Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 35-36

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*35&36*

 

 

…….kasa mgn Ammi tayi tana dai tsaye bakin k’ofar d’akin tana bin Amaan da kallo tana fatan Allah yasa ta sami lafiya!…kodai ban farka bane?”ta fad’a cikin sanyin muryarta tana mutsutstsuka idanuwanta tare da k’ok’arin sauka daga saman bed d’in”Amaan! da sauri ta d’ago kanta suka had’a Ido da Ammi”saita fasa sauka daga saman bed d’in “Alhamdulillah! da Alama kin warke Amaan ko?”tsuramata fararen kyawawan idanuwanta tayi tana girgiza kanta tace”wacece ke dan Allah?”kamar na sanki a mafarki sunanki Ammi”harda hamma nah da Abdallah”dan Allah kodai mafarkin nakeyi ne har yanzun?idan kuma bashi bane to Ina mommy da daddy dasu hamma yusuf??? ta k’are maganar tana sakin kuka”kinga ba mafarki kikeyi ba”hamman ki da kike mgn shima ba’a mafarki kika san shiba da gaske ne yafaru, Abinda kike zaton mafarki ne….kasa mgn Amaan tayi ta rakub’e gefen bed d’in tanata kalle kalle jikinta na rawa”Ammi dake kallonta tace” yah salam! ki nutsu bara na kira shariff d’in kuyi mgn bazamu cutar dake ba kinji ko?”shiru dai tayi tana share hawayenta tana kallon kayan jikinta da zobban dake a yatsun hannunta”Atake ta tuna lokacin daya bata su harda chacoolates”saidai ta d’auka har yanzun mafarki takeyi… Ammi na fitowa daga d’akin shariff na sakkowa k’asan zai tafi masallaci da farar jallabiya Ajikinsa”yana yin yadda yaga Ammin saida gabansa yafad’i yama d’auka ko wani abu yasami Amaan d’in”shariff Alhmdllh Amaan da Alama ta warke”saidai tak’i yadda damu dukta rud’e”kazo kamata bayani kota sami nutsuwa”kasan dole ta damu taga wad’anda bata sani ba”dukda dai yadda ta nuna tasan kowa na gidan nan a mafarkinta”yanzun haka kiraye kirayen sunayen y’an gidansu takeyi….dam! k’irjinsa yayi wani irin mugun bugawa”be furta komai ba ya tamke fuska yanufi cikin d’akin”Ahankali ya shigo da sallama cikin k’asaitacciyar muryarsa….wata iriyar fad’uwar gaba ce ta ziyarci k’irjin Amaan sakama kon lallausan muryan shariff dataji”ta d’ago kanta jikinta na wani irin b’ari idanuwanta da nashi suka sark’e”Atake taji yamata kwajini musammun daya d’aure fuska….saita lumshe idanuwanta tana sauke Ajiyar zuciya”murya na rawa tace”dan Allah inane nan,kuma suwaye ku danayi mafarki daku,daga k’arshe Ina iyayena dazan ganni Anan???duk ta tambaya ajere batare data yadda ta koma gigin kallon k’wayar idonsa ba”shi kuwa tsaye yayi yazuba mata Ido sbd gaba d’aya bbu Abinda ta sauya harta muryarta irinta wacce yafara sanintane da ita….kuka ta fashe dashi”yadako mata wata razananniyar tsawa yana fad’in dallah malama yimun shiru”Anbfad’a miki muna cutar da wanine balle mufara akanki?”ki nutsu ki tuna meya faru last 4 month”ranar friday on 11 /5/ 2022″yana fad’in hakan yazaro wayarsa yafara neman layin mus’ab”Adaidai lokacin Ammi ta shigo tazo gefenta ta zauna ta kama hannunta tana rarrashinta”sai gab da zata tsinke mus’ab yad’aga yana fad’in ranka yadad’e yayan *Amaan shariff*! gabanta yafad’i sbd taji me mus’ab yafad’a “saita tsare shariff da Ido”shi kuwa tab’e baki yayi yace”ada kenan Amma banda yanzun”sanin kankane bana kalan dangi” yanzun haka ta sami lafiya”tana neman tayarwa Ammi nah hankali da kanta”idan bbu damuwa kazo tare da mlm bayan sallar isha’i kuyi mata bayanin wacece ita da yadda naganta”yana fad’in hakan ya yanke wayar”ya d’ago kansa suka had’a Ido da ita “wata uwar harara ya wurgo mata yana fad’in Ammi ki k’yaleta kije kiyi sallah ai yanzun tana hayyacinta”daga haka yanufi k’ofa…..hamma! banza yamata yaja tsaki yafita sbd tabashi