Yarima Suhail 68
PAGE* 6⃣8⃣
Tana gama sa kayan bayan yarima tabi suka fito, kallon part d’in jamila tayi taga a kulle yake kasancewar jamila taje anguwa, har cikin ranta bataji dad’iba dabasu samu sunyi sallama da jamila ba.
Suna janye da trolly d’insu sukafito zasu nufi wajen motar yarima, daidai lokacin aka hangame gate motoci hud’u a jere suka shigo, tsaye sukayi suka zuba ma motocin ido cike da mamaki dan basusan ko suwanene ba a ciki.
Tun kan a ida yin parking ummi tabud’e murfin mota tafito dagudu tanufi wajen yarima.
Mutuwar tsaye su yarima sukayi tana zuwa tafad’a jikinsa tarungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa kaine my son, daman zan k’ara ganinka?
Tsaye yarima yayi yakasa ta6uka komai, d’ago kai tayi takallesa tare da shafa fuskarsa tace suhail d’ina kaine a gabana ko mafarkin da nasaba ne?
Muryar yarima tana rawa yace ummi na.
Rungumeta yayi sosai a jikinsa yace ba mafarki kikeba nine dai a zahiri ummina nayi missing d’inki.
K’ara shigewa tayi a jikinsa tace shine kuma katafi kabarni baka nemeniba? Meyasa? Meyasa kaimin haka suhail.
Ahankali yabud’e baki zaiyi magana hango su memartaba da yayi sun zuba masa ido yasa maganar ta lak’afe a bakinsa.
Takowa memartaba yayi yanufo inda suke,,,ganin haka yasa yarima yajanye ummi daga jikinsa tare da d’an ja baya kad’an.
Memartaba yana isowa wanka ma yarima mari yayi, gabad’aya wajen ido aka zuba masa cike da mamaki ganin yadda yake d’okin ganin suhail ammah daga had’uwa sai mari, zarah ko jikin sultana bilkisu tafad’a tana kuka,,
Duk’ar da kansa yarima yayi ammah ko kad’an bai gezaba,,,muryar memartaba tana rawa yace sake guduwa kake shirin yi a karo na biyu saboda kar muzo gareka? ka kyauta suhail yanzu har kayi tsawon wata ukku batare da kazo ka nemeniba? Hakan da kayi daidai ne?
Cike da mamaki yarima yad’ago yakallesa,,,,memartaba yacigaba da cewa eh suhail koda ni nakoreka ammah ai cikin fushine kaduba kaga yadda nakoma duk akan rashinka, ni kaina nasan na aikata babban kuskure da na iya korarka daga cikin danginka, suhail taya kake tunani zan iya yafema kaina bayan daga baya nagane kaine akan gaskiya, wlh sumayya ta cuci rayuwata, ya zanyi a yanzu inwanke wannan laifin da na aikata kaicona ina ma ace duk cikin mafarkine.
Girgiza kai suhail yashiga yi cikin sauri yafad’a jikin memartaba yace ranka yadad’e kayi hak’uri bahaka bane, ni ban rik’ekaba ko kad’an kawai dai umurninka nacika, kayi hakuri da bijire ma maganarka da nayi wlh nima bahakanan na rabu da ku ba kawai dan gudun abinda za’a aikata daga baya azo ana da nasani ne domin zarah kwata-kwata batada laifi acikin maganar, ina tsoron in cuceta domin na tabbata sai Allah ya bi mata hak’inta, tunda tana k’ok’arin kyautata min taya zan saketa batare da tayi min komai ba, kayi hak’uri ranka yadad’e,
Shafa bayansa memartaba yayi yace hakan da kayi shine daidai suhail nidai burina kabiyoni mukoma gida.
Janye jikinsa yayi daga na memartaba tare da yin murmushi ahankali yace zarah,,,sai a lokacin memartaba yakalli zarah da take a jikin ummi, murmushi yayi yace d’iyata zo mugaisa mana,
Ummi janye zarah tayi daga jikinta, nan zarah taduk’a cikin sauri tagaishe da memartaba.
Amsa mata yayi cikin sakin fuska sannan yace kiyi hak’uri da abinda yafaru zarah.
Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace bakuyi mana komai ba ranka yadad’e duk abinda kukayi akanmu daidaine tunda kune sama da mu, mune yafi dacewa mubaku hak’uri tunda mu mukayi laifi.
Jinjina kai memartaba yayi cike da jin dad’in lafazin zarah, yace Allah yai muku albarka.
Sultan abbas isowa yayi yarungume yarima, yace yarimana naji dad’in ganinka dafatan zaka yafe mana abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace abbana akodayaushe bakwa laifi nine dai nayi muku laifi.
Yarima ma baya laifi hakan da yayi shine daidai,,,cewar sultan abbas.
K’ara shigewa jikinsa yarima yayi yace nagode sosai abbana.
Yarima janye jikinsa yayi daga na abbah yaje yarungume dadynsa cikin jin dad’i yace daddyna kayi hak’uri kayafe min nasan nayi muku laifi.
Shafa kansa yayi yace kar kadamu my son tuni laifinka yagogu daga garemu bare ma suhail d’ina baya laifi, Allah yaimuku albarka
Dariya Yarima yayi yace nagode sosai daddyna, ina alfahari da ku,,,kallonsa yakai ga su dada dasuke gefe d’aya tsaye ita da sultana sadiya, murmushi yayi sannan yawuce yanufi inda suke tsaye ganinsa yasa dada tahad’e hannunta biyu waje guda cikin kuka tace suhail,,,rungumeta yarima yayi cikin sanyin murya yace meyasa matata zatayi kuka bayan ga mijinta a tare da ita? Cikin kukan tayi dariya tare da rungume yarima tace suhail ina farin cikin ganinka, kayi hak’uri da abinda yafaru kayafemin wlh duk abinda nakeyi maka sumayya ce take kawomin zuga.
Murmushi yayi tare da d’ago kai yakalleta yace kakata duk abinda kikayi daidaine kuma kin cancanci kiyi fiye da haka saboda kin isa da jikanki.
Itama d’agowa tayi tace dagaske, d’aga mata gira yayi yace toh ya kikace.
Jan kumatunsa tayi tace suhail bakada dama ammah nagode da naganka.
Murmushi yayi yace nima haka matata,,, daganan yamatsa kusa da sultana sadiya da taduk’ar da kanta tana hawaye, gyaran murya yayi, kamar daman jira take cikin sauri tafad’a jikinsa tare da fashewa da kuka tace suhail kayafemin na cuceka na k’untata ma rayuwarka tun kana k’arami na d’aura maka karan tsana, dan Allah kayafemin akan abubuwan da nayi maka wlh nayi nadama insha Allahu yanzu zan gyara rayuwata.
Janyeta yayi daga jikinsa yace ummah kidaina tunawa da abinda yariga yawuce na yafe miki tun tuni.
Cikin kuka tace nagode sosai suhail Allah yabiyaka.
Ameen ummana.
Nan sultana sadiya da dada sukaje cikin jin kunya sukaba zarah hak’uri akan abinda sukayi mata.
Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace wlh bakuyi min komai ba inma kunyi toh na yafe.
Dr mu’az da yake tsaye chan baya yana kallonsu takowa yayi ya iso inda suke nan yaimusu jagora suka shiga cikin gida
Sultana bilkisu tana manne da yarima haka suka shiga kamar wani ya ce zai k’wace mata shi
A main parlour suka yada zango nan zarah taje tad’auko musu ruwa da lemu, memartaba yai gyaran murya yace Alhmdllh gaskiya naji dad’i sosai da naga yarima a yanzu ji nake duk wani ciwo da yake tare da ni ya warke, dan haka gida kawai zamu koma gabad’ayanmu gobe.
Girgiza kai yarima yayi yace kagafarceni ranka yadad’e a yanzu banaji zan iya komawa gida kubarni nan kawai inyaso zan dawo daga baya.
Gabad’ayansu ido suka zuba masa, memartaba ne yai k’arfin halin cewa saboda me suhail, me zaka zauna nan kayi? Kodai baka huceba?
Cike da girmamawa yace ba haka bane ranka yadad’e ina nufin zamu tafo daga baya.
Ina wlh bazaka k’ara kubce manaba k’afarka k’afarmu kayi hak’uri kawai mukoma gida,,,,cewar dada.
