Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 14

Sponsored Links

Page 1️⃣4️⃣

 

Ganin inda idonshi yake ne yasa tayi saurin sa hannunta duka biyu tarufe kirjinta ahankali yasa hannunshi yarike kugunta wani irin kasalane yasauko mishi lokaci daya idonshi harwani lumshewa sukeyi kokarin kwace kanta takeyi Amma yamata rikon da bazata iyaba dayan hannunshi ne ahankali yake mata tafiyan tsutsa harya iso kirjinta dawo da kallonsa yayi kansu Yana kare musu kallo bakaramin tsokale mishi ido sukayi ba cikin bacin Rai FANAN tace wannan wani irin iskancine kasakeni banaso kallonta yayi yatsanshi Daya yadaura akan libs dinta shhhh kimin shuru cikin murya me sanyi yake magana bazanyi dinba kasakeni ko in maka ihu kafeta yayi da rikitattun idanunshi kawo bakinshi yayi Dede nata kamar zeyi kissing dinta runtse ido tayi bakinshi yakai kunneta Yana mata magana mekama da rada wayace miki kisa irin wannan kayan akufule tace Ina abinda yadameka ne Ina ruwanka da abinda nasaka Kara matseta yayi yace akwai gashi kinyi tsirara agabana innalillahi wainna ilaijiraji unnn azuciya take magana dama haka yake dama azaad Dan Iska ne jiyanda yakemin maganar banza wayyo Allah na ka kawomin dauki gaba Daya tagama kashe mishi jiki bayaji ze iya saketa nan kusa suna ahaka sukaji takun tafiya wani irin karfine yazo mata ta tureshi da iya karfinta kwashe liffayanta tayi da gudu tashige toilet tana danasanin abinda yakawota dakinsa dubashi daga yau afalo zatake dubashi Yana tsaye yanda tabarshi yakasa Koda daga kafarshine zeenat ce tashigo dakin Yaya Ina fanan najita shuru Kuma abinci zamuci uhmmm yanzu tafita kidubata afalon kasa ko waje okay tace sannan tafice fanan najin fitanta tafito dasauri tana gyara nadin liffayan datayi a toilet hartakai bakin kofa taji anruko hannunta dasauri tajuya jawota yayi tafada kan faffadar kirjinshi cikin kasala yace kidena irin wannan shigan kinji gudun karya bata mata lokaci ne wani yasake dawowa yasamesu ahaka ne tace to saketa yayi harta kusa fita afalon tace allah ya Isa tabamin jiki dakayi tagama magana tana murguda mishi Dan bakinta kafin tafita dagudu Dan karya biyota cize libs dinshi nakasa yayi yafada kan gadonshi Yana kallon celling rufe idonshi yayi shape dintane yahasko dasauri yabude idonshi.

Gyara nutsuwarta tayi kafin tahaura falon ummi anty Amina ce tace Ina kikaje naji tundazun zeenat take nemanki uhmmm Ina falon kasane tana karasa maganar tana inda inda zama tayi ummi fah? tana bacci tashiga zata Dan huta ahankali tace afito lafiya ameen daukan hand bag dinta tayi tace anty Amina zanwuce SE zuwa gobe tofa tafiya tun yanzu eh zanshiga asibiti ne ayyah shikenan se gobe allah yakaimu Ameen fitowa tayi afalon kasa tahadu da zeenat zaune take tana chatting tom madam zeenat sarkin chatt nawuce dama kamar kinsan kenake nema yanzu tafiya zakiyi bamuci abinci ba noo karki damu sewani lokaci fitowa sukayi suna hira hangota zeenat tayi nan take tabata fuska tazo Dede da FANAN ta bangajeta seda takusa faduwa da sauri zeenat ta tarota ke ramlat wannan wani irin haukane iyeee bakiga mutane bane wani kallon Tara saura tamata tana nunata da yatsa keni tsarar kice dazaki tsaya fadamin magana anfada miki kiyi abinda zakiyi ganin abin na neman jawo fadane yasa FANAN ta ja zeenat tana bata hakuri kekuma awa Karar kada Miya shegiya yar matsiyata dukda zagin yabatawa FANAN Rai Amma seta danne tana Jan zeenat ramlat ganin bata kulata bane yasa tace bagidajiya dakin kulani dayau Banga me hanani cin uwarki ba afusace fanan Takoma wajanta tana zuwa batayi wata wata ba ta dauketa da Mari masu zafi har biyu kafin ta nunata da yatsa ke inbakisan darajan naki iyayen ba Ninasan nawa Kuma kece babbar bagidajiya wacce batasan inda yake mata ciwo ba tafiya tayi tabarta agun har titi zeenat tarakota tana bata hakuri akan abinda ramlat tayi bakomai senazo gobe to shikenan semunyi chatt okay tashige napep yaja suka tafi

Duk abinda yafaru akan idon mommy ranta yayi matukar baci har hancinta nafito da hayaki wannan yarinyar tafara wuce gona da iri yata zatasa hannu ta mara lallai taja ruwan dama kanta ciki ta koma tana cika tana batsewa.

