Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 6

Sponsored Links

Cikin ƙanƙanin awanni Jirginsu ya shigo garin Mumbai India .
Wani mahaukacin gida da bata taɓa ganin irinsa ba ko a kalle kallen Fina finan ta ,tsakiyar gidan jirgin ya sauka .tsorone taji ya fara kamata ,amma dai ta dake ta fara addu’a a cikin zuciyarta .

Gabaɗaya gidan remoting system ne ,don haka komai da remote ake sarrafa shi daidai da labulai da ƙofofi . Ta wani ƙofa suka bi sai ga su sun ɓullo ta ƙafan benen da zai sadasu da ɗakunan ƙarƙashin ƙasa..Kenan gidan bayan bene kuma yina da under ground

Jikinta sanyi ƙalau yayi idonta suka fara cikowa da ƙwalla
Bakinta na rawa tace “Ina ne nan baiyi kama da asibitin da kace ba”

Murmushi yayi “Na hango tsoro a cikin ƙwarar idonki a kaina feel free ni Ba mugu bane”

Wayancewa tayi saboda kar ta bada kanta

“I do”

Haka ta cigaba da binsa har suka sauka a wani irin wargajejen falo wanda yafi na saman girma da tsaruwa ,wanda zai kwashe kujeru seti goma ,amma set ɗayan kujerune farare sol na leather seats sai manyan cup boards na littafai sai table ɗin tarkacen su desk top da laptops

“Zauna”

Ya bata umurni ,a ladafce ta zauna cikin sallamawa ,shikuma ya wuce wani ɗaki ,minti biyu sai gashi ya fito hannunsa da wani dogon bottle kamar na giya da cups guda biyu,gabanta yazo ya ajiye ya tsiyaya masu rabin cup

“Bissmillah”

Ƙiris ya rage ta fashe da ihu haka ta daure

“Menene wannan ,badai giya bane ko?”

Dariya yasoma ƙyaƙyacewa dashi har yana daga ciki,itakuwa ƙurr ta kafesa da ido ,ashe dama ya iya dariya har haka yake ɗaure fuska? Sosai taji yana ƙara burgeta

“Bana shan giya ,a normal drink ,haba If_babebakisan drink din nan ba duk wayewanki? Kefa Lagos babe ne kuma University babe acan dinma hot cake”

“Wallahi ni ba wayyayi bace kawai duk bugene ,so ban taba ganin drink din nan ba kar inje insha giya saboda kar ace mun ƴar ƙauye”

“Shikenan…shikenan your man baya shan giya da duk wani abu ma da bai dace ba ,amma zamu iya browsing sai mu bincika drink din a gabanki if you’re doubting”

“No I trust you” ta amsashi da sauri tana ɗaukan glass cup din

Kafeta da ido yayi ,har saida takai glass din saman bakinta ta ɗago idanuwarsu ya sarƙe da na juna ,washe baki yayi

“Oh really ?”

Jinjina masa kai tayi
“Hmm” kawai yace ,shima ya dauki nasa ya ɗànyi sipping kaɗan ya ajiye

“Ina ne nan? Kuma meye dalilinka na baroni da Nigeria ba tare da consent ɗina ba ka kawo Ni nan ”

“Saboda Inyi building trust tsakanina dake ….yeah nan da kika gani gida nane ,shine karshen privacy na ,idan na gaji da mutane nan nike gudowa ,ba wanda yasan gidan nan dagani sai mamata sai ke yau”

“me yasa ni?”

“Kinada yawan tambaya ifty ,wannan tambayar naki shine abu na farko da ya jawo raayina akanki …karki damu i love it…..Ammm kince mai ya kawo mu nan ? Saboda mu kwayewa junan mu hijabin da muka lulluɓe kanmu dashi ,abun nufi ,ki bani labarin ke wacece nima zan baki labarin kaina daga nan sai in fada maki matsayin tafiyarmu”

“Ba abu mai dadi da zakayi fatan ji a wajena ,in short Ni ƴar talakawane ,talakawan lilis mu barshi hakan”

“Hmmkin manta naje har garinku na dauko mamanki still Baki yarda in na ga dama a rana daya zansan komai naki ba? So nike ki fada mun da bakinki

Gyara murya tayi

“Da fari sunana Iftihal_khair Mohammed ,Ni ƴar talakawane ,mamana maririya mara lafiya na fito daga maƙasƙancin family dake rugan bunzun jihar Gombe ,Ni kadai iyayena suka haifa, Babana makiyayine sana’arshi kiwon dabbobin mutane in ya kiwata ma masu hali dabbobinsu sai a biya shi guminsa ,haka dai rayuwa ta kasance har nakai shekaru takwas a duniya lokacin Babana ya hadu da wani mai gidansa a birnin Gombe ,ana kiransa Alhaji ɗan Nasi ,mutum mai kirki ya dauki Babana ya sashi a harkar nemansa ya danka masa dukiyarsa yina zuwa dasu fatauci yina saro masa raguna da shanaye ,Cikin ƙanƙanin lokaci Babana ya fara walwala bayida lokacin zaman rugan mu kuma ,don haka yazo ya ɗauke mu muka koma cikin gari muka zauna a bq ɗin gidan Alhaji Ɗan nasi

Buɗi ya cigaba da samun mu ,Mamata tana ma matar Alhaji aikin gida suna biyanta ,Ni kuma Alhaji ya sani makarantar da yaransa keyi saboda yace yina sona ,lokaci ƙalilan na sanu a makaranta saboda ƙwazo na ,gani dai baƙace amma kowa na sona.

