tace” wato baka son maganar aure koh ” toh inna ai da saurana” murmushi tayi Bata ce komai ba, yanzu yaushe zata koma sai nazo na maidata ” kayi hakuri zatayi kwana biyar daga nan zai maidata da kaina ” idan ta shirya komawa ki min magana sai nazo muje tare Amma bazata sake zuwa ba sai ta rubuta jssce ” Allah ya kaimu lokacin Nima bazan Kara barin tazo ba idan badai Wani abu ne ya taso ba Kuma bana fatan haka,Amma Ina son ka sani Babu alaka tsakaninta da dan uwanka saboda Basu dace bah, Kai Kuma dawainiyar da kayi Allah ya biyaka ya saka da alheri nagode sosai bazan manta da halaccin da ka mana ba ” shiru yayi gabansa ya Fadi da Jin zancen nata Amma koma menene Yana fatan nan gaba Allah zai kawo musu mafita. tashi yayi ya mata sallama wayarsa ya d’aga ya kira Fauzan cikin kankanin lokaci ya shigo tare da sallama ya gaisa da inna sannan ya ajiye ledojin dake hannunsa inna tace ” ku Baku gajiya da dawainiya haka jiya Dan uwanka ya kawo mana abin alheri, mungode Allah Bada lada” ba komai inna kayan bikin kani na ne da akayi ” toh Masha Allah shine Kai bakason zancen aure, toh Allah ya Basu zaman lfy” Fauzan ya mikawa zobo da kunun inna tace ” tsaya bari a karo muku ” Bata Jira amsarsa ba ta koma cki ta zuba dayawa a cikin Leda ta fito ta mikawa Fauzan suka mata bankwana suka tafi. Hajjo na kwance da earpiece a kunnenta inna ta shigo tace ” abunda kika koya a makarantar kenan Jin wake waken banza koh ” murmushi tayi tana kashe wakar da ta kunna cikin wayar maman Nana dake hannunta ” inna wannan ba dan uwan besty bane ” gidanku da bestyn waye Kuma besty ” inna Aman nake nufi ” bansani ba meyasa Baki tambayesa ba ” shiru tayi tana tura Baki ta juya tayi kwanciyar ta.

Back to top button