Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 63

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*63*

Washegari da wuri ta tashi ta shirya 11 take da test din but tanason fita da wuri zataje wajen inna ta nuna mata sabuwar mota da ta samu, ta soya egg da bread tayi breakfast Bata Jira matar gidan ba saboda da alama Basu tashi ba, 9am ta kammala shirinta tana jiran ya fito su gaisa ta wuce tana zaune tana dan Duba books nata ya tura kofa ya shigo bakinsa dauke da sallama qamshin turarensa ne ya fara cika falon ta d’aga fararen idanunta suka fada cikin nasa Wani lallausan murmushi ya sakar mata sanye yake da fararen shadda gezner sai sheki suke black Fendi sandal shoes da black leather wrist watch ya saka , cikin takunsa na kasaita ya karaso inda take ya zauna ” morning baby girl”
“Good morning my Yaya dafatan ka tashi lafiya”
“Alhamdulillah hop u too..wannan fara’a dis early morning Allah yasa ba yaudarata zakiyi ba ”
Lumshe Ido tayi ta sake budesu tana kallonsa ta langabe Kai tare da cure baki ya zuba mata idanu tayi matukar kyau a Hakan ” umm…dama so nake naje na nunawa inna motata ta min adua”
“Ehen…I sense it dama nasan wannan murmushin na yaudara ce ”
“Yaya… bahaka bane fah ka manta Ina da c.a ”
“Yeah..I know but ki bari sai da yamma sai muje wajen inna tare yanzu ki wuce school kawai kin manta last time tayi fada tace Ina barinki kina fita anyhow ” tura baki tayi cike da shagwaba tana make kafada tana cewa

“Um..um nidai ka bari na tafi yanzu nasan baratayi fada ba ai tasan mota naje nuna mata ba Wani Abu bah…” ta karasa maganar tamkar zatayi kuka, ” come here…”
Ya furta Yana Bude hannu alamar ta taho wajensa, Babu gardama ta shige jikinsa ya rufe tana shakar qamshin turarensa ya d’aga fuskarta suna kallon juna yace ” please kiyi hakuri ki bari sai na dawo office sannan na kaiki ok … please don’t say no please..” Kai ta gyada masa, ya kwantar da kanta bisa kirjinsa ” good girl..haka nake so thanks”
Lamo tayi a kirjin nasa tana son kasancewa cikin wannan yanayin Yana saukar mata da nitsuwa Koda tana cikin bacin rai ne, ” by what time zaki tafi school”
” By 10 cos 11 ne zamu shiga ” “ok ki bari 10:30 don banason ana yawan kallon ki , Fauzan zaiyi dropping dina yanzu sai ya dawo ku tafi zai jiraki ya dawo dake” gyada Kai tayi alamar gamsuwa , Yana matukar kaunar yarinyar Yana Jin tamkar bazai iya rayuwa Babu hajjo ba tabbas yayi zurfi cikin son Hajjo Wanda Allah ne ya jarrabesa da Hakan. Sauke numfashi yayi Yana raba jikin nasu
“Zan tafi baby girl”
“Kayi breakfast ne ?”
Lumshe Ido yayi ” abin mamaki Mai mata 2 zai fita da yunwa ” ware Ido tayi ” meyasa?”
“Failuzaa tana can tana bacci ke Kuma kin shirya zaki fita Baku bani abinci ba” tabe baki tayi tare da kwafa tace ” ni zan baka abinci matarka tace na mata shishigi”
“Toh meyasa kika tambaya”
“Sorry…” ” Ok am going u take care of yourself” shiru tayi sai Kuma tace ” yanzu haka zaka fita baka karya ba ”
“Toh ya zanyi hearty …
“Ka tsaya na hada Maka tea ”
“I’ll love that gaskiya cos yunwa nake ji sosai ”
tausayi ya Bata Kai wasu mata Basu da tunani ya zatayi tana bacci har mijinta ya shirya ya fita, tashi tayi ta fice Yana kallonta Yana Jin dadi wannan ba sabon Abu bane a wajensa fita office da yunwa haka Failuzaa take Bata son tashi da wuri har ya Saba a office yake breakfast, Sauke numfashi yayi she is so nice tasan hakkin miji Kuma ta iya kula da miji.

