Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 3

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*3* free page

*maitama new extension Abuja*

Wani katafaren mansion na gani na fada fentin gidan farine kal ga motoci sunkai 8 a harabar gidan gate din gidan kadai abin kallo ne don daukar ido yake kamar zinari, cikin gidan kuwa Wani tangamemen falone a shimfide babu iyaka komai na cikin falon abin kallone don tsabar kyau da tsari tana kishingide bisa kujerar dinning table mai kujeru 12 bowl ne cike da farfesun kafar sa Wanda yaji kayan miya ga qamshin sinadaran girki dake tashi, tana rike da spoon tana sipping na ruwan farfesun a hankali idanunta na kallon screen din waya. Wani matashin saurayine fari tas dashi ya sakko daga shimfidediyar matakalar benen mai fadin gaske yana taku a hankali har ya karasa inda take ” morning Ammi” hararinsa tayi ” morning a gidan Uban waye, yanxu 11:39 kake tashi daga barci, Aman yaushe zaka fara jin magana ne wllhi kayiwa kanka fada wannan ba gata bane ” hannu ya dora bisa kafadunta ” Haba Ammi nayi sallan asuba fa just na gajine shiyasa na kwanta sorry ok ” ” Allah ya shiryeka, mutum ya girma amma har yau bakayi hankali ba, an turaka UK baka zauna ba ka dawo Baze university dsame tin ka koma Nigerian Turkish ( Nile) still dsame wllhi zanyi maganinku, state university zan turaku kuma dole kuyi karatun ka shirya Ayman yazo ka tafi da driver Ku dakko shi” turo baki yayi yace ” ni Ammi kinsan ba shiri muke dashi ba, meyasa bazaki turo driver yaje ya dakko sa ba ” ” sannu ubana kaji, wllhi maza ka wuce ka tafi tun kafin raina ya baci ai duk halinku daya yara daku baku son karatu sai shiririta ” sunkuyar dakai yayi ya wuce entrance na falon ya fice. Yana fita motoci uku aka tada lokaci guda da sauri wani bodyguard ya bude masa motar tsakiya ya shiga dama can sunsan da zancen zuwansu airport domin dauko babban baqo na musamman wato Ayman bn sultan Abdool.
Aman na cikin mota bai fito ba Ayman kuwa na cikin private jet yana xaune yana jiran isowar Wanda zasu daukesa a haka har suka share 1 hour babu Wanda ya nemi Dan uwansa saboda kowanne na jida kasaita, Ayman Dan sultan Aman kuwa d’an SGF wato secretary to the govt of d federation yana takama da dukiyan ubansa saboda ubansa na daga cikin manyan kusocin gwamnati masu fad’a aji a fadar shugaban kasa da kasar baki daya, Ammi ta Kira Ayman tana tambayarsa suna Ina yace suna airport tun 12 salati Ammi tayi ta kashe wayar take ta Kira Aman tana fada kamar ta fito cikin wayar ta masa duka, Aman ya Kara cika yayi fam cike da bacin rai ya umarci bodyguards nasa da cewa su fita su duba cikin jiragen dake tsaye su tambaya Wanda ya fito Sudan na Sennar kingdom su taho da mutumin. Sun tafi sunyi yawo daga karshe suka gane jirgin suna xuwa dogarawa suka taresu ance babu mai shiga sai da suka fadi sakonsu kafin wani dogari yace ” kuje Ku taho da mota saboda yarima ba dan talakawa bane da zai taka daga nan har xuwa inda kuka ajiye motocin ” dole bodyguards din suka koma suka fadi sakon tsaki Aman yaja yace ” don Uban