Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 1

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*NASARAR RAYUWATA*

Bismillahi Rahmanir Raheem Allah ya nuna mana karshen lafiya, ya bani ikon isar day sakon dake cikin wannan labari, Alhamdulillah Allah nagode maka da ka bani lafiya da basira, Allah ya karawa annabi ( s. A. W) daraja, godiya mai tarin yawa gareku masoyana masu kirana a waya masu bina private da masu turamin sakon text nagode Allah barmu tare yasa mu karu da juna thanks for the love and support Reefat loves you all.

*1* free page

Matar na gindin murhun icce tana faman hura wuta da bakinta idanunta yayi ja saboda hayaki ta kwalawa y’arta Kira ” hajjo.. Hajjo! Kina Ina ne ki fito kije ki kawomin Kara a bayan gida wutar taki kamawa, da harshen fullanci take magana wata yarinya ce bata wuce 12 years a duniya ba ta fito daga dakin tana daura dankwali wani silifas ta saka Wanda ya mutu ya tsufa ya lalace tana susa kai ga kitson duk ya dunkule don tsabar tsufa da datti, ” toh Inna na tafi ” ” a dawo lafiya ” ya juya ta fice. Wata mata ce ta shigo gidan da sallama ” Inna hajjo yau Allah ya kawoni nace bari nazo na cika alkawari ” ” ah maraba da xuwa mutan birni yaushe a garin dai? ” ” wllhi yau nazo nace gara nazo na sanar dake Ku fara shiri saboda jibi insha Allah zamu tafi” zare ido tayi tace ” jibi kuma Kande, ni Ina naga kudin mota wannan tafiyar gaugawa haka ” kwantar da hankalinki ba dai kin amince zaki tafi ba, kudi ba matsala bace” ” shikenan Allah ya kaimu Nagode da tunawa dani “ruwan randa ta debo mata ta ajiye bata sha ba har suka gama tattaunawa kande ta tashi ta tafi sunyi akan jibi zasu hadu a tasha tun asuba, Inna ta zauna ta buga tagumi tana tunanin wannan tafiyar da zatayi babu yadda ta iya dolece zaisa ta tafi yau shekara biyu kenan babu mijinta babu labarinsa tun lokacin da ya tafi kasar kamaru kasuwanci, ita bata da kowa a garin sai yan uwan mijin nata danginta na can maiduguri ita asalin shuwa shuwa ce aurene ya kawota jahar Adamawa, bata da labarinsu saboda rashin waya Aisha hajjo ita kenan Allah ya bata y’a d’aya tilo bata sake samun ciki ba shekaransu goma sha biyar da aure da Malam Sule rabone ya kawota nan garin Wanda bata taba mafarkin zuwa ba, taurin kai ne yasa iyayenta suka yarda suka aura mata Sule. Kauyen kojoli wani kauyene dake cikin karamar hukumar Jada a cikin jahar Adamawa fulani ne suka fi yawa a cikin kauyen suna aikin noma da kiwo kuma suna kasuwanci iri daban daban, hajjo ta dawo da icce a ka ta daura da y’ar tsumma ta jefasu kusa da murhu ta zauna tana haki Inna tace ” ke da son guduwa kullum Ina hanaki baki ji Allah dai ya tsareki ” murmushi tayi tana tura iccen cikin wuta nan da nan wutar ta Kama ci.
Da dare bayan sallar isha Inna ta fara shirya kayansu cikin yar Ghana must go hajjo tace ” Inna tafiya zamuyi? ” ” ehh jibi zamuyi asubanci, zamu koma garin Habuja da zama ” ” Inna Baba na kuma yaushe zai dawo, idan ya dawo bai samemu ba kuma fa? ” wani guntun murmushi tayi batayi magana ba taci gaba da shirya kayan, sallama akayi ta amsa wata makociyarsu ce dije ta shigo ta xauna suka gaisa tace” yanzu da gaske tafiya zakiyi Inna, baki tsoron kar mijinki ya dawo bai sameki ba, ya matsayin auren naku yake” ” nima bansani ba, amma nasan nagaji nagaji da jiransa shekara biyu ba wasa bane, babu ci babu sha babu sutura, ke kinsan halinda muke ciki kinsan yadda muke rayuwa, danginsa babu Wanda yake xuwa inda muke babu mai tallafa mana saboda haka gara na tafi can duniya don bazan iya kaiwa iyayena dawainiya ba kuma da kunya na koma garesu da wannan labari zan zamo abin zagi a cikin dangi wasu zasumin dariya suce mijina ya gudu ya barni nagaji goggo dije bazan iya ba zamu tafi insha Allah ki tayamu da adua sannan ki bani lambar wayarki wataran zamu gaisa zamu sake haduwa ” rungume juna sukayi suna kuka Hajjo tayi jugum tana kallonsu duk da karancin shekarunta amma tagane halinda mahaifiyar tata ke ciki toh amma meyasa Babanta zai gudu ya barsu meye laifin innarta? babu mai bata wannan amsa, cikin wannan dare suka kwashi yan tarkacen kayansu na amfani suka kai gidan dije saboda dare yafi sirri.

