Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 4

Sponsored Links

page 4⃣

 

tana fita daga d’akin yarima part d’inta tawuce ko ta kan su jakkadiya batabiba da suke tsugunne suna ta kwasar gaisuwa wucewa tayi tashige bedroom d’inta, wayarta tad’auka takira zinat, zagaye d’akin tashiga yi tak’agara zinat tad’aga wayar ammah har tatsinke bata d’agaba, tsaki gimbiya taja tace itafa matsalata da ita ayi ta kiranta sai taga gama take d’auka,

k’ara Kiranta tayi bugu biyu tad’aga
ko gaisawa basuyiba tace zinat kinajin wancan d’an rainin hankalin wai bazai barni inyi business d’inba

zinat cikin tsawa tace what! shi har ya isa yahanaki kuma kihanu? gambiya tace hmm yoh ke kina tunanin ma zan hanu?

zinat dariya tayi daga chan 6angaren tace wlh innice yanemi yaraina min hankali tuni zan nuna masa iyakarsa ke ak’arshema zan iya kashe auren tunda dama dashi yake tak’ama,

 

gimbiya zaro ido tayi kamar tana gaban zinat tace kirufa min asiri ai wlh ba zan iya rabuwa da shi ba saidai nasan ta inda zan 6ullo masa kibarni da shi.

 

zinat tace toh shikenan nidai ina jira cikin week d’innan inga alert saboda so nake inje ingama komai dawuri indawo,

gimbiya sumayya tace toh shikenan kar kidamu, nan sukayi bankwana.

suna gama wayar gimbiya ummanta takira saida takusan tsinkewa sannan sultana sadiya tad’aga da sallamarta, sumayya ko gaisheta batayiba tace ummana wlh yarima baida mutunci

sultana sadiya a rikice tace nashiga ukku shalele miyake faruwa ne? wlh indai wani cin mutuncin yayi miki zan rufe ido inci masa mutunci shima daga shi har mahaifiyartasa a tafin hannuna suke, kifad’a min abinda yake faruwa.

Sumayya cike da jin dad’in ganin yadda mahaifiyarta take kula da ita, sannan tabata labarin business d’in da takeso tayi da yadda suka kwashe da yarima.

sultana sadiya tace ai bai isaba Indai ina raye ba zaki ta6a yin kukaba ammah kafin ind’au mataki da hannuna kije kifara samun dada kuyi maganar domin nasan ita zata fahimceki sosai inko ta yarda nasan yarima ma zai amince ko da ace baya so.

cike da jin dad’i sumayya tace hakafa za’ayi ummana wlh saisa nake k’ara sonki saboda duk abinda nake so kema kina sonsa.

‘yar dariya sultana tayi tace idan ban so abinda kikeso ba toh nawa zan so? kekad’ai fa ce namallaka, ke nifa ba ma wannan ba wai har yanzu ba wani bayani?

sumayya ta fahimci inda mahaifiyarta tadosa ammah sai tanuna bata fahimtaba tace ummah wane bayani kuma?

ummanta tace ke gidanku ni zakiyi ma kwana-kwana? ke ni ban yarda da keba anya bakiyin family planning?

dariya sumayya tayi tace ni babu abinda nakeyi kuma nima insha Allahu sai na shekara biyar sannan zan haihu.

sultana sadiya tace nashiga ukku ke gidanku wa yace miki ana gudun haihuwa a gidan sarauta?

gimbiya cikin shagwa6a tace ummah kema fa saida kika dad’e sannan kika haihu.

 

ummah tace toh ai nima ba dan ban soba Allah ne bai baniba a lokacin, inma kinsan kina yin wani planning toh wlh kidaina,

gimbiya tace nidai yanzu dai shikenan ummah tunda nace miki babu abinda nake ai sai kibar maganar, ni nafi buk’atar business d’innan bari dai inje muyi magana da dada, ummah ba dai dan ta yardaba tace toh shikenan sai najiki,

 

gimbiya tana gama wayar wanka tashiga tayi bayan ta fito shiryawa tayi cikin shigarta gwanin sha’awa sannan tafito nan kuyangi da bayinta suka take mata baya har suka shiga turakar sarki,

 

lokacin da tashiga parlour dada tana kishingid’e ana mata tausa, nan duk ma’aikatan dada suka gaisheta tare da yi mata kirari, tana yatsina ta amsa musu, nan bayinta suma suka zube suka kwashi gaisuwa a wajen dada, gimbiya zama tayi gefen dada tagaisheta,