Wanka yayi yafito daure da towel akugunshi da yar karama Yana goge gashin kansa zama yayi kan kujeran Dake gaban mirror shafa Mai da perfume yayi kafin yasa kayan bacci yakoma falo yadau laptop dinsa yakoma ciki yazauna yafara aiki Kiran layin zeenat yayi yace tasa akawo mishi coffee ☕ bayan kamar 5mint me aiki takawo Yana sipping Yana aiki.

 

Bayan fitar fanan asibiti tawuce taje taduba mutane tazo zataje office din doctor ammar ne taci karo da doctor Ib bata fuska tayi ciki ciki ta gaishesa my sweet baby kinganki kuwa bakaramin kyau kikayi ba dole in biya kudin kwalliyan nan ba bukata nagode muje office dina innuna miki wani abu girgiza Kai tayi tace okay bari inje in amsa Kiran doctor ammar SE in sameka a office dinnaka washe baki yayi Jin abinda tace yau gaskiya yanada saa tunda ita dakanta tace zatazo office dinsa wucesa tayi, tayi gaba abinta abakin kofa tahadu dashi Yana rufe office din ah ah fanan kece eh nice dama nazo gunkane gaisawa sukayi kafin yace gashi Kuma zanshiga urgent meeting to shikenan doctor SE gobe innazo okay yau kinje kinduba azaad ne eh naje dama akan batunshi nazo okay muje tafiya sukeyi tafara da am dama sonake inji haryanzu begama recovery bane eh to gaskiya FANAN da Dan saura tukun nan Kinga alluranshima saura na 1week daga nan shikenan kingama hamdala tayi Amma meyasa kike tambayata dasauri tace nooo bakomai kawai inaso injine natafi seda safe to shikenan allah yakaimu kan mangrib Takoma gida tasamu kowa yahallara afalo kallone yadawo kanta oyoyo oyoyo suhaima ce taje ta rungumeta darling sis seyanzu gaskiya nayi missing dinki hhhhh sekace dagaske Danaga kiranki ai sorry banida charge ne to naji zubaida gaishesu tayi suka amsa mata jekiyi sallah kizo babane yayi maganar fuskanshi ahade jiki asanyaye tashiga daki tabbas wani Abu yafaru kokuma tayi laifi alwala tadauro tazo tagabatar da sallah kafin tafito da dogon hijab dinta tazo tazauna akasa tace gani baba wato yanzu FANAN ni ban Isa dakeba kenan ban Isa ince kiyi Abu kiyi ba ko dasauri tadago tana kallonshi mena fada miki kobance miki duk sanda kikaga alamar zakiyi dare awaje ki kira azo adaukeki ba ahankali tace kafada baba kayi hakuri in sha Allah bazan sake ba allah yasa sannan yace bawai batun bazakisake ko Zaki sake ba FANAN tunda kike arayuwarki kintaba ganin munbari kinyi dare awaje girgiza Kai tayi Masha Allah sesau Daya Shima namiki uzurine sbd shine karonki nafarko karnaji Karna gani yanda muke kiyayewa kema ki kiyaye to baba hakan baze Kara faruwa ba allah yasa Ameen suka amsa kitashi kisa muku abinci to abinci tadibo musu tuwon semo da Miyan ganye wucewa daki sukayi gaba Daya jikin FANAN yayi sanyi dafata suhaima tayi kallonta tayi suhaima jikina Yana bani akwai wani Abu Amma sunkasa fitowa sufadamin ajiyar zuciya suhaima tayi tace nima nakula dahakan saboda kafin kishigo sekinga yanda hankalinsu yake atashe gashi wayarki bata shiga baba yayi fada sosai hmm rananma fah dazakuje siyan fruit nace zanje mama tace babu inda zani sau kusan 5 kenan innace zanfita gidansu Amira bayan sallah mangrib ake hanani itakuma tana zuwa karki damu Zakiji komai bata wani ci abincin sosai ba

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story Written by (MRS ISHAM )

 

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci

 

 

 

___________________________________________

 

Back to top button