Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 82

Sponsored Links

82
Hanyar barin gari sosai ya dauka Yana waiwayowa ahankali ahankali Yana kallan fuskan Bena din wadda itama Anne Bena din take kalla tana tabata tana Kiran sunanta ahankali kaman batason Wanda yake tareda su din yaji hakama jikinta gabaki Daya ma ya mutu zuciyarta ta narke Dan kuwa ko a halin rashin hankali Bena dinta daban take da komai bata son ko hadewan fuskanta da damuwa bare Kuka ko hali irin wannan.

Shi kuwa time din motar ya kalla yaga lokacinda ya kamata ya koma Yana sake qaratowa Dan haka yake sake buga motar sosai yana sake daukan hanya.

Tin suna tafiya Yana Dan waiwayowa cikin kulawa me tsanani da damuwa Yana kallan Bena harya Dena waiwayowa ya mayar da hankali sosai a tuqin.

Tafiyar awa uku cif sukai kafin Bena ta fara motsawa a hankali tana kokarin Bude idanuwanta ga kanta kaman zai fashe sbd nauyi da tsananin ciwo.

Sosai ta Bude idanuwanta suka Bude daidai ta tashi daga jikin Anne tana kallan Annen taga lafiyarta kalau ta mayar da kallanta cikin tsananin bugawan zuciya kirjinta har amsa sauti yakeyi sbd mummunan tsoro da firgicin Daya cika zuciyarta.

Tsoron leqa fuskarsa takeyi ta kalla sbd takasa yarda da Abinda idanuwanta ke ganar mata.

“Ya…yaa BILAL”…..Ta furta cikin yayyankewan kalamai da tsoron Dayake Neman juya kanta da cikinta Daya kulle waje Daya take ta sake zubewa jikin Anne ta sume a Karo na biyu sbd Tama rasa Gane inane take tsakanin duniya da lahira.

Bai tsayaba sake waiwayowa yayi ya kalleta Yana ci gaba da tuqi sbd komin dare Abuja yakeson Isa a ranar.

Zuwa wannan lokacin Anne hankalinta Neman sake juyewa yakeyi sbd ganin Bena na mutuwa tana tashi ahakan itama bacci ya dauketa abinka da Wanda ba cikakke.

Tafiyar awanni ce ta wuni Daya ta kaisu Abuja sai Daya gansa cikin garin Abuja dasu ya sauke numfashi tararda ajiyan zuciya me qarfin gaske kafin ya tinkari anguwar Daya sauka bayan dawowarsa Nigeria kwana uku dasuka wuce.

Wani gida ne me kyan gaske da tsari sosai irin ginin turawa me kyau sosai Amma ba mahaukacin girma sosai.

4 bedroom apartment ne Dayake cikin estate Amma still kowa da gate dinsa da harabar ajiye motacinsa kaman biyu haka.

Parking yayi ya sake sauke ajiyan zuciya tareda hamdala da adduar isowansa lafiya dasu Annen.

Bude kofan baya yayi daidai lokacin Anne ta farka itama Bena lokacin ta sake Bude idanuwanta ta kallesa idanuwanta na Neman sake shiga mummunan hali yayi saurin Kiran sunanta tareda matsawa baya Dan taga tsayinsa da kyau shi din ba fatalwa bane
Shine a Raye gabanta.

Tana ganin Hakan jikinta ya dauki mummunan rawa zuciyarta na kokarin Faso kirjinta idanuwanta na sake rinewa zuwa jajir ta fito motar rawar qafafunta na qaruwa bakinta cikeda tsoro da fargaba tareda tashin hankalin amsar tambayar Datake bakinta tana son furtawa tsoron amsar na Neman gigita kwakwalwanta.

Bude bakin tayi tana sake damqe hannuwanta dake kakkarwa tana kallansa ta furta

“Ina….su..mayyahhnmu?
Itama…tana..ray…..

Maganarta Bata gama fitowa ba aka Bude kofar qayataccen palon sumayyah ta fito da gudu wata ‘yar dattijuwa na bayanta da sauri tana Kiran sunanta,
Bata tsaya koina ba sai jikin Bilal din ta maqalqalesa tana dariyar farin cikin ganinsa kyakyawan fuskarta na Wani irin sheqin Hutu da zallan farin cikin asalin kyakyawar rayuwa.

Rungumeta yayi da kyau jikinsa Yana juyowa zai Kalli benazir da Anne sai yaga babu ko dayansu
Da sauri ya Maida kallansa qasa sai kawai yagansu a qasan duka sume.