________________________

*Birnin Sennar Sudan*

Birnin sennar tana amfani ne da monarchy system of government wato sarki ko sarauniya ke mulki a wannan gari kuma suna amfani ne da shariah law mutane ne masu koyi da sunnar ma’aiki (s. a. w) , dayawa daga cikin mutanen birnin yan izala ne kuma kashi 91% na mutanen garin musulmai ne sarkin wannan gari kuma ana kiransa da Sultan. Babban masarautace mai girman gaske Wanda aka sani shekara da shekaru tun zamanin baya, Sultan Abdoo- bn Mahmoud shine Sultan na wannan lokaci mutum ne adali mai tsanin kwarjini da jarumta asalin bafulatanin Sudan ne ya gaji mulkin wajen mahaifinsa, matansa biyu Gimbiya Suhaila y’ar sarkin khartoum da Gimbiya Fateema Fulani y’ar lamidon Adamawa Najeriya yana da yara 8 maza 2 mata 6, Fulani itace matarsa ta biyu kuma yafi qaunarta saboda macece mai sanyin hali bata da hayaniya kuma abun duniya baya gabanta y’ay’anta uku Alia ce babba tayi aure tana birnin khartoum sai Kafeela tana karatu a jami’an Maryam Abacha American university na kasar Niger sannan Ayman Wanda shine auta matashi Dan shekaru 25 baya son karatun boko a rayuwarsa yafison na addini, kasancewarsa babban d’a namiji wajen Sultan Abdoo ( Abu Hanifah) tun yana karami aka turasa karatu a birnin jedda ta kasar Saudi Arabia amma baya maida hankali yanxu an dawo dashi gida zai koma birnin khartoum shi kuma baya son zuwa. Gimbiya suhail y’arta ta fari itace Hanifah shiyasa ake kiran sultan da suna Abu Hanifah sai wasu mata 3 sai Aseem Wanda shi kadai ne namiji yana da girman kai da son girma ga nuna takama da isa Ayman ya girmesa da shekara biyu amma idan baka sani ba zaka dauka shine babba don sabar son girma na nuna isa wannan kenan.
Babban fada ne mai girman gaske kamar gari guda ga manyan gini dogaye na gargajiya da na zamani ga manyan bishiyoyi ga furanni ga katangar an zana tambarin sarauta duk inda ka duba bayine birjik suna kaiwa da kawowa gasu nan maza da mata suna sanye da kaya iri d’aya, a can lambun gidan Fulani ta fito kilisa ga tsuntsaye na yawo ga wata karamar korama farin ruwa na gudu wajen shiru kake ji sai kukan tsuntsaye, darduma aka shimfida aka shirya kayan marmari irinsu ayaba kankana inibi tuffa aka shirya da lemuka iri daban daban ga kaskon turaren wuta guda hudu aka shirya akowace kusurwar daddumar, manyan trow pillows aka shirya ta kishingide bisa d’aya ga kuyangi zagaye da ita suna mata hidima wasu na fifita wasu na danna mata kafafu wata kuwa tana bata labari mai nishadantarwa, farace kal kamar a taba jikinta jini ya fito don tsabar hutu da jin dadin rayuwa fuskarta dauke da murmushi tana sauraron labarin wayarta tayi Kara kuyanga mai rike wayar tace ” Allah ya kara miki daraja da daukaka Ammi ke Kira ” murmushi ya dada bayyana a fuskarta tasa hannu ta karbi wayar , cikin girmamawa kuyangin suka tsunkuyar da kai ta d’aga hannu take suka watse don bata damar amsa wayar ” assalamu alaikum ya y’ar uwata rabin jiki, kamar kinsani kina raina sai kika Kira ” shiru tayi tana sauraro can ta amsa ” kowa lafiya