Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 37

Sponsored Links

*37*

 

 

 

Mamakine ya cika Dad yace “bangane ba wannan wacce irin tambaya ce?” Kit ta yanke wayar ya juya ya kalli mutanen dake gurin ga mamakinsa sai yaga Mainah Abdu yayi murmushi ya juya ya fice daga dakin gda ya wucce ya hadowa Samha kayanta kamar yanda fulani Amina da Dr Hasina suka fada masa.

 

Itakuwa Mamy tana kashe wayarta wayar fulani Hadiza ta kira tana dure duren ashariya tace “wannan ma ai iskanci ne yama zaayi ace Aisha ta haihu har yaya uku Ina wlh bazai taba yuwuwa ba dole saidai a sake lale yaya uku fa Hadiza” gaban fulani Hadiza ne yabada wani rass tace “kutmar ubancan yaya uku kuma duk na Abdu ne yayansu ne yaushe ma akayi auren da har zaace an haihu?” Katseta tayi da cewa “qyaleni Hadiza wannan bokan ya ruguzamin shirina gaba daya wai ba cewa yayi zai turo aljani ya tsinkar mata da jini ba kuma yasawa mijin mantau harsai jininta ya qare ta mutu yayanta su mutu kowa ma ya huta idan yaso saimu waiwayi waccan karfar matar uban nata da tasa ya aura to meyasa yayimin haka…” katseta fulani Hadiza tayi da cewa “tabbas an samu akasi wannan shegiyar yarinyar ta zame mana matsala kamar yanda kafirin mijin nan nata ya zamemin wlh na rasa ya zanyi da zuri’ar Amina musamman Abdu duk inda na biyu da sauri na shi saina tarar a guje ya kereni kawai mu zuba musu ido ni Ina ganin zaifi Lubabatu na fara tsoron yaron nan wlh har guba nabawa Abdu a Apple yaci amma bai mutu ba sai baqar wuya da yaci ya tashi…”

 

Katseta Mamy tayi tace “kinga dakata kada ki kashemin gwiwa nayi rantsuwa da nonon uwata kamar yanda na batar da Maryam uwar Aishatu na mantar da duniya labarinta iyayen da suka haifeta ma suka manta da ita na rabata da yarta Aishatu tun kafin a yanke mata cibiya na kadata duniya na dauki Aishatu na riqe naci kashinta naci fitsarinta nayi wahalar shekara ashirin da ita batare da ku kanku kunsan banice na haifeta ba sannan na juya qwaqwalwar ubanta ya manta da matar dana aura masa yayi auren sirri da ita ta haifa masa Aisha duk dan cikar burina guda daya tak a duniya to shakka babu wannan dalilin kadai ya isa yasa na shafe labarin Aishatu da yayanta harma da tsinannen la’anallahun yaron nan da yake amsa sunan mijinta idan zaki bini mu tafi tare ki biyoni Idan kuma gabanki ya fadi tun yanzu to ki kwanta ki huta amma ki sani ni Lubabatu takenane yar sa’a haba haba Hadiza nice fah maza nawa na kashe before nazokan uban Samha to wlh da Gidado da Aisha da tsinannun debabbun yaran nan guda uku da mijinta wato Abdu gaba dayansu rayuwata a tafin hanunsu take wannan ma kuskuren aikine kawai a yau zan diro Katsina kuma a yau saina aika yarannan lahira zan hada baki da likita a kashemin shegiyar yarinyar kowa ya huta dama qawata Barira tace min dan hakinnan dana Raina wato Samha idan nayi wasa saita tsonemin ido”

 

Kashe wayar tayi a fusace ta figi mayafinta ta watsa wayoyinta a jaka ta fice daga gdan a mugun guje har dakawa driven duka take tana cewa ya qara gudu so take cikin minti talatin taganta a Katsina
Allah ne kawai ya kaisu Katsina lfy tana zuwa kai tsaye palace hospital tasa driven ya wucce yana zuwa yayi parking ta fito a mota har tana gurgudewa ta shiga a guje tana shiga kafin takai shikuma Mainah Abdu yana fitowa karo sukayi kowanne yaja baya da sauri bude idonsa yayi tarr a kanta itama shi take kallo cikin wani matsanancin baqin ciki da taketa qoqarin dannewa tanason yin mgn murmushi yayi ya rigata cewa “kin iso kenan dama nasan zakizo kuma kedin nake jira saidai kuma kin makara My Aysha da yayana duka yanzunnan suka daga daga qasar nan zuwa wata qasar zaa kulamin dasu har zuwa lkcn da zasu samu kansu sannan mu dora wasan dake yanzu muka fara kada ki janye nima bazan janye ba nida dake zanga cikakken dan halak”