 

dada cike da fara’a ta amsamata tace ‘yar albarka meyake tafe da ke Allah yasa ba wannan sarkin ‘yan iyayin bane yayimiki wani abu.

gimbiya k’ara 6ata fuska tayi tace dada kamar kau kin sani wlh k’ararsa nakawo,

dada tace oh ni Asma’u yanzu yaron nan nake ganinsa miskili ashe shima ya iya mugunta.

yanayin yadda dada tayi maganar yaso yabata dariya, gimbiya kallon bayin tayi da suke tsugenne tace dallah kutashi kuba mutane waje kunzo kun saki kunnawa kuna saurarenmu.

dasauri suka rausaya gaba d’ayansu sukace Allah yahuci zuciyar gimbiya mun barku lafiya, sannan suka tashi suka fita.

dada kallonta take cike da mamaki tace sumayya ashe har yanzu kina nan da halinki na wulak’anci?

gimbiya murmushi tayi tace toh ai sune basusan suba mutane waje suyi maganaba sai suwani yi zaune kuma idan nasakar musu fuska sai surainani.

dada sakin baki tayi tana kallonta har saida takai aya sannan dada tace sumayya na haneki da wannan halin ya kamata kizauna da kowa lafiya domin wata rana mijinki shi zai kasance sarkin garin nan.

murmushi sumayya tayi tace toh ranki yadad’e tuba nake, murmushi dada tayi irin nasu na manya sannan tace ina saurarenki me mijin naki yayi miki?

gimbiya gyara zamanta tayi sannan tace dada daman kasuwanci nakeso inyi shine natambayi yarima yabani jari sai yahanani kuma wai ba zanyiba.

murmushi dada tayi tace in banda abinki sumayya me kika nema kika rasa a gidan nan? kuma na tabbata babu abinda zaki nema wajen yarima kirasa domin nasansa da kyauta.

sumayya 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace dada nima inaso indinga cin gashin kaina kuma fa k’awatace zata dinga kular mana da kayan ba sosai zan dinga zuwaba ita zata dinga yi mana komai.

 

dada ganin sumayya ta 6ata fuska yasa taji babu dad’i domin tana son jikartata sosai jininsu ya zo d’aya dan haka tace kikwantar da hankalinki yanzu kiramin shi awaya.

 

 

yarima bayan ya fito wanka yashirya cikin shigarsa ta alfarma ya yi kyau sosai wayansa yad’auko yakira shahid inda yashaida masa yazo suje yarakasa gidan gona akwai abinda yakeso yayi a chan.

shahid yace to shikenan ranka yadad’e daman yanzu haka zan fito daga fada sai kafito muhad’e,

yarima yace ohk sai nafito.

cike da k’asaita yake tafiya duk inda yagifta kallonsa ake cike da sha’awa, ana kwasar gaisuwa yarima yau ‘yan jin kan suna a kansa ko hannunma basu samu matsayin da yad’aga musuba

lokacin da yafito dogawara duk suka taso d’aga musu hannu yayi alamun a’a har ya kusan kaiwa wajen motar sai yaji wayarsa tana ringing tsayawa yayi daga tafiyar da yake yad’auko wayar ganin mai kiransa kamar ba zai d’agaba har saida takusan tsinkewa sannan yad’aga batare da ya ce komai ba yakanga a kunnensa.

gimbiya sumayya jin baiyi maganaba yasa tamik’a ma dada tace gashi kuyi magana,

dada tana kangawa a kunnenta tace toh sarkin miskilanci bakaji ma zaka iya magana,

yarima jin muryar dada da yayi yasa yad’anyi murmushi yace toh me zan ce?

dada tace eh babu fa abinda zakace yanzu dai kazo ina son ganinka.

yarima yana jin haka yasan da wata a k’asa musamman ma da yaga da wayar gimbiya aka kirasa,

dada tace toh ko nima wahalar yimin maganar ake ji? murmushi yarima yayi yace dada yanzu fita zanyi kibari sai nadawo sai muyi maganar.

dada tace sannu babana toh idan ni kana ganin ka rainani toh sai inkira ubanka shi da ya isa da kai sai yasa kazo.

yarima yace shikenan kakus gani nan zuwa ai abun bai kai ga hakaba,

dada tace ina saurarenka, yarima batare da yabata amsaba yakashe wayarsa kallon shahid yayi da yake tsaye yana kallonsa yace shahid bari inje wajen waccen tsohuwar tana nemana tun kan tajamin sharri wajen daddy.

dariya shahid yayi yace toh ranka yadad’e sai ka fito.