Cikin sauri da tashin hankali ya Kalli dattijuwar data biyo sumayyah yace

“Momyn Abdul riqeta Jata ki mayar da ita ciki kada tashiga tsoro ko firgici zanji dasu idan sun samu kansu sai akawota ta gansu.”

Gyada Kai momyn Abdul tayi tareda kamo hannun sumayyah zata Jata sumayyahn ta maqalesa tana girgiza Kai alaman bazataje ba.

Shaf fuskarta yayi tareda hura mata iska a fuska ahankali take ta lumshe idanuwanta ta sake sa momyn Abdul ta kama ta sukai ciki batareda tama lura da Wainda ke gurinba tinda ba cikakkiyar lafiyar hankali ne da itaba.

Suna shigewa ya su kuya ya fara daukan Bena yakai ciki kafin ya dawo momyn Abdul ta dauko masa Anne wadda batada jiki ko Wani nauyi da zaa rasa iya daukanta.

Kai tsaye daya daga cikin dakunansu dake gidan suka nufa dasu suka Kwantar ita Bena Yana ajeta tana farkawa a gigice ta tashi zaune jikinta na sake daukan rawa da fizga ta sauko gadon tana kallansa hawayen na bushe mata Basa iya fitowa da rawan baki ta sake maimaita ambatan sunan sumayyah tana rarraba idanuwanta inda zata ganta.

Ganin halinda take ciki bayan an sanar dashi batada lafiya sosai Daman can ya sakashi saka momyn Abdul rirriqeta Yana kokarin Kwantar mata da hankali suyi magana a tsanaken Amma Sam ta fita hayyacinta Neman zaucewa tayi sbd ayau mummunan ranar baqin cikin rayuwarta,
Ta Gane miji Daya suke aure itada sister dinta tsawon shekaru da Basu ganta ba har sun cire Rai daga rayuwarta tini, a ayau din ma an rabota da Zuciya da ruhinta Amnah da dadynta sannan ta fito babu Abinda idanuwanta ke Gani sai matattun da suka Fi shekaru da rasuwa,.Tayaya hankalinta zai dauki wannan lamarin duka a lokaci Daya Rana daya.

Sosai jikinta ke jijjiga tana girgiza Kai tareda rintse idanuwanta gam tana qin budewa sbd kanta bazai dauka ba zafi qwaqwalwanta keyi, zaucewa takejin tana Neman Yi.

Ganin mummunan halin data shiga ya sakashi sakinta yabarwa momyn Abdul ita ta riqe da kyau yaje har bedroom dinsa inda ya wuce sumayyah a palonsa zaune tana kallan cartoon harya wuce ya fito Bata dago ta kallesaba sbd idan tana kallan cartoon babu Abinda take sake iya kalla sai an kashe tv din.

Yana fitowa dakin da Bena din take ya nufa da sauri cikin alluran Sumayyah ne da itama duk ranarda ta dawo hayyacinta haka take rikice musu da tambaya da son komawa gurin Bena da Annensu taka zata fara jijjiga tana Neman mace masa sai yayi mata allurar take kwantawa duk jikinta ya sake tayi bacci tana tashi shikenan zata tashi kalau Saidai lafiyarta dataqi dawowa daidai duk yawan Da yayi da ita na qasashe a tsawon shekarun ya kasa samun cikakkiyar lafiyarta ta dawo lafiyayyar sumayyahnta ta baya.

Yana Isa yayiwa Bena alluran wadda take bana cutatarwa bane take jikinta ya saki tayi sanyi ta silale a kan gadon a hankali take bacci ya dauketa.

Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke shi da momyn Abdul.

Mayar da kallansa yayi kan Anne da itama Sam ko matso jikinta bayayi yace momyn Abdul ta tsaftace ta zai kira likita yanzu yazo ya dubata ita.

Ficewa yayi daga dakin Yana sake sauke ajiyan zuciya sai alokacin ya samu Kansa ya wuce dakinsa Kai tsaye yanajin gajiya ma tana Dan taso masa sbd tsawon rayuwarsa a jirgi yake yawo Bai iya Tina wen last yayi tuqi me tsayi irin wannan din sbd ko yau din Daya Isa jirgi ya hau ya Isa can sai Kuma gashi ya juyo baiyi Shirin juyowa a yau din ba sbd abubuwa da dama dasuka kawosa.