Sultana bilkisu ma rik’o hannunsa tayi tace suhail kar kace haka ka amince kawai mutafi ‘yan uwanka suna chan suma suna burin ganinka.
Eh suhail ka amince kawai,,,,cewar sultan abbas.
Shuru yarima yayi nad’an lokaci sannan yakalli mu’az da yazuba masa ido, nan mu’az yad’aga masa kai alamun eh, murmushi yarima yayi sannan yace shikenan na amince zan biku.
Gabad’aya nan sukayi murna, haka sukayi ma mu’az godia sosai akan kulawar da yaba su yarima, murmushi mu’az yayi yace duk abinda nayima yarima ban biyasaba domin shi yamin fiye da haka addu’a ce kawai zanyi masa inbiyasa.
Nan memartaba yasa aka kira waya yace ayankar musu ticket.
Jamila ma koda tadawo nan tatarar da su memartaba cike da girmamawa tagaishesu nan mu’az yagabatar da ita.
Sai gab da magrib sannan memartaba yace sutashi sukoma masaukinsu dan su shirya, yaso su yarima subisu masaukinsu ammah yarima yace a’a sai dai goben zasu shigo, ummi rik’esa tayi dan gani take kamar zai k’ara kubce mata.
Murmushi yarima yayi yace kar kidamu ummina babu inda zanje ina tare da ke, kuje kawai gobe zan shigo dasafe.
Kwallah ce tacika mata ido tace kayi alk’awali?
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace eh ummi.
ajiyar zuciya tasafke nan sukayi musu rakiya har wajen motocinsu, saida sukaga tafiyarsu sannan suka dawo, mu’az zama yayi saman kujera tare da dafe kansa.
Ganin haka yasa yarima yazo gefensa yazauna tare da cewa abokina ya dai?
‘Dago kansa yayi Cike da damuwa yace prince yanzu tafiya zakayi kabarni? Ya zamuyi idan kuka tafi wlh mun saba da ku bamuso kutafi.
murmushi yarima yayi yace mu’az wa yace maka zamu iya rabuwa? Ai ko muntafi zamu dinga kawo muku ziyara inma takama dakaina zan neman maka transfer kakoma hospital d’ina kacigaba da aiki tunda dama bakada kowa a garinnan aikine yakawoka.
Murmushin jin dad’i Dr mu’az yayi yace prince wlh da ka gama min komai, dan Allah idan kakoma kayi min wannan taimakon.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu kafi k’arfin haka wajena insha Allahu zanyi iya k’ok’arina.
Nagode sosai prince Allah yasaka da alkhairi.
Koda su yarima suka koma part d’insu kallon zarah yayi da takasa kulle baki saboda murna yace kina murna zaki tafi gida ko?
Eh man sosai ma, kaima kana murna?.
Shuru yarima yayi yakyaleta,,,matsowa tayi kusa da shi tare da tallabo fuskarsa saida takalli cikin idanunsa sannan tace kaima nasan zakaso mukoma garinmu dan zamanmu cikin family d’inka shine kwanciyar hankalinmu.
jan hancinta yayi yace kedai tunda kina murna shikenan ammah ni nafison zamanmu a nan.
Marairaicewa tayi tace saboda me kace haka,
Murmushi yayi har saida beauty point d’insa suka lotsa sannan yace saboda a nan babu mai takura mana, a chan ko baza a barni inhuta da matataba.
Murmushi itama zarah tayi tace kar kadamu hearty babu abinda zai hanamu kasancewa da juna dan a yanzu mun riga munzama d’aya.
Ajiyar zuciya yasafke yace hakane dear, ammah zanso kihaihu nan.
Langwa6e kai tayi tace kayi hak’uri mukoma chan garinmu tunda kaga haihuwar da sauran lokaci kuma zatafi dad’i muna cikin danginmu,,,kaga fa kungama magana da su memartaba cewa gobe tare zamu tafi
Shikenan dear tunda kinfi son mutafi toh nima na amince.
Rungumesa tayi a jikinsa tace Nagode sosai my heartbeat.
Su sultan abbas sunkira su waziri a waya sunce gobe zasu dawo nan cikin jin dad’i sukayi musu addu’a akan Allah yamaidosu lafiya.