Kwai ta tsaya ta soya masa ta dauki bread dake Basu rabuwa dashi ta hada kayan tea bisa tray dama akwai tea din da ta tafasa Wanda yasha hadin citta da kanumfari sai strawberry Lipton din Akbar, cikin Yan mintuna ta hada komai ta Kai falon ta dawo ta dauki sauran ta koma ta ajiye a kasa tasan Bai cika cin abinci bisa table ba . Kallonta kawai yake ta zuba masa tea cikin mug cup tana dan juya spoon ciki qamshin dake tashi ne yasa ya leka cup din yace
“Wannan qamshin fah ?
“Spicy tea sunansa ”
ta fada cikin wasa tana murmusawa yace ” can’t wait to sip gaskiya wannan qamshin is something else ”
ta Bude plate din din kwan da ta soya tuni Wani sabon qamshi ya daki hancinsa ya dawo kusa yace ” can’t wait any longer hajjajo ”
Murmushi tayi ta ajiye cup din ta since bread din ta shirya bisa plate nan ya fara ci Yana lumshe Ido gaskiya Allah ya mata baiwan sarrafa abinci, sai da yaci kusan slice 3 kafin ya d’aga Ido ya kalleta ” what about you ”
dariya tayi ” sai da ka koshi zaka tuna dani, wato yau ko feeding din baka nema ba ”
“Zolayata zakiyi koh,.. am hungry ne wallahi jiya banci komai ba haka na kwanta ”
Cike da mamaki take kallonsa ” but why…?

“Uhm..kind of miyar taushe ta dafa ni Kuma banso ” ” but Yaya meyasa baka fadamin ba ko indomie da na dafa ma ” murmushi yayi ya dauki cup din tea ya dan Yi sipping ” kinsan nayi tunanin Hakan lokacin da na shigo Kuma Ina ganinki na manta meya kawoni ”
“Ka iya zolaya ”
” am serious wallahi a duk lokacin da nake tare dake nakan manta da duk wasu matsalolina , u are my happiness and the best gift from almighty ”
Shiru tayi tana kallonsa tana Jin dad’in kalaman nasa , ya gama ya ajiye cup din Yana hamdala kafin yace ” ki hadamin tea din zan Kaiwa Fauzan da bread din”
“Toh kodai a soya masa egg ”
“No..sauri nake Ina da meeting banason ya fita empty stomach ne kawo tea n bread din idan yaso sai ya Siya abinci anjima a eatery ” “is ok ”
ta hada kayan tea din ta koma kitchen ta dauko Wani cup tana fitowa ne suka Hadu da Failuzaa sai buga hamma take ,
“Anty amarya Ina kwana , wannan kwalliya haka sai Ina ”
“Kin tashi lafiya ya meenal, school zan tafi ”
“Owk.. wallahi kin ganni nagaji sosai jiya kamar zan kiraki ki kawomin dauki ”
“dauki Kuma ?” Hajjo ta tambaya cikin rashin fahimta ” ehh..jiya mijinki kamar zai kasheni nace me kika bashi yasha ne irin wannan karfi haka gaba d’aya bamuyi bacci ba sai asuba ana Abu guda ” dakyar Hajjo ta hadiye Wani miyau Mai dacin gaske ta kirkiro murmushi tace” yayi kyau haka akeson namiji ai ” Wani dariya Failuzaa ta kyalkyale tayi gaba tana dariya irin ta rikakkun Yan duniya, hajjo ta tsaya Jim…tana nazarin kalaman nata wato shiyasa Bata fito ta hada musu breakfast ba lallai Ayman namijin duniya ne shine idan suna tare zai nuna mata duk duniya Babu kamar ta ashe karyane , a hankali ta d’aga kafa ta fara tafiya cikin rashin kuzari ta shiga ta ajiye masa ta koma ta zauna Yana bin fuskarta da kallo ” lafiya…meya faru?
“da Wani abu ne ?”ta bashi amsa Kai tsaye
“No..as in your mood bahaka kika fita ba meya faru kin Hadu da Failuzaa ne ?”
“Idan na Hadu da ita sai me?” Ya Gane tana cikin bacin rai donhaka ya tashi ya dauki kayan ya fita.
Kwanciya tayi bisa kujera tana runtse Ido tana Jin zuciyarta Babu dadi Kai kishiya kishiya batayi ba yanzu tazo ta Bata mata rai cikin Yan mintuna, wata zuciyar tace toh ba matarsa bane dama me kike tunani kinsan dole Wani abu ya shiga tsakaninsu tunda ke kin hanasa ita kuwa tana masa abunda yake so, ya Dade tsaye a kanta Bata sani ba idanunta a rufe tana tunani.
“Baby girl what’s wrong “…. Firgit..ta tashi ta zauna tana daidaita nitsuwarta tace ” Babu komai” zama yayi ya rike hannunta ” please tell me meya faru tace Miki Wani abu ne”
“Nifa ban Hadu da matarka ba ”
“No…u aren’t saying the truth gashi na sameta a kitchen” ware Ido tayi
” Kace mata me?
” Na tambayeta me ta gaya miki ta Bata Miki Rai ”
“But meyasa zakayi Hakan nidai bana so please ”
” Wasa nake Miki ban tambaya ba but u tell me” ” Babu komai fah ” d’aga kafada yayi
“Well… since you insist, ni zan tafi Allah ya Bada sa’an test idan ya ajiyeni zai dawo ya daukeki da motar ki, sannan idan kin dawo ki mana lunch zan turosa ya karbo min ”

