Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 25

Sponsored Links

*25*

 

Kamota yayi ya rabata da jikin Dad yaa qoqarin hadata da jikinta ta turje tare da cewa “ka sakeni Abdul ka sakeni na fada maka banasonka na tsaneka macuci fasiqi azzalumi Allah ya is…” Rufe mata baki yayi ya durqushe a gabanta yana kallonta cikin tsananin damuwa yace “duk abinda zaki fada akaina na cancanta babu abinda zaki fadamin da zaikai girman kalmomin Dana fada miki a baya Samha bakida wata kalma da zaki fadamin da zata goge tabon da nayiwa rayuwarki amma Ina neman alfarmar ki daina ciwa bakya sona nasani bazaki taba daina sonaba har numfashinki na qarshe….” Qarya kake makiri munafuki qaryane kace yata bazata daina sonka ba tama daina Wlh indai nice na haifi Samha to qarya takw ta rayu dakai” cewar Mamy dake shigowa tana zuwa ta finciko hanun Samha ta dage ta sharara mata mari tace.

 

“Dama wannan dan iskan fitsararren tujararren yaron shine Abdul din da kike mgn akai to kuwa ba so ba ko mutuwa kikeyi kina dawowa bazaki taba zama dashi ba saidai idan bana numfashi…” “Eh zakuwa ki mutu Lubabatu tabbas zaki mutu saboda a yanzu baa anjima ba zaki bawa Mainah Abdu matarsa saboda haka ga hanyanan ki zaba ko aurenki ko auren yarki” da sauri Mamy ta dago tare da sakin hanun Samha tace “akan auren Aishatu da tambadadden yaronnan da ya daga hanunsa ya mareni tun baisan kansaba kake tunanin hanke igiyoyin aurena dakai Gidado to bari kaji bari kaji ba igiyar aure ba idan kasheni zakayi bazan fasa fada ba na tsani zuri’ar Amina da Hassan dinka Sa’eed kuma bazan taba barin yata daya tilo a duniya ta rayu da tsinanne yaronnan ba”

 

Tana fadin haka ta qara fincikar hanun Samha da har yanzu take kuka kuka biyu takeyi na tsana da baqin cikin aurenta da Abdul da kuma na rikicin daya sarqe tsakanin iyayenta akan aurenta to wai wannan wacce irin matsala ce da tasa Mamynta take qin dangin mijinta haka meye a boye wanda ya raba kan zuri’ar tasu a baya tabbas Dad dinta idan yana bata labarin asalinsa yakance Hassan dinsa amma baitaba cemata shi dan sarauta bane to meye ma matsayin wannan azzalumin Abdul din a gurinta suna nufin shine Mainah Abdu data dade tanajin lbrnsa a gurin Dad dinta” dagakai tayi ta kalli Mamy da take janta kafin ta ida sauke idonta akan Mamy taji Abdu ya sanya hanunsa ya ruqota yace.

 

“Banso kika kasance suruka a gareni ba Hajiya Lubabatu banso kece mahaifiyar Samha ba amma babu yanda zanyi bazan taba canzawa tuwo suna ba kin haifi matata kuma qanwata da abaya ta soni ta qaunaceni nima kuma nake sonta sona gsky” wani murmushi yayi yace “kamar yanda baffana ya fada miki tabbas zaki mutu akan aurena da Aysha Sa’ad Dandoki domin ba hadinki bane hadi….”

 

Wani saukakken mari yaji a kuncinsa daya sashi saurin cije lebansa ya dago yaga Mamy ce take wata irin tsuma akansa yayi murmushi yace “kinci arziqin matata da Babana amma da baki qara mari ba a duniya” sake finciko Samha yayi daidai lkcn da Mai martaba ya shigo parlourn saboda tuka tukar da akaje aka fada masa ta qarke a cikin gdan sarautar yana zuwa ya wucce inda Abdu yake ya sake janye Samha daga jikinsa yace “meye yake faruwa ne inacan waliccin daurin auren babanku Gidado a sabuwar Unguwa aka sanar dani kananan kanawa surukarka rashin kunya anya kuwa Mainah Abdu ka dauko hanyar da zaka zauna lfy” kallonsa yayi yayi qasa da kansa cikin girmamawa yace “Allah yaja kwana ya qara maka lfy…” daga masa hanu yayi yace “kaje waje yan kilisa suna jiran amarya da ango” ficewa yayi daga dakin ya juyowa yayi ya kalli Mamy yayi mata murmushi tare da daga mata hanu yace “ina gaisuwa surukata” yayi ficewarsa binsa Samha tayi da kallo tabbas duk yanda Samha take tunanin rashin mutuncin Abdul ya wucce haka akwai rikici a gabanta ta tsani duk mutumin dazai kawo mawa iyayenta raini matsalarta da iyayenta tatace bazai taba yuwuwa mijinta ya raina uwarta ba balle wannan mutumin da takejin tsanarsa a cikin jininta.
“Lubabatu yau laifi biyu mukayi miki Na daura auren danki Abdullah da yata Aishatu batare dana nemi izininki ba wannan ya faru ne saboda wasu bayanannun dalilai tun daren jiya Mainah Abdu ya dawo ya bayyana mana Aishatu itace “yarinyar da yake nema itace yakeso da aure amma bamu bashi goyon baya ba so da dare kuma waliyyin Mus’ab ya kirani yake fadamin dansu Mus’ab ya fasa auren Samha saboda dalilansu wanda ba kowane ya janyo ba sai Abdu saboda haka na yanke shawarar mayar da auren kansa alhmdllh an daura yau Aishatu zatayi kwanan turaka wanda wannan kwana shine cikar darajar duk wata ya me tarbiyya kuma shine yancinta, wata irin murdawa cikin Samha yayi ta zame jikinta da sauri daga na Mai martaba ta nufi dakin bangaren Yasmin ta fada toilet ta fara gudawa saboda tashin hankali.

 

Daqyar ta fito ta fada gadon ta rushe da kuka tana kiran “ innanillahi wa Innah ilaihirraji’un Allahummah ajjirni fih musibati wa’akalifni khairin minha” dama wannan dalilin yasa Abdul yaqi yarda da aurenta tun farko saboda yanajin tsoron wannan tonon sililin ashe da gaske har yanzu ana wannan jahilar al’adar yanzu irin wannan baqar wahalar da tasha lkcn da yayi Mata fyade irinta zata kumasha sake murdawa cikinta yayi ta sake tashi ta shiga bandaki taci gaba da tsuga gudawarta fitowarta kenan fulani Amina surukarta ta shigo ta tarar da ita a zaune ta hade kai da gwiwa sai risgar kuka tsugunawa tayi ta dago kanta tace “nasan me kikeyiwa kuka Aisha Abdu ya fadamin komai daya faru tsakaninku kiyi hqr nasara tana tare dake ki saki jikinki a wannan daren sai kin kankaro qimarki Aisha”…….

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/14, 8:17 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

Back to top button