Memartaba fadar sarkin garin yasa suka wuce suka gaisa tare da yi masa godia akan karamcin da yayi musu a nan suke shaida masa gobe sukeso suwuce garinsu.
baiji dad’iba da yaji sun ambaci tafiya nan yashiga rok’onsu akan suk’ara kwaana biyu.
ammah memartaba yace a’a nan suka shaida masa har ticket sun sa a yankar musu.
ba yadda ya iya kan dole yahak’ura a nan sukayi sallar magrib sannan suka wuce masaukinsu, tare da yi musu alk’awali gobe dashi za a je rakiyarsu.
Koda suka koma had’a kayansu suka shigayi cike da farin ciki biyu ga lafiyar da memartaba yasamu ga ta bayyanar yarima.
Daga chan 6angaren su yarima ma haka zarah tak’ara shirya musu kayansu, duk yadda yarima yaso tazo sukwanta k’iyawa tayi saida tagama shirya duk abinda tasan suna so sannan taje takwanta.
Washe gari tun k’arfe goma wayar da ummi tayo masane ta tashesu daga baccin da suke, bayan sun gaisa nan take shaida ma yarima flight d’in k’arfe biyu zasubi dan haka sugama komai dawuri kafin biyu.
Wajen k’arfe sha biyu suka gama shirinsu gwanin kyau, a parlour suka tarar da su Dr mu’az suna jiransu nan suka gaisa sannan suka wuce sukayi breakfast daga nan sukahau yin hira saboda gabad’ayansu basuson rabuwa da juna,
yarima key d’in motarsa yad’auko yadamk’a ma Dr mu’az yace gatanan ka k’ara, zaro ido Dr mu’az yayi yace ranka yadad’e kodai a ajiye maka ko inje dakaina inkai maka har gida?
Girgiza kai yarima yayi yace kod’aya na mallaka maka ita halak malak yanzu tazama taka.
Dr mu’az da matarsa godia sukayi ma yarima sosai cikin jin dad’i har da duk’awa k’asa saida sukaga ran yarima ya fara 6aci sannan suka daina godiar
Memartaba ne yadamesa da kira dan haka suka tashi gabad’aya suka nufi chan masaukinsu har da su Dr mu’az,
Rungume yarima Memartaba yayi cikin jin dad’i, sultana sadiya ko jan zarah tayi kusa da ita, duk yadda zarah take nok’ewa ammah duk motsi kad’an da zatayi sai sultana sadiya tayi mata sannu.
Bayan sunyi sallah sarkin garin dakansa yasa aka shirya motoci nan yazo dakansa masaukinsu, lunch ma daga masarautarsa yasa aka kawo musu, bayan sungaisa nan Memartaba yagabatar mashi da yarima da matarsa.
Sosai sarkin garin yanuna farin cikinsa akan ganin yarima da akayi.
Bayan sungama kimtsawa gabad’ayansu suka nufi airport nan suka zauna har saida flight d’in ya iso sannan sukayi bankwana da juna cikin rashin jin dad’in rabuwa da za’ayi.
Dr mu’az, matarsa da zarah har da ‘yar kwallarsu yarima ma ne maik’arfin halin basu baki.
Basu sukabar wajenba har saida flight d’in yatashi sannan.
A cikin flight d’inma Memartaba yana tare da jikansa, inda zarah take gefen dada kad’an kad’an da tad’aga ido sai taga yarima idanunsa suna a kanta gabad’aya sai taji kunya saboda su Memartaba da su daddy dan hakama sai tadaina kallonsa.
A chan airport d’in garin gazban tun kan su iso ya cika da jama’a kowa yana farin cikin son ganin memartaba dan basusan tare suke da yarima ba.
Lokacin da flight d’insu yasafka gabad’aya wajen yarikice da murna musamman ma da Memartaba yazo fitowa tsaye yayi yana d’aga musu hannu cike da jin dad’in ganin jama’arsa yadda sukazo tarbarsa.
Ai suna ganin yarima sai wajen ya ida rikicewa nan aka cigaba da murna dan ma dogarawa sun hana kowa yamatso inda suke nan aka bud’e musu motocin da aka tanadar masu suka shiga dakyar suka samu hanya sai emir palace,
A chan d’inma mutanene dank’are suke jiran isowarsu, nan ma anyi murna sosai da ganin yarima, shaheed ko rugowa yayi yarungume abokin nasa cikin jin dad’i shima yarima yarungumesa.