 

Wuccewa yayi ya barta a gurin a tsaye sororo cikin tsananin tsoro da mamaki saida yaje qarshen gurin sannan ya juyo yace “na barki lfy surukata” ji tayi kamar ya qara caka mata mashi a zuciyarta juyawa tayi a salube ta fice daga asibitin ta kira driven ta yazo ya sake daukanta daganan gdan sarautar ta nufa tana zuwa ta shiga sashinsu ta bude bangarenta ta shiga ta fada saman kujera a zafafe zuciyarta na tafasa ta jima a zaune ta rasa sanin abinyi miqewa tayi ta shige dakinta ta Kira wayar qawarta bugu biyu ta daga tace “akwai babbar matsala Barirah” nanta zayyane mata komai aikuwa ta qunduma uwar ashar tace “lallai kin sake yaron nan ya rainaki har kika bari yake iya caka miki mgn haka meyasa bazaki haukata shege ba yabi duniya Lubabatu matsawar kika qyale Mainah Abdu tare da Samha burinki bazai taba cikaba kina kallo fah ciwon cikin da mukasa aka tura mata da qarfin addu’ar sa ya tarwatsashi ya dawo kanki kikayi kamar zaki mutu saida mukaje boka ya karyashi duk wani sihiri da zamu tura mata indai ya fahimta kanki yake dawowa saboda haka yanzu shi yakama mu fara kawarwa kawar da wadannan yan tayin yayan da uwarsu yafi komai sauqi” ajiyar zuciya tayi tace “bantaba sanin kanki naja ba sai yau tabbas Abdu shine barazanata kuma matsalata shi yakamata na fara kautarwa daga doron qasa sai yayansa da matarsa subi bayansa amma tayaya zai tabu mutumin da aljanu ma tsoronsa sukeyi kinaji fah Boka Jegus daya kira aljaninsa zai turawa da tsinanniyar matar tasa a lalata cikin jikinta a gabanki aljanin yace bazai iyaba saboda sukansu aljanu suna tsoron hatsabibin mutum irin Abdu nifa inajin tsoron ko ya gane banice na haifi Samha ba saboda yanda yakemin baya nuna ya daukeni da muhimmanci ga wata shegiyar sara tashi ya gama cin mutunci na sannan yace min surukarsa”

 

Murmushi Barirah tayi tace “haba Lubabatu saikace bake ba Ina surukarki Aishatu mahaifiyar mijinki Gidado? Ina Umar Dandoki mahaifin mijinki? Ina mahaifiyar Samha Maryam matar da kika aurawa mijinki auren sirri yayi zaman aure da ita yayi Mata ciki har aka haifi Samha kika karbeta a matsayin yarki ta cikinki batare da kowa ya sani ba kuma kika batar da uwarta a duniya tsayin shekara ashirin babu labarinta? Lubabatu wadannan tunda suka shigo gonarki kin batar dasu kinga bayansu sarki Hassan baban Abdallah shine kadai ya gagareki to akanme zaki karaya akan wannan qaramin alhakin?”

 

Kamar tayiwa Mamy allura ta miqe tace “tabbas wannan haka yake dolene dukiyar Gidado da duk wasu kadarorinsa su zama mallakina dole ne na gyara dammara yaqi bazan taba sarayar da burina ba” saurin katseta tayi tace “amma fah saikin nutsu tun farko kikayi sakaci mijin yarki ya rainaki da kika nuna qiyayyarki a fili Lubabatu baacin naman maqiyi cikin sauqi saboda haka ki koyi boye qiyayya kuma ki koyi juriya ki dake ki shiga cikin hidimar haihuwar nan ayi dake kija Samha a jiki magungunan mata irin namu na Shuwa hada Mata a ciki zaki rinqa zuba mata asirin da aka baki tanasha yana ratsata ki mallaketa sosai ta yanda ko cewa kikayi ta kashe mijinta bazatayi miki musu ba in yaso ma hanya me sauqi saiki sanyata ta kasheshi da hanunta yanda babu me zarginki kinga riba biyu kenan dukiyar Mainah Abdu ta zama ta matarsa da yayansa to da daidai saiki aika yayan nasa sannan ki aika Gidado daganan sai itama Samha tabisu wannan itace way mafi sauqi da zamubi”