 

yarima ko da yashiga baiyi mamakin ganin gimbiya sumayya ba dan haka zama yayi bisa kujerar da take opposite d’in wadda su dada suke a bisa, nan yagaishe da dada cike da girmamawa itama ta amsa masa.

daga nan shuru yabiyo baya chan sai dada tace suhail kaban mamaki wlh,

yarima kallonta yake da mamaki ammah baice komai ba.

dada batayi mamakin shurun da yayi ba saboda tasan halinsa dan haka tacigaba da cewa saboda Allah dan matarka tanason tayi kasuwanci sai kahanata?

yarima harara yawurga ma sumayya sannan yamaida kallonsa ga kaka .

kaka tace kai tambayarka nake shine kayi min shuru?

yarima cikin rashin damuwa yace dada ai nad’auka ta baki amsar abinda nace mata.

dada rik’e baki tayi tace wai kai wane irin mutum ne amsar ma bakaji zaka iya bani?

yarima shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba chan kuma sai yace toh ai nace mata ban aminceba saboda babu abinda narageta da shi kuma indai kud’ine zan iya bata ammah ban yarda tayi kasuwanci ba ai sai taja mutuncina yazube a idanun mutane, daka ma gimbiya tsawa yayi yace ke ba haka nace mikiba? ??

Gimbiya ta tsorata da tsawar da yayi mata ammah sai tadake tad’auke kanta daga kallonsa.

dada ta6a hannu tashiga yi tace nashiga ukku yanzu a gabana kake mata tsawa ai da had’emu kayi ni da ita kadokemu sai inga kamar zai fi maka sauk’i.

yarima yace Allah yabaki hak’uri ammah dai yakamata kiduba kiga maganar nan bai daceba ace tadinga yawo tana chakud’a cikin maza,

kaka kallon sumayya tayi da taci face sannan tamaida kallonta ga yarima tace ai tace ba sosai zata dinga zuwaba abokiyar kasuwancin ce zata dinga kula da komai dan haka inaso kabata kud’in inkuma baka iya bata sai inkira ‘ya’yana su subayar tunda su na isa da su.

Yarima baice komai ba yad’auko cheque yacike mata yamik’a mata yace gashinan kuma duk abinda yafaru kiyi kuka da kanki.

dada tace insha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi, kuma dan bak’in ciki baka ji zaka iya bata cash, yarima suhail mik’ewa yayi yace dada so kike kijasa min ciwon kai, bari intafi ana jirana.

dada tace ka dai ji dashi marar mutunci kawai,

yarima murmushi yayi yace na barki lafiya ‘yar tsohuwa, sannan yaficce yabar turakar.

Gimbiya sumayya tana ganin yafita tatashi tahau tsalle da murna daga k’arshe da rungume dada tace nagode sosai ranki yadad’e Allah yak’ara tsawon rai wlh kin gama min komai.

 

dariya dada tayi tace ni sakarni ja’irar yarinya kawai ammah a gaban yarima bi kikayi kika marairaice kamar da gaske.

itama gimbiya dariya tayi tace ai wlh dan ina neman abu a wajensa saisa nabarsa yaci min mutunci son ransa ban tankaba.

dada rik’e ha6a tayi tace toh daman ashe bashi kad’ai yake rashin mutuncin ba harda ke, toh wlh kigyara domin aure ba abun wasa bane kuma kidaina ganin nasashi yabarki kiyi toh wlh kikama kanki kirik’e mijinki kar kififita kasuwanci akan aure kuma dan kince k’awarki zata dinga kula da komai saisa nagoyi bayanki.

gimbiya sumayya tace naji dada zan kula, nagode sosai.

mik’ewa sumayya tayi tana gyara alkyabbarta sannan takwala ma jakadiya kira, dagudu jakadiya tashigo tare da zubewa k’asa tace na amsa kiranki ya shugabata,

kallonta gimbiya tayi tace kuzo kucigaba da aikinku na kula da dada , jakadiya tace toh ranki yadad’e.
sannan gimbiya tayi gaba tana cewa kakus na wuce, dada tace toh sumayya

gimbiya sumayya tana fitowa nan bayinta suka mik’e suka take mata baya takoma 6angarensu.