haushi sosai”Ammi ta girgiza kanta tace”ki bari suzo Ayi mgn zaki fahimci mu masu kaunarki ne Amaan “Amaan kuma?”Eh sunan da hamman ki shariff yasaka miki kenan”nifa sunana *salma*”to shikenan kije kiyi Alwallah kizo kiyi sallah kinjiko?”bara nashiga toilet”daga haka Ammi ta mik’e tsaye tashige bath room “Amaan ta sauke Ajiyar zuciya tana hango kyakykyawar fuskarsa Acikin zuciyarta”saidai taji mugun shakkarsa”ta turo baki data tuna hararar daya mata”tambayar kanta takeyi Ina su mommy da sauran y’an gidansu,kuma nan inane??”tana wannan tunanin Ammi ta fito”hakan yasa itama Atsorace ta tashi ta shiga bathroom”sbd gani takeyi kamar cutar da ita zasuyi….cak ! tunaninta yatsaya data tuna da kalaman shariff game data tuna Abinda yafaru last 4 month…. Atake komai yadawo kanta”tasan itadai ta fito daga cikin get d’in gidan su ta hau nafef”daga nan sai tayi mafarkin su hammanta sai yanzun data farka”tana kukan da batasan dalilin yinsaba tana Alwallah”bayan ta fito ta kabbara sallah….bayan sun gama sallar Ammi taci gaba da Azkhar “Amaan kuwa kasa yin wani Azkhar tayi”tana rakub’e gefe, gaba d’aya zuciyarta ta rikice da wasi waasi…. idanuwanta cike da k’wallah “Abdallah yashigo cikin d’akin da Alama daga masallaci yake”koma rikicewa tayi data gansa sbd shima tasan Akwaisa Acikin mafarkin datake ganin tayi”Ammi pls ki bani kud’in dana baki Ajiya”ke kuma Anty Amaan kije ki d’auke teddy d’inki inji yaya sadeeq kin barta a parlour”k’in mgn Amaan tayi saidai kuka data fashe dashi”kaga dan Allah jeka parlourn gani nan”bece komai ba yafita yana mamakin dg yamata mgn sai kuka…..bayan sallar isha’i shariff yashigo cikin d’akin fuska a gimtse ko kallon inda take beyiba yace”Ammi kizo gasu nan A parlour”to shikenan kaje gani nan zuwa…..yanata cin magani yace”niba sai najeba kuje yamata bayani da zata wani damu mutane da wasu koke koke”Aida kukan jini tayi sannan zan san bata yadda damu ba…..kallonsa kawai Ammi keyi dan ita dariya ma yabata”tasan duk wannan masifar da fad’an dayake ma Amaan k’arfin haline da zafin zuciya”zai huce daga baya”bata samu damar yimasa mgn ba yafita kamar zai tashi sama “ita dai Amaan na zaune duk tana sauraronsa tana kallon sa”tasha Alwashin idan Ansanar mata koma miye zata gaya masa mgn itama son ranta dan bata d’aukar raini da wulakanci….tashi muje! cewar Ammi”bbu musu Amaan ta tashi tsaye da hijab d’in datayi sallah Ajikinta suka fita”nanma da suka fito ta kalli parlourn dasu mus’ab da mlm ke zaune koma rudewa tayi domin duk ta sansu”kan carpet ta zauna tayi k’asa da kanta ta gaishesu”mus’ab dai nata kallonta yakuma fahimci tabama Abokinsa haushi”sallama mlm yyi bayan sun gama gaisawa da Ammi Anutse yace “Alhamdulillah ! muna godiya ga ubangiji me iko Akan komai buwayi gagara misali”dayake jarabtar bayinsa yakuma yaye musu bisa Adalcinsa”muna tayaki murnan samun lafiya”ki godema Allah da yallab’ai shariff “ranar juma’a 11/5/2022 da yamma…..yashiga sanar mata da komai”tun kafin yakai Aya azancensa Amaan na kuka ta dakatar dashi gun cewa”duk nasan Abinda yafaru”na d’auka mafarkine Ashe da gaske ne?”tabbas Anty zabba’u kishiyar mommy nah itace tamun wannan Asirin sbd ta rabani da yaya Nasir”wanda ni banama sonsa….ta k’are maganar tana matsowa ta fad’a jikin Ammi tana fad’in Ammi bayanke banida wata uwa Ayanzun”dake da mommy nah duk matsayinku guda”ta d’ago kanta ta kalli mus’ab “dan Allah yaya mus’ab kabama hamma nah hak’uri yayi fushi dani sosai”gaba d’aya kasa mgn sukayi suna binta da kallon tausayi”ta share hawayenta tana fad’in zan sanar daku yanzun wacece ni da kuma Ahalinah! saidai bazan iya