 

Wata uwar guda Mamy ta saki tace “Ahayyehhh nanaye saini Lubabatu duniya makwantar rikici kinyi taki kinyi ta yaro kuma nayi tame qaramin qarfin aminyar Barirah qulle qulle tabbas kin kawo shawara wannan abu anyi an gama rayuka shida zasu sheqa barzahu kuma duk bazasu wucce shekaran nan ba nagaji da zaman dukiyar nan a hanun Gidado dole ta dawo hanuna sannan shima wannan qaramin alhakin da aljanu ke tsoro to zamu gwabza dashi kamar yanda yace shege ka fasa ni Lubabatu na haifu cikin Jummala mai alagidigo kuma saina nuna masa shine shege ta hanyar aikashi barzahu amma wani hanzari ba gudu ba kinsan kamar yanda boka Jegus ya fada fah dole aiki bazai tafi ba sai an dorawa Gidado jinyar da bazai warke ba idan ba hakaba akwai matsala” dariya sosai Barirah tayi tace “kin damu da Gidado qaramin alhaki ki qyaleshi wannan shine yafi komai sauqi tunda yana kwana dake kema kinada matsala kinsani boka Jegus ya fada miki su irin Gdan sarautar nan basa tabuwa sosai saita hanyar matansu saboda Allah yayisu jarababbu ki bude masa kawai ya rinqa ci wannan qaurace masan da kikeyi kanki kikeyiwa illah shima wannan shegen yaron me qananun idanu kamar idon bura dole saidai mu fara binsa ta gindin matarsa don da ganin idanunsa akwai jaraba cikinsu”

 

 

Haka suka yini suna saqa da mugun zare hardai suka cimma matsaya yanzu damuwar Mamy itace ina su Samha suke wacce qasa aka kaita ita da yaranta tasan dai ko giyar wake tasha bazata taba iya tarar idanun hatsabibin mutum irin Mainah Abdu ta tambayeshi ba gashi tun safe take kiran wayar Dad yaqi dagawa saboda ba qaramin tashin hankali ta jefashi ba najin yanda hankalinta ya tashi dajin cewa yarsa ta haifa masa jikoki har uku ba dake layinsa International ne tunda suka sauka a qasar Egypt din yake ganin kiranta amma yaqi dagawa dashi da Dr Hasina ne sai fulani Amina da Mai martaba shikam danme da bin diddigin tsiya Mainah Abdu cewa yayi ya wakilta Dr Hasina amana akan yayansa da matarsa zaiyi wani aiki wanda yake na dole ne amma very soon zai shigo shima kulawa shugaban qasane yabawa Dad jirgi sukayi tashin gaggawa zuwa qasar Misran suka sauka a wani babban asibiti me suna Raudhatul Haqq kulawar da ake bawa Samha da yan ukunta ta musamman ce, kwananta biyu a asibitin ta fara motsawa amma bata bude idonta ba yaran kuma har yanzu suna cikin Inquivetoor anaci gaba da kula dasu saidai a fito dasu a basu abincin da magunguna a gyarasu a mayar dasu su fulani Amina sunga abu Abdu kiran Dad yace masa shifa kafa kada a rinqa jagwalgwala masa yaransa shima yananan zuwa a kwana na hudu ya diro qasar da magrib ya jima yana kallonta kafin ya tashi ya koma gurin yaransa mamakin girman da suka qara a cikin kwanaki hudun yakeyi sosai sai wutsil² sukeyi haka yasa aka fito masa dasu ya rinqa daukansu yanayi musu addu’a yana tofa musu yana hawaye tare dayi musu huduba Muhammad Ahmad da Al’ameen………….

 

 

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/19, 12:05 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Check Also
Close
Back to top button