Yana shigowa sumayyah dake Kallo har lokacin ya kalla ya qarasa gurinta tareda sauke ajiyan zuciya ahankali ya rankwafo yayi kissing forehead nata ahankali,.dagowa tayi tareda Dan juyowa ta kallesa ta saki murmushi me kyau Daya sake qarawa fuskarta kyau Shima murmushin ya sakar mata ya Dora bakinsa kan lips nata Suma yayi kissing ahankali kafin ya miqe ya juya ya nufi bedroom dinsa yanajin koyaushe son sumayyahnsa sabo yake koma a ransa fatansa dai Allah ya Bata lafiya suji Dadi kaman kowanne ma’aurata da suke rayuwa duk da ahakan ma son juna sukeyi sosai,shi kadai ne Wanda ta sani matsayin uwa,Uba,miji,Dan uwa,aboki hakama masoyi.

Sam Bata yarda Yana barinta sai daqyar da dubara yake fita kullum tinda suka samu kansu a rayuwar kwanciyar hankali ta iya su Biyun yake kulawa da ita sbd tinda ta farfado bayan tsawon lokacin data dauka a coma,
Ta jima sosai kusan shekara a coma kafin Allah yasa zata tashi ta tashi saidai ba acikin hankali isasheba haka suke rayuwar har yanzu dasuka dawo Nan din.

Yana shiga bedroom wanka ya fara tubewa yayi da ruwan dumi kafin ya fito ya goge jikinsa da towel jikinsa ya Dan sake sosai daga gajiya Dan haka Yana shiryawa cikin qananun designers kaya marasa nauyi ya fito palonsa yayi sallah tareda sumayyah wadda bataiba,
Magrib da ishai da baisamu Yi ba kan time yayi suna idarwa yayi adduoinsa sumayyah nayin duk Abinda yayi tana murmushi sai da suka gama ya janyota jikinsa tareda zare mata hijabin sallanta ahankali Yana kallan fuskarta itama shi take kalla tana murmushi tace

“Kaima kana Jin yunwa ko?
Ni dai inason zanci abinci da yawa.”

Ajiyan zuciya ya sauke tareda Jan hancinta ahankali Yana shafan fuskarta dake sake kashesa da sonta kullum yayi kissing gefen fuskarta ahankali cikin nutsuwa da sanyin sauti yace

“Zaki ci abinci?
Me kikeso momyn Abdul ta kawo Miki?
Kin Tina sunan Bena da Anne???

Shiru tayi Jin sunayen a cikin kunnuwanta sun Bata Wani sautin Daya Isa harga zuciyarta ta dago ta kallesa tana lafewa jikinsa batareda ta iya cewa komaiba.

Shima shiru yayi kafin ya dagota daga jikinsa suna miqewa tsaye ya kama hannunta cikin nasa suka fito main sitting room na gidan ya nufi dining da ita suka zauna.

Sai alokacin jikinta da yayi sanyi ya hau murna ganin Abinda takeso ne duka su snacks sai pasta wadda takewa cin shedana har ta Koya masa matiqar zasuci spaghetti to Rabin cin duk lalata ne.

Cin abincin suka hau Yi sai a lokacin Dr din Daya kira yace masa ya iso.

Momyn Abdul ce ta shigo dashi tai masa jagora har dakin da Anne take kwance kan gado bayan ta Dan gyarata.

Dubata sosai likitan yayi ya tabbatarda zuciyarta da komai nata Yana Aiki kawai dai shock be dayayi mata yawa ya sakata Suma.

Ruwa ya daura mata Dan taimakawa saurin farfadowanta kafin yabar maganin da zaa sakawa raunikan jikinta Daya Gani wainda na mummunan dukan da Ababa yayi mata ne na bankwana.

Bayan tafiyarsa daga Anne har Bena kowanne na daki daban daban gyara musu kwanciya momyn Abdul tayi ta rufe kowanne kafin ta jawo musu dakunan ta fito ta nufi nata sbd dare da yayi sosai.

Sumayyah da Bilal kuwa tini suka wuce dakinsa Wanda yake nasu su Biyun sai Daya taimaka mata gurin wanka Dan Daman shine kullum yake taimaka mata da wanka sbd Bata iya Yi da kanta jiqo jikinta takeyi har kanta da kayan jikinta shiyasa tinda sukai auren tsawon shekarun shine yake mata wanka da komai sai idan zai fita Aiki momyn Abdul ta kula da ita wadda itama Momyn Abdul din sun Dade sosai tareda ita sulaiman ne Mai napep dinsa yakai masa ita qanwar mahaifiyarsa ce Kuma mahaifiyar Nafisat Nanny din Amnah anintacciyar me aikin Bena.
##MAMUH#

 

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button