bayar da tarihin rayuwata ba bayan hamma baya nan wajen”ta k’are maganar tana jin tsananin k’imar shariff da girmansa shida mahaifiyar sa Aranta”banida bakin yi muku godiya sai Addua”Allah yasaka muku da Alkhairi Ammi “Ameen Amaan….Au salma ko?”cewar Ammi tana mata murmushi “ita dai tayi k’asa da kanta dan wata iriyar kunyar Ammin takeyi sbd tuna irin tab’arar data dingayi Abaya….tashi kije hamman yana parlourn sa ki kirashi kuzo sai muyi mgn kar Atsayar da mlm ko?”babu musu Amaan ta mik’e tsaye cikin nutsuwa tana nufar upstairs….shariff na zaune a parlourn yana ganin komai ta cikin CTV camera daya saito a laptop d’in sa”gaba d’aya jin zuciyarsa yakeyi wasai bbu b’acin ran da Amaan ta hadda masa”yana ganin ta mik’e tsaye ya rufe laptop d’in yakama dannar waya zuciyarsa na tsananta bugawa”Ahankali ta turo k’ofar”tamkar besan da zuwan taba yad’ago kansa suka had’a Ido “d’aure fuska yayi cikin shan k’amshi had’e da basarwa yake fad’in karki k’araso! ki kowa wajen wad’anda kika yadda dasu….gabanta yafad’i! taji kamarma karya dena mgn”sbd muryarsa ba k’aramin burgeta taji tayiba”saita girgiza kanta bata fasa k’arasowarba”saidai tana k’ok’arin duk’awa gabansa saiya kauda kansa gefe”ya aza hannunsa guda saman kujerah yayi tagumi dashi”bataji haushiba tadawo inda ya juya ta tsugunna”cikin sanyayyar muryarta tace”hammahhhhhhhh! har cikin jini da jijijyarsa yaji sunan yakai masa”karkayi fushi dani pls”yaka mata kamun uzuri”ko wacece ta tsintsi kanta Ahaka dole ta shiga rud’ani”dan Allah kayi hak’uri kayafemun”banida wani yayan daya fika”dakai da hamma yusuf duk d’aya kuke Awajena”banida bakin yimaka godiya sai Addua”bansan yaya zan misalta maka irin farin cikin danaji daka ceci rayuwataba”ka rik’eni bisa gata da kulawa”cina,shana ,tufatarwata duk Akan”bayan bakasan wacece niba musammun da zamani ya lalace”sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in bazan tab’a yafema Anty zabba’u ba sbd itace sanadin komai….ta k’are maganar tana aza kanta gefen hannun kujerar tana kuka….ya isa haka! tashi ki zauna muyi mgn “bbu musu ta d’ago kanta ta zauna k’asa kan carpet”handcheef yazaro daga gaban Aljihun jallabiyar sa yamik’a mata batare daya yi mgn ba “turo d’an bakinta gaba tayi bata yadda ta kalli k’wayar idonsa ba ta nuna masa fuskarta”Alamar shi yagoge mata”sbd gaba d’aya jitakeyi yacika mata wajen”ga wani irin kwajini daya mata”gaba d’aya k’amshin jikinsa dana cikin parlourn da sanyin da Akeyi duk sun sakar mata kasala da mutuwar jiki”sarai ta fahimci ba k’aramin MISKILI NE ba”Amma saita basar sbd itama indai miskilancine ta iya”kallon hannunsa tayi be fasa mik’a mata ba”saita basar ta nuna kamar bata ganiba”saima cewa tayi hamma kazo muje su mlm da yaya mus’ab na jiranmu”daga haka ta mik’e tsaye tana share hawayenta da tafikan hannayenta”miskilin yatab’e baki beyi mgn ba yamik’a tsaye yabiyo bayanta”ita kuma tana daga gaba tana tuna idan sukayi fad’a kota masa laifi irin yadda sukeyi”tayi d’an murmushi tana jin sautin takunsa Abayanta”sai tak’ara sauri ta rigashi sakkowa k’asan”mus’ab na ganinsu yakama murmushi yana fad’in Amaan shariff da hammanta”kai yaya mus’ab harda zolaya?”harararta uban gayyar yayi ya zauna kan kujerah “jeki kira Ammi tana daki”cewar mus’ab yana b’oye dariyarsa”bayan wucewar Amaan cikin tsokana yace”kaga Abokinah saina sanarwa mansoor yazo suyi mgn….wani irin mugun kallo shariff yajefesa dashi batare daya furta komai ba”mus’ab yakama murmushi, dama tsokanace kawai yayi sbd yaga yaya shariff zaiyi”Ammi ta fito rik’e da hannun Amaan,ta zauna kan kujerah ita kuwa Amaan k’asa kan carpet ta