alhmdllh, sultan na lazimin yamma yaronki kuwa ya shiga gari ” ta sake yin shiru daga bisani tace ” toh ya zamuyi yaron ne yaki zaman can, yanxu dai Sultan ya yanke hukuncin maidashi khartoum wllhi Ammi bana son zamansa kusa da gida kinsan makiya sun saka masa ido, ni Allah na tuba gani nake zancen makarantar ba banza aka barsa ba amma kinsan sultan bazai taba yarda da hakan ba duk abunda ya faru sai kiji yace daga Allah ne baya taba yarda da zancen akwai makiya wllhi, ni na rasa mafita Ammi don Allah ki samo min mafita please ” launin fuskarta ya canza haka ta cigaba da waya har ta gama ta ajiye, bayan yan mintuna kuyangin nata suka dawo suna cigaba da hidimominsu. da dare batasan meya faru ba kawai wata kuyanga tace wani dogari yazo ya isar da sakon cewa Sultan na son magana da ita a fadarsa na cikin gida, tace a fada masa tana nan zuwa nan da nan masu mata hidima suka fara shiryata don zuwa ganawa da sultan turare na musamman aka fesa mata bayan an turara wata doguwar riga mai hade da hula kamar alkebba amma irinta kasar Sudan, hadimai shida suke taka mata baya har suka fito waje nan suka tarar dA dogarai 7 suna tsaye suna jiranta aka bude mota ta shiga aka tattara rigar aka shigar da Wanda yake ja a kasa. Wani katafaren falone mai girman gaske anyi mAsa ado da lu’u lu’u da zinari ga lallausan darduma mara iyaka da trow pillows masu shapes daban daban Ac da fanka ke aiki sAi wani ni’imataccen qamshi me sanyaya zuciya ke tashi, a bakin kofa duk suka tsaya don wajen ne iyakarsu ita kadai ta wuce ciki tare da sallama yana kishingide bisa royal chair yayi zama irinta manyan sarakuna masu fada aji, ta karasa ta xauna a kasa ” ranka ya dade dafatan ka yini cikin lafiya ” murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yana matukar qaunar nitsuwarta komai nata cikin nitsuwa take bata da rawan kai ” kin fito lafiya Gimbiya Fulani ” lafiya alhmdllh ranka ya dade, dafatn lafiya sultan ke nEmana cikin wannan lokaci Allah yasa ba wani laifin yarima ya aikata ba ranka ya dade ” ” lafiya kalau sai alheri, dama Aminatu ce ta kirani mun gama magana zan tura yarima wajenta gobe da izinin Allah ” wani boyayyiyar ajiyar zuciya tayi nan take murmushi ya bayyana a fuskarta tace ” masha Allah nagode ranka ya dade, Allah Kara girma” “ameen Gimbiya, zaki iya tafiya idan ya dawo yazo ya sameni ” ” godiya nake Allah Kara maka lafiya, na barka lafiya ” ta tashi ta fita tana fitowa aka fara ” takawarki lafiya sarauniya Fulani, Allah Kara girma dA lafiya” ta wuce aka biyota mai bude mOta ya bude ta shiga ta koma bangarenta.

*Reefat Yahya* is back again with the amazing story of *NASARAR RAYUWATA* but is not for free it cost 300 naira only, ki biya dari ukun ki kacal ki karanta wannan labari mai nishadantarwa da fadakarwa da ilimantarwa ki tuntubi 07030077024 for details of payment WhatsApp only.
*marubuciyar*
Shine zabina
Mai sona
Nida shugaban kasa
Hukuncin uwa
Mace zinariya
Rayuwarmu a yau
Hijra
Jauro bajam
And more, hurry and patronize at 300 naira only thank you.

Back to top button