Shaheed yace abokina ina katafi kabarni? shine katafi kabarmu muna ta nemanka.
murmushi yarima yayi yace kayi hak’uri shaheed yanzu gani nadawo ba inda zan k’ara tafiya inbarka.
cikin jin dad’i yace dagaske?
‘Daga masa kai yarima yayi alamun eh.
nan shaheed yayi murmushi yace nagode sosai abokina ammah fa nayi kewarka.
Memartaba baishiga gidaba saida yatsaya suka gaisa da mutane tare da yi masu godia sannan suka rantaya a turakar su Memartaba, rahama da husna dasauri suka nufo dan tarbar iyayen nasu ganin yarima yasa suka rikice suka nufi wajensa har da kukansu, rungume ‘yan uwannasa yayi cikin jin dad’i, rahama cikin kuka tace Bro meyasa katafi kabarmu? Baka tunanin halin da zamu shiga, kaduba kaga tun bayan tafiyarka gabad’ayanmu bamu cikin kwanciyar hankali.
shafa kanta yayi yace kiyi hak’uri Lil sis yanzu gani nadawo yayanki zai kasance da ke akowane lokaci,
murmushin jin dad’i tayi tace nagode sosai yayana, nan takoma wajen zarah tarungumeta cikin jin dad’i.
Kallon husna yayi da take ta kuka yace akan me babbar yaya zata dinga kuka bayan ga k’anenta a kusa da ita? ‘Dago kai tayi takallesa nan yad’aga mata kai, cikin sauri tafad’a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
rungumeta yarima yayi yace please sis kukan ya isa haka indai baso kike nima kisanyaniba.
Cikin sheshek’ar kuka tace meyasa katafi kabarni, kai kanacan hankalinka kwance bakasan halin da muka shigaba saboda rashinka.
Murmushin k’arfin hali yarima yayi yace big sis duk inda suhail yakasance toh shima tunaninsa yana a wajenku, daidai da kwana d’aya ban ta6ayiba batare da kuna a raina ba.
toh dan Allah kar kak’ara tafiya kabarmu.
Jan kumatunta yayi yace angama big sis, cikin jin dad’i takai mai peck a goshi sannan suka rantaya zuwa turakar su memartaba.
Gabad’ayansu a saman carpet d’in da yake shimfid’e tsakiyan d’akin suka zauna inda memartaba da dada suka zauna saman cushin.
gyaran murya memartaba yayi sannan yace Alhmdllh godiya ta tabbata ga Allah da yasa cikin ikonsa nasamu lafiya akan ciwon da ni kaina banyi tunanin zan tashiba saidai cikin ikon Allah ayanzu gani garas saidai d’an abinda ba a rasaba.
gabad’ayansu sukace Alhmdllh Allah yak’ara lafiya da nisan kwana.
Shuru yayi nad’an lokaci yacigaba da cewa yarima suhail munatayaka murnar dawowa cikin family d’inka tare da baka hak’uri akan abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace bakomai ranka yadad’e.
masha Allah sannan magana tagaba itace……shuru memartaba yayi alokacin da yaga sumayya ta shigo d’akin, gabad’ayansu ido suka zuba mata.
daga nesa dasu kad’an tatsugunna tana kuka,,,abban sumayya ne yai k’arfin halin cewa ubanmi kikazo kiyi mana nan? Ko kitashi ko insa6a miki.
Cikin kuka sumayya tace dan Allah kuyi hak’uri kuyafemin abinda nayi maku wlh nayi nadama nadaina bazan sakeba.
Memartaba jinjina kai yayi yace zancen banza koda kikaga na k’yaleki bansa aka had’a da ke aka sa prison ba toh nabarkine yarima yadawo yayanke miki hukunci dakansa saboda shi yafi dacewa yayanke miki ba niba tunda kuma yanzu gashi ya dawo toh alhmdllh wuk’a da nama suna hannunsa dan haka suhail ga sumayya nan kayanke mata hukuncin da yadace da ita.
dada tace tabbas hakane suhail duk abinda kazartas daidaine.