Lokacin da nakai shekaru 10 lokacin babanmu ya gina mana gida a unguwar Alƙali amma bamu tare ba ,saboda wani fatauci da ya samu babanmu zuwa ƙasar Niger ,a wannan rutsutsin turawa suka kawo ma makarantar mu ziyara aka ɗauki hotuna damu yara ,shikenan bayan kwana biyu sai mukaji labarin hotona yina raining larabawa da turawa suna ta saka hotona a shafukansu ma sada zumunta wai nafi kowacce yarinya baƙa ƴar Afrika kyau ,sanadiyyar haka muka samu daukaka na ban mamaki .

Sai me?

Baƙin ciki da ƙyashi sai ya kama matar Alhaji ,ta koremu a gidanta ,muka koma gidan da babana,ya gina mana .mun koma da sati guda mummunar labari ya riske mu Babana ɓarayin shanu sun saceshi kuma mutanen da aka kama su tare sun tabbatar an kashesa .

Rayuwa tayi mana ƙunci ,bamu dakowa a Gombe sai Allah ,kullum kuɗin kyaututtukan da na sama sanadiyyar admiring din da larabawa da turawa sukayi a kan kyawuna shi mukeci muke rayuwa ,ba’a yi wata shida ba kuɗi ya tasamma ƙarayewa ,mamana ta fara sana’ar koko da ƙosai a tasha ,ta cireni a makarantan kudi na koma public school sbd alhaji yaki biyanmun matarshi ta zugashi

Takai ta kawo daƙyar nike zuwa makarantar saboda inataya mamata saida koko da ƙosai da safe
Na zama tantagaryar street child ,da taimakon Allah na gama makaranta na shiga Secondary shima tsintar karatun kawai nike har na kai SS3 lokacin mamata ta daina siyar da kosai a tasha tanayi a kofar gidanmu da yamma Ni kuma in saida awara ,rayiwa dai sai a hankali abu daya ke mun ciwo yanda kare bai taba tare Ni da sunan yina sona ba for that long ,kodon Ni baƙace?????

I dunno !

Har watarana muka kai ziyara rugar mu ,nan yaron mai unguwa ya liƙe zai aureni nikuma na daki ƙasa nace bazan auri jahili ɗan ƙauye ƙazami ba,a ƙarshe ma nace ma mamana mu tattara mu gudo ƙauyen bayan dangi sun mun caaa wai in gode ma Allah lamido yace zai aureni bayan na rigada nayi kwantai.

Mamana tabi raayina muka dawo Gombe ,sai me? Sai ciwo duniya ta tsaya mun cakkk

Tun ina tunanin sauki zaizo har mamana takai sai a kwantar a tayar daga ƙarshe ɓarin jikinta ɗaya ya shanye . A Lokacin nayi mock exams kuma nafi kowa ci a makarantar mu don haka gomnati ta biya mun waec da neco nikuma na siya jamb ,Kuma nayi jarabawa cikin nasara naci cleaned saidai duk jami’ar da nayi applying a arewa sun hanani Admission sai University of lagos.

Don haka na tattara harkar karatu na watsar tunda ba mai sponsoring ɗina ,abun takaici wai saiga ƴan ruganmu sunzo sun ɗauke mamana wai za ayi mata maganin gida tunda na gargajiya yaƙi ,da ban yarda ba amma sukayi mun ƙarfa ƙarfa .

Kuma suka hanani zaman jejin sai bisa condition zan auri lamiɗo.

Nikuma lokacin ƙuruciya da zafin zuciya na kafe bazan Aurèsa ba ,na yarda in koma gidanmu na Gombe in cigaba da rayuwa ta ni kadai ,bayan nadawo gida da kwana uku na kakkabe takarduna na Sakandire wai zanje neman teaching abun dariya

Proprietor din makarantar macece ,sanda na shiga office dinta aka dakatar dani saboda suna magana da yarinyarta wai zatabi jirgi zuwa Lagos ta samu Admission acan .

Samun waje nayi na zauna a réception din kisan awa guda kafin yarinyar ta fito . Yarinya mai fara’a tana ganina ta washe mun baki

“Ke kike neman momy ?”

Gyada mata kai nayi

“School din nan zaki shiga,har yanzu baki gama Secondary ba?”