“Ok me zan dafa Maka?
“Fried rice and chicken sai zobo irin Wanda inna takeyi, idan Baki iya ba kuma ki kirata ta koya maki ” hararinsa tayi cikin wasa tace ” zobon ne ban iya bah , toh duk Wanda kake Sha a gida ni nakeyi ” murmushi yayi ya tashi Yana gyara links nasa yace ” toh ni na tafi ”
“Allah ya tsare ya Bada sa’a a dawo lafiya Yaya nah ” lumshe Ido yayi cikin Jin dadi yace ” Ameen….matata nagode” har bakin kofa ta rakasa ganin yayi hanyar kitchen ta juya ta koma part nata ta cigaba da karatu.

Fauzan yayi parking cikin harabar school din dai dai nan Ummeey ta sauko daga cikin motar gidansu duk mutanen dake wajen sun kurawa motar Ido duk da cewa dama makarantar ta y’ayan manya ne kowa naji da naira ga motoci birjik Amma wannan Lambo din ta dauki hankulan mutane saboda baa cika ganinta a nan gida Nigeria ba sai kasashen turai Wanda yawanci manyan celebrities Wanda duniya tasansu sune suke shiga irin wannan motar, hajjo ta fito cikin dogon jilbab nata har kasa tana sanye da fashion rubber shoes da fararen eye glasses na Dior tayi kyau sosai tana rataye da mini skul bag kallo d’aya zaka mata ka fahimci cewa tana cikin kwanciyar hankali, naima ce ta fara murmushi tana cewa ” oyoyo amarsu masu dad’in sha’ani”
Ummeey ta tabe baki tace ” aifahh..kina ganin yadda yarinyar nan take Wani shining kodai har an kunsa Miki cikine ”
Hararinta hajjo tayi ” Amma fah kwanan nan raini ya shiga tsakaninmu Dake besty nice ma yarinya koh ”
“Ke don’t tell me wannan ne sabuwar motar tamu Kan Uba yarinya kin samu waje ”
Naima ta juya ta sake kallon motar tace ” haba Kai amarya congratulations wallahi am happy for you Allah yasa mu a damshin ki ”
“Ameen nagode Anty Na’ii..” hajjo ta fada tana murmushi, Ummeey tace ” ni kizo ki bani labari Anya ba cikine Dake ba besty Kinga yadda kike shining ko wata fa bakiyi ba” “toh idan nayi cikin laifine ”
“A’a ba laifi bane Amma zanyi mamaki ne saboda kin nuna Baki sonsa ”
“Toh yanzu na fara son kayana ”
” Gaskiya ne amarsu wallahi kar ki tsaya wasa wannan mijin naki ba abin wasa bane ga kyau ga ilimi ga naira d whole CEO ” dariya sukayi harda tafawa Ummeey tace” CEO wife ba naji kwanan nan zai Bude bank koh ”
tabe baki Hajjo tayi tace ” Kinga ni bani da labari bansani ba wallahi ”
“Ahtoh dama yaushe zaki tsaya Wani zakewa ya raina Miki wayo karki yarda ki sake jiki dashi da wuri haka zaice saboda abin duniya ne ”
Naima tace ” tohhh…ni Kuma idan nice wallahi shige masa zanyi sosai na dauke hankalinsa na mamaye zuciyarsa sai ya manta da wancan na gidan ”
Hajjo dai batayi magana ba ta Bude material tana ta fara karatu , wata mata ce tazo da sallama da zauna kusa dasu Hajjo da naima ne suka amsa Ummeey kuwa ta kauda Kai gefe

Back to top button