 

Yarima suhail yana fitowa fuskarsa a d’aure yakar6i key d’in mota hannun driver dasauri d’aya daga cikin dogarawansa yabud’e masa motar yashiga.

shahid ganin yarima bai ko kallesaba kamar baisan da shiba ya shige mota dan haka shima yaje yabud’e yashiga yana cewa yau dakanka zaka ja mu?

yarima baice komaiba yaja motar yabar gidan, gudu yakeyi sosai da motar shahid yanata yi masa magiya akan yarage gudu ammah yarima kamar ba dashi ake ba.

cikin k’ank’anin lokaci ya isa gidan gona horn yashiga yi dasauri maigadi yazo yahangame masa gate yashiga da motar yana yin parking fitowa yayi yashige ciki bai ma kula da gaisuwar da ma’aikatan gidan sukeyi masaba.

shahid numfashi yake maidawa cike da jin dad’in sunzo lafiya domin bai kawo ma ransa zasu iso lafiya ba, daga k’arshe dai yabud’e motar yafito nan yatsaya saida suka gama gaisawa da ma’aikatan sannan yawuce cikin gidan.

A parlour yatarar da yarima kwance saman kujera idanuwansa a lumshe ya yi matashin kai da hannuwansa,

shahid tsayawa yayi gefensa yace wai yarima meyake faruwa ne naga tun da kadawo daga kiran da dada tayi maka fara’arka tagushe?
kuma dan mugunta kadinga gudu da mu toh idan kai bakason ranka toh ni inason nawa.

yarima idanuwansa a lumshe bai tanka masaba.

shahid tsaki yaja tare da zama yace kai nifa matsalata da kai kenan sai anayi maka magana kashare mutane kamar ba da kai akeba.

shidai yarima suhail baice komai ba saida yayi kusan minti biyar sannan yabud’e baki dakyar yace shahid wlh sumayya batada mutunci yanzu saboda Allah duk mutuncina ammah tana nema tazubar min dashi.

shuru yayi nad’an lokaci sannan yacigaba da cewa ni duk abinda takemin ban ta6a kai k’ararta ga kowaba ammah ita da mun d’an samu sa6ani toh sai kowa ya sani, ya za’ayi matar aure kuma matar yarima kamarni ace wai nabarta tana business har dada tagoya mata baya ai sai aja mutane suzageni.

Shahid cikin ransa yace ai indai wannan marar mutuncin ce zata aika domin bazan ta6a mance rashin mutuncin da tayi minba ranar da nazo wajenka.

chan kuma sai shahid yace kayi hak’uri kasan mata sai da hak’uri kacigaba da hak’urin da nasanka da shi.

yarima bud’e idonsa yayi da suke a lumshe yayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace shahid kallon da akemin nine macuci cutar sumayya nakeyi babu Wanda yata6a tambayata yadda zaman aurenmu yake ammah wai ni zan saki matata tadinga yawon kasuwanci garuruwa.

shahid cike da tausayi yake kallon abokin nasa domin yasan ba’a ta6a jin matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yau shine yake fad’a masa abinda yake damunsa tabbas yasan ba k’aramin 6ata masa rai akayiba, shahid yace dan Allah yarima kacigaba da hak’uri kadinga yi mata fatan alkhairi kar kad’auki mataki insha Allahu dakanta zata daina abubuwan da take.

Yarima shahid maida idanuwansa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa,

ganin haka yasa shahid yatashi yafita yana zagaya gidan gonar….

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

 

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_Sak’on gaisuwata agareki aduk inda kika kasance my Aysha hak’ik’a ina yinki irin sosai d’in nan, ina tayaki murnar sabon novel d’inki da zaki fara mai suna *K’AUNACE SILA* Allah yasa afara lafiya agama lafiya my dear, Happy Birthday in advance_

 

_*Ba zan gaji da sadaukar muku da page ba Masoya ina jin dad’in comments d’in da nake samu daga gareku a group’s da masuyimin ta pc wlh ina yinku over, wannan page d’inma kuje da shi nabakushi a kyauta sis Nerja’art tana sonku irin sosai d’in nan*_

 

Back to top button