Girgiza mata kai nayi “Uhm uhm na gama har na samu Admission a uni lag Amma Banda halin zuwa yanzu aiki nazo nema a nan”

“Aiki?wazai daukeki aiki da qualification don secondary ,Saidai in aikin nany kikeso da share share”

Rausayar dakai nayi “To Nagode bari inje in nema ko aikatau ne a gidajen masu hali”

“Bakida iyayene ?”

Cikin ƙosawa nace mata “Eh”

“Allah srki sorry for the lost Allah ya jikansu ,in kin yarda ki bini ,yanzu zaaje a biyamun Flight zuwa Lagos sai mu nema motar haya muje dake a mota nima kinga jami’a da kika samu na samu ,sai In biya maki kudin makaranta da canjin jirgin kinji” murmushi nayi cikin mamakin wautan yarinyar

“Ke za ayi maki fada a gida”

“baza a sani ba ,nidai kawai ki yarda naji Inaso ki zama ƙawata….”

Kaji sanadiyyar haduwata da Lili

Lili ƙawar Amana ,ita tayi mun registration tasamar mana daki muna zaune tare ,kayan lili su nake sawa Ina flexing ,Baban lili babban ɗan kasuwa ne so suna da kudi daidai su,sanda tayi ƙorafin hold up din Lagos aka aiko mata da mota ,batayi kasa a gwuiwa ba ta koya min mota . Lili na so na sosai,she’s humble Batada ƙarya da ɗagawa ga son Addini ,zamana da Lili yasamun wayewa da jama’a saidai zafin talaucin da na ɗanɗana a rayuwa shi ya saka mun azaban son masu kudi ,sannan Ina bala’in son expensive life kaji fa shirmeeee…..”

Har ta kawo nan a zancenta ya rafka tagumi ne yina kallonta ,ankara da tayi da haka yasa ta kai hannu ta daki table ɗin gabansa

“Hunnnn” yaja ajiyar numfashi alamun ya tsorata

“Me kake kallo?”

“Awwn inata kallon yanda queen of beauties na Africa Tasha gwagwarmayan rayuwa ne ,I can’t imergine wannan ɗan ficilin pink lips ɗin naki zai ci towo miyar kuka bai dafe ba ya dawo choco kalar kuncinki ba”

Shagwargwaɓewa tayi kamar za tayi kuka “Kaima tsokana ta kake ko? Da ƙawayena in suka ganni da pink lip gani baƙa sai su ringa zagina wai kamar biri ,Inyi ta kuka …amma da na shiga jami’a naga yanda ake admiring lips ena ….awwwwnnnnnn”

Fashewa da dariya yayi “Kin iya wasa kanki da kanki”

“Karkaga laifina an dade ana kusheni wannan ya sani koyawa kaina son kaina ,I luv meee
Kasan menene idan na kalli madubi na ga kyau na na tuna wuyar da nikesha ,haka zanta masifa a mirror ,nasha cema Lili idan naga mijin da zan aura duk ranar da ya fara zuwa wajena sai nayi masa faɗa ince “Ina ka shige ka bari ana ta kalle maka Ni ,kanacan kana kallon matan wasu …mtseww late comer kawai,kuma sati biyu nikeso a saka mana ranar aure”

Wangale baki yayi kawai ya fashe da dariya “Oh I see wato kinanan kin ƙullaci mijinki”

“eh mana”

“Sati biyu ya isheki ai aure”

“eh mana ai na dade ina jiransa..so banason wani i love You i waye waye ,kawai muyi maza muyi aure mu haifa ƴan biyu biyu sau bakwai”

Dariya ya fashe dashi har yina dukan ƙafan sa a ƙasa

“Na shiga tara haka kike da barkwanci …?”

“Barkwacina yasa akecemun lover girl wannan kuma dalilin yasa nike da tarin maƙiya…. Now is your turn ,ka bani labarin kanka sannan kuma ka fada mun dalilin da yasa ka kawo Ni nan ,kuma ka fada mun me yasa kaimun ƙarya kace zamuzo India inga jikin mamata ,wai ka kawo ta asibiti”

“Bana ƙarya har yau banga halittar da ya taɓa bani tsoro da har zaisa in ɓoye masa wani abu in kasa faɗa masa ba,soooo da gaske ne mamanki na ƙasar nan kuma kafin mu tafi zamuje ki ganta….”

 

 

 

Littafin kuɗi ne
Regular 300#
VIP 500
Special 1k

Zaki biya ta katin mtn ma wannan Number 09065990265

Ko ki tura ma asusun banki na

7782217014
Mohammed Hassana,fcmb bank

Shaidar biya ta nan
09065990265

 

 

Oum Aphnan️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Book 2
Page *B*

Na…
Oum Aphnan ✍

“`Littafin kuɗi ne ,in kika fitar mun dashi kin cutar dani“`

________

Back to top button