mutum dole dai a binnesa a kasa idan ya mutu, Ku dauki mota daya Ku tafi ya na iya da Ammi ” haka suka dau mota sukaje aka ajiye a bakin matakalar jirgi dogarawa na gaba wasu na baya da kuyangi mata shida suka fito Ayman yana taku dai dai har ya sauko idanunsa na makale da bakin gilashi har aka bude masa gidan baya ya shiga dogarawan suka ce Ina sauran motocin saboda dole zasu tafi da mutum goma Wanda zasu na yiwa yarima hidima, Ayman ya Kira shugaban dogarawan ya masa magana a hankali babu Wanda yaji meya fada daga haka dogarin yace ” Allah ya tsare Allah ya kare mana yarima Ayman sultan maijiran gado, Allah ya ja zamanin dan sultan jikan sultan jikan lamido ” daga haka suka juya dogari daya kadai suka bari Wanda ya kasance yardajjen bawan Ayman Ana kiransa da suna Fauzan tun yana dan yaro suke tare, suna tsaye har aka ja motar suka tafi kafin hadiman suka shiga jirgi suka koma. Aman na kallon window from time to time yana faman jan tsaki ga yunwar da yake ji an hanasa Karin kumallo saboda wani can Ayman. Motar ya hango ta doso inda suke daga haka sauran suka mara musu baya suka jera suka fita daga harabar Airport din Nnamdi azikwe international airport Abuja.
Ammi na falo sai duba agogo take minti minti tana faman jan tsaki amma zatayi dealing da Aman kuwa saboda taurin kansa yayi yawa, diran motoci taji ta tashi da sauri ta fito balcony a lokacn Aka bude musu motoci suka fito tare Ayman na ganinta ya sake mata wani lallausan murmushi ” welcome welcome my son barka da zuwa yarima dan gidan Amminsa ” ” Ina yini Ammi Nah ” lafiya alhmdllh ya hanya ” lafiya kalau ” kauda kai Aman yayi yazo ya wuce ta gefensu ya shige gida, hararinsa Ammi take ta rike hannun Ayman suka shiga tare kai tsaye wajen cin abinci suka nufa Aman na xaune Ana xuba masa abinci. Bayan sun zauna masu aiki suka tambayi Ammi me zasu xubawa baqon nan ta basu umarni aka xuba masa shinkafa da miya sai kayan fruits da aka kawo dayawa, Aman ya fara ji yana danna waya ko kallon inda suke baya yi Ammi ta kallesa tace ” wllhi Aman ka kiyayeni, yanxu kayiwa dan uwan naka ko ci kanka bare sannu da xuwa, bayan ka ajiyeshi a airport duk bai isheka ba, yanxu idan wani Abu ya faru dashi kuma me zaka ce min ” ajiye spoon yayi yace ” com on Ammi meyasa kike son dole sai nayi hulda dashi ne, shi da yazo ya min magana ne? ” ehh lallai ka girma Aman, wllhi bari Dady ya dawo state university zaka tafi da kai da Ayman din duk tare zaku tafi kuma daki d’aya zaku zauna naga ta tsiya, yara sai girman kai kaman me ” Ayman ya sunkuyar dakai kasa yana wasa da spoon din dake hannunsa Aman kuwa kallon bangaren Ayman yake cikin kallon jin haushi. Ammi ta tashi ta wuce sama saboda lokacin salla yayi tana tafiya Aman yace ” guy me zaka nunamin kake wani jida kanka, naga babu abunda kake dashi Wanda ni na rasa ” murmushi Ayman yayi yace ” akwai, kai farine ni kuma bak’i, kai gajere ni kuma dogo kuma na girmeka da shekaru har biyu kaga kuwa akwai abubuwan da nake dashi kai kuma ka rasasu ka gane man ” tsaki Aman yayi ya buga table ya tashi ya tafi.