Mik’ewa sumayya tayi tamatso kusa da yarima tatsugunna cikin kuka tace yarima ban damu da hukuncin da zaka zartas ba akaina nidai burina d’aya kataimaka kayafemin abubuwan da nayi maka wlh duk abinda nayi ba yin kaina bane zinat ce silar komai, tasha fad’amin cewa bazan iya rabuwa da itaba saboda akwai abinda tashirya min tun farkon had’uwarmu, indai zinat zatayi magana toh tatanake d’auka inbar ta kowa koda ace ta iyayenace, sannan nasha k’ullah makirci dan inga nashiga tsakaninku da zarah dan ina gani nice nadace da kai ba zarah ba ammah a yanzu nagane cewa zarah ita tafi dacewa da suhail,
Kallon zarah tayi tace zarah nai miki abubuwa dadama ammah baki ta6a d’aga ido kin kalleniba dan tsakani ga Allah kike zaune da ni.
Zarah da tunda sumayya tafara maganar kuka take dan ta bata tausayi sosai musamman ma da taga duk ta fita hayyacinta.
Yarima Kallon memartaba yayi yace ranka yadad’e dalilin da yasa ban fad’a mukuba tun farko saboda nafiso ku ma kugani da idanunku gudun kar kuk’i yarda musamman ma dada da ummah gabad’aya basuson laifin sumayya a lokacin.
Uhm kaidai bari d’annan ai yanzu dai mungane komai,,,cewar dada.
Jinjina kai yarima yayi sannan yace ashe saida k’awartata tak’ara dawowa gidannan,
Memartaba yace yanzu ma haka tana a prison bari insa atafo da ita, nan memartaba yayi waya.
bayan mintuna kad’an saiga wani barde yazo da zinat duk ta yi bak’i ta k’ok’e inba ka kalletaba sosai bazaka ta6a cewa ita bace hatta ita kanta sumayya da taganta saida tafirgita.
Daga nesa dasu kad’an taraku6e tana hawaye, kallonta sumayya tayi cikin kuka tace zinat dan Allah kiwanke ni wajensu susan banda laifi a ciki.
Zinat ma cikin kuka tace idan bakida laifi toh wa yake da laifi? wlh sumayya kin cuceni.
Duk mutanen da suke zaune wajen shuru sukayi sukarasa megaskiya tsakaninsu,,,yarima ne yace bari akira dogarawa suzo atambayesu.
Zinat a tsorace dan ta tsorata sosai da bulala tamanin d’in da akayi mata cikin kuka tace dan Allah kar kakira ni zan fad’i komai ammah kar kasa ak’ara dukana.
Indai har kika fad’amin gaskiya batare da kinmin k’aryaba toh babu wanda zai dakeki sannan zani sallameki kiyi tafiyarki.
Share hawayen fuskarta tayi sannan tace tabbas sumayya batada laifi a ciki nice silar fad’awarta wannan harkar dan tun muna school sumayya tana da wulak’anci bata yadda tayi abota da kowa sai ‘ya’yan masu kud’i nikuma tun lokacin da nafara ganinta naji ta burgeni ganin nima d’iyar masu kud’i ce yasa nayi amfani da dadamata muka k’ullah abota nan mukacigaba da wulak’anci saida naga sumayya ta saba dani batada abokiya kamarni sannan nabijuro mata da buk’atata akanta ammah tak’i yadda ban nuna mata 6acin rainaba daga k’arshe naje wajen wani malami yaimin aiki akanta yazamana duk abinda nakeso shi takeyi bata iya tsallake maganata, a lokacin wani saurayina yanuna yana buk’atarta yabani kud’i masu yawa nikuma naimasa silar samun sumayya shima saida taga raina yana neman 6act sannan ta amince har yayi zina da ita.
gabad’aya d’akin suka saka salati cike da al’ajibin abun kowa yana Allah wadai.
memartabane yatsaidasu, nan zinat tacigaba da cewa tun daga lokacin nima nafara neman sumayya har nasaba mata da harkar itama tabi layi.
a lokacin da take fad’amin zatayi aure na nuna bak’in cikina sosai saboda inason sumayya banaso inga abinda zai rabani da ita, daga k’arshe koda tayi aure ni nadinga hure mata kunne akan kar tayi ma mijinta biyayya duk wani abu da sumayya takeyi da sa hannuna a ciki saboda bata iya tsallake maganata, hatta pills ni nasakata tana sha duk dan kar tahaihu saisa kukaga bata ta6a ko 6atan wataba,
ahaka nacigaba da bibiyarta gidan aurenta mukacigaba da harkarmu batare da tsoron komai ba sai gashi lokaci guda dubunmu tacika ankama mu muna aikatawa.