zauna”tanaso ta kalli shariff tana jin tsoron kallon cikin k’wayar idanuwansa”sai kawai tayi k’asa da kanta tana fad’in sunana salma sulaiman! ni haifaffiyar garin Adamawace”mahaifiyata bafulatane ce gaba da baya”kowa da kowa nawa na’acan”Hjy bilkisu sunyi Auren saurayi da budurwa itada Alh sulaiman”sunjima kafin su fara haihuwa” yusuf shine na farko sai sulaiman (khalifa) daga shi sai sadeeq “sannan salma Autah”wacce tasami bala’in gata a wajen mommynta sbd ita kad’ai ce y’a mace data mallaka Aduniya “tun mommy na goyon hamma khalifa daddy yak’ara Aure sbd masifar mahaifiyarsa wai mommy ta mallakesa”tun bayan ya Auro zabba’u Hjy bilkisu tadawo zaman hak’uri Agidan”tana kuma k’ok’arin masa biyayya da kyautata masa saidai matarsa ta janye hankalinsa Akanta wajen yawon bin bokaye da y’an tsubbu”harta kai duk ranar kwanan Hjy bilkisu sai jini yazo mata”sauran cikunnan data samu daga bayan khalifa kawai rabone da Allah ya kaddara”sbd sai suyi shekara biyu be kwanta da itaba”ita kuwa zabba’u sai Allah yasa ta dinga haihuwar y’ay’a mata masu kama da ita”gashi tunda tazo gidan d’an Abin hannunsa yarage”dan dama bame kud’i bane Akwai rufin Asiri dai princepale ne”lokacin da Hjy bilkisu ta haifi salma k’arara zabba’u ta nuna jin zafinta”sbd yarinyar tafi kowa kyau Agidan “gashi dangin Hjy bilkisu masu kud’i ne yayanta ma yakaita makka”komai yimata sukeyi bama a had’asu da zabba’u wajen wadata”Ahaka rayuwa ta Lula yusuf da khalifa da sadeeq duk sunyi nisa a karatu”salma ta taso cikin gata “hakan be hana Abata tarbiya ba”Allah yamata farin jini duk inda zata shiga sonta Akeyi ga k’ok’arin tana dashi a skul”tun tana y’ar 13 yrs tayi saukar Alkur’ani me girma”shi kansa daddynta sonta yakeyi”da yayunta”zabba’u “saida ta haifi y’ay’a mata biyar Agidan sannan ta dena haihuwa” shamsiya,hafsat,sumayyah,Fatima,Amina….. shamsiya yanzun haka tanada 27 yrs ita dake babba”tayi NCE har yanzun batayi Aureba bbu tsayayye sai kai kanta inda Allah be kai taba takeyi”wacce ke bimata hafsat nada 24 yrs”sai sumayya nada 20 yrs”itace tsarar salma”duk yawan su Acikin gidan kullum Aiken gudane ,shine salma tazo”ita kuma bata kula maza”namiji guda d’an yayar Alh sulaiman me suna nasir kawai take kulawa”shima ba wani sonsa takeyiba kawai daddy ne keson ta Auresa”Nasir babu laifi mutumin kirkine yanada kyau da iya d’aukar wanka”yayi degree nasa yafara Aiki yana kuma kasuwanci”tun salma bata sakashi a rantaba harta fara sakashi”aka fara zancen zai kawo kud’i Asaka rana”daddy ya Amince Amma yace” sai ta Ida kammala NCE nata ayi biki sbd tana gab da kammalawa”kuma harda bikin hamma yusuf za’a saka…..tunda zabba’u taji wannan magana hankalinta yatashi tana ganin yazata bari salma tayi Aure ga nata y’ay’an tulke Agida”kuma zata Auri wanda zata huta”tazo tana d’agawa su sumayya kai”ta hak’ura da finta da mahaifiyar salma tayi Amma bazata hak’ura salma tafi y’ay’an taba”saita famtsama bin bokaye sbd Ajuyar da hankalin Nasir dana mahaifiyarsa Hjy hauwa sbd suce Anfasa”Abin mamaki sai taga Ankawo kud’in gaisuwa dana neman Aure”Aka kuma tsaida sati na sama za’a saka biki….. Ayau friday tunda wuri salma ta shirya sbd zataje gidan kawu bello”babban yayan mommy d’inta”sai tsokanarta sadeeq keyi tanata shagwab’a mommy na masa fad’a “ta d’akko mayafinta da hand bag nata ta fito ta musu sallama”tasan dai ta fito daga gida kuma ta tsayar da nafef ta shiga ciki daga nan bata koma sanin komai ba saidai ta farka Ayanzun…..wannan shine tarihin rayuwata Atak’aice”cewar Amaan tana share hawayenta… tunda…✍️
wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button