*****************

Shugaba ta gama raba musu robobin bara kowa ya Kama hanyarsa sai yamma kuma kamar yadda suka saba, bayan ta gamane ta lura da Inna da hajjo dake tsaye tace ” baiwar Allah amma dai Ku baqi ne saboda ban taba ganin wannan fuskokin ba ” gaisheta sukayi ta amsa Inna tace ” wani ne ya kwatanta mana wannan gida yace muzo zaki bamu masauki ” dariya tayi tace ” tabbas zan baku masauki amma dai Ina da sharuda idan zaku iya shikenan bani da matsala, kinga dai zan baku daki ga bayi can amma dole zaku fita bara kullum ku kawo min kud’ade sannan na sallameku daga cikin abunda kuka kawo, abinci kuma a can zaku nemo ku ciyar da kanku, idan kika nuna wayo kika b’oye kudi kuma zan saba muku wllhi saboda bana son cin amana” shiru Inna tayi tace ” babu damuwa na yarda ” washe baki tayi tace ” masha Allah ya sunanki maza kuxo ku wuce, ke Abulle kizo ki rakasu saman gada ki dawo yanxu ” ” sunana Amina sunan yata kuma hajjo” wata budurwa ce baxata wuce 16 years ba taci kwalliya daga gani Yar wajen shugaba ce don tsananin kamanninsu, hajjo dai sai raba ido take sukabi bayan Abulle suna tafiya tana gaisawa da samarin unguwar sai wani rangwada take suna biye da ita suna tafiya ta rike hannun hajjo tace “ya sunanki kyakyawar yarinya ” “Hajjo! ” ta amsa mata haka suka cigaba da tafiya sunyi tafiya mai dan nisa kafin suka bullo kasuwar maraba saman pedestrian bridge ta nuna musu, mutane maza da mata wasu na saman gada wasu na kasa suna a cike makil yara da manya duk Wanda suka gani suzo suna rokonsu ko wata mota idan ta tsaya suje suna musu aduo’i ana basu kudi da abinci wajen very busy place ne gaba daya Inna ta rude saboda bata taba xuwa busy area kamar haka ba, Abulle na nuna musu ta juya tace ” toh sai kun dawo ko hajjo” ta juya tayi tafiyarta Inna da hajjo sai raba ido suke su kalli nan su kalli can kowa na shaanin gabansa babu mai kula wani yan kasuwa kowa da abunda yake saidawa. Inna ta rasa waye zata tambaya gaskiya baxata iya wannan sana’a ba Sam.. haka hajjo zata tashi a gindin gada tana bara har girmanta babu ilimi Ina zata samu mijin aure, gaskiya baxata iya maula ba abunda manzo (s. A. W) yayi hani dashi mezai kaita aikata wannan gara dai ta hakura ta nemi wata sana’ar amma ta Ina, waye zai basu masauki inda zasu zauna bare suyi sana’a.. Wata mata ta taka kafarta cikin rashin sani ” sannu baiwar Allah sorry ” matar daga cikin mabaratan ne tana goye da jinjiri a bayanta Inna tace ” babu komai, don Allah tambaya zan miki idan bazaki damu ba” ” ayya halan ke baquwa ce don ban taba ganinki a nan ba ” ehh ni bakuwa ce Ina neman masauki don Allah ina zan samu? ” murmushi tayi tace ” ai nan garin kowa takansa yake, kin ganni nan tuwo nake saidawa dashi nake rayuwa da y’aya uku, mijina ya gudu ya barmu yau wata 10 kenan tun Ina dauke da ciki har na haihu shine na tashi na tsaya Ina neman na kaina saboda tsira da mutunci na” toh yanxu ya zamuyi ni babu inda zan samu masauki? ” gaskiya babu sai dai ki Kama dakin haya ” ” baiwar Allah Ina naga kudin haya nida jiya muka zo garin ” ” toh taimako d’aya zan miki shine kizo mu hada kudi mu biya dakin da zan Kama sai mu zauna tare ” kuma har nawa kudin ” ” dubu talatin ne kinga sai ki kawo sha biyar, dakin da mijina ya Kama kudin sun kare shekaran jiya shine aka bamu notice xuwa gobe zamu fita ni kuma na nemi mai saukin kudi ” shiru Inna tayi tana tunani matar tace ” muje can ku zauna idan na gama sai mu tafi tare, daga wane gari kuke? ” ” daga Adamawa ” ” Allah sarki akwai makociyarmu Dada fadi Yar Yola ce ” hira suke bayan sun koma under bridge inda matar ke siyar da tuwo da miyan kubewa da kuka, masu baran ne suke siya da almajirai ga zafin rana ga yaronta a goye ga wasu da jarirai haka suke tsaye suna maula duk motar da tazo wucewa su taru suna roqo, ta xuba musu abinci a plate na roba ta mikawa hajjo tace ” ungo ci, nasan yunwa kike ji ” kallon Inna tayi sai da Inna ta mata alama ta karba hannu hajjo tasa ta karba tana godiya sannan ta ajiye gaban Inna ” baiwar Allah ki cire kunya kici abinci nan bariki ne babu mai kula wani ” murmushi Inna tayi tace ” saboda bariki kuma sai mutum ya manta da al’adunsa, gaskiya ni bazan iya cin abinci a wannan kasuwa ba ” ” toh kuje can kasan gadan ku zauna ku ci, zama da yunwa ba dadi ” kudi Inna ta cire dari biyu ta mika mata tace ” ki Kara mana wani ” matar ta karba tana godiya ta basu canjin 100 suka koma karkashin gada suka bada baya suna ci a hankali har suka gama, ruwan sanyi suka siya akace musu 20 naira suna mamaki haka suka bada kudin. A takaice yinin ranar a under bridge sukayi har wajen karfe biyar kafin suka shirya suka koma unguwar Aso tare da wannan mata mai tausayi da imani suna tafiya tana nuna musu hanya har sukaje gida, wani gidane mai dauke da dakuna sha biyu a nan suka shiga ta bude dakinta babu komai ciki sai tsohuwar katifa da jakar Ghana must go biyu cike da summokara tace ” ku shiga nan nake kafin gobe muje mu biya kudin daki ” zama hajjo tayi tana karewa dakin kallo Inna tace ” Ina bayi yake zanyi sallah” matar ta debo mata ruwa a buta ta nuna mata toilet din tana xuwa taji motsi da alama akwai mutum ciki, dole ta jira ta koma gefe ta tsaya wata mata tazo da bokiti cike da ruwa tana yan wake wakenta Wanda ke ciki ya fito wani namijine yana fita matar da tazo daga baya tayi wuf ta shige, Inna ta sake baki tana kallon ikon Allah matar nan bata fito ba sai da aka fara kiran sallan magarib sannan Inna ta shiga ta fito ta samu layi a waje ta wuce taje ta zauna tayi alwala. Da dare suna hira matar ta shimfida musu tabarma tace su kwanta a kai ita kuwa tare da y’ay’anta a bisa katifa, babban Yar sunanta Nana sai Sadik sannan jaririn kuma jabir suna hira da Inna hajjo kuwa tayi bacci saboda a gajiye take.

*ki biya 300 kacal ki mallaki naki Yar uwa, tuntubi 07030077024 for details of payment thanks for the love*

Back to top button