Dan Allah tunda na fad’a maka gaskiya kabarni intafi wlh bazaku k’ara ganin ko k’eyataba nima nadaina.
Gabad’aya matan da suke d’akin kuka suke, sultana sadiya cikin kuka tace Allah ya isa ashe kece kika 6atamin d’iya.
sumayya girgiza kai tayi tace zinat babu abinda zance miki saidai kawai kije munhad’e gobe k’iyama gaban ubangijinmu ammah hakanma nagode da kika wankeni a wajen dangina.
Sultan abbas murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace kema sumayya harda laifinki a ciki nasha kwatanta miki akan kibi rayuwa a sannu ammah rawan kanki ya hana daman ita rayuwa *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka dan haka kije gashinan duniya ta nuna miki hankali daman ita duniya ta ishi kowa riga da wando.
Sultan ahmad da memartaba shuru sukayi kamar ruwa ya cisu
Yarima kud’i yad’auko yamik’a ma zinat batare da ya k’irgasuba yace nabaki minti ukku kifita kibar gidannan ko k’eyarki kar kibari ink’ara ganinki.
cikin sauri zinat takar6i kud’in gudu-gudu sauri-sauri haka tafita.
Sai a lokacin yarima yakalli sumayya yace kije kawai sumayya duk abinda kikayi min dan kanki daman tuni nagano haka kawai dai gudun kar zargi yashiga tsakaninmu shiyasa ban ta6a magana ba ammah yanzu Alhmdllh da gaskiya tabayyana
Rik’o hannunsa tayi cikin kuka tace dan Allah suhail kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko na sami sauk’in abinda nakeji.
Fizge hannunsa yayi, ganin haka yasa zarah cikin kuka tace dan Allah kataimaka kayafe mata tunda ta gane laifinta kuma kunji batada laifi a ciki.
murmushi yarima yayi yace shikenan dear ta ci albarkacinki nayafe mata.
Cikin jin dad’i tace nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, koda taje wajen zarah tunkan tayi magana zarah tace kar kice komai sumayya ni tuni na yafemiki daman ban rik’ekiba.
haka sumayya tazagaya wajen kowa tanemi gafararsa kowa yace ya yafe mata cikin jin dad’i tayi musu godia.
memartaba sai a lokacin yayi magana yace toh Alhmdllh tunda anyafe ma juna, dan haka yanzu wannan ya kamata yazama darasi ga kowa, kekuma sumayya yanzu tunda kin nuna kin tuba kicigaba da neman gafarar ubangiji akan abinda kika aikata sannan kicigaba da zama har Allah yakawo miki miji kiyi aure.
Cikin jin dad’i sumayya tace toh nagode sosai ranka yadad’e.
Memartaba kallon yarima yayi yace suhail ga part d’inku chan nasa angyara maku zaku koma kucigaba da zamanku guards d’inka da ma’aikatanku duk suna nan.
Sosa k’eyarsa suhail yayi yace ranka yadad’e da gidana da nagina naso inkoma da zama idan ka amince.
Girgiza kai memartaba yayi yace a’a suhail kar kayi haka kayi hak’uri kucigaba da zama nan kusa da ni dan hankalina ya fi kwanciya da haka.
murmushi yarima yayi yace toh ranka yadad’e yadda kakeso haka za’ayi.
Toh masha Allah, Allah yasafke matarka lafiya, idan da me magana sai yayi.
gabad’aya shuru sukayi alamun babu memagana dan haka memartaba yasa sultan ahmad yarufe taron da addu’a aka sallami kowa yawatse cike da farin ciki da jin dad’i.
_Comment_
*Nd*
_Share_
_Sis Nerja’art✍_
[5/2, 5:19 PM] Sis Naj Atu:
_*YARIMA SUHAIL*_
_*Written By~Sis Nerja’art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